BABI NA SITTIN DA BAKWAI DA NA SITTIN DA TAKWAS
Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 15 min read
***Tun a lokacin Uncle Khaleel ya soma bautawa jikina da wata irin soyayya da lallashi na musamman,tun ina kuka har sai da hawayena suka k'afe k'af saboda zuk'e su da yayi,ina a jikinsa ya hanani motsi sai yadda ya juyani,har tsayuwa ta gagare mu sai gamu mun zube a gefen gado cikin numfarfashi.
Sai nake ji a zuciyata an ya za a samu mutumin da ya iya rarrashin mace da kalamai da gab'ob'i irin Uncle Khaleel kuwa?domin bai barni ba sai da kuka na ya tsaya tsaf ! har ma ya sakani murmushin da ban shirya ba,daga nan kuma ya jani toilet d'in cikin bedroom d'in muka d'auro cikakkiyar Alwala tare ,Bayan fitowar mu muka gabatar da Sallah Raka'a biyu a nutse.
Mun kwashe lokaci mai tsawo muna addu'o'i ni da Uncle Khaleel,kafin ya saka hannuwansa masu albarka ya kama kaina yayi min adduar da duk wani Ango yake wa Amaryarsa a daren farko,adduar da Manzon tsira alaihis salatu wassalam ya koyar da mu,tunda ya kama kaina yana karanta adduar nake jin wani sanyin dad'i na shiga tsokar jikina,wani yammmm ! nake ji, babu inda bai amsa ba a sassan jikina,tsigar jikina na mik'ewa yarrrr !
Ina Zaune tsuru tsuru ilahirin jikina ya mutu murus ban san dalilin hakan ba,har Uncle Khaleel ya mik'e tsaye ya fice daga d'akin,na sauke ajiyar zuciya ina runtse idanuwa na,wani sanyi sanyi nake ji tamkar wadda zazzab'i zai kawo mata farmaki.
Ina nan zaune ya sake shigowa da sallama,da k'yar na amsa cikin kasalalliyar murya,yazo gabana ya zauna kafad'ar sa na gogar tawa,a tare muka sauke numfashi tamkar wutar lantarki ta jamu saboda wani maganad'isu dake fizgar junanmu,ajiye tray d'in hannun sa yayi wanda ke d'auke da wani plate da gasassun kaji cike fal sun sha kayan had'i sai k'amshi ne ke tashi,ga kuma sassanyen juice da yoghurt a gefe,sai cups da fork .
Da kan sa ya ciyar da ni duk da na so yi masa gardama,amma wani kallo da yayi min tilas na bud'e bakina yana ciyar da ni har na k'oshi,da zarar hawaye ya ratso idanuwana zai kafeni da na sa idanuwan da wani sihirtaccen kallo wanda yake kassaramin gab'ub'uwan jikina,tilas nake maida hawayen ba da shiri na ba.
Sai da ya tabbatar da na k'oshi sannan shi ma ya ja gaban sa ya fara ci,a na ci yana kallona,da mun had'a idanuwa ya sakar min murmushin sa me k'ara masa kyawu da cikar kamala,a haka har ya kammala,ya sake jajibata muka yi toilet muka wanko bakin mu muka fito.
Wardrobe ya wuce ya bud'e ya zaro wata sleeping dress me azabar kyau,sai dai tana da d'an kauri ba mai bayyana jiki ba ce,har in da nake tsaye a tsorace ya iso gareni,Mik'o min yayi yana murmushi Sosai sannan ya ce.
"Karb'i ki sanya ki kwanta kiyi baccinki nasan kin gaji ko?"
Gyad'a kaina nayi cikin dukan zuciya na mik'a hannu na karb'i rigar daga hannunsa,Ya wani lumshe min idanuwansa yana karya wuya idanuwansa a kaina tamkar ya lasheni,a hankali kuma ya juya yana fad'in.
"Ina zuwa."
Ni dai jikina a sanyaye yake har ya fice daga d'akin,cikin matuk'ar tsoro na sauke ajiyar zuciya na nemi gefen gadon na zauna,babu abin da ke raina sai Umma da Ya Hamza,ko ya suke yanzu?ko sunyi barci?ko suna cikin kewata?Hawaye mai d'umi ya zubo min ! Na sa bayan hannuna na share ina shesshek'a zuciyata tana ciwon rabuwa da su a muhalli d'aya.
Sai da na share Mintuna goma a haka,ganin Uncle Khaleel bai shigo ba sai na mik'e na cire kayan jikina na mayar da rigar baccin a jikina,na d'an fesa turare kad'an saboda iya k'amshin da ya manne min a fatar jikina ma ya wadatar,ko ya ya ka matso jikina tilas ka shak'i k'amshi mai dad'i da nutsar da zuciya.
Har na kammala bai shigoba,hakan ya sa na haye gadon na takure guri d'aya,sai nake jina tamkar wata marainiya a lokacin ! tamkar wadda ta rasa komai da kowa !duk da zan iya cewa na rasa komai d'in,babu mahaifiya a tare dani balle mahaifi,babu Ummana a kusa da ni,babu Ya Hamza GARKUWA TA"
To amma ai akwai Uncle Khaleel,wanda Ya Hamza yayi ta nanatamin cewar a yanzu shine komai nawa ! shine GARKUWA TA,shine komai a gareni.
Zuciyata ta kuma karyewa ! wani kuka ya tawo min irin me tokare k'irjin nan,nayi ta shatatar da hawaye yana jik'a min pillow d'in da na d'ora kaina,tsawon lokaci ina kukan da ban san tak'amaimai dalilin yin sa ba,ni dai kawai na samu zuciyata ne cikin matsanancin rauni da kewar Abubuwa,a hakan naji motsin shigowar Uncle Khaleel...
Chak ! na tsayar da kukana,saboda bana son yaji har na saka shi a damuwa,bai nufo in da nake ba sai ya nufi wata drower ya d'auko alk'ur'ani mai girma ya zauna kan wata kujera da ke gefe ya soma karanta suratul Rahman cikin murya mai dad'i da Nutsuwa,Wannan karatu da yake yi shi ya sanyaya min ruhina na dinga jin salama a k'irjina da ya tokare,Idanuwana a lumshe tamkar me bacci ko motsi bana yi,ya jima yana karatun kafin yayi addu'o'in sa ya shafa,ina ji yana tayi wa Ya Hamza addu'a da fatan alkairi mara yankewa,yawanci adduarsa akan Ya Hamza take,hakan yasa na k'ara tabbatar da cewa Uncle Khaleel ba k'aramin so yake wa Ya Hamzana ba.
A lokacin da ya kammala yaje ya maida alk'ur'anin sai naji takunsa ya nufo in da nake,na sake runtse idanuwana tamkar mai bacci ina sakin numfashi a hankali,nan kuwa tsoro ne ya cika zuciyata kamar ta faso k'irjina ta fito,ina jinsa ya hawo gadon a hankali wai gudun kar ya tasheni,bai san idona biyu ba,Can gefe ya kwanta rigingine yana ajiyar zuciya tare da runtse idanuwansa,sai naji yana ta ambatar "Alhamdulillah" ya dinga fad'a har ban san adadin yawan Hamdalar da ya dinga yi ba.
kusan minti Ashirin sannan naji yana matsowa a hankali har ya iso dab da ni,k'irjinsa ya had'u da bayana,tsigar jikina ta mik'e yammm! yayin da naji ya saki gwauruwar ajiyar zuciya me tsananin k'arfi,zuro hannuwansa yayi ta gabana yayi min wata kyakkyawar runguma da taso rikitani,amma na maze na cigaba da nuna cewa ni d'in fa bacci nake yi,a haka ya dinga mannemin har saida jikinmu ya game wuri guda,sassanyar Numfashin sa na sauka a kan dokin wuyana yana tada tsigar jikina.
Shi a zatonsa bacci nake,shiyasa naji ya fara wata irin magana a hankali cikin rad'a,wata irin magana da ta dinga ratsa fatar jikina zuwa naman jikina har ta b'ulla cikin k'asusuwa ta kassara b'argon jikina,ina matse a jikinsa yake maganar dab da kunnena cikin rawar jiki da shesshek'a....
"D'azu Aboki yace min kar na bar komai....Na cinye komai...kar na rage komai....yace min idan yace komai to yana nufin komai.....Su Sumayya suka yi min rowar ganinki wai sai na sayi bakinki,Ni kuma basu san cewa dukkanki nake so ba ba iya bakinki ba....Wallahi ina sonki Hidaya...ina sonki tun ranar da na fara ganinki a duniyata....Na rayu da dakon soyayyarki tsawon shekaru wadda naso na bayyana miki ita a daren yau....sai dai ba zan iya katse miki baccin da kika fara ba....amma a yadda nake jina zan kwana ne cikin wahala da kewa ! ina ma bakiyi bacci ba ! ina ma na iskeki ido biyu ! ina ma zaki karb'i bak'unci na a yanzu ! ban tab'a jin wani yanayi mai tsananin girma a tare dani kamar yanzu ba Hidaya !I love you ! I love you very much ! I cant explain how much I love you !
Sai ya sake wani irin k'ank'ameni kamar zai maidani cikinsa,ina jin ruwa mai d'umi na sauka kan dokin wuyana yana gangarawa k'irjina,na san ba kowane ruwa bane face hawayen Uncle Khaleel da yake kwarara ! hawayen Soyayyah ! hawayen k'auna ! hawayen bege ! hawayen sha'awah ! hawayen komai !
Bantab'a jin tausayinsa ba irin lokacin,na dinga jin wani abu na ratsani yana mamayeni mai kama da soyayyarsa da k'aunarsa,sai naji kamar na bayyana masa cewar ba bacci nake ba ko dan ya samu cikar burinsa,amma na kasa hakan,wani hawaye ya tawo min,nayi hanzarin shanye abuna don kar ya gane.
Haka ya dinga sambatun sa a jikina,sambatun soyayyah! har bacci yayi nasarar kwasheshi yana ta ambatar yadda yake sona! Ni kuwa idanu ba bacci,zuciyata na ta kai kawo ! sai bayan awa biyu da baccin sa sannan nima baccin ya saceni,wani irin bacci mai tsananin dad'i da ban tab'a samun irinsa a rayuwata ba.
*************
Wajen k'arfe goma sha d'aya na daren Umma na zaune babu bacci a idanuwanta,babu abinda take jira sai shigowar Hamza cikin gidan saboda dare yayi,ragowar y'an bikin duk sun yi baccin gajiya ita kuwa idanuwanta tar babu alamun bacci a cikinsu,sai Sha d'aya da rabi ta ji shigowar sa ya kulle gidan,sannan taji ya bud'e d'akinsa ya shige,a hankali ta mik'e ta nufi d'akin nasa don ganin yanayin da yake ciki.
Lokacin da tayi sallama ta shiga a tsaye ta tarar da shi yana k'ok'arin cire rigar da ke jikinsa,ya waiwayo a hankali rigar a hannunsa yana amsa sallamarta,a hankali ya saki murmushi murmushin da ya fito da tsananin ramar da yayi a fili,cikin k'aramar murya ya ce.
"Ummana baki yi bacci ba kenan?"
Umma ta samu kujerar d'akin ta zauna tana dubansa cike da tausayawa tace.
"Banyi ba Hamza,ina jiran shigowarka ne naga dare yayi amma baka shigo ba"
Ya d'an sunkuyar da kai yana jin k'aunar mahaifiyarsa na linkuwa a ruhinsa,ya d'an zame ya zauna gefen gadon sannan ya d'ago kai yayi murmushi yana duban Umman yace.
"Na tsaya tawowa da su Hansa'u ne Umma,daga nan kuma na tsaya sallamar ragowar abokanan mu da suka zo taya mu muranar biki"
Umma ta jijjiga kai,cikin rauni tace.
"Alhamdulillah da aka gama bikin nan lafiya lau,naji dad'i sosai,to ya ka baro min Fad'imar?dafatan dai ta daina kukan?"
Ya girgiza kai,a hankali yace.
"Ban sani ba ko ta daina,domin nidai ban shiga ciki na ganta ba"
"Me yasa hakan Hamza?"
Umma ta tambaye shi idanuwanta a kansa.
Yayi shiru bai ce komai ba kansa a sunkuye,har Umma ta sake kiran sunansa .
"Hamza"
A hankali ya d'ago kai k'walla na taruwa a idanuwansa ! Umma taji tausayinsa matuk'a,shiyasa ta sanyaya murya tace masa.
"Kayi hak'uri kaji Hamza ! Ka cire komai daga ranka,ai kayi namijin k'ok'ari kuma Allah yana sane da kai da hak'urin da kayi,kuma zai maka babban tukuici ta inda baka zata ba,na san kana jin ciwo a zuciyarka sosai,na san kana jin kewa a ruhinka ! na san ba wanda zai san abinda kake ji sai wanda ya tab'a d'and'anar abinda ka d'and'ana Hamza !amma duk abinda kake ji da sanin Allah ! domin tuni Allah ya rubuta komai da zai faru har izuwa tashin k'iyama.
Allah yana cewa.
" ألم تعلم أن الله يعلم ما فى السماء والأرض,إن ذالك فى کتب,إن ذالك على الله يسير"
Ma'ana( Shin ba ka sani ba ne,cewa Allah yana sane da abin da yake cikin sama da k'asa.Lalle wannan yana cikin littafi.Lalle wannan wani abu ne mai sauk'i a gurin Allah).
Don haka duk wani yanayi ko halin da ka samu kanka a ciki to da sanin Allah,kuma idan kayi hak'uri da juriya to zaka rabauta,Allah da kansa yana yin albishir zuwa ga masu Hak'uri,kasan wannan sai dai na tunasar da kai Hamza,Don Allah kayi hak'uri ka fawwalawa Allah komai,ka rage yawan damuwa duk da nasan kana k'ok'arin hakan,amma ramar nan da kake tana tayar da hankalina Hamza"
Hamza dai hawaye tuni ya wanke fuskarsa,kuka sosai yake yi nasihar Ummansa na shigar sa,babu abin da ya sake raunata zuciyar sa irin maganar da Umma ta cigaba da yi akan ya daure ya nemi matar aure shi ma yayi aure,hakan zai sa ya samu sauk'in wani abin,sai yake ji a zuciyar sa anya kuwa zai iya son wata bayan Hidaya?wadda ya rayu da ita da sonta tsawon shekaru masu yawa?to ba zai yanke hukunciba dai tunda Allah shine masanin komai da kuma abin da zai faru a gaba.
Umma dai bata bar d'akin ba har sai da ta sa Hamza ya karanta alk'ur'ani mai girma domin ya samu sauk'in zuciyar sa kan damuwar da ta cunkusheta,domin duk lokacin da kake cikin wata damuwa in dai ka karanta alk'ur'ani za ka samu sauk'i, Ambato ne mai hikima ! tafarki madaidaici !shine wanda soye soyen zukata ba sa karkacewa da shi ! harasa ba su rikicewa da shi,malamai ba sa k'oshi da shi!baya tsufa saboda yawan karantawa ! Abubuwan mamakin sa ba sa k'arewa ! wanda yayi magana da shi ya yi gaskiya ! wanda yayi aiki da shi zai sami lada ! wanda yayi hukunci da shi ya yi adalci ! wanda yayi kira zuwa gareshi ya yi kira zuwa tafarki madaidaici ! wannan shine littafin Allah wato (Alk'ur'anil kareem).
Kafin wani lokaci sai damuwar Hamza ta yaye a daren,saboda falalar karanta alk'ur'ani,har ma ya samu bacci mai dad'i wanda ya jima bai samu ba a rayuwar sa.
***********
Ina takure kamar mai jin sanyi a lokacin da muka idar da sallar asuba,har ma gari ya fara haske saboda karatun da muka tsaya yi,idanuwa na suka soma lumshewa alamar bacci na kawo min ziyara,Uncle Khaleel ya rufe alk'ur'anin gaban sa ya dubeni da murmushi akan kyakkyawar fuskarsa,a hankali kamar me rad'a ya ambaci.
"Barci....?"
Gyad'a kaina nayi ina yin hamma,ya k'ura min idanuwansa da na hango zallar sha'awata a cikinsu saboda wani irin sauya kala da suka yi,da sauri nayi k'asa da kaina saboda yadda naji jikina ya soma rawa rawa,idanuwansa a kaina yace min.
"Je ki ki kwanta,amma ki cire wannan hijabin"
Da hanzari na mik'e na nufi gadon,na cire hijabin na ninke na ajiye kan bedside drower,sannan na haye gadon ina kwanciya,duk abin da nake idanuwan sa a kaina,sai a lokacin ne ya naji yo muryar sa mai tsananin dad'i yana ce min.
"Ki d'an rage min guri kad'an zan zo na tayaki baccin ni ma,kinji My love"
ina jin maganarsa sai na matsa can lokon gadon na bar masa fili mai yawa,har ya kammala abin da yake ya iskeni har in da nake.
chak naji ya d'aukoni kamar jaririya ya dire ni a kan k'irjinsa,ya mamayeni ya rungumeni tsaf,k'amshin da jikinsa ke fitarwa mai tsananin dad'i ya cika min k'ofofin hancina,kunya ta saka ilahirin jikina rawa kar kar kar,ya saka hannuwansa masu taushi yana shafa bayana tare da k'ara nutsar da kaina a k'irjinsa,na sake runtse idanuwana ina sauke ajiyar zuciya a sanda naji yana shafani tamkar wata mage,sannan cikin k'aramar murya yake fad'in.
"Za ki iya tuna sau nawa na tab'a cewa Ina sonki?"
Girgiza kaina nayi domin ba zan iya magana ba,jikina ya mutu murus da sak'on da yake aika min,sarai yaji girgiza kan da nayi,shiyasa cikin wata irin shesshek'a ya sake ce min.
"Tun da nake ambata miki soyayyar na tab'a nuna miki ita a zahiri kuma a aikace?"
Nan ma girgiza kai nayi har hawaye ya soma ciko idanuwana tsabar jin dad'in abubuwan da hannun Uncle khaleel suke min,birkitoni yayi yana tallafe da ni,na koma k'asa yayin da yake saman jikina,amma bai sakar min nauyi ba duk da shi d'in siriri ne,runtse idanuwa na sake yi hawaye na fito min,yayin da naji bakinsa dab da hancina yana wata irin magana,k'amshin da ke fitowa kad'ai daga bakinsa ya isa rud'ar da mutum.
"To Don Allah Hidaya ki bani dama mana !bani dama ko da y'ar kad'an ce yau na nuna miki ! Na rantse miki Soyayyar ba irin wadda ake juyawa baya ba ce! kinji Hidayanahhhhh......!
ji nayi ma kawai ba zan iya yi masa musu ba,gabad'aya Uncle Khaleel ya birkita min kaina,wata irin birgima ya soma yi a jikina tare da wasu abubuwa tamkar zai shid'e min,fad'i yake cikin kyarmar murya da sark'ewar numfashi.
"please Hidayaaaaa ! Na rok'eki don Allah Hidayaaaa! don Allah ! don Allah ! don Allah !
Ganin zai zauce min ban san lokacin da na bashi dama ba,hakan ya k'ara rura wutar abin da yake ji,kafin wani lokaci Uncle Khaleel ya zama mahaukaci tuburan a jikina,domin tsintar bakinsa nayi cikin nawa yana wasu abubuwa da ban san da su a duniyar mu ta mutane ba,kafin ya cire bakin sa ya gangaro k'irjina,anan wuta ta d'auke min d'if.
Ban tashi dawowa hayyacina ba sai da naji yana kuka sosai yana karanto wata addu'a,kafin kuma ya had'e jikinsa na jikina cikin wani yanayi mara fassaruwa,ni dai azabar da ta ratsani ji nayi kamar zan sume,babu abin da ke yawo a kaina sai kukan Uncle Khaleel cikin wani yanayi yana fad'in.
"Hidaya Zan mutu ! zaki kashe ni Hidaya ! wayyo Allah My Love...!
Daga hakan ban sake tuna komai ba har zuwa sanda ya gama bidirinsa,yayi kid'ansa yayi rawarsa,yayi biji biji da ni a wannan lokaci.
Ban tashi sanin in da kaina yake ba sai da na jini cikin ruwan zafi,na saka kukan da ya tayar masa da hankali,ya dinga lallashina yana sakamin albarka har ban san adadi ba,shine ya gasa min jikina yayi min komai,bakinsa bai gajiya da yabona da saka min albarka da kuma nanata min kalaman soyayyah ba...
Hatta break fast da kansa ya dafa min,da riritawa da lallashi da labaran ban dariya ya dinga ja na har na samu naci wani abin,ina jikinsa ya cikani da soyayyarsa wadda ta cika ruhina taf,domin tashi d'aya naji Uncle Khaleel d'in ya mamaye ko'ina a sassan jikina da zuciyata har ma da Raina.
Lokaci guda wayarsa ta d'auki k'ara,ina a jikinsa ya d'aga alokacin da naji yana mik'a gaisuwa zuwa ga wanda ya kira,na tabbatar da daddyn sa ne,har suka kammala wayar ya ajiye,ya dawo da hankalinsa kaina yana tallafo fuskata ya sakar min murmushi,lumshe idanuwa nayi saboda kunyarsa da nake matuk'ar ji,a kunnuwa na naji maganar sa yana cewa.
"Shine jiya kika dinga kiran Umma da Aboki su zo su ceceki ko?amma gaskiya Aboki ya yarfeki da yak'i amsa kiranki ya zo ya k'waceki a hannuna,ko da yake ma ai shine yace min in cinye komai ! kar na rage komai ! kuma na karb'i shawarar sa na cinye komai d'in ko My love?ko akwai abin da ya rage wanda ban cinye ba yanzu na cinye shi?"
Ban san lokacin da na k'ara nutsa kaina a k'irjinsa ba,kunya kamar ta kashe ni,shi kam dariya ya dinga yi min yana sake rungumeni,haka ya cikani da tsokana da soyayyah har ya direni kan gadon ya mik'e tsaye yana cewa.
"Bari naje daddy na kira na,yanzu zan dawo mintuna kad'an"
Fuska a k'unshe na jijjiga kaina,yayi murmushi ya sunkuyo ya d'an lalubeni ya ragewa kansa zafi,kafin ya kad'a kai ya fice fuska cike da annashuwa da farinciki.
Sai da yayi wajen minti biyar da fita sannan na samu y'ar nutsuwa na bud'e idanuwa na,nayi kasak'e zuciyata k'al,can kuma takardar da Ya Hamza ya bani ta fad'o min a rai,takardar da yace ta fito ne daga hannun mahaifiyata a lokacin da ta dank'a masa amanata,take naji zuciyata na zakwad'in ganin me takardar ta k'unsa,da hanzari na mik'e jikina na rawa na nufi jakata da na sakata a ciki,d'akkota nayi na dawo gefen gadon na zauna na fara k'ok'arin bud'e envelope d'in,ina bud'ewa na fara k'ok'arin zazzago abin da ke ciki,abubuwa guda biyu ne suka fad'o kan cinyata,wata farar takarda mai d'auke da Rubutu,sai wani hoto guda d'aya tal da na bishi da kallo ina yi masa kallon sani daga nesa nesa,ajiye hoton nayi na d'auki takardar na warware domin ganin abin da ta k'unsa......!
Comments
share
vote
pls
*GARKUWA BIYU*
BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️