BABI NA SITTIN DA D'AYA DA NA SITTIN DA BIYU
Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
***Gabad'aya kan Daddy ya kulle ya rasa mafita,ji yake tamkar kansa zai tsage tsabar tunani da tsananin tashin hankalin da ya samu kansa a ciki,wata Zuciyar na ayyana masa ya kira Khaleel a Daren ya bayyana masa komai domin ayi ta ta k'are,yayin da wani b'angaren ke gargad'insa akan hakan,domin dai komai zai iya cab'ewa har a rasa hanyar gyarawa.
B'angaren Khaleel yana tare da abokanan sa wad'anda suka yo tattaki tun daga England domin halartar d'aurin Auren sa,amma Hamza baya tare da su yana gida,babu yadda Khaleel bai yi da shi akan yazo su kwana tare ba amma ya k'i yarda,yace akwai uzurin da yake son gabatarwa a Daren Wanda yana buk'atar killace kansa,haka Khaleel ya hak'ura ba don ransa yaso ba.
A Daren misalin k'arfe d'aya da rabi dare ya tsala,Hamza ne zaune a d'akin sa ya rasa abin da yake masa dad'i,hannayensa dafe da kan sa da ke barazanar tarwatsewa tsabar damuwa,idanuwa sa sunyi jajir sun koma ciki tsabar kukan da ya sha,har a lokacin ma Kuma hawayen ne ke sintiri a kyakkyawar fuskar sa ,ya kai Hannu ya share hawayen a sanda wasu suka k'ara b'ullowa,shi dai ya san ya hak'ura da Hidaya, da zuciya d'aya ya barwa Khaleel ita,to amma bai san menene ya sa ta kasa barin Zuciyar sa ba,sai yanzu ne ma yake jin wata matsananciyar k'auna da soyayyar ta,bai san ya zai yi ba,zafin da yake ji a tsakiyar k'irjinsa yana sawa yaji tamkar ba zai kai safiyar gobe da rai a jikinsa ba.
Hannuwa biyu ya d'aga yana wa Allah kirari da rok'o a gareshi domin ya yaye masa damuwar sa,hawaye na zuba a idanuwan sa yake rok'on ubangiji kan ya cire masa son Hidaya daga Zuciyar sa,ya san Allah yana jin sa Kuma yana ganin sa,kuma shine yace kada a kirawo waninsa idan ba shi ba,domin babu mai amfanar ka Idan ba shi ba,shine da kan sa yace a rok'eshi zai amsa ,Allah (S W A)yayi umarni da addu'a a cikin ayoyi masu yawa,a cikin suratul gafir ya ce.
"و قال ربکم ادعونی أستجب لکم"
Ma'ana(Kuma Ubangijinka ya ce ,ku rik'e ni,na amsa muku)
A cikin suratul yunus ma ya sake ce wa.
"ولا تدع من دون اللہ ما لا ینفعک ولا یضرک،فإن فعلت فإنک إذا من الظلٰمین"
(Kada ka kirawo wani ba Allah ba,Wanda ba zai amfaneka ba,Kuma ba zai cutar da kai ba,idan kuwa ka aikata haka,to lallai kai kana cikin azzalumai)
Sannan wannan lokaci na tsakiyar dare Allah yana amsa addu'ar bayin sa,ya zo a cikin sahihul bukari ,Manzon Allah (S A W) ya ce.
"Ubangijinmu kan sauka kowane dare zuwa saman duniya yayin da sulusin dare na k'arshe ya rage,sai ya ce" wanene zai kira ni na amsa masa? Wanene zai ne mi gafarata na gafarta masa?"
Wad'annan ayoyi da Hadisai su ne suka sake bawa Hamza k'warin gwiwar mik'a kokensa zuwa ga Ubangijin sammai da k'assai,Wanda ya halicci zuciyar mutane Kuma kowa da irin ta sa,ya sanya k'addara da jarrabawa a tsakanin bayin sa domin ya gwada imanin su da tauhidin su.
Hamza yayi addu'o'i masu yawa cikin Daren,a k'arshe ya fashe da kuka sosai yana fad'in.
"Ya Ubangijina makad'aici na fake zuwa gareka cikin lamarin ka,na d'aga tafukan hannayena na k'ask'antar da kaina,ka yarda dani ko zan rabauta,kayi min Rahama da gafara ya Allah,ka cire min Hassada da bak'inciki a zuciya ta,ka haneni da cutar da D'an uwana musulmi,ka cire min son wannan baiwa ta ka a zuciya ta da RUHI na,Ubangijina ina son in had'u da kai lami lafiya ina mai farinciki,bana son ka kamani da mummunan laifi na son matar Aure, Allah ka karb'i rok'o na ka sanyaya min zuciyata ka mu sanya min da mafi alkairi a rayuwata,duk abin da ka aiwatar a kaina dai dai ne,bana bak'inciki da jarrabawarka ya Allah,na karb'eta da Hannu bibiyu ina mai biyayya a gareka,Allah ka bani ikon jure rashin ta da kewarta a duniyata,Allah kai ka halicci zuciyata da tsananin sonta,sai kuma ka hanani ita domin ka jarraba imani na,na hak'ura ya Allahu,na barwa Khaleel ita,Allah ka sa hakan ya zama mafi alkairi a garemu baki d'aya"
Yana kammala wa ya ji wani sanyin dad'i a ransa,wata irin nutsuwa ta saukar masa,take ya mik'e da k'arfin gwiwa ya nufi wardrobe d'in sa ya bud'e,idanuwan sa suka sauka kan abin da yake son gani,Hannu ya mik'a ya d'auko abin cikin k'ura masa idanuwa yana tuna lokacin da aka damk'a masa amanar abin.
Envelope ce wadda mahaifiyar Hidaya ta dank'a masa ranar ta bashi amanar Hidayan,ya kuma rik'e amanar bai tab'a jin sha'awar bud'ewa domin ganin abin da ke ciki ba,ya runtse idanu yana tuna sanda mummyn Hidayan ke jaddada masa ya ajiyewa Hidayan envelope d'in,Sannan ya bata a lokacin da ta girma ta mallaki hankalin kanta,to idan kuwa hakane babu wani lokaci da ya cancanta ya bawa Hidaya wannan sak'on irin wannan lokacin da take shirin zama matar Aure, a yanzu Hidaya take da cikakken hankali domin rayuwar ta za ta sauya akasin ta baya.
A hankali ya bud'e idanuwan sa yana sakin numfashi ya sauke kallon sa kan envelope d'in da ta sha ajiya tsawon shekaru,ya girgiza kan sa ya bar gaban wardrobe d'in,ba tare da b'ata lokaci ba ya taka a hankali ya fice zuwa tsakar gidan su da yake tsit, baka jin motsin komai…..
Hasken da ya gauraye tsakargidan shine ya ba shi damar lura da Hidaya da ke zaune a dandaryar k'asa,kanta matse a tsakanin cinyoyin ta,duk da kanta a sunkuye yake hakan bai sa ya kasa shaidata ba,ko cikin miliyoyin mata Hidaya ta shiga zai iya binkito ta saboda tsabar sanin da yayi mata,k'irjinsa ne yayi matsanacin bugawa ganin ta zaune a wajen cikin talatainin Daren da kowa yake bacci,gidan na su cike yake da mutanen da suka zo kwanan biki,musamman dangin Umma na kano.
Cikin sanyin jiki yake tafiya har ya k'ara sa kusa da in da take zaune,tsugunawa yayi dab da ita yana kallon ta cikin dukan zuciya,cikin kyarmar murya ya ambaci sunanta a hankali tamkar me yin rad'a.
"Hidayaaaaaa"
Bata yi tsammanin jin kiran ba,shiyasa ta d'ago kanta a zabure, cikin tsoro ta sauke ganin ta kan Hamza da ke tsugune a gaban ta,idanuwansu na had'uwa suka ji wata irin fad'uwar gaban da basu tab'a ji ba,Hawaye ne shab'e shab'e yayi wa fuskar Hidaya Zane,har fuskarta ta ta kumbura,kallon da Hamza ke mata cikin tsananin mamaki ya sa ta hanzarin mik'ewa tsaye da sauri,shi ma mik'ewan yayi har lokacin idanuwan sa a kanta ya kasa magana,bai yi aune ba sai jin Hidaya yayi ta afka k'irjinsa da k'arfi,ta rungumeshi k'ak'am tana cusa kanta cikin tsakiyar k'irjinsa da ke mugu mugun bugu,ta fashe da wani irin Kuka na rauni da soya zuciya,muryarta har ta dusashe da k'yar take iya magana wadda Hamza ne kad'ai yake jin me take cewa cikin kuka.
"Ya Hamza na kasa jurewa… Ya Hamza na kasa daurewa rashin ka…Don Allah Ya Hamza ka aureni…ni na yarda na cire kunya ta na bayyana maka soyayyata….wallahi ba zan iya rayuwa ba tare da kai ba…Ina sonka …ina k'aunar ka…da kai na rayu tun daga k'uruciyata zuwa girmana…..ban san kowa ba idan ba kai ba....babu wanda ya kai ka sanin kimata da mutuncina...ka taimakawa Ruhina da Numfashina ka cigaba da zama GARKUWA ta,Ya Hamza don girman Allah ko sau d'aya ne ka furta cewa kana So na….kar ka barni…kar ka gujeni….kar ka juya min baya please Ya Hamza na…i can't explain how much I love you,you are the hope of my life,I'm always happy when I see you beside me,you are the happiness of my life,I love you more than anything in my life,I love you so much Ya Hamzaaaaaaa….…!
Hidaya gabad'aya ta rikicewa Hamza,shi ma ta rikita shi,domin wani irin tsattsauran rik'o da tayi masa tana malalar da hawayen ta a jikinsa,yanayin da Hamza ya shiga ba zai fassaru ba,shi tsoro ma yake kar Umma ko wata ta fito a gansu a haka,cikin tsakiyar dare a tsakargida rungume da juna,jikinsa ya kama karkarwa yana rawa,Hidaya so take ta kasheshi kawai ta huta,bata San dauriyar da yake ba tana son tayar masa da hankali,ganin irin k'wak'umar da take masa cikin fitar hayyaci tana shirin suma a jikinsa sai ya sake tsorata,da sauri ya rik'o kafad'unta yana jijjigata domin ta dawo hayyacin ta,ganin yadda take langab'ewa tana shirin zubewa a k'asa kawai sai ya cafki hannun ta ya fizgeta suka fad'a cikin d'akin sa da hanzari jin motsi kamar za a fito.
Yana rik'e da hannun ta guda d'aya,ya tura k'ofar d'akin da Hannu d'aya ya rufe,sannan ya waiwayo ya dubeta cikin tsananin tashin hankali,sosai jikinsa yake mugun rawa ganin yadda Hidayan take wani irin kuka tana had'iyar zuciya tamkar ta shid'e,mugun tausayin ta ne kawai yake d'awainiya da shi,shiyasa ya rik'e hannun ta ya zauna kan d'aya daga cikin kujerun d'akin jikinsa a sanyaye,yayin da ya janyo hannun ta ya durk'usar da ita a gabansa tana ta faman kuka.
Da k'yar ya iya bud'e baki ya fad'a mata gajeriyar kalma.
"Kiyi hak'uri…!
Ta girgiza kai tana k'ara damk'e hannunsa sosai kamar Wanda zai gudu ya barta,a hankali tayi magana tana kallon sa hawaye na sharara.
" Na ka sa hak'urin Ya Hamza…Ba zan iya ba"
"Za ki iya Fad'ima"
Yayi saurin katseta cikin rauni tamkar shi ma ya fashe da kukan,Hidaya ta k'ura masa idanu jin ya ambaceta da Fad'ima, sunan da Umma ce kawai tafi ambatar ta da shi.Ya ci gaba da magana cikin sanyin murya idanuwan sa a kanta.
"Hak'uri wani abu ne da yake da wahala a rayuwar duniya Hidaya,amma Idan kika jure kika jajirce za ki iya,Hak'uri tamkar ingarman da baya tuntub'e ne,tamkar takobin da baya dakushewa,tamkar rundunar da ba a tab'a karyata ba,tamkar ganuwar da bata rusuwa,Hak'uri da nasara y'an uwan juna ne,duk in da aka samu hak'uri to wataran za a yi nasara,babu wani k'arfi ga bawan da bashi da hak'uri, kamar yadda babu shi babu cin nasara a rayuwa,Hidaya Allah ta'ala yana ce wa.
"یأیھا الذین ءامنوا اصبروا و صابروا و رابطوا واتقوا اللہ لعلکم تفلحون"
Ma'ana(Ya ku wad'anda suka yi imani,ku yi hak'uri, kuma ku jure,kuma ku zama a cikin shiri,kuma kuji tsoran Allah ko kwa rabauta).
Bayan haka Allah ya bayyana k'aunarsa ga bayin sa masu hak'uri.ya ce,
"واللہ یحب الصبٰرین"
(Allah ya na son masu hak'uri).
Hidaya ba Wani Abu ba ne hak'uri face hana kai raki,da hana harshe kokawa,da kuma hana gab'b'ai make make da kekketa suttura da makamantan hakan,Hidaya duk wani Abu da kika ga ya faru to da sanin Ubangiji, shine ya tsara komai akan mu da rayuwar mu,shine ya tsara cewar ke d'in ba matata ba ce,matar Aboki na Khaleel ce,shiyasa Allah bai nufe ni da furtawa ba har ya riga ni,tabbas ko zan b'oyewa kowa ba zan iya b'oye miki ba,Ina son ki ! Na fara son ki a ranar da idanuwa na suka had'u da naki tun kina k'aramar ki,ranar da mahaifiyar ki ta dank'a min amanarki a hannuna,tun daga ranar nake son ki har rana irin ta yau da nake san son da nake miki ya sauya zuwa na y'an uwan taka,domin na had'u da Allah na lami lafiya Hidaya,kar ki damu kinji,ko baki sameni ba kin samu makwafina,babu ta in da Khaleel zai gaza da ke a fannin rayuwa da zamantakewa,ni dai ina so ki cire komai a ranki kiyi zaman aurenki cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,ki manta da cewar Hamza ya tab'a yi miki So na soyayyah,hakan zai sa na k'ara tabbatar wa Hidayana mai hak'uri ce,Hidayana mai juriya ce,Hidayana mai biyayya da tarbiyyace,Hidayana mai k'ok'arin bin abin da Allah yake so ce,Hidayana mai…….
Wani irin rik'o da tayi wa hannun sa tare da fashewa da kuka shine ya dakatar da shi,cikin kukan take kallon sa zuciyar ta na bankwana da shi,harshen ta na karkarwa wajen furta masa kalamai kamar haka.
"Madalla da kai Ya Hamza,Madalla da nagartaccen mutum irin ka mara son zuciya,Madalla da samun irin ka a duniyata,Madalla da kyakkyawar rayuwar da na gabatar tare da kai daga yarinta zuwa girmana,Kalmar da ka ambata min ta ka kana so na ta wanke min dukkanin k'uncin zuciya ta,kuma daga yau zan sa d'ambar Hak'uri da jajircewa domin ganin na cim ma nasara kamar yadda kake kwad'aita min,Ya Hamza na hak'ura da kai,zan auri Uncle Khaleel nayi masa biyayya,fatana ka cigaba da yi min addu'a da d'orani akan hanyar dai dai da zarar zan kauce….!
Wani irin murmushi ne ya sub'ucewa Hamza,ya lumshe idanuwan sa yana jin salama a zuciyar sa,yana fatan Allah ya cigaba da ba su dangana,sakin hannuwan ta yayi sannan ya juya a hankali ya d'akko envelope d'in nan ,ban da aikin kallon sa babu abin da Hidaya take yi,yayi mata alamar ta mik'o hannun ta,a sanyaye ta d'ago hannun a lokacin da ya d'ora mata envelope d'in kan tafukan hannayen ta yana shirin magana,a lokacin ne kuma suka ji yo muryar Umma tana buga k'ofar a hankali tana ambatar sunan Hamza…….!
Comments
share
vote
pls
*GARKUWA BIYU*
BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️