← Book details Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 26

Sashe 20

Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shi da wannan matakin da take shirin dauka akansa ai gara da tun farko hanashi auren tayi,yasan da biyu tafadi haka dan kawai ta hanashi kwanciyar hankaline tunda duk da cewa yayi sabuwar amarya ai kowacce mace daban take da yar uwarta,
Yana ji husnah sai faman zuba godiya takeyi tanata murna ita alallai wacce aka bawa kyautar miji har na tsawon wata biyu,tab ina ai wallahi hakan bazata taba faruwa ba inbanda shirmensu a ina suka taba jin anyi haka,
"To idan angama shikenan ni zan shiga ciki lokacin dora girki ma yakusa.... ango miko min Mimi muje ciki"
Wata lafiyayyar harara ya watsa mata sannan yamike yana rike da Mimi ahannunsa batare da yamika mata itaba yakalli husnah,
"Asma'u jeki part dinki ina zuwa bari naje dakina akwai abinda zan duba..."
Da to ta amsa masa tajuya tafita tana yiwa bilkisu sallama,tun kafin husnah tafita bilkisu tanufi hanyar da zata sadata da bedrooms dinta,saida yaga fitar husnah sannan yabi bayan Bilkisu yana faman yin kwafa tare da jan guntun tsaki bila adadin.....
*Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*
*_Ummi Shatu_*
[1/27, 3:40 PM] Nawarty
: *Yar uwa littafin kumallon mata labarine da ba ataba yin makamancinsa ba a duniyar rubutun hausa dan haka kidaure ki mallakeshi ki karanta domin sharbar romon sakonnin dake cikinsa,littafine da yadace ace kowacce mace ta karanta shi matar aure,budurwa ko bazawara, naira 300 ne idan kina bukatar siyanshi sai ki tuntubi wannan number +447894142004 ko kuma wannan 08169334980.*
17***Tana shiga cikin bedroom dinta ko zama bata kai gayiba sai gashi yashigo,ajiye mimi yayi wacce yake dauke da ita,
Juyowa bilkisu tayi ta kalleshi sakamakon karar rufe kofa da taji,
"Baby wai meye haka kike shirin aikatawa?

Wannan wanne irin shirmeni kike kokarin yi?

A ina kika taba jin anyi irin wannan shirmen?"
Tunda yafara magana kawai kallonsa takeyi har saida taji yayi shiru sai faman huci yakeyi alamar bacin rai yana rikeda da dukka kafadunta guda biyu,
"Shirme?

Wanna irin shirme kuma?"
"Ohh tambayata ma kikeyi?

Baby gaskiya idan kikayi haka bakiyi aiki da tunani ba sam....wacce matar kika taba jin ta sallama mijinta dan kawai yakara aure?"
"Idan babu matar da ta taba haka sai afara akaina....menene aciki?

Ai kai godiya ma yakamata kayi,nagane kun jima bakwa tare da juna sannan abukace kuke kuma amatse da junanku shiyasa nabaku watanni kaga sai ku mori junanku sosai amma ai kwana uku yayi muku kadan...musamman ma ita da take yarinya nikuwa ai kaga na kwana biyu abunma yafara fice min arai.....kuje kawai Allah ya kaimu watanni biyu kamar yaune"
Jin abinda tafada yasake kular dashi barinma da yaga tanata wani murmushin da yakasa gane ma'anarshi,
"Ba wani fice miki arai da yayi....ai kinfi husnah bukatata ahalin yanzu,ke ai acikin jarababbun mata kina sahun farko...."
"To yanzu dai nace bana bukata kaje kaji da amaryarka ni abarni inhuta,hidimar yarana ma ta isheni"
"Wallahi baki isaba,idan ke kin barmata ni nikuma ban bariba... wannan wacce irin bakar mugunta ce?

Tun wuri kifada mata dawasa kikeyi tunda dama ke kika fada tun farko tom....."
Daga haka yajuya zai fita ransa adan bace karo sukaci da mimi wacce ke bayansa atsaye,cikin sauri ya dagata ya dora kan gado yafice yana hararar Bilkisu,
"Zaki wani ce kin bamu wata biyu to me kike nufi da hakan?

So kike Allah ya kamani da hakkinki ko me......"
Garam taji yarufe kofar bayan yafita yana ta mita,zama tayi gefen gadon tana lallaba mimi ko wai zata samu tayi bacci amma taki dole daga karshe sai goyata tayi saboda girkin rana take son dorawa,
Kitchen tashiga ta fara shirya abubuwan da yadace ta girka, lemon rice da miyar kayan lambu ta dora sannan ta dauko carrot domin hada juice,sai farfesun kaji,
Tana cikin kitchen tajiyo sallamar husnah da baki, yan uwanta ne dake nan kano sukazo kamar yadda aka saba sannan kuma wadanda zasu koma kaduna suma zasuyi mata sallama,da fara'a Bilkisu ta taresu suka gaisa sannan suka tafi,har part din husnah ta rakasu sai lokacin taga yanda aka shirya mata bangaren nata, komawa nata bangaren tayi taci gaba da girkinta tana dab da kammalawa yashigo yana rikeda ledoji a hannunsa,
Zuwa tayi ta karbi kayan hannun nashi tana kallon fuskarsa yayinda shi Kuma yake kokarin ciro wayarshi daga aljihun gaban rigarshi saboda neman agajin da ta fara yi,
"Hello ya Abba sakona yashigo kenan?"
Bata san me yaya Abba yace ba tajishi ya danyi dariya kadan sannan yace,
"Ai ni ba aminin gwauro bane biyu gareni...shikenan karka damu anjima sai nakawo maka"
Daga haka yakatse wayar yabita cikin kitchen din ta bayanta ya tsaya yana kokarin karbar mimi daga bayanta wacce tuni ta jima da yin bacci,
"Ji yadda kika langabarwa da yarinya kai sai wuyanta yayi ciwo....saukota inkaita inkwantar da ita"
Kunce goyon tayi batare da ta tankaba saboda tasan neman hanyar da zaiyi mata fada yakeyi tunda awuya yake da ita,
Ta can yawuce part din husnah bayan ya kwantar da mimi adakin bilkisu,kwance yasameta tana bacci sakamakon gajiyar dake tattare da ita ga tarin bacci dake idonta,bai tasheta ba yabi gefenta shima ya kwanta domin baccin yake ji shima sosai.

Bilkisu kuwa tana gama girke girkenta ta wuce bedroom ta sheka wanka sannan ta zauna ta dan yi kwalliya sannan ta saka maroon din atamfa mai adon flower ajiki,dan kwali ta daura ta feshe jikinta da turare sannan taturawa Fahad da text massage kamar haka,
_Ranka yadade lunch yazama ready,ko nan za akawo muku?

Tunda ango kake._
Jin shigowar text massage din yasashi mika hannu ya dauko wayar yana rikeda husnah a kirjinshi ganin abinda bilkisu tace yasashi yin murmushi sannan ya mayar mata da reply kamar haka,
_Duk da ni angone ai dole nazo naga kyakkyawar fuska baby na duk da dai tana yimin rowar kayana amma wallahi kishirya karbata jibi..._
Kallon husnah yayi yace tatashi ta kintsa zasuje suci abinci bilkisu tace ta gama, tashi tayi idonta cikeda bacci tanufi toilet,
Bilkisu na falo tana zaune ta dora daya akan daya tana kallon tashar zee world suka shigo,ba Fahad ba ita kanta husnah saida bilkisu ta burgeta woww irin wannan kishiyar akeso wacce take jan ajinta yanda ya kamata yanzu gashi taci adonta sai zuba kamshi take sannan fuskarta awashe taboye kishinta acikin ranta,murmushi tayi ta mike tana cewa,
"Barkanku da fitowa amarya da ango....

Bismillah mu karasa kan table"
Binta sukayi abaya kowannensu yana kare mata kallo musamman ma fahad wanda kamar yaune yafara ganinta.

A farfajiyar club din suke zaune itada shi gaba daya wurin ya kaure da warin hayakin wiwi da na sigari,basu damu da kusancin dake tsakaninsu ba domin amanne suke da juna shi yana aikin shakar wata farar hoda ita kuma tana yin game awayarta,
"Guy yakamata inkoma hostel fa haka saboda nafada maka ranar Tuesday inada exam......"
"Babu matsala baby....yanzu abinda zai faru shine bari nakarasa wannan hawa network din sai mu wuce kawai...."
Cigaba yayi da shakar hodar ita kuma tana yin game dinta lokacin misalin karfe 12 saura na dare,kamar daga sama taji dirar mutane nan wasu suka zabura da niyyar guduwa amma kafin sukai ga hakan jami'an hisbah duk sun yimusu kofar rago sun cafkesu,har wadanda ke cikin club dinma suna cin karensu babu babbaka duk ankamosu anfito dasu kai tsaye office dinsu suka wuce dasu nan suka turasu cikin cell maza nasu daban haka suma matan nasu daban,duk hankalinta yatashi kasancewar wannan shine karo nafarko data tsinci kanta acikin cell,
"Nashiga uku ni bahijja gashi ranar Tuesday inada exam......innalillahi" tafada tana dora hannunta aka,gashi duk ankwace wayoyinsu an ajiye,kasa bacci tayi sakamakon cizon sauro da kukansa ga duhu,ahaka suka wayi gari nan akace kowa yabada number din iyayensa za akirasu,
Harga Allah ita kam bata son yaya sagir yasan da wannan al'amari amma yazata yi yazama dolenta tabada number shi kamar yadda suka bukata dan sunce idan mutum zai shekara anan bazasu sakeshi ba dole har sai wani nasa yazo yayi belinsa,
Aranar aka kira ya sagir aka fada masa shi kuwa faruk tuni har Dad dinsa ya aiko anfitar dashi bayan anja masa kunne,
Wurin lokacin sallar azahar Yaya sagir yazo,bata dai san yanda sukayi ba taga anzo anfitar da ita sai lokacin taji kunyar shigar dake jikinta wacce yaya sagir yahanata tunba yauba,baice mata komai ba yafita tana biye dashi bayan anbata wayoyinta da komai nata da suka karba.
Chapter 20 · 0% Book details