Sashe 19
Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wallahi bazai yuyuba"
Zuhuriyya ce tashigo cikin dakin dan ganin meke faruwa saboda jiyo kukan amrah da sukayi wanda ya cika gidan,yashe zuhuriyya taganta akasa tana yin wani gigitaccen kuka yayinda itama shamsiyya ke nata kukan tana rikeda waya ta dora hannu daya aka,
"Wai anty shamsiyya meyake faruwa?
Rasuwa akayi?" Zuhuriyya ta bukata,
"Zuhuriyya kinji abinda abban musaddiq yace?
Nashiga uku wallahi sai na illata badiyya....meyasa zata munafurceni?
Wai harni abdurrahman zai cewa yana son cikin dake jikin badiyya...
Sannan wai ita zai aura idan ta haihu"
"Kawai fada fa yake anty amma taya hakan zai faru"
Jiyo kukan amrah wanda yaki tsagaitawa yasanya su Inna zuwa dan ganin abinda ke faruwa dan har lokacin yarinyar bata bar kukaba duk da tana hannun zuhuriyya tana faman jijjigata, zuhuriyya ce ta rattabo musu abinda ke faruwa kasancewar ita shamsiyya har lokacin kukanta yaki tsayawa,sakare dukkaninsu sukayi banda mahaifiyarsu wacce jin abinda zuhuriyya tafada yasata barin wurin takoma daki,
Shamsiyya kamar wata zautacciya tazama sai sumbatu take yi tana kiran sai ta balla badiyya,duk abinda akeyi badiyya na daki tanaji itama sai hawayen take fitarwa haba shiyasa ashe taga dazu yaturo mata da text message yana cemata Wai ta kwantar da hankalinta insha Allah shi zai zama gatanta sannan zai share mata hawayen da suke gudana a idanuwanta ahalin yanzu,
Wani kukan tasake fashewa dashi tana jin rayuwar duniya nafita daga ranta saboda wannan bala'in da take ciki ahalin yanzu gani take kamar duk duniya babu wanda yakaita shiga tsaka mai wuya,taya ma abdurrahman zaice wai zai aureta?
Tayaya zata iya zaman aure dashi?
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un,
Tsabar tashin hankali tana daga zaunen da take jiri takeji yana daukarta,daren ranar bata samu bacciba,
Garin Allah na wayewa tafito zata shiga bandaki da buta ahannunta haka shamsiyya tafito ta shaketa tana kuka tana cewa,
"Wallahi baki Isa ki aurar min mijiba...ko mutuwa nayi balle ina raye, gara inkasheki kowa yahuta inyaso nima akasheni..."
Dakyar su mardiyya suka banbare badiyya daga hannunta,daki abasiyya ta mayar da ita wato dakin gwaggo amarya tana dafe da kirjinta suna shiga ta yanke jiki tafadi jini na fita daga jikinta cikin tsoro da fargaba abasiyya ta kwalla kara babu shiri kowa yanufo dakin ganin abinda ke faruwa yasa Inna sabuwa da gwaggo amarya fara neman agaji dan ahanzarta kaita asibiti dan jinine ke zuba bana wasaba.
Dakyar suka samu suka kaita asibiti mafi kusa nan aka karbeta aka bata gado,duk wasu yan bukatu da ake nema kama tun daga kan kudin magani da jini wanda za akara mata basuda shi saboda duk cikinsu babu wanda yakeda naira dari biyar tashi ta kansa,gashi baba yana wurin sana'arsa har lokacin ma shi baida masaniyar abinda yake faruwa,
Su shamsiyya na gida itada mahaifiyarsu da zuhuriyya da abasiyya dama da iya mardiyya kadai aka tafi asibitin,wayar badiyya ce keta faman kururuwa daga cikin dakin gwaggo amarya tun dazu wannan shine kusan karo na biyar da wayar keta faman kururuwar neman agaji,
Zuhuriyya ce takatse dinkin hular da takeyi ta mike tashiga dakin gwaggo amarya dan ta dauko,bakuwar number ce dan haka tayi azamar dagawa muryar abdurrahman taji yana cewa,
"Badiyya lafiya kuwa inata faman kira amma shiru ba adauka ba....hello kina jina?"
Jin muryar abdurrahman yasata saurin fita daga cikin dakin tana amsa masa da,
"Ba ita bace ita suna asibiti bata da lafiya....rikicine keta faman barkewa tsakaninsu da anty shamsiyya...dan Allah yaya abdurrahman kayi wani abu akai"
Kafin yabata amsa shamsiyya tafito ta warce wayar cikin kaushin murya tafara magana,
"Munafuki annamimi macuci...me kuma yahadaka da wayarta?
Ko yanzunma laifinane?
To cikin shege dai na barar dashi sai kasake zuwa kayi mata wani"
Cikin kaushin murya shima taji yace,
"Shamsiyya ina mai gargadinki akaro na biyu akan cikin nan mutukar yazube sai nayi shari'a dake dan ayanzu babu abinda nakeso sama dashi...."
Bai bari ta sake magana ba yakatse wayar mintuna ishirin tsakani sai gashi agidan lokacin baba mahaifiyarsu tasa shamsiyya agaba sai fada take yimata akan abubuwan dake faruwa,bai shiga gidanba yatura yaro yayi masa sallama da mardiyya ko abasiyya, abasiyya ce tafito domin ita mardiyya tana bayi,ganinshi yasata dan fadada murmushinta bai jira dogon bayani ba kawai yadauketa amotarshi suka tafi asibitin da aka kwantar da badiyya,
Shine yabiya komai da ake bukata na magunguna da kuma jinin da za akara mata daga karshe dai likita yasanar dasu cewa cikin dake jikinta yafita,
Duk da cewa cikin ba na halak bane saida yaji ciwon rasashi amma ita badiyya dadin jin hakan taji koba komai tarabu da kwallon mangwaro tahuta da kuda, lokacin data farfado zuhuriyya ce kadai acikin dakin ga kayan ciye ciye nan Kala Kala wanda abdurrahman yakawo wasu sabbin hawayen take sake zubarwa zuhuriyya nabata hakuri ahaka har iyayen nasu suka shigo,
Tun a asibitin lokacin da ta fara samun lafiya abdurrahman yafara nuna mata bukatarsa shiyasa take daure fuska da zarar taganshi tunda kullum yana asibitin, aganinta ko giyar wake takesha mezai kaita auren mijin yayarta uwa daya uba daya alhalin kuma tana raye?
Kai ai koma mutuwa tayi bata jin zata iya auren mijinta,
Kwananta hudu a asibitin amma dai cikin hukuncin ubangi ba ayi mata wankin cikiba likita yace babu matsala dan harma ta dan warware kuma aranar ake son ma a sallameta dan harsu gwaggo amarya ma sun tafi yanzu daga ita sai mardiyya wacce itace ke bi mata,suna zaune kan gadon asibitin suna dan tattauna matsalar da tafi addabar gidansu ayanzu yashigo dauke da bakar leda a hannunsa na dama dayan hannun kuma wata blue din leda ce mai kyalkyali a rubuta kamore communication,daure fuska tamau badiyya tayi tana sake gyara zamanta yayinda ita kuma mardiyya cikin fara'a da sakin fuska tasoma gaidashi cikin sakin fuskar shima ya amsa mata sannan yaja farar kujerar roba wadda ke ajiye gaban gadon ya zauna yana kallon badiyya wacce ta tattaro girar sama da k'asa duk tahada ta daure tamau,
"Sannu yajikin?" Shiru tayi kamar bata jiba sai da ta dan ja lokaci sannan ta amsa cikin daurewar fuska,
"Dasauki..."
Ledar hannunsa yamika ya ajiye kusa da ita sannan cikin sanyin murya yace,
"Ga wannan..wayace na siyo miki sannan dan Allah inaso kibani koda mintuna biyune muyi magana..."
Sunkuyar da kanta tayi batare da tace komai ba hakan yabawa mardiyya damar tashi tafice daga cikin dakin,
"Badiyya kamar yadda na sanar dake abaya ayanzu banida matar da nake burin aura wacce ta wuceki....kiyi hakuri kibani dama domin nine na cancanci zama mijinki tunda nasan abunda yafaru....abunda yafaru wallahi k'addara ce tunda ba ason raina yafaru ba kema ba ason ranki yafaru ba sannan dukkanmu ba halinmu bane....yayarki ce ta zalunceni har nakai ga aikata haka dan Allah ki amince kibani dama..."
Cikin damuwa da bacin rai ta kalleshi,
"Allah ya sawwake in aureka wallahi"
"Badiyya....kalleni...kalli idona nace..."
Dagowa tayi ta kalleshi na tsawon 5 seconds sannan tajanye idonta,
"Kikace bazaki aureni ba?
Saboda me?"
Maimakon tabashi amsa sai kawai yaga ta fashe da kuka nan taki cemasa komai sai kuka da taketa yi har yagaji yafita cikeda damuwa ahaka mardiyya tashigo ta sameta tana wannan kukan mai cin rai ita abu dayane yanzu ke sakata kuka zamanta a asibitin nan ya yi sanadiyyar da zazzafar kaunar abdurrahman ta shigeta batare da ta shiryaba tabbas wannan kaddarar biye take dasu tunda gashi tana jin abdurrahman acikin zuciyarta kamar jinin jikinta,yanzu menene mafita agareta?.
Zama dukkansu sukayi kan 3 sitter husnah na katarin Fahad wanda hakan yaso baiwa bilkisu dariya amma ta maze tana mikawa mimi hannu alamar tazo ta dauketa amma taki tasake makale fahad,
"Alhamdulillah.... husnah... bilkisu yau dai gaku kun sake haduwa amatsayin matana akaro na biyu....
Ina fata dukkaninku zakuyi hakuri ku hada kanku dan mugudu tare mu tsira tare....zaman lafiyarku shine zai zamemin jagora wurin yin adalci atsakaninku dan Allah kuzama masu hakuri acikin zamanmu sannan ku gujewa yan bani na iya wadanda ke yada maganganu na rikici tsakanin mutane.....ke husnah kece karama dan haka ina umartarki da kizama mai biyayya agareta, bilkisu kekuma ki daure ki rike girmanki dan Allah.... husnah kanwa take agareki kekuma husnah ki dauki bilkisu amatsayin yayarki.....insha Allah bayan nagama kwanaki uku adakin husnah zaku fara rabon kwana kamar yadda shari'a ta tanadar amma sai abinda muka shawarta yanzu atsakaninmu tukunna.... sannan maganar hada girki ko rabawa sai yanda kuka zaba tunda kune masu yi.......
Bilkisu me zakice?"
Murmushi bilkisu tayi saboda yadda husnah ke sake matsar fahad abin nata sakata dariya acikin zuciyarta,
"Ranka yadade ai kagama magana sai dai ni in danyi tambishi kadan.... maganar rabon kwana ai ba yanzuba saboda idan kagama kwanaki uku adakin amarya ni nakara muku watanni biyu ciss yadda zakuji dadin kulawa da junanku.....sai maganar girki shima karku damu insha Allah kullum zan rinka girki daku ai anzama daya kuma husnah kanwata ce kamar yadda kafada....ko ba hakaba husnah?"
Cikin fara'a da sakin fuska husnah ta daga kai tana cewa,
"Hakane anty...nagode madallah Allah yasaka da alkhairi amma girkin ai da kin raba sai nima inrinka yi bazai yuyu kita shan wahala ke kadai ba"
Murmushi bilkisu takuma yi sannan tace,
"Babu komai amarya ai bazai yuyu inbarki kishiga kitchen tun daga yanzu ba kedai kawai ki kula da oga...."
"Insha Allah anty...." Husnah tafada tana yin kasa da kanta,duk hidimar nan da sukeyi Fahad najinsu sai watsawa bilkisu harara yakeyi afakaice amma taki yarda su hada ido, gaskiya bilkisu kishinta dabanne wato ita kuma da wannan damar zatayi amfani ta hukuntashi akan yimata kishiyar da yayi?