BABI NA CASA'IN DA BAKWAI DA NA CASA'IN DA TAKWAS
Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 17 min read
*** Ranar da aka yi zama na biyu a kotu sai da Hidaya ta razana da taga Khaleel,saboda wata irin rama da taga ya sake yi,idanuwansa kuwa sanye suke da glass ba a ganin k'wayar idanuwan kwata kwata,shi ba gwanin sanya glass bane ma ,amma ranar ya sanya domin b'oye idanuwansa,hatta Hamza sai da yayi masa tambaya akan ramar da yaga yayi,kawai murmushi yayi yace masa bayajin dad'i ne,ya taya shi addu'a kawai.
A ranar an cigaba da gabatar da shaidu ne akan shari'ar,inda ba a samu wata cikakkiyar shaida daga Alhaji Mudassir ba,saboda duk tsawon wannan lokacin Alhaji Maude ya k'i yarda suyi magana balle ya samu wani abin daga gareshi,ta b'angaren Mummy dai an samu shaidar wannan jaka da ta binne wadda Alhaji Taufik' ya bawa Sulaiman,shi kuma ta b'angaren Alhaji Maude an kamo mutanen da ake zaton su ya tura suka yi kisan,kuma har da su akayi zaman kotun,dukkansu suna tsaye a b'angaren tuhuma,kuma duk wata tambaya da akayi musu sun dage ne akan su dai Alhaji Mudassir ne ya saka su aikata kisan,amma babu ruwan Alhaji Maude a ciki,hakan ya faranta ran Alhaji Maude,ya tabbatar shine ke da nasara akan shari'ar domin Mudassir bai da wata gamsasshiyar shaida da zai bayar,shi kam Daddy rud'ewa yayi sosai,domin dai ya san bashi ne ya aikata hakan ba,shi kansa Khaleel shari'ar ta fara bashi tsoro,da farko yana ta hango nasara,amma a yau duk jikinsa yayi sanyi sosai,daga nan ne Alk'ali ya d'aga shari'ar zuwa wata d'aya mai zuwa,kuma rana ta k'arshe da zai yanke hukunci,dan haka ya umarci kowane b'angare na masu k'ara da wanda ake k'ara da su gaggauta samo shaidu k'warara da manyan hujjoji wanda kotu za ta yi la'akari da su,a take Alk'ali ya buga guduma kowa ya mik'e tsaye.
Bayan mutane sun firfito waje ne aka sake fito da Alhaji Maude da Daddy da wad'annan mutane da aka kamo,za a wuce da su gidan Ajiya kafin ranar da za a dawo kotu,anan ne Khaleel ya sake neman alfarmar magana da mahaifinsa wanda da k'yar ya samu suka yarda suka basu minti biyu suka koma gefe tare da wani d'an sanda da ke rik'e da bindiga,tun kafin ma Khaleel yayi magana Daddy ne ya fara dubansa ya ce.
"D'ana kana cikin damuwa ko?domin na lura duk lokacin da kake cikin yanayi na damuwa ka kan rufe idanuwanka dan kar a gane yanayin ka,to amma ni naji a jikina akwai damuwa a tare da kai,ga kuma rama da naga ka kuma yi sosai,me yake faruwa da kai ne?don Allah ka taimaka ka rage wannan damuwar,in dai don wannan shari'ar ne in sha Allahu mu ke da nasara,Allah ba zai tab'a tab'ar da GASKIYA ba,domin kullum GASKIYA ce a gaba da K'ARYA Khaleel.
Murmushi Khaleel yayi hawaye na tawo masa amma ya shanye,ba zai iya misalta damuwar da ke ruhinsa ba,tabbas yana cikin damuwa mara iyaka,sai kawai ya ce wa Daddy "Babu abinda yake damuna Daddyna,kawai dai bani da lafiya ne shiyasa kaga yanayi na ya sauya,amma na fara jin afuwa ma a jikina"
Daddy ya rik'o hannun Khaleel yana masa sannu,sannan ya ce "To kaje kaga likitanka mana,bana son a samu matsala har ciwonka ya tashi,kaga dai abinda ke gabanmu akan shari'ar nan" Sai Khaleel ya jinjina kai da fad'in "In sha Allah babu abinda zai faru sai alkairi" sannan ya zarce da cewa "Daddy Kayi k'ok'ari ka samu wani abu daga Alhaji Maude ko mutanen da za a had'aku da su a yau,saboda bamu da wata cikakkiyar hujja da za mu gabatar,amma tunda akwai wannan na'ura a tare da kai to na san za ta yi mana amfani sosai muddin kuka yi magana kai da Alhaji Maude" Daddy ya fara bawa Khaleel amsa sai wannan d'an sandan ya matso yana fad'in "Lokaci ya cika" sannan ya sanya Daddy a gaba suka wuce zuwa mota,yayinda Khaleel ya bisu da kallo zuciyarsa a jagule.
Tun daga lokacin su Khaleel suka maida addu'a aikinsu,sosai suke kaiwa Allah kukansu akan ya basu nasara da sa'a akan shari'ar,wata d'abi'a kuma da Khaleel ya shigo da ita shine d'auke k'afa daga gidan su Hamza,kwata kwata ya daina zuwa ganin Hidaya,sai dai ya kan yi mata aike da dukkan abinda ya san tana buk'ata har ma wanda bata buk'ata ba,Umma har cigiyarsa take amma Khaleel ya kasa zuwa kullum sai yace abubuwa sun masa yawa,duk sai Hamza yake jin sa cikin wata matsananciyar damuwa da kewa,hakan ya sa yaje ya samu Khaleel akan ya fad'a masa dalilin sauyawar sa,amma Khaleel ya ce shifa babu komai,kawai yanayin rayuwa ne ya kawo hakan,tilas Hamza ya hak'ura ya barshi ba dan ya so hakan ba,sai dan yayi iya yinsa amma Khaleel d'in ya kasa fad'a masa damuwar sa.
*************
*RANAR ZAMAN K'ARSHE A KOTU*
Dukkan wanda zai halarci kotun a ranar ya wayi gari ne da fargabar abinda zai afku,Nasara ko rashin nasara?hakan ya sa kowa jikinsa yake a sanyaye,dan tun safe Hamza ke jin matuk'ar fad'uwar gaba mai girma,har ya kasa yin shiru ya fad'awa Umma,sai tace ya dinga addu'a zaiji sauk'in abinda yake ji,shi ma Khaleel haka ya samu kansa da fad'uwar gaba sosai,sai da Aunty Kubra ta dinga k'arfafa masa gwiwa sannan ya d'an saki ransa.
Hidaya kuwa an so hanata zuwa kotun ma saboda yadda cikinta yayi wani irin girma kamar cikin wata tara,alhali cikin wata bakwai ne kacal,da k'yar take iya d'aga k'afa saboda girman cikin hakan yasa Ya Hamza yace tayi zamanta a gida ba sai taje ba,sai ta fara rok'onsa har da kukanta wai ita dai yayi hak'uri ya bari ta je taga yadda za a yankewa Alhaji Maude hukunci a gabanta,har Mummy sai da tasa baki tace "Hidaya me yasa bakya jin magana ne,tunda Hamza yace ki zauna a gida to ki zauna mana,yanzu a haka zaki shiga kotun da wannan d'irmemen cikin?ke ana guje miki wahala amma bakya ganewa"ganin Mummy nayi wa Hidaya fad'a hakan yasa Umma ta saka baki ta ce" Don Allah Zainab ku rabar min da y'ata haka,tunda tana son zuwa kuma zata iya to ku barta taje mana,ai gara mu tafi da ita da a barta a gida ita kad'ai" sai Mummy da Hamza suka yi shiru ganin Umma ta goya mata baya,ita kam Kakar Hidaya dariya ta dingayi tana tsokanar Hidaya da mai raguwar zuciya,wai ita ba jaruma ba ce tunda abu kad'an ke sanyata kuka,sai Aunty Sajida ce ke kare Hidayan tana cewa"To ai yawan kuka shine yake nuna mutum yana da cikakken imani a zuciyar sa"
A lokacin da motar su ta tsaya a harabar kotun dai dai lokacin ma motar Khaleel ta tsaya,Hamza ya fito ya bud'ewa su Umma k'ofa suka firfito,a lokacin Khaleel ya k'araso gare su shi da Aunty Kubra,ya tsuguna yana gaida su Umma,su Mummy suka amsa yayinda Umma tace "Ba zan amsa gaisuwarka ba Khaleel tunda ka gujemu,yaushe rabon da na ganka?"ya sunkuyar da kai yana shafa wuyansa yana d'an murmushi yana bawa Umma hak'uri,ta d'an yi dariya tana fad'in "To shikenan na hak'ura,amma sai kayi min alk'awarin za ka dinga zuwa ina dama maka kunun gyad'a ka dinga sha ko dan ka maida jikinka,wannan ramar da kake yi tayi yawa Ibraheem,sai k'arewa kake kamar ruwan aski" Dariya yayi sannan yace wa Umma in sha Allah zai dinga zuwa.
Bayan su Umma sun gaisa da Aunty Kubra sai suka d'unguma suka wuce cikin kotun,sai a lokacin Hamza ya zagaya ya bud'ewa Hidaya b'angaren da take zaune,ta sako k'afafuwanta waje tana kumbura baki wai ya manta da ita cikin mota bai bud'e mata da wuri ba,harararta yayi yana fad'in "Sai ki fito ko" da k'yar ta yunk'ura ta iya fitowa daga motar tana kwab'e fuska.
Tana fitowa Khaleel ya bita da wani irin kallo yana mamakin yadda cikinta yayi girma sosai,ko dan ya jima bai ganta ba ne?ita ma kallonsa ta dinga yi kamar ta fashe da kuka,Uncle Khaleel d'in ta duk ya zabge ya k'are,wanda bai masa cikakken sani ba ba lallai ya shaida shi ba tsabar ramar da ya kwantsama,hakan ya sa ta tsura masa idanu kawai tana kallonsa,sai shine ya kawar da shirun ta hanyar duban Hamza yace masa.
"Aboki haka Hidaya tayi nauyi daman?"
Hamza ya harari Hidaya saboda haushin da ta ba shi,sannan ya juya yana rik'o hannun Khaleel ya ce.
"Eh fa,amma da yake yarinyar nan kunnen k'ashi ne da ita nace mata ta zauna a gida kar tazo shine har da kuka,ita kuma Umma ta goya mata baya"
Khaleel yayi murmushi kawai sannan ya ce.
"To meye abin fushi Aboki,ai gara ka barta ta zo taga k'arshen shari'ar ko?"
Hamza ya waiwaya ya dubi Hidaya ya ce.
"Kalli fa Khallel,kalli yadda take d'aga k'afa da k'yar,haka kawai salon ta wahalar mana da d'an mu ko y'ar mu" Sai Khaleel ya fashe da dariya,Hidaya ta bishi da kallo ganin kyawun da dariyar tayi masa,sai taji yana cewa Hamza " Au wai kai ta jaririnka kake ma ko Aboki?ni kam ta ita nake,domin ita ce bana son ta wahala ba jariri ko jaririya ba"
D'an k'aramin tsaki Hamza yayi yana fad'in "daman ai bakin ku d'aya kai da ita" Khaleel ya cigaba da dariya yayin da Hidaya ke wa k'eyar Hamza gwalo ganin Khaleel ya goyi da bayan ta.
A tsakiya suka saka Hidaya suna takawa a hankali suka nufi cikin Kotun,yayin da Khaleel yayi k'asa da murya ya ce wa Hidaya.
"Ki tayani addu'a yau burina ya cika,ina son yau suna na ya tashi daga Ibraheem Khaleel ya koma GARKUWAR HIDAYA.
************
Bayan Alk'ali ya shigo an mik'e an yi gaisuwa kowa ya zauna,a lokacin ne lauyoyi suka fara mik'ewa suna gabatar da kansu gaban mai girma mai shari'a,kotun tayi tsit mutane dank'am ta cika tayi taf,daga nan ne kuma shari'a fa ta fara d'aukar d'umi in da kowane b'angare ke k'ok'arin bayar da hujjar da za a gamsu da ita,yayin da Khaleel ya isa gaban Alhaji Maude ya tsaya,Alhaji Maude ya bishi da wani kallo na tsana a yayinda Kaleel d'in ke ce masa "Alhaji Maude ka ce ba kaine ka sa aka kashe Sulaiman ba,kuma ba kaine ka b'atar da Oga Taufik' ba a wancan lokaci,amma alamu da dama sun nuna kana da hannu dumu dumu a cikin aikata hakan,me yasa ka tsaya jayayya da kotu ka kasa amsa laifinka?kana son ka bawa kotu wahala ne ko me?"
Alhaji Maude ya ce "Kamar yadda na fad'a a baya yanzu ma haka zan fad'a,ba nine na sa a kashe Sulaiman ba,kuma ai ko da aka tambayi wad'anda suka yi kisan sun fad'a da bakinsu cewar Mudassir ne ya saka su,dan haka Alhaji Mudassir ke da alhakin kisan ba ni ba"
Sai Khaleel ya juya ya kalli Alk'ali ya ce.
"Ya mai shari'a,Alhaji Maude kawai yana so ya wahalar da kotu ne,amma tabbas shine ya sa akayi wannan kisan bi sa ga wata k'wak'k'warar shaida da zan bayar a yanzu"
"Objection my lord" abinda Lauyan Alhaji Maude ya fad'a kenan yayin da ya mik'e tsaye cikin huci,sannan ya zarce da ce wa" Ya kamata Lauyan masu k'ara ya daina tabbatar da cewar Alhaji Maude shine ya aikata hakan,tunda har yanzu zargi ake yi ba a tabbatar ba, Na gode"
Alk'ali ya tsawatar wa Khaleel,Sai Khaleel ya bayar da hak'uri da fad'in zai gyara,daga nan kuma ya nemi da a bashi dama domin ya gabatar da hujjar sa ta k'arshe,wadda yake ganin ita ce za ta kawo k'arshen komai akan shari'ar,Alk'ali ya ce da Khaleel "An baka dama barrister Ibraheem Khaleel"
Matsawa yayi kusa da Daddy ya karb'i wannan na'urar,sannan ya kaita gaban Alk'ali a matsayin hujjar sa,kotu tayi tsit yayinda alk'ali ya danna wannan na'ura,bayan tayi shuuuuu na tak'aitaccen lokaci sai ga magana ta fara fitowa,in da muryar Daddy ke magana tana cewa.
"Yanzu Maude amanar da ke tsakanina da kai ya kamata kayi min haka?me nayi maka a rayuwa kake neman mak'alamin sharrin da bani na aikata ba?a dalilin me za ka ce nine na sa aka kashe Sulaiman?bayan tun a wancan lokacin ka san ni ne nace maka bana son kisa ya shigo cikin lamarin"
Maganar Daddy ta tsaya,sai dariyar Alhaji Maude ta fito da k'arfi hahahahahaha, kafin kuma a jiyo muryarsa yana mayarwa da Daddy raddi da cewa.
"Kai Mudssir har kayi k'warin wuyan da za ka ce za ka ja dani ?ni zaka tonawa asiri saboda kana tunanin d'anka Lauya ne zai kare ka?to bari kaji in gaya maka,duk yadda kake tunani na na shallake hakan wallahi,kuma Alk'awari nayi yadda naga bayan Taufik' da Sulaiman kaima sai naga bayanka,daman ni ba son gaskiya nake maka ba,dan haka ka shirya kaima sai ka bak'unci lahira kamar yadda Taufik' da Sulaiman suka bak'unta,nine da nasara a wannan shari'ar,wannan Alk'awarina ne Mudassir" ya sake fashewa da dariya.
Sai ga muryar Daddy cikin Kuka yana cewa.
"To me yasa ka zab'i aikata hakan?me yasa kake so kaga bayana?me nayi maka?
Alhaji Maude ya ce "Babu abinda kayi min,kawai ganinka ne bana so na dinga yi a duniyar,dan haka nake so ka kauce ka bani wuri,kuma tabbas nine na sa aka sace Taufik',kuma na sanar da kai cewar Kurciya me dogon zango na sa akayi masa,da yake kai me tosasshiyar k'wak'walwa ne sai ka kasa fahimta tun a wancan lokacin,abin da baka sani ba tun a daren bayan na sa an sato shi da hannuna na kashe shi,kuma muka je muka cillashi cikin teku ta yadda halittun cikin ruwa za su cinyeshi ba za a sake jin d'uriyarsa ba,haka nan nine na sanya aka je aka kashe Sulaiman,shi ma da hannuna na jefa gawarsa cikin teku bayan sun kawo min gawarsa,kuma nine na sa a b'atar da iyalin Sulaiman,amma sai nayi matuk'ar mamaki da naga sun bayyana a yanzu,hakan yasa nayi tunanin wanda na bawa aikin b'atar da su ne baiyi dai dai ba,kuma shima ina nan zuwa gareshi sai nayi masa hukunci kan abinda ya aikata,sai naga bayansa bayan naga bayanka,dan haka ka k'ara sani Mudassir,nine da nasara a wannan shari'ar,domin baka da wata hujja da zaka gabatar gamsasshiya da za ta k'waceka,kana gani zan yi free,kai kuma a yanke maka hukuncin da ya dace da kai"
Iya nan maganar ta tsaya sai dariyar Alhaji Maude dake tashi cikin na'urar,b'angare d'aya kuma kukan Daddy na tashi.
Alk'ali na kammala ji sai kotu ta d'auki hayaniya da surutai,yayinda Alhaji Maude ya tsorata ya firgita ya gigice,banda gumi babu abinda yake yi.
Alk'ali ya tsawatar tare da buga guduma,kotu tayi tsit kowa na mamakin wannan dambarwa,Zuciyoyin su Mummy K'al kamar madara saboda jin dad'in abinda ke faruwa,yayin da Alhaji Maude da lauyansa da mutanen da suka yi kisan suka yi tsuru tsuru kamar mage a kwali,sunyi matuk'ar tsorata da wannan gundumemiyar shaida da Khaleel ya bayar,Lauyan Maude bak'inciki kamar ya kashe shi,ya akayi Alhaji Maude ya saki baki ya dinga kwarara jawabai har haka? Ni kuwa a zuciyata nace Hakkin rai ne ,dan hakki ba zai tab'a barinsa ba.
A lokacin ne Khaleel ya matsa gaban wad'annan mutane guda biyar,sannan ya dube su ya ce.
"To ga dai maganar da oganku Alhaji Maude yayi,ya tabbatar da shine ya kashe oga Taufik',kuma shine ya sanya kuka kashe Sulaiman,da ragowar k'ulla k'ullar da kuka aikata,shin har yanzu kuna kan bakarku na cewa ba laifin Alhaji Maude ba ne?ko kuwa za ku bi hanyar GASKIYA ku bar dokin K'ARYA? ya rage ruwanku ku fad'i gaskiya domin ku tsira daga la'antar da Allah mad'aukakin sarki zai sanya a kanku,domin Allah da kansa yake ce wa a cikin littafinsa mai girma.
"فنجعل لعنت الله على الکذبين"
(Sannan kuma mu sanya tsinuwar Allah akan mak'aryata).
Duk wata shaida da zaku bayar a halin yanzu to ina baku shawara da ta kasance gaskiya ce.
"واجتنبوا قول الزور"
Allah ya ce (ku nisanci fad'ar shaidar zur).
"و لا تکتموا الشھدة,و من يکتمھا فإنه ءاثم قلبه ,والله بما تعملون عليم"
( Kada ku b'oye shaida,duk kuwa wanda ya b'oye ta,to hak'ik'a shi mai kangararriyar zuciya ne,kuma Allah masanin abin da kuke aikatawa ne).
Ku sani cewar wannan rayuwar za ta k'are,za ku je gaban ubangijin ku kuna masu tab'ewa idan har kuka b'oye gaskiya,kar ku d'auka za ku dawwama ne,wallahi duk wani abu da yake doron k'asa mai k'arewa ne.
"کل من عليھا فان ,و يبقى وجه ربك ذو الجلل و الإکرام"
(Duk wanda yake kan doron k'asa mai k'arewa ne.fuskar ubangijinka ce za ta wanzu,ma'abocin girma da d'aukaka).
Yanzu zab'i guda biyu ke gareku,imma ku fad'i gaskiya ku tsira gurin ubangijinku ku samu aljannan mad'aukakiya,imma ku fad'i k'arya kuje kuyi wata irin rayuwa ta danasani bayan mutuwar ku,tun kafin ma kuje gaban Allah ku fara had'uwa da fitinar k'abari,ku had'u da azaba,kafin Allah ya tashi duk wad'anda suka mutu a k'aburburan su,Allah ya tara bayinsa domin yin hisabi a gare su, ku da kuke tunanin Alhaji Maude zai ceceku babu abinda ya isa yi a wannan rana domin shi ma ta kansa yake, kuma a ranar ne kowa za a nuna masa aikin da yayi imma na alkairi ko na sharri,daga nan kuma a fara hisabi,muminai su karb'i littafin su da hannun dama,kafirai da munafukai su karb'a da hannun hagu,Allah ta'ala yana ce wa.
"ووضع الکتب فترى المجرمين مشفقين مما فيه و يقولون يويلتنا مال ھذا الکتب لا يغادر صغيرة و لا کبيرة إلا أحصھا ووجدوا ما عملوا حاضرا ولا يظلم ربك أحدا"
(Kuma za a aje littafi,wannan lokaci za ka ga masu laifi a tsorace saboda halin da suke ciki.kuma suna cewa,"Kaicon mu! wane irin littafi ne wannan ?baya barin k'aramin laifi da babba sai ya lissafa su.Kuma suka samu abin da suka aikata a halarce,Kuma Ubangijin ba zai zalunci wani ba).
Daga nan sai hawa kan sirad'i,gada ce da take k'ark'ashin Jahannama,wannan gadar ta fi gashi sirantaka,kuma ta fi takobi kaifi,muminai za su wuce ta kan wannan sirad'i kamar walk'iya,wasu kamar iska,wasu kamar ingarman doki,wasu su tsira su kub'uta,wasu kuma su kukkuje a wuta,har na k'arshe su zo da jan ciki.
Haka y'an aljanna za su shige cikinta suna masu murna da farinciki,Allah zai kora y'an wuta zuwa jahannama jama'a jama'a (Allah ka kiyashe mu 👏😭)
Ya ku bayin Allah kuji tsoran Allah ! ku sani mafi darajar mu a wajen Allah shine mafi tsoran sa,duk wanda aikinsa ya dak'ilar da shi to dangantakarsa ba za ta ciyar dashi gaba ba.Ku sani Allah yana lissafa muku ayyukanku da kuke yi,dan haka duk wanda ya samu alkairi to ya godewa Allah.Wanda kuma ya sami kishiyar wannan to kar ya zargi kowa sai kansa"
Tunda Khaleel ya fara jawabi kotun tayi tsit,masu kuka na yi,wato masu k'ara jin imani a zuciyar su kenan,sai ga wad'annan mutane guda biyar sun fashe da kuka matsananci,yayin da nan take suka zab'i fad'ar GASKIYA domin su tsira daga azabar Ubangiji ranar lahira,a take kuma suka yi bayani akan cewar tabbas Alhaji Maude ne ya saka su aikata wannan d'anyen aiki,kuma ya umarcesu akan su mak'alawa Alhaji Mudassir alhakin abun,Mai girma mai shari'a ya sauke numfashi bayan ya kammala jin jawaban su,sannan yayi shirin yanke hukuncin da ya dace da shari'ar,Zuciyar Alhaji Maude kamar ta fito dan bak'inciki,bai tab'a tunanin talala Mudassir yayi masa ba,bai tab'a sanin ya d'auki maganganun da suka yi ba,wata tsanar Mudassir ta sake linkuwa a ransa,yana ji a zuciyarsa ko me za a yi ba zai bar Mudassir ba sai yaga bayansa,zuciyarsa ta taurara k'warai da gaske.
Alk'ali yayi jawabai Sosai,sannan ya gabatar da hukunci kamar haka:
Alhaji Mudassir an yanke masa hukuncin d'aurin shekaru goma gidan yari tare da aiki mai tsanani,bi sa ga yadda aka had'a baki da shi wajen cutar da Oga Taufik' da Sulaiman.
Mutane guda hud'u daga cikin mutane biyar d'innan an yanke musu hukuncin d'aurin rai da rai,saboda da su aka had'a baki wajen kisan Oga Taufik' da Sulaiman.
Sai ragowar mutum d'aya daga cikinsu wanda da hannunsa ya kashe Sulaiman,shi kuma da shi da Alhaji Maude an yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya,saboda sune suka yi hukuncin da hannunsu.
Sannan yayi hukunci akan dukiyar da Oga Taufik' ya bari,akan a nemo danginsa na nesa domin a raba ta kaso uku kamar yadda yace,danginsa suna da kaso d'aya,su Mummy da Hidaya na da kaso d'aya,sai kuma kaso d'ayan a kai gidan Marayu.
Kotu ta d'auki kabbara da wannan hukunci da aka zartas,yayin da Hidaya ta d'aga murya da k'arfi ta mik'e tsaye ta ambaci sunan Khaleel tana hawaye,ya waiwayo yana dubanta fuskarsa cike da murmushi,sai ta d'aga masa hannu tayi masa jinjina,sannan ta fad'a da k'arfi kowa yaji,ta ce "Lallai yau ka amsa sunan GARKUWAR HIDAYA,Uncle Khaleel a yau kaima ka za ma GARKUWA TA"
A d'imauce kowa ya maida hankalinsa b'angaren da Alhaji Maude yake,ganin ya fizge bindigar hannun d'an sandan da ke kusa da shi ya ture shi k'asa,sannan ya saita Alhaji Mudassir da bindigar yana faman nishi kamar kumurci,dukkan mutanen da ke wajen mik'ewa suka yi cike da firgici,Mai shari'a ya dinga bawa Alhaji Maude umarnin ya ajiye bindigar hannunsa,kar yayi harbi da ita a kotu yake,amma Alhaji Maude ya cigaba da zare idanu yana kallon Daddy da ya d'aga hannu sama,take Alhaji Maude ya fara magana cikin tsawa.
"Duk wanda ya motsa sai na harbeshi,yau k'arshenka ya zo Mudassir,za ka fara mutuwa kafin ni na mutu,wallahi ba zaka rayu a duniya ni na mutu ba,yadda ka tonamin asiri nima sai naga bayanka kafin kaga bayana" Ya sake saita bindigarsa saitin da Daddy yake ,Alk'ali na magana amma inah ,Alhaji Maude niyyar harbi kawai yake,a dai dai lokacin da yake niyyar d'ana kunamar bindigarsa Hamza da Khaleel suka fara takowa suna nufo in da Daddy yake,Alhaji Maude yayi magana cikin kakkausar murya.
"Duk wanda ya matso inda yake tare zan harbe ku,dan haka ku barni na aiwatar da abinda nayi niyya" a lokaci d'aya Hamza da Khaleel suka nufi Daddy suna shirin tureshi saboda kar harbin ya same shi,a lokacin ne kuma Alhaji Maude yayi harbin ,k'arar harbin da ta gigita kotun,ganin mutum d'aya daga cikin mutane uku ya fad'i alamar shi harbin ya sama,sai ga Hidaya ta k'wallara wata irin k'ara da ta sake hargitsa mutanen kotun,take kuma ta fad'i rub da ciki akan cikin ta kafin ma a taro ta......😭
Shin wa harbin ya samu? Alhaji Mudassir? Khaleel? ko Hamza? 😭😭😭
Comments
Share
Vote
Pls
*GARKUWA BIYU*
BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️