← Book details Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 6 OF 31

BABI NA ARBA'IN DA TARA DA NA HAMSIN

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

*Kuna son karanta littafin nan amma sharhi yana gagarar ku*🤗


***Ji yayi gabad'aya kunnuwan sa sun toshe,idanuwan sa sun makance,k'afafuwan sa kuwa tamkar an sage masa su,tashin hankali mara misaltuwa ya samu kansa ciki,ya tawo da tashin hankalin b'acewar Mummyn Hidaya a idanuwan sa,sai kuma ya zo ya tarar da wani tashin hankalin da yake Neman katse numfashin sa…


Tamkar Khaleel ya san da zuwan sa ya waiwaya ya dubeshi,da wani irin hanzari ya nufo shi fuskar sa cike da fara'a,yana zuwa ya bud'e Hannu ya rungume shi yana k'ank'ame shi,ya runtse idanuwan sa yana jin wani farinciki na d'awainiya da shi,burinsa ya cika,zai cigaba da zama da Hamza yana ganinsa yana jin dad'i…

Hamza kan k'ok'arin aro jarumta kawai yake,amma ya kasa,ji yake tamkar Zuciyar sa zata fad'o k'asa tsabar bugun da take,lamo yayi a kafad'ar Khaleel yana k'arewa Hidaya kallo tamkar ya sume,ita kanta jikinta har lokacin rawa yake tayi wani tsuru tsuru tana tsuma…

Yanayin yadda Khaleel yaji jikin Hamza ba k'wari sai ya d'ago shi daga jikin sa,cikin wani yana yi ya tsura masa idanu yace .

"Aboki ya na ganka haka…!?

Cikin daburcewa Hamza ya samo abin cewa.

" Ba na jin dad'i ne Khaleel, cikina naji yana ciwo,ga zazzab'i da ke son rufe ni yanzun nan"


Khaleel ya dafa kafad'ar sa cikin jimami yace.

"Sorry Aboki,bari nayi wa su Daddy magana suna ciki,mu fara zuwa hospital a duba ka kafin mu wuce gida ko…!?

Hamza yayi saurin girgiza kai yana rik'o hannun sa yace.

" Ah ah barshi kawai,akwai magani a gida idan na koma zan sha,tunda na riga na ganka ma inason mu wuce yanzu,saboda Umma tace min na dawo mata da Hidaya da wuri,kar mu kai dare…"

Sai Lokacin ma Khaleel ya juya ya kalli Hidaya da ke tsaye kanta a sunkuye,sai ya k'yalk'yale da dariya ya dawo da kallonsa zuwa ga Hamza yace.

"Aboki wannan K'anwar ta ka Y'ar k'auye ce gaskiya,magana d'aya duk ta rikita ta,wai fa cewa nayi ina sonta,ina son Auren ta,shine duk ta rikice haka…"

Hamza ya ji tamkar ya dab'a masa wuk'a,amma haka ya shanye ya had'iye,cikin matuk'ar basarwa yace….

"So kuma..!?Hidayan kake so Khaleel..!?

Khaleel ya gyad'a kai yana lumshe idanu cikin shauk'i yace..


" Eh Aboki,ina matuk'ar sonta da k'aunar ta,tun ranar da ka fara haska min fuskar ta a asibiti da muka yi video call,ban k'ara samun sukuni a rayuwa ta ba,k'aunar ta ta mamaye min ruhina Aboki, babu abin da ke haskawa a idanuwana idan ba K'anwar ka ba,kayi min alfarma Aboki,ka amince min ka bani K'anwar ka Hidaya na Aura,za ka bani ita Aboki….?


Da wani irin sauri Hidaya ta d'ago kai jin maganar Khaleel, ta k'urawa Hamza idanu tana son jin kalar amsar da zai bayar,shin zai amincewa Khaleel ne ko kuma zai bayyana na sa son da yake mata,domin ta riga ta hango sonta a idanuwan sa,bata san dai dalilinsa na k'in furtawa ba…


Hamza kam shiru yayi yana duban Khaleel, b'angare d'aya na Zuciyar sa na fad'a masa cewar"Hamza kar ka cuci kanka,ga damar ka ta samu,kayi amfani da ita wajen bayyanawa Khaleel cewar Hidaya taka ce,kai ne zaka Aure ta,kar ka bari wannan damar ta sub'uce maka,Hidaya da kai ta fi dacewa ba wani ba"yayin da d'aya b'arin ke ce masa"inah !tabbas Hamza ka makara,kayi nauyin baki har Khaleel ya riga ka furtawa,muddin kuma ka hana Khaleel Hidaya baka yi adalci ba,Khaleel yayi maka komai a rayuwa,kai mai iya hak'ura da farincikin ka ne domin ka sadaukar masa da shi,musamman da ya kasance mai lalura,idan ka hana shi Hidaya komai zai iya faruwa da shi,haka Allah ya k'addara,daman can Hidaya ba rabonka ba ce shiyasa kayi nauyin baki wajen furtawa har Khaleel ya riga ka…..


Ganin yadda Hamza yayi shiru ya k'i furta komai sai khaleel ya narke,ya marairaice fuska ya rik'e hannun Hamzan har k'walla ta soma taruwa a idanuwan sa,cikin wani yana yi ya juya ya kalli Hidaya da soyayyarta ta yi masa mugun kamu,sannan ya waiwaya ya zuba wa Hamza ido cikin sanyin murya ya fara magana.


"Don Allah Aboki kar kace min ah ah,kar kace min ba zaka bani Hidaya ba,ba rantse da Allah na yadda nake jin ta a zuciya ta zan iya mutuwa idan ban sameta ba,don Allah ka bani ita wallahi ina sonta….

Yayi shiru tare da zirarowar hawaye,cikin k'arfin hali Hamza ya d'aga Hannu ya goge masa hawayen,sannan yayi murmushi mai kama da yak'e yace.


" Khaleel…da gaske kana son Hidaya…!?

"Ina son ta ….!?Khaleel ya ambata yana lumshe idanu.

Hamza yaji rauni matuk'a a ruhin sa,amma duk da hakan ya daure yayi murmushi yace.


" Duk wani Abu da ya dangance ni mallakin ka ne Khaleel, ita kanta Hidayan tana yi min wani kallo ne na nine komai na ta,ma'ana nine uwa,uba,D'an uwa,dangi,da komai na ta,kaga kuwa ina da iko da ita kenan,kuma babu wani Abu da zan umarceta da shi ta k'i yi,haka ne ko ba haka bane….!?

Hamza Khaleel yake tambaya,amma a fakaice Hidaya ya cillawa tambayar,wadda ke gefensu tsaye cikin matuk'ar tsoro da razana,idanuwan ta na kan Ya Hamza tana girgiza masa kai hawaye taf a idanuwan ta,domin ta fuskanci abin da yake son yi,kuma shine Abu na k'arshe da zai yi Wanda za ta fitar da rai ga Auren sa,domin babu wani Abu da zai umarceta ta kasa yi masa,Hamza bai sani ba ne,amma tana ganin duk wasu Abubuwa da ya lissafo yanzu k'imar sa ta zarce hakan,Hamza shine komai,idan aka ce komai to komai d'in fa kenan……


Jijjiga kai Khaleel yayi da fad'in.

"Hakane Aboki…!

Hamza yayi murmushi mai ciwo ya kalli gefe ya fara magana.


" To idan kuwa hakane babu abin da zaka nema a guna ka rasa muddin mallakina ne,Khaleel da yawun bakina nake furta maka har zuwa zuciyata,cewar,na mallaka maka Hidaya ta zama matar Aure a gareka…..


Hidaya ta runtse idanu da mugun k'arfi,tana jin hajijiya na kwasar ta kamar ta kifa,shikenan Ya Hamza ya gama da su!ya cutar da zukatan su!ya saka musu tabo mara gogewa har abada!innalillahi wa inna ilaihir raji'un.

Shi kam Khaleel tsabar murna bai san lokacin da yayi tsalle ya fad'a k'irjin Hamza ya rungume shi ba,ji yake Hamza ya gama yi masa komai a duniya,kalaman godiya da yabo da jinjina kawai Khaleel ke zubawa Hamza,yayin da Hamzan ya kasa gane matakin da Zuciyar sa take ciki,kawai dai ya san zai iya hak'ura da komai domin Khaleel.

Zubawa Hidaya idanuwa yayi,wadda ke masa kallon da ya kasa gane yanayin sa,kafin tayi wani irin murmushi da bai tab'a ganin sa a fuskar ta ba,sannan ta girgiza kai ta juya ta bud'e murfin motar su ta shige tare da rufewa da k'arfi.

Hamza ya runtse idanuwan sa yana jin wani iri,sai dai aikin gama ya gama,a dai dai kuma lokacin da su Daddy suka iso gare su suna kallon su rungume da juna.


*******************


A matuk'ar kunyace Daddy ya iya gaisawa da Hamza,saboda matsananciyar kunyar da ta rufe shi bisa ga cin mutuncin da ya dinga yi masa shi da mahaifiyar sa,amma sai Hamza ya nuna ma kamar babu wani Abu da ya faru,har ya sake bawa daddy mamaki bisa ga furucin da yayi,saboda yadda daddyn ya dinga Neman afuwarsa da yafiyar sa da fad'in sharrin shaid'an ne da zuciya,da kuma abokai masu bashi shawara akan k'in talakawa,a lokacin ne Hamza da ke durk'ushe gaban daddy ya sunkuyar da kai ya fara magana.

"Ka daina bani hak'uri Daddy, ai kai d'in ubana ne,kuma duk wani Abu da uba zai yi wa D'an sa ba zai kasance da cutar wa ba,duk wasu Abubuwa da suka faru a baya sun wuce,ban tab'a kallonka da su ba,ni a mahaifi nake kallonka,musamman da ya kasance bani da wani uba da zan kalla naji dad'i,ban san mahaifina ba,ban tab'a ganinsa ba,na zo duniya ne a lokacin da shi kuma ya barta,don haka kai mahaifina ne Daddy, ni dai rok'ona a gareka ka barni da Khaleel, kar ka kuma rabani da shi,ina son Khaleel Daddy, kuma domin Allah nake sonsa ba domin abin hannunsa ba.. …

Wad'annan kalamai sun dad'a girgiza Zuciyar Daddy, har ma da Anty kubra da ke gefe tamkar tayi hawaye jin kalaman Hamza,Daddy ya sake tabbatar da cewa lallai Hamza ya cika D'an halak,domin duk irin tozarcin da yayi masa bai d'auki fushi da shi ba,har ma yana kallon sa a matsayin uba?kenan ya tura masa aniyarsa?irin su Hamza kad'an ne a duniya..

Khaleel kam wannan rana babu Wanda ya kai shi farinciki,babu wani guri a Zuciyar sa da yayi ragowa Wanda babu k'aunar Hamza a ciki,bai had'a komai da Hamza ba,amma tun ranar da suka fara ganin juna Allah ya jarrabesu da wata irin k'auna tamkar sun fito ciki d'aya ne.

Babu yadda su Daddy basu yi ba akan Hamza ya bi su gida ya huta ya ci abinci kafin ya koma Kaduna,saboda su basu ma san shi da Hidaya ya zo ba,a tak'aice ma dai basu san wacece Hidaya ba,amma ya kafe akan cewa Umma tana jiransa ne,kuma yana son komawa gida ya sha magani,ya dinga basu hak'uri,tilas suka hak'ura,nan Daddy yake cewa Hamza ya gaida Umma,kuma ya bata hak'uri kan abubuwan da suka faru kafin ya zo da kansa, daga nan Daddy da Anty kubra da yaran suka wuce wajen motar su suna jiran Khaleel ya kammala magana da Hamza ya zo su wuce gida.

Khaleel kam bai so rabuwa da Hamza a wannan lokacin ba,yana ta shagwab'a,sai da Hamza ya dinga bashi hak'uri kafin ya yarda,sai kuma Khaleel yace.

"Aboki da ka bari na sa driver'n Daddy ya tuk'a ku ya maida ku Kaduna,tunda baka jin dad'in jikin ka anya za ka iya tuk'i kuwa..!?

" Zan iya insha Allah Khaleel..! Cewar Hamza yana murmushi.

Khaleel ya jijjiga kai ba Dan ya so ba,suka tattaka suka k'arasa gaban motar Hamza,Khaleel da kansa ya bud'ewa Hamza murfin motar bayan sun rungume juna,Hamza ya shiga ya zauna k'irjinsa na ta dokawa,musamman da ya waiwaya ya kalli Hidaya da ke zaune a gefe ta k'udundune kanta kan cinyar ta,sai ya girgiza kai ya sauke ajiyar zuciya.

Shi kam Khaleel duk ya za ci kunya ke damun Hidaya,shiyasa ya zagaya b'amgaren ta ya lek'o kansa ta tagar motar yana tayi mata dariya da tsokanar ta akan in zata sake ta sake,domin shi d'in D'an soyayya ne,dole ta zage ta rage kunya ta koyi soyayya a nunawa juna k'auna,wannan kalamai da Khaleel ke yi ya sake saka Hidaya cikin wani mugun hali,balle kuma Hamza,Wanda ke ta murmushin yak'e Zuciyar sa na ci da wuta.

Da k'yar suka yi sallama,Khaleel na fad'in gobe zai zo Kaduna da wurwuri,duk da yadda Hamza ya so hanashi saboda ya zauna ya huta ko dan doguwar tafiyar da yayi amma ya k'i hanuwa,wai shi k'arewa ma tattarawa zai yi ya dawo Kaduna da zama,da k'yar dai Khaleel ya bar su suka tafi,kuma har lokacin Hidaya bata d'ago kanta ba duk wata magana da suke yi,a haka Hamza ya ja mota cikin sanyin jiki suka fice daga airport d'in,yayin da Khaleel ya bi su da kallo yana d'aga musu Hannu yana jin tamkar ya bi su…….


Sun yi nisa da tafiya akan hanyar su ta komawa Kaduna,da k'yar Hamza ke iya jan motar saboda yadda yake jin jikinsa tamkar ba na sa ba,tsananin tashin hankalin da ke tare dashi ba don Allah ya kiyaye ba zai iya zubar da su a hanya,kad'an kad'an yake juyawa yana duban Hidaya da ke k'udundune da kanta a cinyar ta sai gumi take had'awa duk da A C d'in da ke motar,ita kad'ai ta san halin da Zuciyar ta take ciki,daurewa kawai take,amma suna zuwa tsakiyar wani daji dauriyar ta ta k'are,ta kasa rik'e kukan ta,bata san lokacin da ta fashe da wani gigitaccen kuka na tashin hankali ba.…

Saura kad'an sitiyarin ya k'wace daga Hannun Hamza saboda wata muguwar tsorata da yayi,da sauri ya gangara gefen Hanya yayi parking,a gigice ya waiwaya yana duban Hidaya wadda ke gurshek'en kuka kamar me,tana jin ya tsaya da motar ta d'ago kanta,fuskarta kaca kaca da hawaye,da hanzari ta b'alle murfin motar ta fice da saurin ta tana kuka,kawai ji tayi ta fara tafiya har da D'an gudunta ba tare da ta san in da za ta ba.

A rud'e Hamza shi ma ya b'alle murfin bangaren sa ya fita daga motar,da hanzari ya taka ya bita yana k'wala mata kira,inah!Hidaya kuka kawai take tana tafiya da D'an gudunta babu waiwaye,Hamza bai san lokacin da ya taka da gudu ya bita ba cikin tsananin tashin hankali,da k'yar ya cimmata ya sha gaban ta,ta kauce tana k'ok'arin sake tserewa,ganin haka sai yayi abin da ya jima bai yi ba tunda ta soma girma,wato ya rik'o hannun ta cikin wani yanayi na rud'ewa da gigicewa,cikin wani irin nishi yake fad'in.

"Meye hakane Hidaya..?ina zaki ne wai..!?

Fizge hannun ta ta yi tana k'ok'arin juyawa cikin kuka,ya runtse idanun sa yana jin kamar ya fad'i,cikin dauriya ya sake damk'e hannun ta k'ak'am yace.

" kar ki bamu wahala Hidaya,jikina babu k'wari zan iya fad'uwa wallahi"

Sai lokacin ta iya kallon sa,idanuwan ta tamkar gauta Dan jan da suka yi,jikinsa ya kama rawa tsigar jikin sa na mik'ewa ganin kalar idanuwan ta,girgiza mata kai yayi,sai ta sake fashewa da kuka,baiyi aune ba kuma ya ji ta fad'a jikinsa tana goga kan ta a k'irjinsa ,tana gurshek'en kuka,Hamza yaji wani bala'in tausayin ta da tausayin kansa,da k'yar ya iya d'ago kanta ya girgiza mata kai,ya kai Hannu ya share mata hawayen ta,yana so yayi magana amma ya kasa,hannun ta ya ja kawai suka nufi gun motar su,har lokacin Hidaya na kuka mai sauti da shesshek'a.

Suna shiga motar ya kulle k'ofofin Dan ma kar ta sake yunk'urin fita,ya juya yana kallon ta duk idanuwan sa sun zurma saboda tashin hankali,kansa kamar ya fashe,da k'yar ya iya yin jarumtar magana.


"Don Allah kiyi hak'uri Hidaya…na yi miki katsalandan cikin rayuwar ki wajen bawa Khaleel ke ba tare da yardar ki ba,wallahi Hidaya Khaleel na da wani matsayi gareni da ba zai tab'a misaltuwa ba,duk wani Abu da na zama ta silar Khaleel ne,ya yi min komai a rayuwa,ba zai iya Neman wani Abu gareni na hanashi ba,nayi masa wannan alk'awarin ne saboda ina tunanin na isa da ke…..

A wani irin slow Hidaya ta d'ago ta zuba wa Hamza idanuwan ta,da sauri ya sunkuyar da kai,ba zai jure kallon idanunta masu cike da Abubuwa ba,cikin wata murya mai cike da rauni ta fara magana har lokacin tana hawaye.


" Ya Hamza…tabbas ka isa da ni,kuma ka isa ka sani aikata komai ko da kuwa zuciyata bata son hakan,matuk'ar dai abin bai sab'awa Allah da manzon sa ba,Ya Hamza ba wai ina kuka ne don ka mallakawa Uncle Khaleel ni ba,ina kuka ne saboda cutar da zuciyata da taka Zuciyar da ka yi,cuta mara warkewa har abada,a yau zan fad'a maka abin da ban tab'a fad'a maka ba,Ya Hamza ina sonka,ina k'aunarka,ina burin na zama matarka,na fara son ka tun ban san menene son ba,na rayu da k'aunarka a zuciya ta ta yadda babu wani namiji da nake gani a idanuwana idan ba kai ba,kamar yadda na san cewa kana sona kana k'aunata,amma ka kasa bayyana hakan a gareni a matsayin ka na d'a namiji,ta ya ya ni da nake mace zan iya ajiye kunya ta na bayyana maka hakan?tabbas mun yaudari zukatan mu Ya Hamza,ba mu yi wa junanmu adalci ba,ni na dad'e da gane cewa kana tsananin sona,amma ban sani ba ko kaima kana k'yamar Auren mace Irina ne,wadda take da matuk'ar rauni da cutar da maza ke gudun mata masu irin ta,mara asali wadda mahaifiyar ta ta gujeta tun daga yarinta……

Chak Hidaya ta tsaya da maganar ta,saboda wata muguwar tsawa da Hamza ya daka mata,wadda taso tsinka mata hanjin cikinta,ta runtse idanu da k'arfi ganin ya d'aga Hannu yana shirin kai mata mari a fuskar ta…..


Comment
Share
Vote
Pls

*GARKUWA BIYU*


BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter 6 · 0% Book details