Sashe 11
Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita kuwa bahijja tana can Kaduna itada Faruk sun kama hotel suna hutawarsu domin Faruk dan gatane sosai babansa babban mutum ne mai tarin arziki shiyasa yake yin abinda ya gadama, tunda sukaje hotel dinnan babu abinda suke yi sai shaye shayen kwayoyi da syrup kwanansu hudu kenan yau daga shi har ita duk sun kashe wayoyinsu, washe gari suka koma bauchi saida suka biya restaurant suka ci abinci sannan suka wuce school zai mayar da ita, awurin da aka tanada domin ajiye motoci yayi parking gaba daya motar tin tac ce baka ganin na ciki,
"Beb sai zuwa gobe ko zanzo muje wani casu na friend dina....."
Murmushi tayi ta dauki red din gyalenta ta dora akanta wanda yake atsefe ta tufkeshi dan hadiyar yawu faruk yayi yana kallon jikinta kasa kasa ita kanta na aduke tana lalubo wayarta zata kunna sam bata kula da irin kallon da yake yimata ba, bakar t shirt ce ajikinta mai gajeren hannu da jan wando pencil wanda ya kamata takalmin kafarta shima jane high hill,
"Babu damuwa guy sai kashigo..."
Daga haka tabude kofar motar tafita tana gyara rigar jikinta, Yaya sagir na zaune karkashin bishiya yana jiran karasowar basira kamar amafarki yaga bahijja tafito daga cikin motar da yaga tsayuwarta da jimawa atsakanin jerin rukunin motocin dake ajiye awurin, tun daga nesa yamike yake binta da kallo daga sama har kasa yana mai sake murza idonsa sosai dan ya tabbatar cewar ita dince yake gani ko kuma idanuwanshi ke yimasa gizo yana fada masa karya?
Kamar yadda yake kallonta kamar bai taba ganinta ba sai yau haka itama ta tsinkayoshi daga nesa, dagaske yaya sagir take gani ko kuwa mafarki takeyi?
Wani irin kadawa yan hancin cikinta sukayi kamar zata saki fitsari haka takeji dan tsananin gigita da razani.......
*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*
*_Ummi Shatu_*
[1/21, 5:08 AM] Nawarty
: 11***Har tagama shirya amrah bata bar mamakin abinda badiyya tayi ba to menene ma'anar hakan?
Wannan tambayar take ta yiwa kanta daga karshe tamike ta fita kai tsaye kitchen tashiga domin shirya breakfast tunda ita wacce tasaba shirya musu yau tayi kaura tabar gidan, saida tagama yan soye soyenta sannan ta fito tashiga dakin abbansu muhibba amma ga mamakinta baya cikin dakin, har toilet taduba amma baya ciki daga karshe tafita har compound din gidan amma babu shi babu alamunsa kuma motarshi ma bata gidan wanda hakan ya tabbatar mata da cewa yafita to ko aiki gareshi a office haka shiyasa yayi wannan uban sammakon?
Ganin bata da amsar wannan tambayar yasata komawa ciki domin gyara gidanta, bayan tagama shirya yara sun tafi makaranta tayi bakuwa matar abokin abdurrahman wadda itama suke dan kawance da ita sakamakon mazajensu abokanai ne, munubiya sunanta yar asalin garin katsina da murnarta da komai ta tarbi munubiya suna gaisawa munubiya tafara shafa mata labarin da yakawo ta,
"Maman muhibba basai ga kabir da neman aureba...
Wai har yakai angani ana so....ni kuwa na bude masa fefen rashin mutunci dan dole yayi collapse..."
"Ai ni ban san meyake damun mazajenmu ba wallahi...
Basu da wata magana saita kara aure idan kayi musu magana suce wai taimako zasuyi idan aikin lada suke so ai akwai hanyoyi dayawa na samun lada bawai dole saita hanyar aure ba...."
"Ai ban yarda na amince ba har saida nayi iya iyawata naga na hana wannan auren...
Akan me nikuwa zan yarda akawo min jangwam?
Kishiya ai bala'i ce...
Tab wallahi bada ni ba"
"Kin yimin daidai wallahi....
Sai mutum yayi magana ace wani wai kishiya dole ce to wallahi ba dole bace su yanmatan dazawaran wani shegen yahanasu su samu mijinsu su kadai su aura?
Ko dole sai mijin wata zasu aura...
Ai ni bana tolerating wannan nonsense din"
"Ai ni kasa hakuri nayi har saida nakirata nayi mata tass nace ta rabu da mijina wai wani nan wai mijinta ne ya mutu yabarta da yara biyu..
To ni na kasheshi"
"Gara da kika yimata haka ai nima lokacin da abban su musaddiq yana neman aure sai da naci mutuncin yarinyar nan sosai infada miki....
Kaca kaca nayi mata"
"Banga laifinki ba wallahi..."
Ahaka hirar tasu ta kare a ire iren wadannan maganganun har wurin la'asar suna tare da munubiya sannan ta tafi, haka taci gaba da zuba idon abdurrahman amma shiru bai dawo ba dama tasan yanayin aikinsu basa tashi sai 6 wani lokacin kuma bama ya dawowa gida sai 8 amma yau kamar lamarin yafi na kullum dan har tayi bacci bayan tagaji da jiransa bai dawo ba kuma washe gari yafice duku duku kamar yadda yayi jiya nan abin yafara tsaya mata arai gashi idan ta kirashi awaya baya dauka ranar ma har tayi bacci bai dawoba amma washe gari tayi nasarar tarar dashi lokacin yafito daga wanka yana shirin tafiya office amma yana ganinta yahade rai yadaure fuska abinda yayi mutukar bata mamaki domin a iya saninta babu abinda yashiga tsakaninsu na sabani,
Zama tayi gefensa tana kallonshi yana kokarin saka safa akafarshi,
"Abban muhibba lafiya kuwa?"
"Me kika gani fa?"
"A'a babu komai kawai dai gani nayi kwana biyu baka samun dawowa gida da wuri sannan kuma da wuwwuri kake fita..."
"Yanayin aikinane ya canja" yafada fuskarshi adaure daga haka kuma bai kara cewa komai ba yakaras shiryawa ya dauki jakarshi yafita sosai abin yabata mamaki to wannan Fushun da yaketa yi na menene?
Ganin tana batawa kanta lokaci abanza kawai yasata yin watsi da tunanin, falo takoma tana tunanin badiyya wato yarinyar nanfa tun ranar da ta tafi taketa kiranta amma taki dauka har yau dinnan ko me tayi mata har haka oho.
Gaba daya takasa gane kan abdurrahman kuma idan ta tambayeshi ko laifi tayi masa sai yace a'a amma haka kawai yaki zaman gidan, ranar lahadi da yamma yashigo gidan tana kitchen tana dafa tuwon dare yara kuma suna islamiyya yauma kamar kullum fuskarshi babu annuri,
"Shamsiyya..." Yakirata,fitowa tayi ta sameshi zaune kan kujera,
"Kibar girkin nan da kikeyi kitafi gidanku na sakeki saki daya...."
A razane ta kalleshi hankalinta amutukar tashe cikin rawar baki tace,
"Abdurrahman....
Ka..sa..ke..ni fa kace...
Anya kuwa lafiyarka kalau?
Laifin me nayi maka?
Muyi ya da yaranmu?"
"Lafiya lau nake....
Karki kara koda mintuna 10 acikin gidannan ki tattara kayanki kibar min gidana, yara kuma bance ki tafi da ko guda daya ba saboda inada inda za arike min su...."
Bai jira tadawo daga sabuwar duniyar da ta tafiba mai cikeda mamaki da al'ajabi yamike yahau sama yana taka step kamar wanda kwai yafashewa aciki,Da saurinta tabi bayanshi amma kafin taje har yashiga daki ya turo kofa, buga kofar tashiga yi da dukkan karfinta amma yayi mata biris kamar ba yaji,
"Abban amrah kabude kaji....
Ka bude kasanar dani laifin da nayi maka"
Shiru yayi mata kuma da alamar bashida niyyar bude kofar wannan dalilinne yasa ta juya ta dawo kasa ta nufi dakinta tana kuka wannan ko shakka babu aikin sihirine, duk yanda akayi tsohuwar budurwarsa wacce ada zai aura yafasa bai aureta ba itace tayi kutun kutun tashiga tafita tayi tsafinta zata rabasu,
Haka zuciyarta taketa raya mata, cikin hawaye tagama zuba duk abinda zata bukata da na amrah yar karamar yarta tajanyo akwatin tafito sai lokacin taji kauri a kitchen cikin sauri taje ta kakkashe komai tafito tana goye da amrah yarta abaya, da kuka tafita daga gidan ta tsaya ta tare napep tahau tana hawaye tana fada masa inda zai kaita.
Ayaune amarya husnah zata tare shiyasa tun safe yan uwanta na nan kano sukazo gidan domin sake tsaftace sashen amarya sannan kuma sune zasu taryi amarya,
Abangaren uwar gida bilkisu itama ba abarta abaya ba dan tunda garin Allah yawaye take kaiwa da kawowa saida ta hadawa fahad breakfast takai masa daki sannan tafara tashinsa daga baccin da yake tayi mai cikeda gajiya da kasala sosai,
"Baby...
Baby tashi kayi wanka ga breakfast kaci"
Dan idonshi yabude guda daya mai cikeda alamun bacci sannan yamayar ya rufe yana sake jan bargo, rike bargon tayi tana cewa,
"To ga dangin amaryarka can sunzo suna jiranka garama ka tashi"
Shiru yayi yabude idonshi daya amma kuma bai tashi dinba,
"Baby wallahi baccin bai isheni ba...."
"To ya za ayi haka zaka tashi kawai, anjima sai kasake yi"
Tashi zaune yayi yana cuno baki sai mutsuttsuka ido yaketa faman yi,
"Bae wai katashi mana...
Nidai ga breakfast dinka nan idan kashirya...
Bari inhada maka ruwa"
Daga haka tawuce toilet tana shiga yabita, rungumeta taji yayi tabaya yana sakin ajiyar zuciya, da taimakonta yayi wankan yafito ta tayashi yashirya cikin sky blue din yadi marar nauyi dan har farar singiletin da yasaka ta dan bayyana kadan ta cikin rigar,
Tare suka karya sannan suka fito tare, hajiya iyallo yafara zuwa yagaisar sunata halin nasu na tsokanar juna sannan ya dauki Mimi yafita, part din amarya yanufa ita dai bilkisu bata bishi ba takoma ciki taci gaba da aikace aikacenta, bai wani jimaba sai gashi yadawo da Mimi dan fita yakeson yi dakyar Mimi ta yarda taje wurin bilkisu sai kuka take yi lokacin da yana bata ita, kumatunta yashafa yana fadin,
"Haba mai kamada Darling....
Sorry daina kuka zan taho miki da ice cream"
Harararsa bilkisu tayi jin abinda yafada,
"Mai kama dakai dai...
Kai ai duk yaranka kamarku daya"
"A'a baby wannan dai dake take dan kama, kallifa idonta"
Goya Mimi tayi abayanta batare da zani ba tana cemasa,
"Wannan large eyes din ai kowa yasan maisu...
Ni bahaka idanuwana sukeba"
Dariya yayi yajuya zai fita,
"Kibari zamu hade a bed anjima"
"Sai dai ku hade da amarya, amma bada ni ba nima yau Allah yahutar dani"
Da dariya yafita bai sake cewa komai ba, ita kuma tanufi dakinta dan ta dauko zani ta goya mimi.