BABI NA CASA'IN DA TARA DA NA D'ARI
Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 29 min read
*GA DUK WANDA YA KARANTA SHAFIN NAN TO YAYI MIN AFUWA*👏👇
***K'arar wani harbin ne ya sake gigita kotun,sakamakon wani d'an sanda da ya harbi hannun Alhaji Maude da ke k'ok'arin sake yin wani harbin,ganin harbin da yayi ba Daddy ya sama ba,take bindigar hannun Alhaji Maude ta fad'i k'asa,yayinda hannunsa ke wani irin karkarwa yana ihu saboda azabar da ta ratsashi,kafin me y'an sanda sunyi kansa sun dak'ume shi.
Khaleel kam a jikin Hamza ya fad'i sakamakon shi harbin ya samu a daidai kafad'arsa ta hagu,tuni jini ya fara wanke jikinsa har ma da jikin Hamza da ke rik'e da shi,wani irin ihu Hamza yake yi yana jijjiga Khaleel wanda bai tab'a yi ba,Daddy ma rik'o Khaleel yake yi yana wani irin kuka da ihu yana ambatar sunan sa,amma Khaleel mirgina kai kawai yake a k'irjin Hamza yana ambaton Allah,kafin kuma Numfashinsa gabad'aya ya d'auke ya sandare a jikin Hamzan,ganin haka take Daddy ya fad'i ya suma a wajen,Hamza kam da ya d'imauce ihu kawai yake yana fad'in "Khaleel d'ina ka tashi,please ka bud'e idanuwanka,Jama'a don Allah ku taimaka min...
Gabad'aya Hamza neman rasa hankalinsa yake yi.
Can gefe ma Fad'uwar da Hidaya tayi akan cikinta sai ga jini ya b'alle mata,kuma ita ma a take ta suma,su Umma na kanta sai kuka suke yi ganin bata numfashi,kowa ya rud'e ya gigice ,dan wasu tuni suka shige k'ark'ashin kujerun da ke kotun saboda razanar da harbin ya haifar musu,yayinda da yawa mutanen da ke cikin kotun sai da suka yi fitsari a wando tsabar tsoro.
A take aka d'ebi Khaleel da Hidaya aka yi asibiti da su, har ma da Daddy da yake kan kulawar y'an sanda Aunty Kubra kuka take kamar ranta zai fita,abubuwa duk sun cab'e mata,ga rashin miji na tsawon shekaru da zata yi,ga kuma k'addarar da ta samu Khaleel,wanda shi zata kalla ta dinga jin dad'i tunda babu fuskar mahaifinsa a kusa da ita.
Likitoci sun karb'i Khaleel da Hidaya da hanzari,in da aka nufi wani b'angare da Khaleel domin cire masa harsashin da ya huda kafad'arsa,Hidaya kuma akayi emergency da ita dan ceton rayuwarta da abinda ke cikinta,sai dai abin ya ci tura,domin Hidaya na cikin matsanancin halin da ko dai a rasata ko a rasa abinda ke cikinta,Lokacin da Likita yayi musu bayanin halinda ake ciki dukkansu kuka suka saka,Hamza ya fad'i k'asa cikin tsananin tashin hankali ya d'aga hannayensa sama yana wani irin kuka idanuwansa tamkar su zazzago,fad'i yake.
"Allah kaine Allah,ina rok'onka ka tak'aita min duk wata k'addara da jarrabawa da za ta sameni a yau....Allah ka ceto min ran Hidaya da Khaleel...Allah ni mai hak'uri da biyayya ne akan duk abinda za ka d'ora min...kuma ba ka d'orawa bayinka abinda ba za su iya d'auka ba...ina rok'on ka Allah kasa kar wannan rana ta zama mafi bak'i a duniyata da rayuwata...wad'annan mutane guda biyu bayan mahaifiyata bani da tamkar su...Allah kai ka had'ani da su har ka sanya min k'aunarsu a ruhina..k'auna mara yankewa...k'auna mai girma...Ya Allah ka basu lafiya....
Sai ga Hamza yana shirin kifewa a k'asa tsabar kuka da tashin hankali,Umma ta taroshi tana rik'eshi jikinta tana kuka,Hamza ya cigaba da kuka yana fad'in.
"Ummana Hidaya da Khaleel...bana so na rasa su...don Allah Umma...
Ya kasa k'arasa maganar saboda abinda ke tokare k'irjinsa.
Mummy kuka,Aunty Sajida kuka,ita kam y'ar tsohuwa kakar Hidaya tafi kowa gigicewa da ganin wannan tashin hankali,sau biyu tana tsula fitsari a wando,yanzun ma tana lakure a gefe jikinta na tsuma sai zare idanu take tana kuka.
Lokacin ne Doctor ya fito ya nemi ganin mutum d'aya wanda ya fi kusanci da Hidaya,ma'ana mijinta ko mahaifinta ko mahaifiyarta,take Mummy ta bishi,saboda Hamza ko iya mik'ewa tsaye ya kasa,Likita ke wa Mummy bayani akan tasa hannu domin a yiwa Hidaya C S a ciro babyn,idan ba haka ba rayuwarsu tana cikin hatsari,take Mummy ta sa hannu tana rok'on likita kan ya taimaka ya ceto rayuwar Hidaya,ita kad'ai ta haifa kuma bata rayu da ita ba,yanzu ne lokacin da za su yi rayuwa tare ya taimaka ya ceto rayuwar Hidayan,likita ya cewa Mummy "Hajiya zan yi iya yina,sauran kuma zan barwa Allah saboda rayuwar Hidaya a hannunsa take"
Nan take aka fara shirin shiga da Hidaya (Operation room),wadda ke cikin wani yanayi na rai kwakwai mutu kwakwai,su Umma kan su da suka ji C S za a yiwa Hidayan hankalinsu ya dad'a tashi ne,amma da likita ya dinga yi musu nasiha nan take suka fara dawowa nutsuwar su,suka fara ambaton Allah da kai kukansu gareshi.
Hamza ma ganin ana shirin shiga da Hidaya d'akin tiyata sai ya fara k'arfafa zuciyarsa,take kuma ya tuna da halin da Khaleel ma yake ciki,take ya mik'e jikinsa na mazari,Umma ta rik'o shi tana ambatar "Ina za ka Hamza?" Cikin wata irin murya yayi magana yana dubanta da idanuwansa da suka jirkice "zan je gun Khaleel ne Umma...ku ku zauna anan ni bari na tafi gun sa" Aunty Sajida ce ta share hawayenta ta jinjina kai tare da duban Hamza ta ce "Mu tafi tare Hamza,su Umma sai su zauna anan a jira hukuncin Allah,can d'in babu kowa sai Aunty Kubra da Y'an sanda" hakan ya sa Umma ta saki hannun Hamza,suka wuce suka nufi b'angaren da Khaleel ya ke.
Sun tarar da Aunty Kubra na zaune tana kuka,nan take sanar musu an shiga da Khaleel d'in d'akin tiyata domin cire harsashin da ke jikinsa,tace musu ita ta tsorata saboda tana ganin kamar Khaleel ba zai tashi ba,nan Aunty Sajida ma ke fad'awa Aunty Kubra halinda Hidaya da d'an cikinta ke ciki,hankalinsu duka ya k'ara tashi suka cigaba da ambaton Allah suna zub da hawaye,Hamza kam jikin garu ya jingina kansa yana jin kansa na juyawa kamar ya mace,tabbas yana cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa.
An d'auki lokaci mai tsawo kafin a kammala aikin cirewa Khaleel harsashin,daga nan kuma likitoci suka yi abinda za su yi sannan suka yi masa allurar bacci aka dawo da shi d'akin hutu aka shimfid'e shi tamkar matacce,har kuma lokacin basu bawa kowa damar ganin Khaleel d'in ba.
A can b'angaren Hidaya an yi aiki cikin nasara,in da aka cirowa Hidaya baby boy me matuk'ar kyawu da d'aukar hankali,su kansu likitoci sunyi mamaki da suka ga yaron tuk'ek'e mai girman gaske,wanda wasu yaran y'an wata tara ma basa yin girma irin wannan,amma sai gashi shi d'an wata bakwai(bakwaini)yayi wannan girman,ikon Allah kenan.
Bayan sun gamawa Hidaya komai ita ma aka gangaro da ita d'akin hutu,likita ya tabbatarwa su Umma lafiya k'alau take sai dai sun mata allurar bacci dan ta samu hutu,Lokacin da aka kawo musu jaririn sunyi matuk'ar murna duk da suna cikin wani yanayi na tunanin halinda Khaleel ke ciki,Allah kenan mai yadda ya so,Khaleel ya samu k'aruwa a lokacin da yake cikin wani yanayi.
Mummy ce ta kira wayar Aunty Sajida take sanar da ita haihuwar, "Alhamdulillah" kalmar da Aunty Sajida ta fad'a kenan wadda ta sanya Hamza bud'e idanuwan sa ya zuba mata su don neman k'arin bayani,haka ma Aunty Kubra ke kallonta,sauke wayar tayi ta ce musu.
"Allah ya sauki Hidaya lafiya,an samu yaro Namiji,da Hidayan da jaririn duk suna cikin k'oshin lafiya"
Wani irin lumshe idanuwa Hamza yayi,hawayen dad'i ya tsiyayo masa,take ya godewa Allah da fad'in "Alhamdulillahi ala kulli halin"sannan ya zarce da fad'in "Allah ya tashi kafad'arka Abokina,ka bud'e idanuwanka kaga wani arzik'i mai girma da ubangiji ya azurtamu da shi"
Aunty Kubra ma tayi murna sosai duk da har lokacin hankalinta a tashe yake.
*************
Kusan lokaci d'aya Khaleel da Hidaya suka farka, a lokacin ne kuma likitocin suka bayar da umarnin ganinsu, ta b'angaren Khaleel akwai Hamza da Aunty Kubra da Aunty Sajida,lokacin da suka shiga d'akin da hanzari Hamza ya isa gadon da Khaleel ke kwance,an nannad'e kafad'arsa da bandeji in da aka ciro harsashin,idan kaga Khaleel dole ka tausayawa yanayin da yake ciki,Hamza na zuwa hannun Khaleel d'in ya kamo yana k'ank'amewa kamar zai had'iyeshi,Khaleel ya bi Hamza da wani irin kallo yana runtse idanuwansa saboda azabar da yake ji a sassan jikinsa musamman k'irjinsa,Sannu suka dinga jerawa Khaleel gabad'ayan su,gyad'a kai kawai yake yi bakinsa ya kasa furta komai,kuma maganar yake son yi,Hamza ke tambayar Khaleel shin ko yana jin ciwo sosai ne a fad'awa likita?Khaleel ya jinjina kai yayi magana a hankali wadda sai da Hamza ya kai kunnensa dab da bakin Khaleel d'in sannan yaji abinda yake fad'a.
"Ina jin ciwo Aboki,musamman a cikin k'irjina,amma likita babu abinda zai iya yi min,domin yayi dukkan wani k'ok'ari da zai iya"
Aunty Kubra ce ta matso sosai tana tambayar Hamza abinda Khaleel ya ce,Hamza ya fad'a mata,sai ta kama sharar hawaye tana fad'in "Allah ya baka lafiya Khaleel,ubangiji ya tashi kafad'un ka"
Jin Khaleel na janyo hannun Hamza sai Hamzan ya sake matsawa sosai jikinsa yana tambayarsa "Kana son wani abu ne?" Khaleel ya d'an yamutsa fuska jin kafad'arsa kamar ba a jikinsa take ba,sannan ya cewa Hamza "Ina Hidaya...?" Wani d'an murmushi ne ya sub'ucewa Hamza a yayin da yake fad'in " Hidaya tana tare da su Umma,a yau kuma Allah ya sauketa lafiya an samu lafiyayyen Namiji,duk da har yanzu banga yaron ba saboda ina tare da kai" Wani kyakkyawan Murmushi Khaleel ya saki duk da ciwon da yake ji,ya k'urawa Hamza idanu yana fad'in "Alhamdulillahi,Allah na gode maka da ka azurtani da babban arzik'i" sannan ya ce wa Hamza "Aboki cikin Hidaya wata bakwai ne fa bai isa haihuwa ba ko?" Hamza ya sake damk'e hannunsa ya ce "Halin da taga ka shiga ne ya sababba mata shiga yanayi mara dad'i,shine dalilin da yasa aka yi mata C S aka ciro jaririn dan kar a samu matsala,amma duk suna cikin k'oshin lafiya a yanzu haka"
D'aga idanuwa Khaleel yayi yana ta hamdala ga Allah,daga nan kuma ya dubi Aunty Kubra yayi magana,lokacin muryarsa har ta fara washewa dalilin farincikin da ya samu kansa ciki, "Aunty don Allah a kawo min jaririn mana na ganshi,idan zai yiwu har da Hidayan ma,ina jin kamar nayi tsuntsuwa na gansu wallahi"
Sai Aunty Kubra ta d'anyi murmushi,sannan ta juya Aunty Sajida ta bi ta a baya suka fice suka nufi b'angaren da Hidaya take.
*************
"Don Allah Umma ku sanar da ni gaskiya idan Uncle Khaleel ya mutu...idan kuma bai mutu ba ku kaini na ganshi....
Abinda Hidaya take ta ambata kenan tana daga kwance,hawaye na tsiyayo mata ta gefen fuskarta,Umma ta kai hannu ta share mata hawayen sannan ta rik'o hannunta guda d'aya tana matsawa a hankali ta ce.
"Me ya sa kika kasa yarda da abinda na fad'a miki?Khaleel yana nan da ransa bai mutu ba Hidaya,kin san ai ba zanyi miki k'arya ba"
Cikin kuka Hidaya ta kuma cewa "Na san ba zaki fad'a min abinda ba haka yake ba Ummana,to amma idanuwana sun kasa manta yadda naga Uncle Khaleel ya fad'i sanda aka harbe shi,don Allah Ummana ki taimakawa numfashina ki kaini naga Uncle Khaleel"
Umma ta dafe kanta,magiyar da Hidaya take mata ta raunata zuciyarta,sai Mummy ce ta matso tana shafa kan Hidayan kafin tayi magana a hankali.
"Ke Hidaya d'ago kanki ki kalleni"Hidaya ta d'ago tana kallon Mummy sai kuka take,Mummy ta girgiza mata kai ta ce "Kiyi hak'uri kinga d'inki ne a jikin ki fa,ko kin manta Haihuwa kika yi?tsaga jikinki fa aka yi aka fito da jariri,kiyi hak'uri bari a kawo miki yaron da kika haifa ki gani kinji"
Girgiza kai Hidaya tayi,hawaye na tsananin zuba ta ce da Mummy "ah ah ni ba shi nake son gani ba Mummy,idan kuna so na kwantar da hankalina na daina kuka to ku kaini wajen Uncle Khaleel,ganinsa kawai zanyi sai ku dawo dani don girman Allah Mummy"
Suka rasa yadda za su yi da Hidaya,gabad'aya ta tashi hankalinsu ta addabesu da rigima da kuka da magiya,ita fa kawai Uncle Khaleel take son gani,a dai dai lokacin ne su Aunty Kubra suka shigo d'akin suka tarar da wannan rigima ta Hidaya,da k'yar ta amsa sannun da suke mata tana kuka,suka karb'i jaririn a hannun Ummansu Sajida suna dubansa cike da murnar samun sa,kyakkyawan jariri fari tas da shi har wani ja yake,Aunty Kubra ta rungumeshi jikinta tana hawaye.
Ganin kukan da Hidaya ke yi ya fara yawa kar ya tab'a mata aikinta sai Kakarta tace a tambayi likita idan zai yuwu ko a gadon marasa lafiya ne sai a turata a kaita ta ganshi domin dai hankalinta ya kwanta,haka kuwa aka yi,shi kansa likitan ya tsorata da kukan da Hidaya take tana numfarfashi,hakan yasa ya bayar da umarnin wasu nurses su d'auko gadon da ake tura marasa lafiya a d'orata a kai sai a kaita,take kuwa suka aikata umarnin likita aka d'auko gadon aka d'ora Hidaya,sai lokacin Hidayan ta ji farinciki a zuciyarta.
Su Aunty Kubra ne suka fara yin gaba rik'e da jaririn a hannunsu,wanda yayi luf da shi cikin shawul yana baccinsa,suna shiga d'akin da sauri Hamza ya mik'e ya taro su ya karb'i jaririn fuskar sa cike da annashuwa yana ta hamdala,wajen Khaleel ya nufa yana rik'e da shi ya haska masa shi yana cewa "Ga kyauta daga Allah ya iso Khaleel" duk da bala'in da Khaleel yake ji a k'irjinsa da kafad'arsa hakan bai hanashi sakin murmushin da ya jima baiyi ba,cikin wata irin murya yace wa Hamza"Aboki d'ora min shi a k'irjina" Hamza ya zaro idanu yana girgiza kai ya ce "Yanzu fa ka gama ce min zuciyarka na ciwo,ta ya ya za a danne k'irjin da ba shi da lafiya?" Khaleel ya lumshe idanu ya ce "Ko ya ya dai taimaka ka d'ora min shi Aboki,ko sau d'aya ne muji d'umin juna ni da shi" Sai Hamza ya rausaya kai,ya matsa a hankali ya d'ora jaririn a k'irjin Khaleel,take Khaleel ya lumshe idanuwan sa hawaye ya tsiyayo,hawayen murna,hawayen godiya ga sarki Allah! mai kyautar abin da babu wani bawa da ya isa yayi maka idan ba shi ba.
A lokacin ne aka shigo da Hidaya cikin d'akin ana tura ta a gadon,su Umma gabad'aya suna biye da ita,har gaban gadon da Khaleel yake aka kai Hidaya,sai lokacin Hamza ya k'araso kusa da ita yana duban ta d'auke da tausayi akan fuskarsa,a hankali yake mata sannu,ta amsa da "Yawwa Ya Hamza" sai kuma ta waiwaya tana duban Khaleel da ke amsa sannun da su Umma ke masa,ta k'ura masa idanuwa take kuka ya b'alle mata,sai Khaleel ya juyo ya tsura mata ido kafin ya girgiza mata kai alamun ta dena kuka,a hankali yace mata " To menene abin kuka kuma?ke da za ki yi farinciki Allah yayi mana babban arzik'i da ba kowa yake samu ba,ki daina kuka kinji Hidaya,komai da kika gani muk'addari ne daga Allah,duk wasu abubuwa da suke ta faruwa a rayuwar mu tuni daman Allah ya rubuta sai sun faru,yanzu dai kinga jaririn na mu ko?"
Tana shesshek'ar kuka tace" Ni ba shi nake son gani ba,baban shi nake son gani daman" Sai Khaleel yayi murmushi yana nuna Hamza da baki sannan ya ce "To ai ga baban na shi can fa" duk suka juya suna kallon Hamza wanda ke murmushi yana sunkuyar da kai.
Khaleel ya sake ce wa Hamza "Aboki d'an matso min da shi,ka sa kunnensa saitin bakina ina so in mishi hud'uba ne" Aunty Kubra ta ce "Hakan na da kyau,bari naje k'ofar asibitin nan naga akwai masu sayar da dabino da zam zam sai na siyo kayi amfani da su"
Bata jima ba kam ta dawo da su a hannun ta,Hamza ya matsar da jaririn Khaleel yayi masa hud'u ba,sannan ya tauna dabinon ya sanya masa a baki,sai ga jariri yana mulmul da baki,Hamza yayi dariya yana fad'in "Kalle shi wai shima daga zuwanshi duniya ya san zak'i...ko da yake gado yayi,mamanshi ma haka take da son zak'i" ya fad'a yana duban Hidaya,ita kam hankalinta gabad'aya na kan Uncle Khaleel"
Khaleel ne ya ce wa Hamza "Aboki zo ka d'auke takwaran ka ka bawa su Umma shi" Hamza ya k'ura masa idanuwa ya ce "Takwarana kuma?" Khaleel yayi murmushi ya lumshe idanu ya ce "Eh takwaran ka mana! Sunansa HAMZA ,da sunan nayi masa hud'uba"kafin Hamza ya ce komai sai Khaleel ya cigaba da magana "Ka san me ya sa na saka masa suna HAMZA? saboda ina son ya d'auko komai na ka,kyawun ka...ibadarka...kirkinka...addininka...halayyarka...ililiminka...ladabinka...biyayyarka...tauhidinka...nagartarka...mu'amalarka...kyawun zuciyarka...iliminka...da komai na ka Aboki...na tabbatar idan ya kasance haka zanyi alfahari da shi...zai zame min ولد صالح wanda ko bayan ba raina zai dinga tunawa da ni yana min addu'a"
Sai Hamza ya fashe da kukan murna,kowa na d'akin godiya yake wa Khaleel domin tabbas jajirin yayi dace da suna mai Kyau,Hidaya kanta murna take yi mai yawa,domin burinta kenan ta samu d'a ta saka masa suna HAMZA,girman sunan da darajar da yake da shi a gareta ba zai lissafu ba.
Sai bayan sallar isha'i ana shirin mayar da Hidaya d'akinta sannan Khaleel ya ce da su Umma don Allah yana son yayi magana da Hidaya da Hamza su kad'ai,sai su Umma suka fita suka basu guri,Hamza ya janyo kujera ya zauna a tsakiya,ga Khaleel kwance kan gadon sa,ga Hidaya ma kwance kan gadon da aka kawota,Khaleel ne yayi gyaran murya ya dubi Hidaya yayi mata wata tambaya.
" Me ya sa kika aureni?"
Shiru tayi ta k'ura masa idanuwa kawai,domin bata san amsar da za ta bashi ba,hakan da ya gani sai ya lumshe idanu ya ce "Ni na san a tarbiyyar da Aboki ya baki ya d'oraki a kan fad'ar gaskiya komai d'acin ta,don Allah Hidaya kar ki min k'arya,kar ki fad'i wani abu dan naji dad'i,fito min da gaskiyar ki ki fad'a min me ya sa kika amince da ni har kika aureni?"
Hawaye ya tawo mata,tabbas Khaleel ya d'aureta da jijiyar jikinta,sai ta zab'i fad'ar gaskiyar kawai tunda ita yake son ji,hakan ya sa ta sanyaya murya tace "Saboda Ya Hamza,domin ka kasance Zab'insa a gareni" Khaleel ya runtse idanu sosai wani abu ya soki k'irjinsa,sai Hidaya ta cigaba da magana tana ce wa "Amma Uncle Khaleel daga lokacin da na aureka naji soyayyarka da k'aunarka ta shiga raina,a lokacin da na fara sonka a lokacin kuma rabuwa ta riskemu bamu zata ba" Sai Khaleel ya bud'e idanuwansa hawaye ya sakko masa,a take yace wa Hidaya "Kin san wani abu?har yanzu bakya sona,kina dai k'aunata kuma kina tausayina,amma so na soyayya ba ni kike wa shi ba ABOKINA kike wa" Take Hamza ya zabura cikin zare ido da gigicewa yake duban Khaleel,bakinsa har rawa yake wajen fad'in "Meye haka Khaleel...wace irin magana ce wannan?ta ina wannan maganar mara tushe balle makama ta b'ullo?yanzu har zafin ciwo ya sa ka fara irin wannan sambatun Khaleel...?don Allah...
D'aga masa hannu Khaleel yayi yana dakatar da shi,cikin wata irin murya ya ce.
"Dakata Aboki babu abinda za ka fad'a min domin na san komai,kullum kai ne me d'oramu a tafarkin gaskiya akan me kake so kayi k'arya a yanzu domin naji dad'i? duk abinda zaka fad'a ba zan tab'a yarda da kai ba Aboki,abin da baka sani ba na san komai,na san son da kayi wa Hidaya,a ranar da naje gidanku baka nan na shiga d'akinka anan ne na ci karo da (diary) d'inka wanda sirrinka ke ciki,ka gafarceni Aboki domin na d'auka na karanta abinda ke ciki,ban tab'a jin tashin hankali irin na ranar ba,domin naga tsantsar So da K'auna da ka nunawa Hidaya a ciki,nayi danasanin shigowa rayuwarku da raba soyayyarku mai girma,me ya sa kayi min haka?me ya sa baka sanar da ni kana sonta ba?me ya sa ka bani ita na aura alhali kana sonta?Hamza wace irin zuciya ce da kai?wane irin so kake min da ka zab'i farinciki na akan na ka farincikin?"Khaleel ya fashe da wani irin kuka,Hamza kam dafe kansa yayi yana jin kamar ya fad'i,sirrin da yake ta b'oyewa yau gashi ya bayyana,shi ma kukan ne ya kufce masa ya matsa yana rik'e hannun Khaleel,hawayen sa na d'isa a hannun Khaleel d'in kafin ya bud'e baki ya ce.
"Ka na ji ko Khaleel..wannan ba komai bane,ba Hidaya ba ko dukkan abinda na mallaka kake so wallahi zan baka,ai mutum na gari baya manta alkairi,menene baka yi min ba a rayuwa Khaleel?duk wani abu da ka san zan ji dad'i ya d'aga darajata kayi min shi,Khaleel ban da mahaifiyata da tayi ta k'ok'ari a kaina bayan rasuwar mahaifina babu wanda ya kaika tallafata a rayuwa,sai kuma dan ka nuna kana son abinda nake so na hanaka?sai nabi son zuciyata na so kaina?ba haka zuciyata take ba Khaleel,ni ina sowa d'an uwana musulmi abinda zan sowa kaina na alkairi,wallahi Khaleel da zuciya d'aya na bar maka Hidaya,tabbas na san na sota so mara adadi,amma da na fallawa raina hak'uri sai Allah yayi min jagora wajen mantawa da komai,banyi hakan da wata manufa ba sai dan ka samu abinda kake so Khaleel,kuma daman Allah ya nufa kaine mijin Hidaya ba ni ba,tunda komai da yake faruwa da sanin Ubangiji ne Khaleel"
Khaleel ya damk'e hannun Hamza yana kuka sosai,a hankali ya girgiza kai yana cewa " Na sani aboki kai mutum ne mai kyakkyawar zuciya da tsantsar imani,kuma hak'urin ka shi ya kaika matakin nasarar da za ka mallaki Hidaya a halin yanzu" Da sauri Hamza ya dubeshi,sai ya jinjina masa kai tare da fitowar hawaye,sannan ya cigaba da cewa "Babu wani d'a namiji da ya dace da rayuwar Hidaya fa ce kai,Hidaya taka ce aboki,shigar sauri kawai nayi maka,amma da yake ita d'in ba matata ba ce sai Allah yayi nufin raba auren da wuri,ka lura da kyau akwai abinda Allah yake nufi da rabuwata da Hidaya Aboki,a yanzu Hidaya bata da wani miji sai kai,ni daman babu wani zama da yayi ragowa tsakani na da ita,domin ni tawa ma ta k'are,wallahi Aboki ciwon da nake ji a zuciyata ba lallai na k'ara kwana d'aya a duniya ba,rok'ona a gareka ka auri Hidaya ka rik'eta da jaririn da ta haifa maka,domin d'anka ne,duk in da aka je HAMZA NE UBAN HAMZA, GARKUWA NE UBAN GARKUWA,rok'ona na biyu gareka shine ka kula min da Mahifina,na san k'ila Allah ba zai sake had'a fuskokinmu ba,ka fad'a masa naji dad'i da ya karb'i hukuncinsa tun a duniya,kuma ina addu'a da fatan hakan ya zame masa kaffarar dukkan laifukan da ya aikata,ka kasance mai yi masa nasiha,domin tabbas Daddy zai yi rashi,zai rasani bayan ya rasa mahaifiyata,bayan Daddyna na sani babu wanda zai kaika kukan rashina Aboki,sai dai kayi hak'uri,Khaleel d'inka ba mai tsawaicin kwana ba ne,Dan Allah Aboki ka auri Hidaya,ka aureta domin ka cigaba da zama GARKUWARTA,naji dad'i da komai ya zo k'arshe,rok'ona a gareku kar ku manta da ni,ku dinga sanyani a addu'arku ko zan samu salama cikin k'abarina"
Kukan da Hamza da Hidaya ke yi yayi yawa,har su Umma da ke waje suka fara jiyo wa,hakan yasa suka shigo da hanzari suna tambayar abinda ya faru,Hamza ya kife kansa kan gadon da Khaleel ke kwance zuciyarsa tamkar ta fito,kuka yake wanda bai tab'a yin irinsa ba,Umma ta nufi Hidaya tana rik'eta ganin tana yunk'urin mik'ewa,cikin tashin hankali Hidaya ke rusa kuka tana cewa da Umma "Umma Uncle Khaleel ne ya saka mu kuka,yana ta cewa mutuwa ziyi kuma ya san ba zamu jurewa rashinsa ba,don Allah Umma kice masa ya daina fad'a domin na san idan ya mutu Ya Hamza ma binsa zaiyi?to ni kuma ya zanyi Umma?ni kad'ai zan zauna a duniyar kenan duk GARKUWATA sun k'are?
Hawaye ya zubowa Umma na tausayin su gabad'aya,a hankali take rarrashin Hidaya,yayin da su Mummy ke gefe kowa yana sharar hawayen tausayi,Khaleel kam hannu yasa yana shafa kan Hamza da ke kife ya jingina da k'irjinsa,a hankali kuma ya rufe idanuwansa yana ta cewa "Kayi hak'uri Aboki....kayi hak'uri Aboki...kayi hak'uri Aboki"
Har wajen goma na dare suna d'akin kafin likita ya zo ya bayar da umarnin mayar da Hidaya d'akinta saboda allurori da magunguna da zai bata,haka aka fita da Hidaya na kuka sosai,babyn ma ya farka yana ta kuka alamar yunwa yake ji,Umma da kanta ta fito da Nonon Hidaya aka sanyawa babyn a baki,nan da nan ya kama yana sakin ajiyar zuciya,Hidaya ta runtse idanu tana jin tausayin d'anta da soyayyarsa a zuciyar ta,bayan ya gama sha likita yazo ya bata magunguna sannan yayi mata allurar bacci,Umma ta ce da su Mummy su koma gida ita da Aunty Sajida da kakar Hidaya,ita za ta kwana da Hidayan,yayin da Hamza zai kwana da Khaleel shi da Aunty Kubra,shima kuma Khaleel d'in an masa allurar bacci ne dan ya samu sauk'in ciwon da ke addabarsa.
Sai can cikin dare Hamza na zaune kujerar da ke gefen gadon Khaleel d'in ya kifa kansa, hannunsa sark'e cikin na Khaleel d'in,ba bacci yake ba zuciyarsa ce kawai babu dad'i,Aunty Kubra kam tana zaune sai gyangyad'i ke kwasarta,Hamza ne ya ji tamkar ana jijjiga hannunsa,da hanzari ya d'ago kansa yana duban Khaleel sai yaga jikinsa na rawa kamar wanda ake jijjigashi da k'arfi,a tsorace ya mik'e yana rik'o shi yana ambatar sunansa,Khaleel juya kai kawai yake azaba ta isheshi,da k'yar ya fizgo magana cikin nishi kamar numfashinsa zai fice" Aboki zuciyata ciwo,danna min k'irjina zai tsage" Hamza ya rud'e ya rasa ya zaiyi,ya k'walawa Aunty Kubra kira ta farka a gigice ta tashi ta nufo su,ganin yadda Khaleel ke yi sai Aunty Kubra ta rud'e ta fashe da kuka tana ambatar "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un....shikenan Khaleel haka zaka yi mana? Hamza ya gigice har bai san lokacin da ya rik'e hannun Aunty Kubra ba,yana ce wa "Menene Aunty?Me zai mana?don Allah menene?" Aunty Kubra ta kuma fashewa da kuka ta ce" Wallahi Hamza Khaleel mutuwa zaiyi,an tab'a yin mutuwa a gabana,duk wasu alamu da na gani sun tabbata a yanayin Khaleel yanzu" Hamza ya girgiza kai kamar mahaukaci yana duban Aunty Kubra" Ba mutuwa zaiyi ba...Khaleel ba zai tafi ya barni ba Aunty...
Aunty Kubra ta katseshi "Shikenan Hamza bari naje na kirawo likita,kai kuma zauna a wannan kujerar kai ta fad'a masa kalmar shahada,amma ni dai na tsorata da Khaleel" tana fad'in hakan ta fice da sauri,yayin da Hamza ya juyar da idanuwansa yana duban Khaleel da ke wani irin nishi da k'arfi idanuwansa a warwaje ya damk'e hannun Hamzan sosai,sai Hamza ya sake fashewa da Kuka yana ambatar "La ilaha illallahu muhammadur rasulallah ( S A W).
**********
Kamar wadda aka tasa daga barci firgigit ta farka,ta d'aga kanta tana duban Umma da ke bacci kan daddumar da ke shimfid'e,a hankali ta yunk'ura ta mik'e zaune tana cije leb'e,ta sanya hannu ta matsar da jaririn da ke gefenta sannan ta zuro k'afafuwanta sa sauko daga gadon,kamar me koyon tafiya haka ta dinga salallab'awa a hankali dan kar ta tashi Umma har ta fice daga d'akin ta nufi d'akin da su Khaleel suke.
Tun daga k'ofar shiga take jin muryar Hamza na kalmar shahada,da sauri ta tura k'ofar d'akin ta afka tana nishi,Hamza ya d'ago yana kuka ya dubeta sanda ta k'araso idanuwa warwaje take cewa "Ya Hamza me ya faru?" jikin ne ya tasar masa?" gyad'a kai Hamza yayi kafin ya sanya hannu ya janyo ta kusa da shi,a hankali cikin kuka ya ce mata"Ke ma ki dinga fad'in abinda nake fad'a" take suka had'a baki suna ta maimaita kalmar shahada suna kuka,tun Khaleel na wani irin nishi me k'arfi da juya kai har ya fara sassautawa,a k'arshe sai ga bakinsa ya kama ambatar kalmar da su Hamza da Hidaya ke nanata masa,ya fad'a kusan sau hud'u sai kuma idanuwansa suka yi sama yana damk'e hannun Hamza sosai,daga nan jikinsa ya fara saki har rai ya k'arasa ficewa daga jikinsa 😭a wannan tsakiyar dare na ranar Alhamis,a lokacin ne kuma Aunty Kubra da likita suka shigo d'akin da hanzari.
Hamza bai san mutuwa ba,amma yana ganin yadda Khaleel yayi ya tabbatar ya rasa shi kenan😭,Khaleel ya tafi ya barshi,k'asa kawai yayi ya durk'ushe yana jin ina ma shima ya mace,Hidaya ta bishi tana damk'ar kafad'arsa tare da girgiza shi tana cewa "Ya Hamza menene ne?ya naga Uncle Khaleel ya daina motsi?" Hamza cikin sark'ewar numfashi ya ce .
"Mun rasa shi Hidaya,yau munyi rashin Khaleel...daman ya fad'a mutuwa zaiyi muna ganin kamar k'arya ne ashe gaskiya ya fad'a...Khaleel d'ina ya tafi ya barni mutuwa ta rabani da shi....😭
Take Hidaya ta sulale a jikin Hamza sumammiya,shi ma Hamzan idanuwansa suka fara lumshewa yana shirin kifewa Aunty Kubra da likita suka taro su cikin tashin hankali.
***************
Ni Hassana D'an Larabawa hannuna yayi kad'an wajen rubuta matsanancin halin da Hamza da Hidaya suka kasance dalilin rasuwar Khaleel,damuwa tai damuwa😭,kewa tai kewa😭,idanuwa sun koka😭,zuciyoyi sun raunana😭,sai dai ya za a yi da hukuncin ubangiji? wanda shine ya halicci Ibraheem Khaleel kuma ya karb'eshi a lokacin da yake so.
A safiyar Juma'a ne kuma da aka wayi gari aka tawo da gawar Khaleel tsohon gidan su na garin Kaduna,anan aka shirya shi,har da HAMZA cikin masu wanke gawar Khaleel, da shi aka shiryashi cikin likkafaninsa,yana kallonsa akwance babu motsi,babu magana,babu murmushin da kullum yake masa,babu mai ambatarsa da kalmar Aboki,sunan da tun ranar da Allah ya had'asu Khaleel d'in ke ambatarsa da shi,amma a yau komai ya k'are,Hamza yana gabatar da abubuwa ne kawai amma ba a cikin hayyacinsa yake ba,kuka kuwa sai da ya zama da k'yar idanuwansa ke bud'uwa,addu'a kam da samun yabo idan yana yawa to zaiwa Khaleel yawa,kowa yabonsa yake domin Khaleel mutum ne mai alkairi da zama lafiya da mutane.
Ana shirin sallatar gawar Khaleel sai ga y'an sanda guda uku sun rako Daddy,duk wanda yaga Daddy da halin da ya shiga dole yayi kuka,musamman da ya fara cin karo da Hamza sai ya rungumeshi yai ta kuka yana fad'in "Ba ni aka yiwa mutuwa ba kai aka yi wa mutuwa Hamza,sai dai kayi hak'uri,amma na san rashin Khaleel zai cigaba da tab'a ka har ranar da za ka bishi" Daddy har gaban makarar da aka saka Khaleel yaje ya tsuguna,yayi masa addu'o'i masu yawa tare da fatan shigarsa k'abarinsa cikin sa'a da tarar da alkairi,har ya dinga surutai wad'anda ke k'ara karya zuciyar mutane suna kuka,musamman da ya ce "Ban tab'a ganin d'a mai biyayya kamarka ba Khaleel,tun kana yaro nake amfani da dama ta nake tank'waraka yadda nake so,baka tab'a bijire min ba sai biyayya a gareni,ko iya wannan ta isa ta shigar da kai Aljanna,bana jin d'acin rayuwar da zanyi a gidan yari kamar d'acin rashinka,na yafe maka Khaleel kuma ina maka fatan samun rahamar ubangiji" Daddy ya dinga kuka hawaye na sharara,sai ga y'an sandan da suka rakoshi suna sharar hawayen tausayi.
Bayan an wa Khaleel Sallah sai aka d'aukeshi domin kaishi gidan sa na gaskiya,da Daddy da Hamza sune suka saka Khaleel a cikin k'abarin sa aka binne shi😭,aka yi addu'o'i sannan aka fara watsewa,Hamza yana ji kamar kar ya tafi,shikenan fa rayuwar,duniya ba matabbata ba,Allah kasa mu cika da kyau da imani👏😭
Daga Mak'abarta sai y'an sanda suka wuce da Daddy,daman an masa alfarma ne dan zuwa jana'izar Khaleel,nan ma Hamza yayi kuka yana tuna wasiyyar Khaleel kan kulawa da mahaifinsa,kuma ya d'auki wannan alk'awari muddin yana da rai zai kula da Daddy tamkar mahaifinsa da ya haifeshi.
Ita kam Hidaya har lokacin tana asibiti cikin mawuyacin hali,Aunty Sajida ke lura da ita,babyn sai kuka yake yi kamar yana da masaniyar mahaifinsa ya rasu,ranar da ya zo duniya ranar ya rasa mahaifinsa,sai dai ba zaiyi maraici ba,tunda akwai Hamza a filin duniya.
A can gida tare da su Umma da Mummy aka cigaba da zaman makoki,Hamza ya kasa hankalinsa biyu ne daga gida zuwa asibiti gano halinda Hidaya ke ciki,idan ya karb'i takwaransa Hamza yana zubda hawayen rashin mahaifinsa Khaleel a kusa da shi,Allah sarki Khaleel,ya tafi ya bar zukata da kewa idanuwa da zubda hawaye😭.
Allah ne kawai ya rubuta da kwanan Hidaya a gaba,amma ta sha wahala matuk'a da gaske kafin komai ya daidaita,kullum haka take sanya Hamza a gaba da kuka har ma ya rasa ya zaiyi,lokacin zuciyar Hamza ta zama tamkar ta mata,shima kukan yake a kullum,Umma ta rasa yanda za ta yi dasu musamman idan aka rasa me rarrashin wani a tsakanin su,sai su sanya Hamza k'arami a gaba suyi ta kuka,a rasuwar Khaleel Hamza ya had'u da lalurar hawan jini saboda tsananin damuwa har sai da ta kaishi ga kwanciya a asibiti kamar shi ma zai mace,nan da nan Hidaya ta fara nutsuwa ganin shi ma za ta rasa shi,a ganinta idan ta rasa Khaleel ta jure ba zata iya jure rashin Hamza ba,mutuwar Hamza tamkar mutuwarta ne.
Har Khaleel yayi watanni hud'u da rasuwa basu dawo cikin hayyacinsu sosai ba,duk juma'ar duniya kuma sai Hamza ya shirya ya kaiwa k'abarin Khaleel ziyara tare da addu'o'i na musamman,da har ya fara zuwa da Hidaya,amma ganin tashin hankali da kukan da take yi sai yake barinta a gida yaje shi kad'ai,Hamza k'arami na ta girma da wayo,k'aunar da Hamza ke masa ba za ta lissafu ba,kusan ma shine me rainonsa da kulawa da shi,ko ya yaji yayi kuka yanzu hankalinsa zai tashi ya dami Hidaya akan ta ba shi Nono,shi kansa yaron yayi sabo da shi ta yadda idan bai ga Hamzan ba sai yayi ta kuka yana neman sa,shak'uwa ce mai girma a tsakanin su.
Hamza yana ziyartar Daddy akai akai domin duba lafiyarsa,idan yaga halinda Daddy ke ciki yana jin k'unci a ransa,sai dai babu yadda zaiyi,kullum yaje suka ga juna sai sun yi kukan tunawa da Khaleel,kuka ya zame musu jiki,Aunty Kubra ma ta jima kafin ta dawo nutsuwarta,ba k'aramin duka mutuwar Khaleel tayi mata ba,Su Alhaji Maude tuni aka zartas musu da hukuncin su,duk da hakan zuciyar Hamza bata yi sanyi ba,dan bai da wani mak'iyi da ya wuce Alhaji Maude wanda shine sanadi ko kuma silar mutuwar Khaleel,duk da babu wanda yake mutuwa sai lokacinsa ya yi,kaf dukiyar Khaleel Hamza k'arami ne ya ci gadonta,domin Daddy yace ba zai karb'i komai ba shima ta sa rabin dukiyar ya mallakawa Hamza k'arami da Hidaya da Hamza babba,rabin kuma ya barwa Aunty Kubra da y'ay'anta guda biyu,a ganinsa babu wata rayuwa a gabansa ta jin dad'i,yana fatan ma kafin ya cika shekaru gomansa na gidan yari Allah ya d'auki rayuwarsa ya huta.
************
Shekaru biyu suka shud'e bayan mutuwar Khaleel,lokacin tuni Hidaya ta yaye Hamza k'arami,a lokacin ne kuma sai ga uban masoya sun fara tuttud'owa domin auren Hidaya,nan da nan hankalin Umma ya tashi ta samu Hamza tayi masa fata fata,tace idan ba zai auri Hidaya ba to wallahi zata bawa wani dama ya fito,zai rasata a karo na biyu,domin zurfin cikinsa yayi yawa,Hamza ya dinga bawa Umma hak'uri yana hawaye ,wai daman yana jira ne Hidayan ta yaye Hamza,kuma yana so yaji idan har lokacin tana son sa,mamaki ya kama Umma har ta ce masa "Da man Hamza soyayya na tsufa ne?ai sai dai masoyan su tsufa,wallahi babu wani namiji da Hidaya za ta so tamkarka har duniya ta nad'e"
"INA SON TA UMMANA,INA MATUK'AR K'AUNAR TA" Hamza ya fad'a kansa a sunkuye,hawaye na saraftu saboda tunawa da Khaleel da yayi,Allah sarki rayuwa...
A wannan lokaci ne aka d'aura auren HAMZA DA HIDAYA,wani aure mai cike da tarihi da zukata ba za su mantaba,rana mafi daraja da soyuwa a zukatan ma'auratan,domin sun fitar da rai da ita sai gashi Allah ya nufe su da ganinta,lallai hak'uri da k'addara da jarrabawa mataki ne na nasara a rayuwa,dole sai an jarrabeka sannan za ka ji dad'i,ko a yanzu ma cikin wata jarrabawar suke ta rashin Khaleel a kusa da su...
Ranar da suka kasance inuwa d'aya makwanci d'aya an tafka soyayyah,soyayya mara iyaka! soyayya mai tsayawa a zuci! wata irin soyayya da bata da misali! a ranar Hidaya ta tabbatar da maganar Khaleel da ya ce ba shi take So ba,Hamza take so,shi dai tana masa k'auna da tausayawa ne,amma so na soyayya kam Hidaya Hamza ta tattarawa,to yau dai ga Hidaya da Hamza sun samu cikar burinsu,amma duk da hakan basu tab'a manta Khaleel ba,babu ranar da zata fito ta wuce basu yi zancensa ba,Khaleel na shan addu'a wajen wad'annan bayin Allah,a haka suke ta rainon Hamza har ya girma sosai ya kai wasu shekaru,Hidaya ta bayar da kwangilar gina makarantu da asibitoci da k'ungiya ta taimakon marayu duk k'ark'ashin sunan Khaleel,domin ya zame masa sadak'atul jariya zuwa makwancin sa.Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar musu cikin kwanciyar hankali da nagartacciyar soyayyah.
**************
Ni HASSANA D'AN LARABAWA na ajiye alk'alami na tare da ajiyar zuciya da sakkowar hawaye a idanuwa na,bayan na kammala rubuta tarihin rayuwar HIDAYA,labarin da ya shiga zuciyar mutane suka so shi sosai,domin akwai Darasin rayuwa da abubuwa da dama da mutane za su d'auka.
Bayan kammala rubutun littafin GARKUWA BIYU da wasu shekaru Hidaya ta samu cikin Hamza,da lokacin haihuwa yayi ta haifi y'an biyu mace da Namiji,macen ta ci sunan Umma namijin kuma sunan Marigayi Khaleel,Shekaru goma cif da mutuwar Khaleel a lokacin ne Daddy yayi free ya fito daga prison,gabad'aya ya sauya tsufa ya sakko masa,duk kammaninsa na baya sun sauya kuma baya gani sosai sakamakon yawan kuka da yake akan tunawa da D'an sa Khaleel,watansa d'aya da fitowa shi ma ya rasu sakamakon ciwon da yayi ta fama,wannan mutuwa ma ta hargitsa su,sunyi kuka har sun godewa Allah,amma suna wa Daddy zaton rahamar Ubangiji,tunda ya tuba ya bi hanyar dai dai.
Rayuwa ta cigaba da mik'awa Hidaya da HAMZA GARKUWA NA FARKO, tare da y'ay'an su,a gefe ga su Umma da Mummy da su Aunty Sajida da Aunty Kubra.
*K'ARSHE....!*
WANNAN SHINE K'ARSHEN LITTAFIN GARKUWA BIYU WANDA NI HASSANA D'AN LARABAWA NA RUBUTA,INA ROK'ON RABBANA YA BANI LADAN ABINDA NA RUBUTA DAI DAI,SANNAN YA GAFARTAMIN KURA KURAN DA KE CIKI,ALLAH KASA WANNAN LITTAFI YA AMFANI DUK WANDA YA KARANTA SHI,GA DUK WANDA YA KARANTA YA AMFANA DA SHI INA ROK'ON ADDU'A GAREKU YAN UWA AKAN WATA BUK'ATA TAWA,KUYI MIN ADDU'A ALLAH YA BIYA MIN ITA,NAGODE MASOYANA TABBAS DA BAZARKU NAKE TAKA RAWA DOMIN IDAN BABU KU TO BABU HASSANA D'AN LARABAWA,GA DUK ME NEMAN K'ARIN BAYANI KO WATA SHAWARA AKAN RUBUTUNA K'OFA A BUD"'E TAKE ZAI IYA NEMA NA AKAN LAMBATA KAMAR HAKA 08080049548,SAI KUMA MUN SAKE HAD'UWA DA KU CIKIN LITTAFIN (BAHAGON LAYI SABON SALO) KO KUMA SABON LITTAFINA DA ZAN FARA MAI SUNA....... IDAN RABBANA YA BANI IKO DA DAMA AKAN RUBUTAWA BAYAN NA HUTA,SHIMA LITTAFIN NA SA SALON DABAN YAKE,LABARIN GASKE NE DA YA FARU MAI TSAYAWA A ZUCIYA DA WATA IRIN RAYUWA,KU DAI KU CIGABA DA BINA TARE DA JIMIRIN KARANTA RUBUTU NA,INA GODIYA GAREKU MASOYA,TABBAS NA GA K'AUNA A GARKUWA BIYU 👌😅💃🏻🥰
Comments
Share
Vote
pls