← Book details Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 26

Sashe 4

Kumallon Mata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zan karasa shirya yara zasu tafi islamiyya..."
Bata jira cewarsu ba tawuce ciki inda su hanfa suke Mariya nata kici kicin shiryasu ita kuma mimi uwar kiriniya sai faman wasa take da kayan da ta baro daga saman mirror dinsu,duk abinda takeyi kawai dauriya take yi amma harga Allah jin zuciyarta take yi tana yimata wani irin zafi tamkar zata kama da wuta ta kone,
Da taimakon su Mariya suka karasa shirya su hanfa mariya da maryam suka kwashesu suka tafi domin driver na waje yana jiransu,canjawa mimi kayan jikinta tayi sannan ta dauketa suka fita har lokacin su fahad nazaune basu dawo daga duniyar mamakin da bilkisu takaisu ba, zama tayi tana ajiye mimi akasa tana nuna mata salim,
"Baby kinga Abba salim can fa, bazaki je ki gaidashi ba?, ce Abba salim ina wuni?......."
Dariya salim yayi yataso ya dauketa yana yimata wasa shi mamakin da yakeyi shine rayuwar nan yanzu batada wahala masifar gudu takeyi wai yau fahad ne keda yara har guda hudu, lallai duniya komai fararre ne kuma kararre,
"Gaskiya hajjaju kinyi mutukar burgeni...

Ban taba zaton haka daga garekiba, wallahi abinda nakawo shine ina fada miki zaki tsigaleni tas sannan ki koreni daga gidan nan kuma ki kirani da munafuki kamar yadda sauran mata keyi idan ansanar dasu mijinsu zaiyi musu kishiya...."
Dariya bilkisu tayi tana mikawa mimi hannu,
"Haba Abba salim dan jahilci ko dan me?

Ai anwuce wannan era din yanzu...

Allah yasa mudace dai kawai"
Maida kallonta tayi ga fahad wanda ke kallansu amma yakasa furta koda kalma daya,
"Ango kagama cin abincin ne?, anjima ina son fita fa kafin yara su dawo kuma motar naga kamar babu isasshen mai ko zaka samo mana?"
Kasa magana yayi sai daga kai kawai daga haka yamike shida salim, salim sai sakawa bilkisu albarka yake yana yimata fatan alkhairi saboda harga Allah ta burgeshi sosai tayi abinda yasan mata da yawa bazasu iyaba wato su boye kishinsu, suna tafiya tashiga daki ta zauna tana rikeda mimi sai lokacin taji hawayen da suka jima suna kwaranya acikin zuciyarta sun fara fitowa ta idanuwanta, duk da mimi kusan jaririya ce amma abinka da mahaifi ganin bilkisu na kuka itama sai tafara tsaga kuka, saida tasha kukanta ta gama sannan ta tashi ta goya mimi taje dakin fahad ta dauko maganin ciwon kai tasha, har lokacin idanuwanta jajur suke saboda kukan da tasha duk da tasaka kwalli tana fitowa daga cikin dakinsa sai gashi yashigo yana rikeda waya wanda bata san ko da wa sukeyi ba, ko kallonshi bata yiba ta raba ta gefenshi zata wuce saurin riko hannunta yayi tajuya tayi masa mugun kallo cikin sauri ya sakar mata hannu tawuce zuwa falo, baiyi kasa agwiwa ba yabi bayanta, wato sufa mata wani lokacin tamkar masu aljanu suke
yanzun nan zasuyi maka abun kirki idan anjima kuma suyi sabanin haka.

Tunda aka fara aikin gyaran part din amarya shamsiyya tasake shiga cikin bakin ciki da tashin hankali kwata kwata taki bari kowa yaji dadin zaman gidan domin hatta masu aikin akule take dasu tana jin kamar duk duniya bata da makiyan da suka fisu, shi kuwa mai gayya mai aiki wato abdurrahman ji take bata ko kaunar ganinsa, ta daina yin girki dashi, ta daina yimasa magana mai dadi sai ta cin fuska da bacin rai,gashi kullum cikin fada suke gaba daya yarasa ya zaiyi da ita dan hatta yaransu ma tadaina kulasu ta daina yimusu wanka ta daina komai da yadace ace uwa tana yiwa yayanta, duk tabi ta lalace shima tasashi yafara fita hayyacinsa, masifar safe daban ta rana daban ta dare kuma tafi ko yaushe domin bata barinsu su rintsa sai har idan bacci barawo ne yayi nasarar saceta.

Cikin nasara yau aka gama gyaran dayan part din da akeyi hakan yasa abdurrahman yace itama tafadi dukkan abinda take bukata na gyara sai azo ayi mata jin yafadi haka yasata fara surfa masifa da bakaken maganganu,
"Ehh dama mana....

Ai dole kafadi haka tunda za acuceni za auro min bakar daga...

Yarinyar da ta gama iskancewa tagama karade gari taki aure shine yanzu ni za akawo min ita to wallahi bazai yuyuba, ko kaffara bazanyi ba wallahi bazaka yi wannan fitinannen aurenba marar albarka....

Macuci kawai azzalumi wanda bai san alkhairiba butulu, inbanda butulci tun fa baka da komai nake tare dakai....

Amma yanzu dan tsabar rashin imani daga yin arzikinka shine zakace zaka karo min kishiya...

Dama namiji ba dan goyo bane, kuma duk matar da ta dauki namiji uba to tabbas zata mutu marainiya, ada baka da komai ni nazauna tare dakai amma dan tsabar rashin adalci shine yanzu kana yin kudi bazaka barni inzauna ni kadai ba...."
Duk maganganun nan da takeyi yana zaune gefen gado yana jinta kuma yana kallonta yayi tagumi ya tallafe kumatunsa.

Saida yaji tayi shiru ta dan tsahirta sannan ya yi magana cikin sanyin murya,
"Shamsiyya yakamata fa ki rinka duba wani abu guda daya, namiji mijin mace hudu ne dan mata hudu aka halicceshi, ko agidanku mata ukune karkashin inuwar mahaifinki...."
"A'a Abdul....

Karka kuskura kasako iyayena cikin wannan badakalar taka....

Karka yadda wallahi, dan gidanmu mata ukune shikenan wannan sai tazame maka hujjar kawo min wata cikin gidan nan?

To wallahi bazai taba yuyuwa ba ehe....

Inma banda sharrin d'a namiji wacce irin wahalarka ce ban shaba, tun kana fakirinka baka da ko taro nake tare dakai amma yanzu kace wannan sakayyar zaka yimin....

Namiji rigar kaya"
Sake gyara zamansa yayi ya kishingida yana kallonta, yarasa meyasa idanuwan mata ke rufewa akan kishi sam basa iya yiwa kalmar zan kara aure duba na tsanaki da nutsuwa sudai da zarar ka fada musu wannan Kalmar shikenan kazama abokin fada da gabarsu, bai sake tanka mataba saboda kawai yabarta taji da abinda ke damunta amma har acikin ranshi ya shirya mata tarin alkhairi wanda da ace ta kwantar da hankalinta da ko amaryar bazata fita gata ba,har ta karaci fadanta da banbaminta tabar dakin bai sake cewa uffanba.

Tana tsaye da mimi goye abayanta ta goya hannayenta abaya sai jijjiga Mimi takeyi yakarasa yana kallonta,
"Baby na sako miki mai amotar fa...."
Bata ko kalleshi ba taci gaba da lallaba mimi dake bayanta dan tasamu tayi bacci,
"Baby magana nakeyi fa...

Kince min zakije unguwa dazu"
"Nafasa" tafada cikin kunar rai daga haka bata sake cemasa komai ba duk kuwa da irin magiyar da yaketa yimata akan ta daure ta sanar dashi laifinsa.

Har yara suka dawo daga makaranta bai samu ta kulashiba sai harkar gabanta take tayi, kitchen ta shiga ta dora tuwo bayan ta kwantar da mimi a dakinta, tana tsaka da tuka tuwon su hanfa suka dawo, su maryam ne suka zo suka tayata karasa girkin bayan sun cire uniform dinsu, har lokacin fahad na gida yana dakinsa kwance acan su hanfa suka sameshi.

Bayan sallar ishah lokacin da zasuyi dinner ta dan saki fuskarta kamar yadda aka saba gudun kada yaran su fahimci wani abu especially ma su Mariya wadanda da wayonsu, sai da sukayi hira da yaran kamar yadda suka saba sannan sukaje tayi musu shirin bacci suka kwanta, ita kam dakinta tashiga tana shiga tarufe ruf da key, dakyar ta iya yin shirin bacci saboda tukukin da zuciyarta keyi sam yau bata b'ata lokaci wurin gyara jikinta ba saboda bazataje dakin fahad ba, wasu zafafan hawaye ke fita daga idonta wadanda tasan direct daga zuciyarta suke tahowa.

Fahad kam ganin shiru shiru bata dawoba yasashi sake shan jinin jikinsa domin kullum yasaba su zauna su sha hirarsu bayan yara sun kwanta, sai sun gama kallo sannan suke tashi suje su kwanta amma yau shiru, ko dakinsa baije ba yafara zuwa nata amma abun mamaki arufe, tsayawa yayi yaita knocking amma taki zuwa ta bude gashi wayarta akashe yakikkira bai sameta ba, saida yagaji da tsaiwa sannan yanufi dakinsa ransa duk babu dadi, to wannan salon fushin da bilkisu ta dauka tafara meye ma'anarsa, da damuwa aransa yayi wanka ya kwanta batare da yashafa ko da mai ba, turare kadai ya iya fesawa ya kwanta, juyi kawai yayita yi yana jin kunci na lullubeshi bai samu cikakken bacciba awannan dare sai bayan asubah sannan bacci mai nauyi ya daukeshi.

K'arfe 9 da wani abu yatashi brush kadai yayi yafita falo saboda jin gidan shiru ai kuwa babu kowa sai shi daya, yara sun tafi school ita kuma tafita aiki amma gida gashi nan neat ta gyara ko ina sannan ga breakfast dinshi nan ta shirya masa akan table, tsayawa yayi cak yarike waist dinshi yana nazarin sauyawar da bilkisu ke neman yi daga jiya zuwa yau.

Tsabar damuwa baiko buda abincin ba yakoma dakinshi yana shiga yadauki wayarshi ya kunna text din bilkisu ne yashigo yana budewa yaga ta rubuta,
_Salam, dafatan katashi lafiya, nafita aiki ga breakfast dinka nan idan katashi._
Tsaki yayi yasoma kiran layin nata amma baya tafiya, hakura yayi ya ajiye wayar yasoma tunanin abinyi cikin haka wayar tashi tasoma ruri yana dubawa yaga husnah ce bai dauka ba yasake jan wani guntun tsaki, itama husban bacin ran da bilkisu ta jaza masa ya shafeta.

Toilet yawuce duk ransa abace yasaba kowacce safiya bilkisu keyi masa komai ta shiryashi ta bashi abinci abaki yana yi yana zuba mata shagwaba, babu abinda yake yi da kansa indai tana gidan sai dai idan bata nan.

Koda yafito daga wanka bai wani bata lokaci ba kawai yazira kaya yabar gidan ko abincin da ta ajiye masa bai ciba.

Kamar yadda tasaba around 1 narana tadawo gida domin shirya lunch, batayi mamakin ganin gidan shiru ba domin su hanfa na makaranta shikuma uban gayyar tasan yana office, agurguje tayi wanka tashiga kitchen tayi girkinta ta kammala lokacin karfe uku na yamma, tana shirya table yashigo sanye da blue din shadda, batare da ta kalleshiba ta dauke kai tace,
"Sannu da zuwa..."
Daga haka bata kara cemasa komai ba tazo zata wuceshi, rikota yayi yana kallon fuskarta,
"Wai dan Allah laifin me nayi da ake yimin wannan azabtarwar?"
Batare da ta kalleshiba tace,
"Meyasa baka ci breakfast din da na ajiye maka ba?"
"Kin damu da inci ne?

Ba fushi kikeyi dani ba?"
"Fushi?
Chapter 4 · 0% Book details