← Book details Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 18 OF 31

BABI NA SABA'IN DA UKU DA NA SABA'IN DA HUD'U

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

***Ya Hamza na d'auke da ni a hannayensa har zuwa gida,yana gaba Aunty na biye da shi a bayansa tana sharar hawaye,shi kam tuni ma hawayensa ya k'afe sai idanuwansa da suka yi jajur,sai wani masifaffen d'aci da yake ji a bakinsa.

Aunty ce ta iya sallama a yayinda suka kutsa kai cikin gidan,yanayin muryarta mai cike da rauni ya sa Umma da wata mata da ke biye da ita suka d'aga labulen d'akin da hanzari suna fitowa daga parlour zuwa tsakar gidan,cikin matuk'ar tashin hankali Umma ta fara zare idanuwa tana nuna Ya Hamza da hannunta,bakinta na rawa take ambatar.

"Me ya faru da ita na ganku haka?me ya faru ne Hamza?ina mijin na ta?

Ya Hamza bai ce da Umma komai ba illah wucewa da yayi ya shige cikin d'akinsa ina d'auke a hannunsa,Umma ta bishi da idanu kafin ta waiwaya ta dubi wadda suka shigo tare da Hamzan,hawayen da ta gani a idanuwanta shine ya k'ara dugunzuma ta,cikin rud'u ta rik'o hannunta tana tambayarta.

"Me ya samu Hidaya naga ba ta motsi?kun sanar da ita cewar Mahaifiyarta ta zo yanzu ne?ko kun sanar da ita cewar ke k'anwar Mahaifiyarta ce?ba cewa nayi da ku kawai kuje ku tawo da Hidayan da mijinta ba?don komai ya zo da sauk'i"

Fashewa Aunty tayi da kuka ta kasa cewa komai,sai kallon yayarta take yi da ta tsura mata idanu cikin wani yanayi,wato(Mummyn Hidaya).

Ganin tak'i yin magana sai kuka take hakan ya sa Umma da Mummy suka dubi juna cikin dukan zuciya,kawai sai Umma ta taka da hanzari ta bi Hamza d'akinsa,yayin da Mummy da Aunty suka rufa mata baya...

Hamza suka tarar zaune ya dafe kansa saboda tsananin sara masa da yake tamkar ya cire, ga Hidaya ya shimfid'eta akan bed d'in sa tayi samb'al ko motsi bata yi,cikin matuk'ar fusata suna shiga Umma ta fizgo Hamza kamar ta kwad'a masa mari ta fara magana cikin fushi.

"Kai wai ba magana nake maka ba ne?me ya same ta ko bata da lafiya ne?ina mijin na ta yake? za ka yi magana ko sai na b'ata maka rai?"

Hawaye ne ya ratso fatar idanunsa,da k'yar ya iya duban Umma yayi magana a hankali.

"Eh bata da lafiya Umma,na kawo ta nan ne domin in yi tunanin asibitin da ya kamata na kaita,domin ba zan kaita asibitin da take ganin likitanta ba"

Umma ta sake magana cikin k'ulewa.

"Babu abinda yake b'ata min rai da kai Hamza irin wani zubin ayi maka tambaya ka bayar da amsa a baud'e,to koma dai menene ya faru ai bai kamata tana cikin wannan halin ka kawo ta gida ka shimfid'eta ba,wai menene yake faruwa yake faruwa ne?menene dalilinka na k'in kaita asibitin da take zuwa?wai shin ma ina Ibraheem d'in ya ke?"

Tambayoyin da Umma ta jero masa kenan,cikin matsananciyar damuwa ya dubeta ya ce.

"Ba zan kaita asibitin bane saboda wasu dalilai masu k'arfi,kin sani Umma Khaleel shine yake d'aukar d'awainiyar komai na Hidaya wajen kula da lafiyarta,to yanzu babu wata alak'a tsakaninsa da Hidaya da hakan zai cigaba da faruwa....

"Ban gane ba,wane irin babu wata alak'a tsakaninsu?ko ka manta cewa yanzu bata da wani makusanci da ya kaishi?ka manta cewar Ibraheem mijinta ne?"

Wani bak'inciki ya sauka a zuciyar Hamza,bai ma san ta yadda zai bud'e baki ya fad'awa Umma cewar Khaleel ya saki Hidaya har saki uku ba,matsawa yayi daga gaban Umma ya k'arasa gaban Mummy da ke tsaye idanuwanta akan d'iyar ta tana yi mata kallon yaushe gamo!kawai sai ya durk'usa gabanta cikin hawaye ya fara magana idanuwansa akan Mummyn.

"Kiyi hak'uri Mummy....a lokacin da kika bani d'iyarki kin bani ita ne cikin k'oshin lafiya da kuzarinta,har ma kika yi ta jaddada min cewar na rik'e miki ita amana bata da kowa...kar na bari a cutar da ita...na zama GARKUWARTA...sai gashi yau da na tashi dawo miki da ita kin ganta akasin yadda kika bani ita...ban rik'e miki amana ba Mummy...ban cancanta a kirani da GARKUWAR HIDAYA ba...

Salatin da Umma ta saka da k'arfi shine ya dakatar da Hamza daga maganarsa,hannayenta akanta idanuwa zuru zuru take duban Aunty da take sanar da ita cewar "Khaleel ya saki Hidaya saki uku" wata hajijiya ce ke kwasarta tana shirin kaita k'asa,tuni hawaye ya ciko idanuwanta ya fara kwarara kan fuskarta...

Kawai gani suka yi Mummy ta fara tafiya a hankali ta nufi gefen gadon da Hidaya ke kwance,a zatonsu gun Hidayar ta nufa,a maimakon hakan sai suka ga ta ci birki gaban wani hoto da ke kan bedside drawer,d'aukar hoton tayi ta k'ura masa idanuwa tana kallo cikin dukan zuciya,a hankali ta waiwayo ta dubi Hamza a rikice tayi magana karon farko.

"HAMZA GARKUWA,bayan kai da na gani a hoton nan,ga Hidaya a tsakiya,wanene wannan da ke gefen hoton kuma?"

Hamza ya kasa magana kai a sunkuye,sai Umma ce cikin hawaye ta ce.

"Shine Khaleel...abokin Hamza da aka d'aura musu aure a jiya shi da Hidaya"

Cikin tsabar tsoro Mummy ta ce.

"Yayi min kama da wata bak'ar fuska ne a idanuwa na,don Allah Umman GARKUWA sanar da ni wanene Khaleel?kuma wanene mahaifin sa?"

Cikin hawaye Umma ta sake magana.

"Ya kamata muyi hanzarin kai Hidaya asibiti saboda ko motsi bata yi,idan muka nutsu komai da kike buk'atar ji sai na sanar da ke"

Girgiza kai Mummy tayi,cikin wata irin murya ta ce.

"Ko sunan mahaifin Khaleel kad'ai ina so ki fad'a min a yanzu,ba zan iya jurewa zuwa lokacin da kike so ba"

"Sunan sa Alhaji MUDASSIR" Umma ta fad'a idanuwan ta akan Mummy"

Wata irin razana Mummy tayi ta saki wata k'ak'k'arfar k'ara kafin idanuwanta su k'ak'k'afe tayi baya tana shirin fad'uwa,da sauri Umma da Aunty suka tarota ta fad'i a jikinsu babu numfashi a tare da ita...


*******************


Kukan da Daddy ya fashe da shi shine ya sake jefa Khaleel cikin shakku da matsananciyar fargaba,ya tsurawa Daddyn na sa idanu yana jin kamar ya mace ya huta da k'unci da fargabar da ke addabar ruhinsa,sosai hawayen da Daddy yake yi ya sake jefashi cikin tunanuka barkatai,cikin raunin murya Khaleel yake ta rok'on Daddyn sa akan ya fad'a masa gaskiya,yana ta ambatar "Don Allah Daddy ka fad'a min....Don Allah ka fad'a min ya mahaifina..." amma ko kad'an Daddyn ya kasa bud'e bakinsa yayi magana sai kuka da yake yi yana rik'e da kafad'un Khaleel d'in.

A hankali Khaleel ya soma yunk'urawa yana niyyar tashi daga jikin mahaifin na sa,ya zame hannuwan Daddy daga jikinsa,da k'yar ya iya mik'ewa tsaye yana cije bakin sa,wata muguwar rama ta bayyana a gareshi yayi wani zuru zuru cikin lokaci k'ank'ani,yana layi kamar d'an maye haka ya wuce Daddy ya fara takawa a hankali,Daddy ya d'ago yana kallon bayansa cikin hawaye sosai,da k'yar ya iya bud'e baki yayi magana yana ambatar sunan d'an na sa.


"Khaleel...!

Khaleel ya k'i juyowa balle ya tsaya,ya cigaba da takawa a hankali yana had'a hanya tamkar ya kifa,Daddy ya sake d'aga murya ya ambaci sunansa da k'arfi.

"Khaleel...juyo ka zo gareni kaji Khaleel"

Duk da hakan bai juyo ba,illah cikin bedroom da ya nufa hankalinsa a tashe,ya bar Daddyn sa tsugune a wajen yana kuka cikin garari.

Kan gadon d'akin ya nufa,hannunsa dafe da k'irjinsa,zuciyarsa ciwo take sosai yana jin kamar ta faso k'irjin na sa,bai tab'a ganin mummunar rana irin wannan da ya rasa komai ba,shi yana jin tunda ya rasa Hamza da Hidaya a duniyarsa to ya rasa komai.

Gefen gadon ya zauna yana dafe kansa,bai san me ma zaiyi ba,d'ago shanyayyun idanuwan sa yayi ya zuba su akan wani hoto da ke gefen gadon,k'arami ne sosai kuma yanayin hoton yayi kama da irin hotunan da,hannun sa na karkarwa ya d'auko hoton ya tsura masa idanuwa yana kallo,hawaye ya sake tsinke masa suka fara sharara da gudun su,rungume hoton yayi a k'irjinsa yana kuka sosai,cikin k'aramar murya da bata fita sosai yake ce wa.

"Ina ma kina da rai ...ina ma kina duniya Mahaifiyata...ina ma baki tafi kin barni ba...da a yadda nake d'in nan gurinki zan zo...ki rungumeni jikinki ki rarrasheni ...ki kwantar min da hankali da kalamai masu dad'i ko zan ji sanyi a raina...sai dai kuma bakya nan ...kin min nisa mai yawa...kin tafi kin barni...gurin wa zanje a yanzu...?a lokacin da babu ke sai Allah ya bani Hamza...sannan ya k'ara min da Hidaya...yanzu gashi duk sun barni...saboda munin abin da na aikata...ni kuma k'addarata kenan...jarrabawata kenan...Innalillahi wa inna ilaihir raji'un....!

Khaleel kuka yake sosai kamar ransa zai fita,bai tab'a tsintar kansa cikin kewa da rauni irin lokacin ba,ji yake kamar shi kad'ai yake rayuwa a filin duniya,ya rasa ina zai jefa kansa yaji sanyi,sai da yasha kukansa ya k'oshi sannan ya iya ajiye hoton mahaifiyar sa,alokacin ne idanuwan sa suka ankara da wani hoto da takarda a gefensa,mik'a hannu yayi cikin sanyin jiki ya d'auki hoton,babu wanda idanuwansa suka gani sai mahaifinsa a jikin hoton,hoto ne dad'ad'd'e tun zamanin yana yaro k'arami,mamakin yadda akayi ya samu hoton a wajen yake,domin shi dai bashi hoton ma kwata kwata,to ya akayi aka same shi har kan shimfid'ar su?

Wani tunani ne ya d'arsu a ransa,da gaggawa ya ajiye hoton ya d'auki takardar da yake ji ita ce musababbin komai,jikinsa na rawa ya warware ta ya zuba mata idanuwansa k'irjinsa na tsananin bugu,fatansa kawai ya karanta abin da takardar ta k'unsa kafin numfashin sa ya bar gangar jikinsa.


*Assalamu Alaikum ya ke y'ata*


*Na san a lokacin da wannan takarda zata riskeki kin girma,kin kai munzalin da hankali ya shigeki tare da nutsuwa,kin san fari kin san bak'i,kin san abu mai kyau kin san mara kyau,k'ila a lokacin da zaki karanta takardar ina duniya ko kuma nima na mutu kamar mahaifinki,yake y'ata,ki sani cewar ban guje miki don wani abu ba,illah don son tseratar da rayuwarki daga hannun wani azzalumin mutum,wanda shine ya kashe mahaifinki,haka nan kuma yake so ya kashe mu ni da ke,na zab'i in guje miki in kai ki gidan marayu ne saboda kar azzalumin mutumin nan ya bibiyeki har ya samu nasara a kanki,domin hankalinsa ba zai tab'a kaiwa ya fahimci kina gidan marayu ba,ni na yarda in mutu idan har ke zaki rayu,domin ki d'aukar mana fansar abinda wannan azzalumin mutum yayi mana,zan tafi in da ba zaki ganni a kusa ba,idan har ina raye lokacin da ya kamata na bayyana a gareki zan bayyana,na san za ki shiga cikin k'unci da gararin rayuwa saboda rashin kowa a tare da ke,gashi kina da lalurar da kike buk'atar matallafi a tare da ke,amma zan barki a hannun Allah,domin babu wanda zai kula da ke sama da shi,shine ya halicceki ya bani ke kuma ya fini sonki*

*Sannan buk'atata a gareki ita ce,ina so in baki umarni a matsayina na mahaifiyarki,abu d'aya za ki yi ki inji a raina cewar kin biyani d'awainiyar da nayi a kanki,wajen d'aukar cikin ki da haihuwarki da rainonki,wannan buk'ata ba wata bace illa ina son ki kashe min wanda ya kashe mahaifinki da hannunki Hidaya,ga hotonsa nan zan bar miki domin ya zame miki jagora wajen gane ko wanene shi,da hannunki nake son ki d'aukar min fansa ki kashe shi kar ki barshi da rai,idan har kikai min haka ko da bana duniya zanyi farinciki da ke,zan san na haifi me share min kukana,zanji a duniya ba a yi wata y'a mai biyayya kamarki ba,wannan hoton mutumin da zaki gani tare da takardar nan shine wanda nake so ki kashe,domin azzalumi ne,mugu ne,mak'etaci ne*


*Zan tafi na barki cikin tsananin sonki da k'aunarki,ina fatan Allah ya kula da ke ya tsareki da tsarewar sa*


*Daga Mahaifiyarki*


Takarda k'arama,amma girmanta yafi girman dutsen dala da gorondutse a idanuwan Khaleel,shike nan ta tabbata Mahaifinsa shine ya kashe mahaifin matarsa?Wannan bala'in daman Hidaya ta gani ta gigice haka har ta aiwatar da abin da ta aiwatar?in haka ne Hidaya bata da laifi kenan?domin idan shine hakan ta faru da shi kisan ma zai iyayi ! mutuncin Daddyn kawai aka tab'a masa ya yanke d'anyen hukuncin da bashi da misali,to ina ga kashe masa shi akayi?kuma yayi ido biyu da wanda ya kashe masa mahaifin?me zai faru kenan?

Bai tab'a jin nadamar zuwansa duniya irin yau ba! bala'in ciwo da yake ji a zuciyar sa ya kai mak'ura,wani irin gigitaccen amai ne na tashin hankali ya yunk'uro masa da k'arfi,take ya fara kelayashi idanuwansa na k'ak'k'afewa,a maimakon aman ruwa ko na abinci sai ga jini na fitowa har ta hancin sa,har da guda guda,malelekuwa kawai yake yana rik'e k'irjinsa da yake jin yayi masa mugun nauyi,adai dai lokacin aka banko k'ofar d'akin aka shigo,Daddy ne da Aunty Kubra suka shigo a gigice,shigowarsu kuma yayi dai dai da fad'owar Khaleel daga gadon zuwa k'asa,jini na zuba yayin da idanuwan sa suka yi sama,Numfashin sa ya bar gangar jikinsa....!


*Kuyi hak'uri yau kad'an nayi,bana jin dad'i ne ina ciwon kai,ku tayani addu'a*👏


Comments
share
vote
pls


*GARKUWA BIYU*


BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter 18 · 0% Book details