← Book details Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 19 OF 31

BABI NA SABA'IN DA BIYAR DA NA SABA'IN DA SHIDA

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

***Cikin tsananin tashin hankali suka nufi Khaleel,Daddy ya tsuguna ya tarairayo shi jikinsa yana kuka da ambatar sunansa,ganin Khaleel d'in baya motsi bare numfashi sai hankalinsa ya sake mugu mugun tashi,ya rasa ya zaiyi sai girgiza shi yake yana kuka yana ambatar.


"Khaleel...Khaleel don Allah ka tashi kar kayi min haka...ka tashi zan fad'a maka dukkan abin da ya faru...don Allah kar ka tafi ka barni kamar yadda mahaifiyarka tayi min...ka tashi d'ana ...don Allah ka tashi ka dubeni....!

Aunty Kubra da ke tsaye tana kuka salati kawai take rafkawa ganin yanayin da Khaleel yake ciki,tana son Khaleel tamkar ita ta haifeshi,saboda biyayyar da yake mata da son y'ay'anta.

Durk'usawa tayi dab da Daddy da ke rik'e da Khaleel d'in yana ta surutai kamar ya zauce,a hankali ta kai hannu kan k'irjin Khaleel da jini duk ya b'ata shi,dafa k'irjin tayi bakinta d'auke da salati tana hawaye,da k'arfi ta sauke wata ajiyar zuciyar jin dad'i,ta waiwayo ta dubi mijinta ta girgiza kai tayi magana.

"Daddyn Khaleel d'aukeshi muyi hanzarin kai shi asibiti,naji zuciyarsa na bugawa da k'arfi ba mutuwa yayi ba,d'aukoshi bari nayi hanzarin fitowa da mota"

Tana fad'in hakan ta tashi ta fice da hanzari,yayin da wani sanyi ya kwarara a zuciyar Daddy,cikin gaggawa ya d'ago Khaleel da ke sume ya sanya shi kan kafad'ar sa yayo waje da shi,duk da hakan hawaye bai bar zuba a idanuwansa ba.


Aunty Kubra ke jan motar,yayin da Daddy ke zaune a bayan motar rungume da Khaleel a jikinsa,tsananin tashin hankali ya kasa tsayar da hawayen da yake saraftun zubowa a fuskarsa,ita kanta Aunty Kubran bata cikin wata nutsuwa sosai,amma duk da hakan tana tuk'i sai da tayi wa Daddy magana ta ce.

"Da wannan kukan da kake dama addu'a kayi masa,domin babu abinda Khaleel ke buk'ata a yanzu sama da ita"

Sai ga Daddy ya fara nemo addu'ar da zaiyi,da ya kamo wannan sai ta kufce,da ya janyo wannan sai ya manta,babu abinda ke d'awainiya da shi sai firgici da k'urewa a fage na tashin hankali. A haka har suka k'arasa babban asibitin da Khaleel ke ganin likitan ciwon zuciya tun bayan dawowarsa daga England.


***************


B'angaren su Hamza tashin hankalinsu ya zarce misali,domin su abin yayi musu rufdugu,ga Hidaya kwance ga Mummy kwance,(wannan shi ake cewa d'a kwance uwa kwance).

Umma da Aunty kuka suke yi sosai,basu ma san ya za su yi ba,har ruwa Umma ta d'ebo ta yayyafawa Mummy da Hidaya amma ko motsi basu yi ba,wannan ya sake d'aga hankalinta ta dubi Hamza da ke sandare a tsaye ta daka masa tsawa har da zagi,abinda bata tab'a yi masa ba.


"Don ubanka don uwarka kaje ka fito da mota mu kai bayin Allan nan asibiti,idan suka mutu za su rataya a wuyanka akan banzan tunanika Hamza,ka kaimu asibitin da Hidayan take ganin likita domin nan ne muke da tabbacin samun abinda muke so"

Ko Umma bata fad'a ba tilas ya aikata hakan duk da ransa bai so ba,shi so yake ya yanke komai da yake tsakaninsa da Khaleel,saboda ya kai mak'ura wajen b'ata masa rai,yayi masa abinda bai tab'a zato ba,ya wulak'anta masa amanarsa,duk da hak'urin da yayi ya bar masa ita,duk da soyayyar da yake mata a filin duniya.

Jikin Hamza a salub'e ,yana jan k'afa da k'yar haka ya fice ya fito da motar,da kansa ya dawo ya d'auki Hidaya da take langab'e tamkar matacciya,Umma da Aunty suka ciccib'o Mummy ,dukan su suka shiga motar,yayin da Hamza ya fige ta da gudu suka nufi asibiti domin ceton lafiyar Uwa da y'arta.


*****************


Asibiti d'aya duk aka nufa da su,Khaleel b'angaren masu ciwon zuciya,yayin da Hidaya aka nufi b'angaren masu ciwon sikila da ita,sai Mummy kuma da wani likitan na ban yake duba ta.

Kafin cikar awa d'aya Mummy da Hidaya sun farfad'o har an musu allurar bacci domin k'wak'walwar kansu ta huta abisa firgicin da suka tsinci kansu a ciki,Khaleel ne dai an sha wahala kafin ya farfad'o,bayan farfad'owar ta sa ma sai bala'in ciwo ya ishe shi,yana shure shuren azaba yake wa likitan nuni da acire masa zuciyar gabad'aya ta isheshi,likitan kansa ya tausayawa Khaleel matuk'a ganin halin da yake ciki, sai da yayi masa wasu allurai sannan zafin rad'ad'in ya ragu,har ma ya samu kansa cikin wani irin wahalallen bacci mai cike da mafarkin Hamzan sa da Hidayan sa.


Sai bayan Yamma lik'is sannan Mummy ta farka daga wahalallen baccin,tunda ta farka kuma take wani irin kuka mai cin rai da zuciya,rarrashi babu irin wanda Umma da Hamza ba su yi mata ba,amma ta kasa yin shiru,daga k'arshe ma tunb'uke ledar k'arin ruwan tayi daga hannunta ta mik'e tsaye a gigice,Umma tayi saurin rik'e ta fuska cike da damuwa take fad'in.


"Ki yiwa girman Allah ki sanyawa zuciyarki salama,kinga ba cikakkiyar lafiya ne da ke ba kar a kuma samun wata matsalar"

Mummy cikin hawaye ta ce.

"Barni Umman Garkuwa,matsala kuma ai na riga da na gama shigarta,tunda jinina ya had'u da jinin MUDASSIR"

Cikin tsananin mamaki Umma ta dubi Hamza da ke zaune idanuwan sa a runtse,gani yake ya fi kowa shiga tashin hankali,a yanzu da yake zaunen nan babu abin da ke zuciyarsa sai Khaleel,ta k'arfi yake k'ok'arin cizge shi daga ransa amma ya kasa,ayanzu haka son ganinsa yake,domin ya san Khaleel d'in yana cikin wani hali na garari,kuma ya san ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba,Zuciyar sa ba ta iya jure manyan tashin hankali.

Juyo da kallonta tayi kan Mummy bayan ta d'auke idanuwanta daga kan Hamza,cikin wani irin murya Umma ta cewa Mummy.

"Me yasa kika ce haka?daman kin san Alhaji Mudassir mahaifin Khaleel?naga daga fad'a miki shine mahaifin mijin Hidaya kika rud'e har kika fita daga hayyacin ki"

Mummy tayi wani murmushi na tsananin takaici da bak'inciki,ta basar da maganar Umma,illah jefowa Umma tambaya da tayi ita ma.


"Ina Hidaya...!?

Umma ta cigaba da kallonta kafin ta bata amsa da cewa.


"An mata allurar bacci ne,yanzu haka Sajida na tare da ita a d'akin da aka kwantar da ita"


Mummy ta runtse idanuwan ta tana sakin ajiyar zuciya,a hankali kuma ta fara bud'e su ta sauke ganinta kan fuskar Hamza,ta ambaci sunan sa cikin dakakkiyar murya.

A hankali ya bud'e idanuwansa da suka sauya kala ya dube ta,tana dubansa ta jefa masa tambaya.


"Ranar da na baka Hidaya na baka wata takarda ka ajiye mata,har na rok'i alfarmar kar ka bata sai ta girma,sai kaje gidan Marayun ka bata,tsawon lokacin da na tafi na barku na san cewar baka kai Hidaya gidan marayu ba,kuma hakan duk yana cikin shiri na da tsari na,haka nan duk wata rayuwa da Hidaya ta gabatar tare da ku ina sane da ita,ina bibiyar lamuranku,fallasa kaina ne kawai na kasa yi saboda ina gudun harin da wani azzalumi zai kawo min daga ni har Hidayan,shiyasa na zab'i b'oye kaina,amma ba don ina son hakan ba,Hamza na san cewa kayi wa Hidaya rik'o na gaskiya,kai da mahaifiyarka,ka zame mata GARKUWA na farko,Bibiyar da nake muku ta yanke ne a ranar da ka ganni a airport har na guje maka,tabbas ni ka gani Hamza,ban san abinda ya kawo ka airport ba a ranar,ni kuma zanyi tafiya ne zuwa wata k'asa domin halartar k'arawa juna sani akan aikin Shari'ah,ni nan da kuka ganni babbar alk'aliya ce,kuma na zab'i na zama alk'aliya ne saboda na aiwatar da wani nufina na yankewa wani azzalumi hukunci,idan har Hidaya bata cika min burina ba,ba wani buri bane kuma illah ta kashe min Alhaji Mudassir mahaifin Khaleel da hannun ta...

Hamza bai razana da jin maganar Mummy ba,saboda ya san kwanan zancen,Umma ce dai ta firgita ainun,cikin zazzare idanuwa take duban Mummy tana mata kallon mahaukaciya,tana shirin magana ta ji Mummy ta cigaba da magana tana tambayar Hamza....


"Shin Hamza ka bawa Hidaya wannan ajiyayyiyar takardar kuwa..!?


Hamza ya lumshe gajiyayyun idanuwansa yana sakin ajiyar zuciya,cikin wani yanayi ya dubi Mummy ya ce.

"A jiya sak'onki na tsawon shekaru ya isa hannun Hidaya,kuma ina da tabbacin wannan sak'on shine ya kawo babban rud'a ni a yau"

Idanuwan Mummy a kansa ta ce.


"Wane irin rud'ani kenan?"

Mik'ewa tsaye Hamza yayi,sannan ya juya baya ya daina kallon Mummy,sauke ajiyar zuciya yayi kafin ya fara magana cikin taushin murya.


"Babban rud'ani,wanda ya janyo sanadiyyar katsewar babbar sunnah ta Annabi,ba kuma komai ya janyo hakan ba sai umarnin da kika bawa Hidaya na aikata mummunan aiki a matsayinki na mahaifiyar ta,a maimakon kiyi mata umarni da kyakkyawan aiki,Umarni da kyakkyawan aiki na nufin umarni da abinda Allah da manzonsa suke so,da abin da shari'a ta yarda a kansa,yayin da umarni da mummunan aiki kuwa yake nufin,umartar aikata abin da Allah da manzonsa suka hana,kuma shari'a ta bayyana muninsa.

Allah mad'aukakin sarki ya umarci bayinsa muminai da kyakkyawan aiki da hani da mummunan aiki,inda yake cewa:


"ولتکن منکم أمة يدعون إلى الخير و يأمرون بالمعروف وينھون عن المنکر ,و أولئك ھم المفلحون"


Ma'ana( A samu wasu jama'a daga cikinku suna kira zuwa ga alkairi,sannan suna umarni da kyakkyawan aiki kuma suna hana mummunan aiki,wad'annan sune wad'anda suka rabauta) suratu Ali - Imrana.

A wani wurin Allah mad'aukakin sarki ya bayyana cewa wannan al'umma ita ce mafi alherin al'ummun da aka samar a cikin mutane,saboda umarninta da kyakkyawan aiki da hani daga mummunan aiki,Allah ya ce:


"کنتم خير أمة أخرجت للناس تأمرون بالمعروف و تنھون عن المنکر و تؤمنون بالله"


(Kun kasance mafiya alherin al'umma da aka fitar wa da mutane,kuna umarni da kyakkyawan aiki,kuma kuna hana mummunan aiki,Sannan kuna yin imani da Allah).


Manzon Allah (S A W) ya bayyana mana cewa umarni da kyakkyawan aiki da hana mummunan aiki wajibi ne na shari'a,da shi al'umma take tsira daga azabar Allah.


A lokacin ne Hamza ya juyo yana kallon Mummy,idanuwansa cike taf da hawaye,ita ma Mummy da jikinta ya fara sanyi ta zuba masa idanu tana kallonsa,cikin taushin murya Hamza ya cigaba da magana.


A cikin tarbiyyar da na bawa Hidaya na gwada mata yiwa iyaye biyayya a bisa umarnin da suka bayar,kullum ina fad'amata darajar iyaye da k'imarsu,na san cewar da wannan tayi amfani wajen yarda da abin da kika umarceta na kasancewarki mahaifiya a gareta,Sai dai abu d'aya da Hidaya ta manta,wanda shi ma na karanta mata shi,babu biyayya cikin sab'awa mahalicci,kisan kai sab'on Allah ne mai girma,ba a yarda ayi umarni da aikata shi kai tsaye ba, matuk'ar ba ta hanyar shari'a aka bi ba.Na san cewar dole Hidaya ta gigita da umarninki,wanda da ta aiwatar da shi da babu abin da zai hana ta shiga cikin bala'i da masifa mabayyani,Na san ke ma a lokacin da kika rubuta wannan takarda ba kya cikin kamalalliyar nutsuwa Mummy,burinki kawai d'aukar fansa,wanda kuma da kinyi hak'uri kin barwa Allah ko kin bi tsarin shari'a to da duk wasu abubuwan basu faru ba"

Sai ga Mummy ta fashe da kuka,hawaye yaraf yaraf ta dubi Hamza ta ce.

"Madalla da kai HAMZA GARKUWA,madalla da wannan bawan Allah mai umarni da kyakkyawan aiki da hani ga mummunan aiki"

Hamza ya runtse idanuwansa ya sunkuyar da kansa k'asa,hawayen sa na d'isa akan tayel d'in da ke shimfid'e a k'asa,cikin murya mai rauni ya ce.


"An karb'o wani hadisi daga Huzaifa d'an yamani,Allah ya yarda da shi,ya ce,Manzon Allah ( S A W) ya ce, "Na rantse da wanda raina yake hannunsa,ko dai ku yi umarni da kyakkyawan aiki,ku hana mummunan aiki,ko ya kusata Allah ya aiko da azaba a kanku,uk'uba daga gareshi,sannan ku rok'eshi ba za a amsa muku ba" Tirmizi ne ya rawaito shi.

Yana tsayawa da maganar sa Mummy ta share hawayen ta,Sannan cikin wani irin murmushi ta ce.

"Godiya ta tabbata ga Allah, Tsira da amincin Allah su k'ara tabbata ga fiyayyen halitta ,manzon Allah (S A W), da iyalensa da sahabbansa,da wad'anda suka bi su gaba d'ayan su har zuwa ranar sakamako,kyakkyawan k'arshe yana ga masu tsoron Allah,da masu umarni da kyakkyawan aiki da hani ga mummunan aiki"


A hankali gabad'ayan su suka waiwaya jin an bud'e k'ofar d'akin,Aunty Sajida ce rik'e da Hidaya da ke takawa a hankali saboda rashin k'warin jiki,ta kuma wani irin zurmawa kanta ko d'ankwali babu sai gashin ta da ya bazo akan kafad'un ta duk ya hargitse,fuskarta tayi wani irin haske,sai dai har lokacin kuma kumburin marin da Khaleel da daddala mata bai baje ba,Kallo d'aya Hamza yayi mata yayi maza ya kau da kai k'irjinsa na tsananin bugawa,sai ya fara ambatar Allah a ransa,yayin da Hidayan ta tsaya cak ta zubawa Mummy idanuwa tana kallonta,wani irin abu take ji yana mamaye jikinta yana ratsa b'argonta,bata san matar ba,amma kallo d'aya tayi mata taji zuciyarta ta girgiza,a hankali Hidaya ta maida kanta kan Hamza da alamun tambaya a idanuwanta,ganin ya kawar da kansa daga gareta sai ta juyar da kallonta zuwa ga Umma,sannan ta d'ago hannuwanta tana nuna Mummy tana tambayar Umma da idanuwan ta shin wacece wannan?Umma tayi wani miskilin murmushi kafin ta bud'e baki cikin taushin murya tayi magana.


"Mahaifiyarki ce Fad'ima....wannan ita ce Mummyn ki Hidaya...je ki gareta kiji d'uminta kamar yadda ko wane d'a yake son jin d'umin mahaifiyar sa"

Sai Hidaya ta zare jikinta a hankali daga jikin Aunty Sajida,a hankali ta soma takawa jikinta na rawa ta nufi Mummy da ke tsaye tana kallonta cikin wani yanayi mara fassaruwa,har Hidayan ta je gabanta ta tsaya cak,suka zubawa juna idanu suna wani irin duban juna, A hankali Hidaya ta d'aga hannunta ta kai jikin Mummy tana tab'ata da niyyar tabbatarwa,zuciyarta na rawa,da k'yar ta iya bud'e baki cikin dasasshiyar murya ta ce.

"Ke ce ?da gaske ke ce Mummy na?ke ce Mahaifiya ta?"

Bakin Mummy ya kasa furta komai,illa jijjiga kai da tayi alamar tabbatarwa da Hidayan cewa ita d'in dai ita ce mahaifiyarta,da Hidaya tayi wani irin juyi na tsananin murna sai gata a k'irjin Mummy ta rungumeta tana cusa kanta cikin k'irjinta,Mummy ta tarbeta suka rungume juna kamar za su had'e su zama abu d'aya,take Hidaya ta fashe da wani irin wahalallen kuka mai ban tausayi,surutai take yi tana jin numfashin ta na sama kamar zai d'auke tsabar murna.

"Ka na ina Ya Hamza...ka zo ka gani yau ga Mummy na ta zo gareni...zo ka tayani farinciki ya Hamza...daman kana ta fad'a min cewar in dai tana raye zan ganta...kana ta cemin komai daren dad'ewa za ta zo gareni...yau ga ranar ta zo...kana ina Ya Hamzana...Lallai yau na dad'a gasgataka.....

Kan Hamza a sunkuye yana zubar da hawayen tausayin uwa da y'a,Aunty Sajida ma na kuka,yayin da Umma ma ke kuka tana ji a zuciyarta duk wanda ya zama dalilin raba tsakanin wannan y'a da uwa na tsawon lokaci to hak'ik'a ya cika babban azzalumi.....!


Comments
share
vote
pls


*GARKUWA BIYU*


BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter 19 · 0% Book details