← Book details Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 9 OF 31

BABI NA HAMSIN DA BIYAR DA NA HAMSIN DA SHIDA

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

***Wani irin shock ya ji a jikinsa kamar an watsa masa Ruwan sanyi,cikin wani irin yanayi ya zame hannunsa daga na Hidayan yana kawar da kan sa,murya a cunkushe yayi magana kamar me fad'a.


"Ke fa kin fiye rigima da yawa,ke naga alamar Hawaye ba ya miki wahalar zuba,Malama wuce ciki kiyi Sallah, idan kin idar ki kawo mana abinci nan"

Khaleel ya k'ura masa idanuwa yana kallon yadda ya ci mur yana wa Hidaya wani kallo,ita kam jikinta ne ya k'ara sanyi,a hankali ta juya ta wuce hawaye na sake kwararo mata kan fuskar ta,ita kad'ai ta san matakin da Zuciyar ta take ciki,Ya Hamza ya gama da ruhinta da gangan jikinta da gaske.


Hamza ya D'an saki k'aramin tsaki yana niyyar wucewa cikin d'akin,amma duk Khaleel ya babbake k'ofar,d'agowa yayi ya kalleshi suna duban juna,ganin wani kallo da Khaleel d'in ke masa sai gabansa ya fad'i,Amma cikin dakewa ya karkace baki yana duban sa a d'age yace.


"Idan ka gama kallon na wa bani Hanya na wuce"


Khaleel yayi farrrrr da ido yana murmushi,ya k'i matsa wa,sai da Hamza yasa hannunsa ya D'an ture kafad'ar sa sannan ya samu hanya ya wuce,Khaleel ya biyo bayan sa yana dira k'afafu kamar me shagwab'a yana kamo hannun Hamza,waiwayowa yayi ya dubeshi ,sannan ya dubi hannunsa da Khaleel d'in ya rik'e,da wata irin murya ya ce.


"Wai meye ne?"

Khaleel ya langab'e kai,sannan ya dubeshi yayi magana a hankali.


"Aboki ka daina yiwa Hidaya fad'a,sannan ka daina zare mata ido kana hararan ta,wannan k'wala k'walan idanun na ka sai su tsorata ta fa.."


Hamza ya masa wani kallo kafin ya saki k'aramin Numfashi ya ce.


"OK,a barta ta sangarce kenan?"

Khaleel yayi shiru yana girgiza kai, Hamza ya kawar da kai yana tab'e baki ya ce.

"Daga kai har ita shagwab'ar ku tayi yawa,ina jin dai idan kunyi Auren shagwab'ar za ku dinga dafawa kuna ci ko?"

Khaleel ya k'yalk'yale da dariya jin maganar Hamza,shi kam murmushi kawai yayi ya kalli agogo sannan ya sake duban Khaleel d'in ya ce.


"Ka tsayar da mu za mu makara a masallaci fa,ka shiga kayo alwala mu wuce"

Yana fad'in hakan ya wuce gun wardrobe d'in sa yana k'ok'arin sauya kayan jikinsa,shi kuma Khaleel ya wuce bathroom d'in Hamza domin d'aura alwala.


*******************


Basu wani jima sosai a masallaci ba suka dawo,Hamza ya haye gado ya kwanta rigingine idanuwan sa a lumshe, ga carbi a hannunsa irin na dannawan nan yana ta salati,shi kuma Khaleel kan carpet d'in ya kashingid'a yana danna wayar sa,suna a haka suka ji sallamar Hidaya,Khaleel ya wani zabura ya mik'e zaune da hanzari, k'urawa k'ofar shigowa ido yayi har ta shigo kanta a sunkuye,hannun ta d'auke da babban tire an jero abinci da abin sha akai,da sauri Khaleel ya mik'e ya nufe ta ya mik'a hannu ya karb'a sai faman sannu yake mata kamar wadda tayi wani aiki,ya ajiye a k'asa ya juya yana kallon ta tana k'ok'arin ficewa daga d'akin,da sauri ya rik'o gefen gyalen ta yayi magana a hankali.


"Ina zaki My love?ki tsaya mu ci abincin tare mana…"

D'an zaro idanu tayi tana satar kallon Hamza da idanuwan sa ke runtse,ta girgiza kai da fad'in.

"Na k'oshi Uncle Khaleel"


Ya langab'e kai yana bin k'aramin bakinta da kallo,yayi narai narai da fuska ya ce.

"Ni fa ba Uncle ba ne yanzu,My Husband za ki dinga kirana kinji"

Hannu ta kai ta rufe idanuwan ta jikinta na rawa,ta san Ya Hamza yana jin su,amma ko motsi bai yi ba balle ya tanka musu,ganin yadda ta k'unshe fuska sai abin ya bawa Khaleel dariya, wata irin dariya ya kama yi yana fad'in.


"Ni dai kunyarki tayi yawa My love,gaskiya ki rage ta Don kar ta dinga cutar da ni"

Ita gabad'aya kusancin da ke tsakanin su ne ya addabeta,duk ya kanainayeta k'amshin turaren sa ya dami hancinta,so take kawai ta bar d'akin amma khaleel ya hana ta,wai tilas ta zauna su ci abinci tare,sai da yaga tana shirin kuka Sannan ya k'yale ta yace ta tafi idan sun gama cin abincin zai sake kiranta.


Juyawa tayi da hanzari kamar ta kifa ta fice,wai k'iri k'iri yau Ya Hamza kallonta ma baya son yi,kuma yana ji ana tababa akan ta ci abinci amma ya share ko bud'e idanu ya k'i yi,mutumin da shine yake sakata a gaba kan ta ci abincin kamar zai mata d'ura,amma yau ya nuna bai damu da ta ci ba,duk ya wani sauya mata kamar ba Ya Hamzan ta mai tsananin son ta da kulawa da ita ba.

Hawaye ya kawo mata ziyara,a hankali ta kai Hannu ta share wasu na k'ok'arin sake zubo wa.

Sai da ta fita Sannan Hamza ya iya bud'e idanuwan sa yana jin kansa na sarawa,idanuwan sa sun yi jajawur sun sauya kala,Khaleel durk'ushe yana niyyar zuba musu abincin,ya d'ago kansa suka had'a ido da Hamza,gabansa ya D'an fad'i ganin yadda Hamzan duk ya wani yamutse,tasowa yayi ya zauna kusa da shi,Hamza ya mik'e zaune suna kallon juna,kamo hannunsa Khaleel yayi ya damk'e,cikin kulawa ya ce.


"An ya Aboki ka ji garau kuwa?duk wani iri nake ganinka ko dai ciwon cikin ne har yanzu?"

Hamza ya girgiza kai ya k'ak'aro murmushin dole,yayi magana a hankali muryar sa kamar ta mai jinya.


"Na ji sauk'i fa Khaleel, ka share kawai,sauko mu ci abincin"

Ya zame hannunsa ya mik'e tsaye ya wuce in da abincin yake,Khaleel ya bi shi da kallo yana girgiza kai, tabbas akwai abin da yake damun abokinsa,kuma in sha Allahu zai yi k'ok'arin binkitowa domin yayi masa maganin sa.

Ko da suna cin abincin gabad'aya ya lura Hamzan ba ci yake ba,wasa da cokalin kawai yake yana jujjuya shi,da sun had'a ido kuma sai yayi masa murmushi ya sunkuyar da kai.


****************


Hidaya kam kai tsaye bedroom d'in Umma ta shige,ta haye gado ta cusa kanta cikin pillow ta saki wani marayan kuka mai cin rai,anya za ta iya hak'ura da Ya Hamza kuwa?za ta iya hak'ura da soyayyar sa da ke cin Zuciyar ta?ya gama zagaye ko ina a jikinta har bata san yadda zata kwatanta ba,duk da shi ma Khaleel d'in ba k'in sa take ba,amma dai bata jin sa a ranta kwatankwacin yadda take jin Ya Hamzan ta..


Kuka sosai take yi har Umma ta shigo ta same ta a haka,tausayin Hidaya ya kama Umma,ta matsa ta zauna kusa da ita tana dafa bayan ta,Hidayan ta d'ago a tsorace tana kallon Umma,sai Umma ta runtse idanu saboda yadda taga fuskar Hidayan har ta fara kumbura saboda kuka,Hidaya ta fad'a kafad'ar Umma ta sake fashewa da kuka.

A hankali Umma ke shafa bayanta tana lallashinta,da gaya mata kalamai masu dad'i da hak'urk'urtar da Zuciyar ta, kamar yadda ta dinga janyowa Hamza ayoyi da hadisai akan hak'uri da k'addara da jarrabawa haka ta dinga janyo wa Hidayan,Umma bata gushe ba tana jin yadda hawayen Hidayan yake kwarara a k'irjinta,ta d'ago kan Hidayan ta share mata hawayen ta da tafukan hannun ta,Sannan tace mata.


"Kar kiji Haushin Hamza Fad'ima, kiyi masa uzuri kinji,Hamza ba zai tab'a iya hana Ibraheem komai ba,Ibraheem mutumin kirki ne Fad'ima,Kuma wallahi yayi wa Hamza halacci a rayuwa fiye da in da ba kya zato,ta kowane fanni Ibraheem yayi wa Hamza tazara da zarra,ya fishi asali da gata,ya fishi kud'i da d'aukaka,ya fishi kyau da ilimi,Fad'ima Abu d'aya Hamza zai gwadawa Khaleel, shine ilimin addini,Wanda shi ma Khaleel d'in ba baya ba,amma duk da hakan Khaleel ya zab'i Hamza cikin dubban mutane domin ya zama abokin sa,ya zama aminin sa,ya zama komai na sa,Fad'ima na rantse miki da Allah Khaleel GARKUWAR Hamza ne,kamar yadda Hamza ya zama GARKUWAR ki,kiyi hak'uri Fad'ima,ki mik'a lamuranki ga Allah k'i cire duk wata damuwa da ke ranki, ki yawaita addu'a, Allah zai zab'a miki abin da Ya fi alkairi a rayuwar ki"


Hidaya ta k'urawa Umma idanu,cikin fitar hayyaci ta kamo hannun Umman ta rik'e,da wata irin murya ta fara magana a hankali.

"Umma na kiyi min wata alfarma,don Allah ina so ki fad'a min asalin had'uwar Ya Hamza da Uncle Khaleel, ko domin na san dalilin da ya sa suke wa junansu wannan zazzafan so haka,Wanda d'ayan su zai iya sadaukar da duk wani Abu da yake so ga d'ayan,komai kuwa son da yake wa abin,don Allah Umma ki fitar da ni daga wannan duhun zuwa cikin haske"


Hidaya ta d'aga hannayen ta alamar rok'o,Umma tayi Murmushi ta d'aga kanta tana tuna baya,ta sauke kallon ta kan Hidaya ta fara magana kamar haka……!


Comments
share
vote
pls


*GARKUWA BIYU*


BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter 9 · 0% Book details