← Book details Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 31

BABI NA HAMSIN DA BAKWAI DA NA HAMSIN DA TAKWAS

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

***Kamar yadda kika sani cewar Khaleel da Hamza abokai ne wad'anda suka shak'u da junan su,ba ke kad'ai ba ni kaina ina mamakin yawan k'aunar juna da suke yi,haka nan mutane ma.

Asalin Mahaifin Khaleel a da mazaunin kaduna ne,cikin wannan Unguwa ta (Tudun wada)wadda ta had'a mutane iri iri kama daga masu kud'i zuwa masu k'aramin k'arfi da rufin asiri.

Ba zan manta ranar da had'uwar Hamza da Khaleel ta samo asali ba,wata rana da yammacin ranar litinin misalin k'arfe biyar na yamma, na cewa Hamza ya d'auki tsintsiyar kwakwa yaje k'ofar gida ya share,saboda a ranar na fita unguwa, da na dawo sai na tarar da k'ofar gidan duk Datti,yara sun sha rake da gyad'a duk sun zubar da b'awon, shine dalilin da ya sa nace ya je ya share wajen domin yayi kyan gani.

Hamza ya d'auki tsintsiyar ya fice domin sharewa,lokacin yana D'an shekara Tara kacal a duniya,lokacin da ya fara sharewa akwai ragowar yaran layin da ke gefe suna ta buga ball,lokacin yammacin yayi musu dad'i saboda a safiyar an yi Ruwan sama gari yayi luf luf,Dan duk gefen hanya ma ga Ruwan nan ya kwanta da cab'alb'ali bai gama bushewa ba.

A dai dai kuma lokacin ne Khaleel ya ratso cikin layin na masu k'aramin k'arfi,akan keken sa mai kyau na y'ay'an masu kud'i,lokacin shi ma shekarunsa ba za su haura taran ba,sanye yake da k'ananan kaya y'an kanti a jikinsa,sabon keke Daddyn sa ya siyo masa shiyasa yake ta shawagin sa a kai,har Allah ya kawo shi layin,da yake bai fiya fita ba ma idan ba makaranta za shi ba,shiyasa duk bai ma san yaran bayan layin ba.

Shigowar sa layin yayi dai dai da sanda yaran suka buga ball d'in da k'arfi,aikuwa ball sai tayi kan khaleel ta buge shi da k'arfi a gefen fuskar sa,zafin da Khaleel ya ji shine ya sa ya saki sitiyarin keken bai sani ba,ya fad'o k'asa cikin cakwakwalin da ya b'ata wajen,keken ya bi shi yana k'ok'arin danne shi Allah yasa ya fad'i gefen bai danne shi ba.

Da sauri Hamza ya waiwaya jin k'ara kamar ihu,yar da tsintsiyar hannunsa yayi da hanzari yayi kan khaleel yana k'ok'arin d'ago shi daga k'asa,su kuma yaran ganin Khaleel ya fad'i sai suka kama dariya har da tsalle,wasu na yi masa gwalo,hakan ya b'ata ran Hamza bayan ya d'ago Khaleel, ya dube su fuska cike da fushi yace.

"Yanzu ku Anas abin da kuka yi ya kamata kenan?kun sa mutum ya fad'i a k'asa sakamakon buga masa ball amma shine kuke masa dariya maimakon ku ba shi hak'uri? Zalintar sa kuka yi fa,Kuma kun manta ko jiya malam Shehi ya karanta mana cewar Allah baya son zalinci?ya haramtawa kansa zalinci,Kuma mu ma ya sanya shi a tsakanin mu abin haramtawa,kada muyi zalinci,haka Allah fa yace,baku kyauta ba Anas,kuyi hanzarin ba shi hak'uri domin kun cutar da shi"

Duk sai jikin yaran yayi sanyi,musamman ma Anas d'in,da sauri suka bawa Khaleel hak'uri,Wanda yake ta yatsuna fuska yana jin k'yank'yamin jikinsa da k'wab'ab'b'iyar k'asa ta b'ata,gyad'a musu kai kawai yayi alamar ya hak'ura,Hamza kam da ya lura da yanayin sa sai ya dube shi cike da kulawa yace.

"Ka yi hak'uri ka ji,ga gidan mu mu shiga sai ka wanke in da ya b'aci a jikin ka"

Khaleel ya D'an k'urawa Hamza idanuwan sa kyawawa,sai Kuma ya D'an saki murmushi ya gyad'a kai,Hamza ya sunkuya ya d'ago keken Khaleel d'in ya rik'e yana turawa,suka jera Hamza na gaba Khaleel na biye da shi a baya suka shige cikin gidan,suka bar su Anas tsaye suna bin su da kallo.

Ina parlour naji muryar Hamza na k'wala min kira,na d'aga labule na fito ina kallon sa shi da yaron da ban sani ba,ya jingine keken jikin bango ya dube ni yace.

"Umma muna da ruwa ko?wannan ne ya zo wucewa kawai su Anas suka buga masa ball ya fad'i,dubi duk jikinsa ya b'aci,bamu ruwa ya D'an wawwanke kinji Umma"

Na girgiza kai ina jajantawa saboda kayan sun yi kaca kaca,idan ma aka ce za a wanke k'asar to zai jik'e ne sharkaf,sai nace da Hamza.

"Ai kayan sun b'aci da yawa fa,ba zai yiwu a wanke suna jikinsa ba,zai iya jik'ewa sosai"

Hamza ya D'an yi shiru,ya kalli Khaleel d'in sannan ya juyo ya kalleni yace.

"To Umma ya cire sai a bashi kayana ya sanya kawai,tunda kanmu d'aya na san za su yi masa ko?"

Mamaki ya kama ni,haka kawai bamu san yaro ba bamu san daga ina yake ba sai mu bashi kaya?amma da naga yadda yaron yake ta kallona sai na amsawa Hamza da to kawai,Hamza yayi murmushin dad'i.

Bayan na bashi kayan ya sauya sai lokacin ya ke gaisheni,har na tambayi sunan sa yace min sunan sa Khaleel, sai naji yaron ya shiga raina farat d'aya da alamun yana da hankali sosai,Hamza da kansa ya wanke masa keken in da ya b'aci,sannan ya dubi Khaleel d'in yace.

"Ka bar kayan na ka anan zan wanke maka,gobe in Allah ya kai mu sai na kawo maka gidan ku,ina ne gidan na ku?"

Khaleel yayi murmushi yana kallon Hamza,yayi magana cikin siririyar murya.

"A layi na biyu nake,gidan mu shine na Uku a layin"

Na D'an ji dammm !saboda ni na gane gidan,Ina bi ta layin wataran,layin gabad'aya masu kud'i ne mazauna cikin sa,amma shi Hamza bai ma gane ba,duk da hakan sai ya gyad'a kai yace.

"To zan kawo maka in sha Allah,ga keken ka ka hau ka tafi kar mamanka tayi maka fad'a ko?"

Sai Hawaye ya ciko idanuwan Khaleel, ya dube mu yace.

"Ai Mamana ta rasu,sai dai Daddy na"

Hamza ya girgiza kai cike da tausayi yace.

"Allah sarki!ni ma Baba na ya rasu!

Na dube su dukan su,sai naga jikinsu yayi sanyi,sai suka ban tausayi,na shafa kawunan su nace.

" Allah ya jik'an iyayen ku,ku dinga yi musu addu'a kunji"

Suka gyad'a kai suna kallon juna,daga nan Khaleel ya d'ane keken sa,Hamza ya raka shi har waje ya tafi,shi Kuma ya d'akko tsintsiyar da ya Yar ya dawo gida ganin magriba ta kawo kai.

Hidaya wannan shine Asalin had'uwar Hamza da Khaleel.

A ranar kafin magriba tuni Hamza ya wanke kayan Khaleel k'al ya shanya su a igiya,sannan ya d'aura alwala ya tafi masallaci, ni dai na zuba masa idanu ban ce komai ba,
Da safe da aka kawo wuta Hamza har da goge wa Khaleel kaya,mamakin yadda ya d'au Khaleel da muhimmanci na dinga yi sosai.

Misalin k'arfe sha biyu na rana na aiki Hamza ya siyo min kayan miya,ni Kuma ina sharar tsakar gida kawai naji sallama,d'agowar da nayi Ina amsawa sai naga Khaleel ne,na washe baki ina fad'in.

"Ibraheem kai ne? Yanzu kuwa Hamza ya ke fad'in zai zo ya kawo maka kayan ka"

Ya k'araso yana murmushi da bak'ar Leda a hannun sa,ya durk'usa ya gaisheni cike da ladabi,na amsa fuska a sake ina tambayar sa mutan gidan su,a lokacin Hamza ya dawo daga aike,ya tsaya turus yana kallon Khaleel, shi ma Khaleel d'in ya juya yana kallon sa,suka yi wa juna murmushi mai k'ayatarwa,sannan Hamza ya k'ara so yana ajiye kayan miyan,ya dubi Khaleel yace.

"Ina ta sauri in gamawa umma aiki na kai maka kayan ka,Ashe ma ka riga ni zuwa kai"

Sai Khaleel ya jijjiga kai yace.

"Ni ma kayan ka na kawo maka fa,nawan Kuma ka barshi ka cigaba da sanyawa"

Nayi sauri nace.

"Ah ah Khaleel na za a yi haka ba,kayan ka masu kyau da tsada sababbi ba zai yiwu ka bada su ba,tuni ma har ya wanke maka ya goge maka,sai kawai ka tafi da abin ka"

Ya girgiza kai yace.

"Allah ni Umma ban zan karb'a ba na bar masa,ina da su da yawa fa sun min yawa ma"

Na yi shiru kawai ina duban Khaleel, yayin da Hamza ya shiga kitchen ya d'akko roba da wuk'a,ya juye kayan miyan yana k'ok'arin gyarawa,Khaleel ya mik'a min ledar kayan Hamza da ya sa,ya matsa kusa da Hamzan yana k'ok'arin taya shi gyaran,sai Hamza ya d'ago ya kalleshi yana murmushi yace

"Ka iya gyaran kayan miya ne?"

Khaleel ma yayi murmushi ya girgiza kai yace.

"Ah ah ban iya ba,koya min zaka yi sai na taya ka kawai"

Ni dai na cigaba da shara ta na bar su nan suna maganganun su da gyara kayan miya,da suka kammala ma tare suka je kai markad'e.

Kafin me Khaleel da Hamza sun yi mugun Sabo a ranar,Kamar sun jima da juna,hatta abincin rana a gidan Khaleel ya ci ranar,naga dai bashi da niyyar tafiya sannan nace masa.

"Ibraheem ya kamata ka tafi gida kar a neme ka fa tunda ka dad'e"

Bai so tafiyar ba,amma sai ya amsa min da to,sannan yace yana so su tafi da Hamza domin shi ma yaga gidan su,ban so hakan ba dai amma na daure nace shikenan suje babu komai,sannan nace wa Hamza kar ya jima ya dawo da wuri.

Hamza ya amsa min sannan ya bi shi suka tafi,basu tarar da Daddyn Khaleel ba,sai matarsa Anty Kubra,har gaban ta khaleel ya kai Hamza yana nuna mata shi a matsayin sabon abokin sa,ta karb'i Hamza Hannu bibiyu da yake mace ce me kirki,ta rik'e Khaleel kamar ita ta haifeshi,sai dai ta yiwa Khaleel fad'an me yasa ya fita ya dad'e?Daddyn sa ya yo waya yana Neman sa,sai k'arya tayi tace yana bacci,shi dai Khaleel dariya kawai yayi ya figi hannun Hamza suka nufi d'akin sa,haka ya dinga rakito abubuwa yana bawa Hamza,shi kam Hamza ma a tsorace yake saboda yadda yaga girman gidan,ga kayan more rayuwa nan kala kala,d'akin Khaleel kan sa abin kallo a yaba ne.

Ya kasa sakin jikin sa,sai Khaleel ne ya dinga Jan sa da hira, ya d'akko hotunan mahaifiyar sa ya dinga nuna masa,abubuwan ci da sha kuwa Hamza har gajiya yayi da ganinsu,ranar dai Hamza ya ga karramawa.

Tun daga lokacin wata irin abota mai k'arfi ta shiga jikin wad'annan yaran,babu ranar da ba za su ga juna ba,ban fiye barin Hamza na zuwa gidan su Khaleel ba,amma shi kam Khaleel kusan kullum sai yazo,da zarar an tashi daga makaranta zai faki ido ya tawo gun Hamza,wata irin k'auna Khaleel yake nunawa Hamza ta musamman,shi ma Hamza yana son Khaleel.

Tun Daddy bai gane yawan fitar da Khaleel yake ba har ya fara ganewa,ya tsare shi kuwa da tambayoyi akan hakan,kai tsaye Khaleel ya fad'a masa cewar gun abokin sa yake zuwa,mamaki ya ishi Daddy,shin waye abokin sa?ta ina suka had'u?Khaleel d'in da ko yaran layin su y'ay'an masu kud'i baya shiga sabgarsu,amma har yake da wani aboki a wani layin?sai Daddy ya barwa ransa cewar zai yi bincike ya gano wanene abokin da Khaleel yake fad'a"


Kwana biyu muka ji Khaleel shiru bai zo ba,hakan yasa naga Hamza duk ya shiga damuwa,amma ya kasa tambayata akan yana so yaje gidan su Khaleel, saboda ya san bancika son zuwan sa ba,ni Kuma akwai abin da nake hangowa,ban cika son mannewa masu kud'i ba saboda ba kowa ke son talaka ba cikin masu kud'in,da kaina dai da naga damuwar Hamzan tayi yawa nace yaje ya dubo yaga ko lafiya,aikuwa ya dinga murna da walwala ya shirya ya tafi.

Sai da yaje ya tarar Ashe Khaleel d'in ba shi da lafiya ne,shi kansa Khaleel d'in yaji dad'in ganin Hamzan,daman kewar sa ta ishe shi,ya dinga murmushi yana daga kwance,Hamza yayi masa sannu ya amsa,suna nan zaune Daddyn Khaleel ya shigo,sai ranar Hamza ya tab'a ganin sa,Daddy ya dubi Hamza shek'ek'e,sannan ya tambayi Anty Kubra cewar wannan wanene?ta ba shi amsa da cewar "shine Hamza,abokin Khaleel".

Yanayin Hamza kad'ai ya nuna wa Daddy cewar ba D'an masu kud'i bane,hakan yasa yaji Sam bai masa a ransa ba,ya dinga ciccin magani yana hararar Hamza,yayin da Khaleel ke tayi wa Daddyn shagwab'a shi kuma yana biye masa.

Daddy ya so ya kori Hamza,amma saboda baya son b'acin ran Khaleel sai ya bar shi,sai dai ya k'udurtawa ransa tilas ya raba abotarsu,baya son D'an sa ya rab'i talakawa balle a goga masa dattin talauci.

Da Hamza ya dawo ya sanar da ni rashin lafiyar Khaleel, sai naji duk na damu,washegari kawai sai Hamza yaga nayi shiri na soya Y'ar awarata nace yazo ya rakani na duba Khaleel, Hamza yayi ta murnar kulawar da na bawa abokin sa,ya d'auki flask d'in awara muka tafi gidan su Khaleel.

Mun samu tarba ta mutunci gun Kubra,Khaleel kam yafi kowa murnar ganinmu,Kuma a gabana ya bud'e kwanon awarar ya ci abarsa,har Anty Kubra na mamaki,ganin ana ta fama da shi yaci abinci amma ya k'i,kayan dad'i kala kala,amma ya b'ige da cin awara.
Ni dai har muka dawo ban ci karo da Daddyn Khaleel ba,saboda an ce min yayi tafiya zuwa Abuja shi da wani abokin sa Alhaji Maude,murnar bud'e wani babban kamfani da aminin su mai suna Alhaji Taufiq ya bud'e.


In tak'aice miki Labari Hidaya,haka abotar Khaleel da Hamza ta cigaba da k'arfi da hab'aka,suna girma suna k'ara son juna,duk yadda Daddyn Khaleel yayi domin ya raba su hakan ya kasa yiwu wa,Hamza makarantar gwamnati na saka shi saboda bamu da k'arfi,amma sai da Khaleel ya san yadda yayi Daddyn sa ya mayar da Hamza ta su makarantar ta yaran masu kud'i,duk da baya son hakan,bak'incikin Daddy bai wuce yadda Khaleel yake matuk'ar son Hamza ba.

Khaleel baya gajiya da hidimtawa Hamza,har suka girma suka kusa kammala secondary school abotar su na k'ara k'aimi,in dai kaga d'aya zaka ga d'aya,babu irin gulmar da ba a kaiwa Daddy akan ya raba su,wai Khaleel yana mana hidima sosai,gadon da mahaifiyar sa ta bar masa duk mune muke cinyewa,tun baya tsayawa ya kula har abin ya fara shigar sa,yaji gara ma su bar garin Kaduna gabad'aya su koma Abuja,ta yadda za su daina ganin juna gabad'aya.

Da ya fad'a wa khaleel za su tashi ranar yaga tashin hankali,don Khaleel da girman sa amma kuka ya dinga yi da birgima akan ba za shi Abuja ba,shi dai a barshi gun Hamza zai zauna,hankalin Daddy yayi matuk'ar tashi ya rasa ya zaiyi,shine ya nemi shawarar abokin sa Alhaji Maude, nan take Alhaji Maude ya bawa Daddy shawarar ya d'auke Khaleel gabad'aya ya raba shi da k'asar ma,ya fake da zai kaishi Holland karatu kawai,ai dole dai ya hak'ura,

Wannan shine Asalin tafiyar Khaleel England karatu,tafiyar da yayi ta cikin tsananin tashin hankali da kuka,domin a ranar da za su tafi har gidan nan Daddy ya ta ko domin ya d'au ki Khaleel Wanda ke mak'ale da Hamza tun farar safiya suna kukan rabuwa,a ranar Daddy ya ci mutuncin mu,yasa Hannu yana Jan Khaleel Wanda ke kuka sosai,daga k'arshe ma sumewa yayi,amma don rashin tausayi haka Daddy ya fita da Khaleel, kuma bai fasa kai shi England ba,yayin da su Daddyn suka koma Abuja da zama gabad'aya.


Ko a lokacin baya da na so raba abotar Khaleel da Hamza Mahaifin Khaleel d'in ne yazo ya ci mutuncin mu Hidaya,shine abin da ya b'ata min rai har na so raba abotar,daga baya kuma tausayin su ya saka na hak'ura na barsu suka cigaba da Abotar su.


Wannan ce Asalin rabuwar Hamza da Khaleel a muhalli d'aya,sai dai zuciyoyin su na manne da juna,basu tab'a mantawa da juna ba duk da basa tare,Na sha wahala kafin Hamza ya jurewa rashin Khaleel a hankali.

Mamakin Daddy bai wuce duk da ya raba su amma basu daina abota ba,Khaleel bai dai na hidimta mana ba,saima abin da ya k'aru,hakan yasa ya sake tsanar mu ni da Hamza.


Hidaya babu abin da za mu ce da Khaleel sai godiya da fatan alkairi,wallahi tallahi bakina yayi kad'an wajen bayyana miki yawan hidimar Khaleel a garemu,Allah kad'ai ya sani,yaron nan ya so mu,ya k'aunace mu,ya hanamu muyi kuka,kullum burinsa muyi dariya,Hidaya ke da kanki kiyi alk'alanci,kinga ya dace Khaleel ya nemi wani Abu gurin Hamza ya hana shi?kina ganin Khaleel bai cancanta Hamza ya sadaukar masa da komai ba?

Hidaya da Hawaye ke zuba a idanuwan ta ta dubi Ummi Umma cikin fitar hayyaci,kawai sai ta fad'a k'irjin Umma ta wani fashe da kuka tana rungume Umman.......!


Comments
share
vote
pls


*GARKUWA BIYU*


BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter 10 · 0% Book details