← Book details Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 16 OF 31

BABI NA SITTIN DA TARA DA NA SABA'IN

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un ! innalillahi wa inna ilaihir raji'un ! innalillahi wa inna ilaihir raji'un !"

Abin da zuciyata take ta maimaita wa kenan,saboda bakina ba zai iya motsi ba ma falle wani furuci ya fito daga ciki tsabar gigicewa da rud'ewar tunani,ban tab'a cin karo da abin da ya tayar da hankalina ya dugunzuma min tunani irin wannan sak'o na mahaifiyata ba,kafin wani d'an lokaci tuni kammaninaa sun sauya,k'irjina na ci da wuta kamar ya babbake,hawaye kuwa tamkar an kunna famfo irin me zuba da gudun nan,hankali na tuni ya soma fita daga jikina,bani da wani buri illah cika burin da mahaifiyata ta umarceni a kansa,bayan hakan kuma fa?sai son ganinta da mararin rab'ar jikinta! domin ni ma d'in naji abin da mutanen duniya suke ji idan suna tare da iyayen su ! to amma tambayar ita ce !

Ina zan ganki mahaifiyata?
Yaushe idanuwan mu za su ga juna?
Yaushe Numfashina da na ki za su gauraya a muhalli d'aya?
Yaushe zan sake jin d'umin jikinki kamar yadda kowane d'a yake son jin d'umin jikin mahaifiyar sa?
Yaushe...?yaushe...?yaushe...? duk yaushe wad'annan abubuwan za su faru...?

Runtse idanuwana nayi cikin matuk'ar ciwon zuciya da sartun hawaye,Na rungume takardar a k'irjina ina kuka sosai ina nadamar bak'inta da na dinga gani,Allah ya sakawa Ya Hamza da alkairi ya biya masa buk'atunsa na alkairi,abinda zuciyata take nanatawa kenan,dalilin shine jigon da yake sarrafani wajen hanani aibata mahaifiyata,wadda a kullum yake fad'amin tafi kowa sona da k'aunata! ban tab'a yarda da hakan ko amincewa ba sai da na karanta rubutun da ya fito daga hannunta.

To wai shin a yanzu menene ya ragemin ne?Na tambayi kaina cikin kuka da Nadamar rayuwa.

Sai naji zuciyata na bani amsa da cewa.

"Cika umarnin Mahaifiyarki shine abu na farko da za ki yi,duk da hakan abu ne mai tsananin had'ari da wahala,kuma gashi lokaci ya k'ure miki,amma duk da hakan ki k'ok'arta ki aiwatar Hidaya,hakan zai sa ko da ba ta duniyar ta kasance mai alfahari da ke domin share mata kukan ta da kika yi"

A lokacin da k'arfin zuciya ya shigeni,alokacin ne kuma na jiyo muryar Mijina Uncle Khaleel yana k'wala min kira tun daga parlour,fad'i yake.

"Kina ina ne?fito kinyi babban bak'o,Daddy da kansa ya zo ya ganki kafin ma kije ki gaishe shi"

Hoton da ke hannuna na sake bi da kallo,kafin cikin hawayen na saki wani irin murmushi wanda ban tab'a yi ba ina girgiza kai,jin muryar Uncle khaleel na sake dumfaro bedroom d'in da sauri na had'a takardar da hoton na cusa su k'ark'ashin pillow,da hanzari kuma na wawuri hijab d'ina na zumbula na jawo shi ya rufemin rabin fuskata saboda bana so Uncle Khaleel ya fuskanci halin da nake ciki a yanzu.

Mik'ewa nayi zan nufi parlour'n,ina zuwa bakin k'ofa muka ci karo zai shigo ni kuma zan fita,da saurin sa ya mamayeni ya rungumeni tsaf a jikinsa,wani sanyin dad'i naji duk da zuciyar ta wa babu dad'i,kuka nake son yi amma na tabbatar idan nayi zan tada hankalinsa,kuma zai nemi jin ba'asi,wanda ko kusa ko alama a yanzu ban shirya sanarda shi komai ba,ajiyar zuciya ya dinga saki a jejjere yana k'ara rungumata,kafin a hankali ya fara magana cikin murya k'arama.

"Kinga wai fa daga zuwa kiran Daddy shine yace min na rakoshi ya ga y'arsa,tun da dai bai tab'a ganinki ba,nace ma ya bari na kawo masa ke amma yak'i yarda,har da ce min wai menene dan Uba ya gaida y'ar sa?ai durk'usawa wada ba gajiyawa bane"

Luf nayi a k'irjinsa ina jin dad'in kulawar da mahaifinsa ya bani,Allah sarki ni da Ya Hamza da muka rasa namu mahifan !hawaye ya tawo min nayi hanzarin mayar da shi.

A haka ya ja hannuna muka fice zuwa parlour'n kaina a k'asa.


A tsaye muka tarar da Daddyn yana jiran isowar mu,Uncle khaleel yayi magana cikin shagwab'a da murmushi hannayen sa rik'e da nawa hannun.


"Daddy ya ka tsaya baka zauna ba?

Cikin zaulaya Daddyn ya bashi amsa da cewa.

"Ina jira a bani umarnin zama ne"

Dariya Khaleel yayi yana jana har gaban Daddyn ya tsugunar da ni shi ma ya tsuguna,sannan ya d'aga kansa sama yana kallon Daddyn da ke tsaye yana duban mu fuskarsa kadaran kadahan,cikin muryar ladabi Uncle Khaleel ya ce.

"Ga d'iyarka na kawo maka Daddy,ka sanya mana albarka da ni da ita"

Daddy yayi murmushi ya nemi waje ya zauna kan kujerar da ke dab da shi,yayin da Uncle Khaleel ya janyo hijabina baya domin fuskata ta bayyana,cikin k'aramar murya mai cike da soyayya kuma yake fad'in.


"ke fa kunyarki tayi yawa,to dai a gaban Daddy kike wanda ya kasance mahaifi a garemu baki d'aya,ya kamata ki bud'e fuska ki dubeshi ya dubeki tunda yau ce rana ta farko da kuka had'u da juna tsawon lokaci"

Haka kawai na samu kaina da fad'uwar gaba ban san dalili ba,a hankali kuma na d'ago kaina da nufin kallon Daddy domin na gaishe shi,a lokacin ne shi ma Daddyn ya karkato da kallonsa zuwa gareni,karaf idanuwan mu suka sark'e da juna,bakina na bud'e da niyyar furta gaisuwa gareshi amma sai maganar ta gagara fitowa tsabar bugawar da kaina yayi tare da matsanancin tsoron da ya shigeni.

K'ura min idanuwa Daddyn yayi cikin wani irin kallo mai kama da na mamaki ko al'ajabi,yayin da jikina ya d'auki wani mugun rawa kar kar kar,wata irin mik'ewa nayi a razane har hijabin da ke jikina na niyyar tad'eni na fad'i,da sauri nayi baya na d'ago hannuna ina nuna Daddyn da hannuna jikina na mazari amma bakina ya kasa furta komai,Daddyn yana daga zaune yake kallona ya kasa fuskantar abin da nake nufi,yayin da Uncle Khaleel ya mik'e a tsorace yana kallona ganin yanayin da na shiga na mugun firgici a take,k'ok'arin takowa yake gareni cikin gigicewa yana ambatar .

"Hidaya lafiyarki kuwa?me ya faru ne?me ya gigita ki haka?

kafin ma ya k'araso na d'aga hannuna na dakatar da shi cikin wani irin nishi da numfarfashi,idanuwana a warwaje tamkar me shirin ta da iskokai,birki ya ci yana zuba min narkakkun idanuwan sa a tsorace,a yayin da na juya da gudu na nufi cikin bedroom d'in da muka fito dan k'ara tabbatar da zargina.


A rikice Uncle Khaleel ya juya yana kallon Daddy,wanda shi kansa Daddyn cikin tsananin mamaki yake,cikin wata wahalalliyar murya da tamkar arota yayi yayi wa Daddyn magana.

"Daddy wai me yake faruwa ne?kalli halin da yarinyar nan ta shiga,an ya kuwa lafiya lau take?

Daddy yayi shiru alamar nazari,kafin ya sauke ajiyar zuciya mai k'arfi ya dubi Kahleel da ke tsaye cikin d'imuwa ya ce da shi.

"Bi ta ka duba halin da take ciki"

Jijjiga kai Uncle Khaleel yayi cikin sanyin jiki,kafin yaja k'afafuwansa da suka yi masa nauyi zuwa in da na nufa.


Ni kam ina shiga babu in da na nufa sai bakin gado,a hanzarce na d'aga pillow na zaro takardar da na gama karantawa yanzu wadda ta fito daga hannun mahaifiyata,ba takardar nake son gani ba,hoton da ke tare da takardar shi nafi muradin sake kalla domin na tabbatar da zargin da zuciyata da idanuwa na suke min,k'urawa hoton ido nayi cikin fitar hayyaci,nan take k'wak'walwar kaina ta cigaba da haska min da tabbatar min da cewar tabbas abin da nake gani d'in gaskiya ne.

A haukace na cillar da hoton,na juya domin nufar palour'n k'irjina na ci da wuta,domin bana cikin hankalina,ji nake yi zan iya yin komai a lokacin.

Dab da bakin k'ofa na sake cin karo da Uncle Khaleel wanda ya biyo ni d'akin dan ganin abin da ke faruwa,gani na a haukace ya sa ya k'ara gigicewa ya rik'o ni gam yana shirin jefani k'irjin sa ya rungume ni,tamkar wata dutse haka nayi k'ik'am a gabansa nak'i bashi damar hakan,ya jefa idanuwansa cikin nawa idanuwan da suke d'auke da buhu buhu na tashin hankali,cikin wani irin yanayi ya soma girgiza kafad'una yana magana a rud'e kuma a gigice.


"Wai meye haka ne?me kike yi haka ne?me yake damun ki ne?Hidaya ki dawo cikin nutsuwarki ki fad'a min menene yake faruwa?za ki tarwatsa min kaina My love....please me.....

kafin ma ya k'arasa maganarsa na fizge jikina daga gareshi,cikin wani irin fushi kuma na sa hannaye na daki k'irjinsa ina tunkud'eshi gefe guda,Da sauri ya durk'ushe k'asa cikin tsananin azaba yana daf'e k'irjinsa tare da wani d'an ihu yana fad'in "ahhhhhh...subhanallah... !, saboda dai dai gefen zuciyar sa na daka,shi d'in kuma me rarraunar zuciya ne wadda take cike da ciwuka.

Ko kallon in da yake ban yi ba na wuce a haukace na zuwa palour'n,in da na tarar da Daddyn a tsaye cikin firgici saboda jiyo k'arar da Khaleel yayi.

Ban tab'a sanin cewar ina da k'arfi ba,ban tab'a sanin cewar ramammu irin mu masu sikila za su iya aikata abin da na aikata ba,sai dai na san cewar b'acin rai babu abin da baya sakawa,domin ban tsinci kaina a ko'ina ba sai gaban Daddy,wanda nake nufar sa jikina na rawa matuk'a da gaske,hankalina kam tuni ya gushe a sanda na ci burki a gabansa,na d'aga hannuna na sharara masa wani uban mari wanda sai da hular kansa ta fad'i a k'asa,gidan kansa sai da ya amsa tsabar k'arar marin,ban kuma tsaya nan ba sai ga hannaye na shak'e da kwalar rigar sa na matse shi ina girgiza shi.

Dai dai lokacin da Khaleel ya rarrafa ya fito daga bedroom d'in,akan idanuwan sa na waskawa mahaifinsa mari !akan idanuwan sa na ci kwalar mahaifinsa ! akan idanuwan sa ni matar auren sa nake girgiza mahaifinsa ! da me zai kwatanta wannan tashin hankalin da yake neman kai shi lahira? kafin ya dawo daga mutuwar ido biyu sai ya tsinto muryata cikin k'ara da tsananin tashin hankali ina fad'awa mahaifinsa munanan kalamai.

"Tunda uwa ta ta haifeni na fad'o duniya har zuwa yanzu da na girma ban tab'a cin karo da tsinannen mutum irin ka ba,gafalalle mara mutunci,mara tausayi mara kyawawan d'abi'u,mara haiba mara kamala,mara kirki mara kyawun zuciya,asararre wanda ya zo duniya a banza zai koma a wofi,Na rantse da girman Allah ko zan yi yawo babu komai a jikina sai naga bayanka ! yadda ka sa mutane da yawa kuka a duniya kaima sai ka koka kafin ka bar duniyar ! domin sai .....


Wani irin wurgi naji an yi dani gefe guda a lokacin da aka fizge hannuwana daga wuyan Daddy,wanda idanuwansa ke warwaje sunyi tulu tulu tsabar shak'ar da yaji,wani irin tari ya sark'afeshi,Uncle Khaleel ya juyo kaina a gigice yana nuna ni da hannunsa d'aya,hannu d'aya kuma yana rik'e da Daddy wanda ke maida numfashin wahala yana ta wani irin tari,da k'yar Khaleel ya iya fizgo maganar da yake son yi har ya samu ta fito.


" Wannan fa mahaifina ne Hidaya! shine fa uban da ya tsuguna ya haifeni ! kin sha k'waya ne da kike furta wad'annan munanan kalaman a kansa? me ya shiga kanki cikin k'ank'anin lokaci ya sauyaki daga halittar da na sanki?

A hanzarce na mik'e daga fad'uwar da nayi ina yiwa Daddyn wani kallo na muguwar tsana mara iyaka,kafin a zafafe na juya na kalli Uncle Khaleel da yake rik'e da Daddyn,cikin wata b'atacciyar murya na mayar masa da raddin maganarsa.

"Ai na fi kowa sanin mahaifinka ne! na san cewar babanka ne ! sai dai ka sani baka yi sa'ar uba ba ! baka more ba da ka zamo jinin wannan azzalumin mutumin mara imani da tsoran Allah ! ayau ina danasanin had'a hanya da shi,ina bak'inciki da na same shi a matsayin uban mijina...kuma wallahil azeem hakan ba zai saka ni fasa k'udirina akan sa ba...domin..

Marin da aka zabga min mai tsananin zafi shine ya dakatar da ni daga maganata,kafin na dawo hayyacina Uncle Khaleel ya cukumeni kamar yadda na cukumi mahaifinsa,cikin k'araji da tsananin masifa kamar ya shid'e yake jijjigani yana kifamin maruka da d'aya hannun a jejjere,bakin sa na kumfa wajen zazzago min kalamai cike da masifa.


"Kar kiyi amfani da damar da kika samu a kaina ki ce zaki wulak'antani,kar kiga son da nake miki ya kai k'ololuwa ki nemi ki kasheni a tsaye,tabbas ina sonki Hidaya,amma son da nake miki bai kai son da nake wa farcen mahaifina ba,wallahi duk wanda yace zai tab'a min mahaifi sai in da k'arfina ya k'are a kansa,zan iya hak'ura da ke da son da nake miki in zab'i mahaifina,me mahaifina yayi miki?me Daddyna yayi miki da kike masa wad'annan mugayen abubuwan?yau ne rana ta farko da kika fara ganinsa a duniyar ki,amma me ya shiga kanki da kika tozarta shi a gabana?giya kika sha?ko haukacewa kika yi?tambayarki nake ki ban amsa kafin nayi k'asa k'asa dake na taka wuyanki,soyayyar da nake miki ta ci uwarta! ita soyayyar ta ci ubanta! na bita na tattaketa na murje mata wuya in dai akan mutuncin mahaifina ne"

Ba zan iya k'irga adadin marin da Uncle Khaleel yayi min ba yana zuba min bala'i da masifa cikin hargowa da kumfar baki,kafin kace me kumatuna sun kumbura suntum,amma ban saduda ba,bala'in da ke ci na a k'irjina ya fi gaban kwatance,zuciyata tafasa take yi ina k'ara jin tsanar Daddy a raina,burina naga bayansa ! muradina naga babu shi a doron duniya !

Cikin wani irin layi na tamkar ina cikin maye nake duban Uncle Khaleel da idanuwa na,wanda nake hangar abubuwa guda biyu cikin na sa idanun,wato Soyayyata da ta jima a tare da shi,da kuma tsanata da ta fara kafuwa cikin mintunan da suka gabata,cikin wani irin murmushi na bak'inciki na dubeshi nace.


"Mutunci...? wannan tsohon najadun kake ambatawa mutunci?wannan tambad'ad'd'en mutumin kake zatarwa mutunci da kima?wannan .....


Wani wawan marin Uncle Khaleel ya sake kifamin wanda yayi sanadiyyar fashewar bakina da hancina,nan da nan jini ya fara bin fuskata,amma duk da hakan banji komai a raina ba,banji zan iya dakatawa da abinda zuciyata ta niyyata ba,ko gezau banyi ba,illa sake k'ura masa idanu da nayi cikin yanayi na masifaffen tashin hankali,a lokacin da na riski hawaye ya fara malala a kumatunsa yana bin jinin da ke fita ta hancina da bakina da kallo,a lokacin ne nima naji wani hawaye mai tsananin zafi ya kawowa idanuwana ziyara,cikin dakakkiyar murya na fara magana ina duban cikin idanuwansa da suke a juye.


"Ko kashe ni zaka yi ba zan fasa kiran wannan mutumin da azzalumi ba,ko ratayeni zaka yi ba zan fasa kiran sa mugu mara imani ba,Uncle Khaleel ko tsireni zaka yi ba zan fasa.

Wani irin shak'o wuyana yayi ya gara ni da garu ya matseni,cikin mugun rawar jiki ya sake kifa min gigitaccen marin da ya kusa wucewa da numfashina,bakinsa na mugu mugun kyarma yake ambatar.


"Ba za ki daina zagin mahaifina a gabana ba ko?ba za ki daina ambatarsa da mugayen kalamai ba ko?za ki sa na yanke miki hukunci mai zafi Hidaya,za ki sa na aikata abinda baya cikin tsarina,za ki sa muyi mutuwar kasko ni da ke ,za ki sa....

Wani irin tari me k'arfi ya sark'afe shi yayin da ya sakeni yake dafe k'irjinsa cikin wahala,ban dubi yanayin da yake ciki ba saboda na kai matuk'ar k'urewa a fagen tashin hankali,shiyasa na cigaba da zagin Daddy a gabansa ina antaya masa bak'ak'en maganganu marasa dad'i,yayin da Daddyn ke durk'ushe kai a k'asa ya kasa ko d'ago idanuwa ya dube ni baiyi ba,sai dai fa hawaye ne ke sharara suna bin fuskarsa.

Duk da azabar da Uncle Khaleel ke ji a k'irjinsa hakan bai hana shi d'agowa ba,yana dafe da k'irjinsa yake kallona yana zubar da hawaye,wani kakkauran zagi da nayi wa Daddy shine ya baiwa Uncle Khaleek damar rufeni da wani irin duka yana gaura min mari,da hargowa kuma yana tsananin kuka yake fad'in.

"Tun da kin k'i jin maganata,tun da kin k'i dainawa na hak'ura da ke,ba zan iya kallon matata ta sunnah tana zagin mahaifina wanda ban da kamarsa ba a gabana,na hak'ura da ke Hidaya... na barki bari na har abada....na hak'ura da soyayyarki ko zata zama ajalina...na haramtawa kaina ke har duniya ta nad'e....domin baki da wani amfani a gareni....na sakeki Hidaya ...saki d'aya...saki biyu.....saki uku....ke idan ma ana saki dubu to ayau na sakeki saki dubu Hidaya.....na sake ki....na sakeki....nace na sakeki Hidayaaaaaaaa


Yana fad'in wannan kalamin yayi wurgi dani hanyar k'ofar fita daga parlour'n,a dai dai sanda Ya Hamza ya d'aga labulen parlour'n da sallama wata mata na biye da shi a bayansa,a lokacin ne na fad'i gabansa tim bisa wurgin da Uncle Khaleel yayi dani.

A gigice Ya Hamza ya durk'ushe gabana,kunnuwansa na masa kuwwa bisa ga kalmar sakin da Abokin sa yake ta furta min,jinin da ya gani yana fita ta hancina da bakina shi ya sake firgitashi,har bai san lokacin da ya saka hannuwan sa cikin kid'imewa ya tarairayoni zuwa jikinshi ba,da k'yar na iya bud'e idanuwa na cikin azaba da wahala na dubeshi,cikin k'arfin hali na rik'o wuyan rigar sa idanuwa na na shirin k'ak'k'afewa,da hannu nake nuna masa Daddy,kafin nayi nasarar fizgo maganar da nake son yi.

"Ya Hamza.....wancan azzalumin ne ....ya kashe min ....mahaifina....Ya Hamza don Allah...ko da na mutu a yanzu ....ina so ka d'aukar min fansa....ni ma ka kashe min shi....don Allah Ya Hamza.....

Ina fad'ar wannan maganar na fara wata irin shak'uwa da nishi,kafin na sulale a k'irjinsa a matsayin sumammiya.....!


*zan tafi hutun sati biyu tunda bakwa comments sosai*🙄🙄🙄


Comments
share
vote
pls


*GARKUWA BIYU*


BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter 16 · 0% Book details