← Book details Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 5 OF 31

BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI DA NA ARBA'IN DA TAKWAS

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

***Wani irin shock taji a jikinta,ta samu Zuciyar ta da shiga K'unci,amma haka ta daure ta amsa cikin rawar murya ba tare da ta juya ba.


"To Ya Hamza,Allah ya kai mu goben lafiya….!


Tana fad'in hakan ta fice da hanzari,ya bi ta da kallo yana sauke ajiyar zuciya,sai lokacin ya tuna ma Ashe waya yake da Khaleel, hakan yasa ya maida wayar kunnen sa suka cigaba da magana.


Da ya sanar da Umma cewar zai d'auki Hidaya su ta fi Abuja taren Khaleel da k'yar ta amince,sai da ya dinga yi mata magiya tukunna,haka kawai taji a ranta bata son ya tafi da Hidayan,bata san kuma menene dalilin hakan ba,tunda ya sha d'aukar ta su ta fi kano dangin Umman,kuma suje lafiya su dawo lafiya ba tare da wani Abu ba.


Washe gari kam k'arfe takwas na safe sun shirya tsaf !daga Hidayan har Hamza suna ta fama da fad'uwar gaba wadda basu san ko ta menene ba,haka nan Hidaya ta kwana da tunanin wayar da suka yi ita da Khaleel a Daren jiya,wadda yake fad'a mata cewar ta taimake shi ta bi Hamza Abuja domin tararsa,yana so yayi wani Abu da zai bata mamaki,ta kasa gane me yake nufi,sai dai ta samu Zuciyar ta da fargaba sosai akan wane mamaki uncle Khaleel yake son ba ta…?

Kamar had'in baki,kayan da Hamza ya sanya iri d'aya ne da na Hidaya,wani boyel ne me kyau green da ya d'inka musu tare,yayi musu kyau sosai,Hidaya ta sha d'inkin doguwar riga wadda ta kamata daga sama,ta bud'e daga k'asa,ta saka farin Mayafi da fashion fari na sark'a da yari,sai agogo shi ma fari,mayafin ta da takalmin ta ma fari ne, Wanda ta yane jikinta da shi,babu kwalliya sosai a fuskar ta illa powder da wet lip da ya sa lips d'in ta suke k'yalli da walwali,don Hamza har satar kallon bakin ta ya dinga yi….

Shi ma sai yayi amfani da farar hula mai ratsin green a ciki,da takalmi green,wani irin kyawu suka yi na ban mamaki tamkar wasu fure,Umma kanta ta k'yasa su,ta dinga murmushi tana kallon su tana addu'a a Zuciyar ta na cikar burinta,har bakin mota ta raka su tana musu fatan alkairi da isa Abuja lafiya.


Sun fara tafiya a kan titi shiru babu me magana,Hamza na kallon gabansa yana tuk'i,Hidaya kam tana kallon gefen hanya da bishiyoyin da su ke wucewa,k'amshin da Ya Hamza yake ya saukar mata da wata irin kasala,duk yau sai taga yayi mata wani mugun kyau da bata tab'a gani a tare da shi ba,fatarsa har wani shek'i take,Zuciyar ta ta sake rauni sosai,tana ji ina ma Ya Hamza ya bayyana mata soyayyar sa,da sonsa ta rayu,babu wani namiji da take jin ya tunbatsa a filin Zuciyar ta sai shi,amma irin kalaman da taji yana zayyanawa akan wacce yake so jiya ya tashi hankalin ta,kwana tayi tana hawaye,da zarar ta ga Umma zata ga hawayen ta sai tayi saurin sharewa,ta san Ya Hamza yayi mata nisa,yanayin yadda yake bata kulawa tamkar alamun so ta d'auke shi,Ashe Zuciyar ta bata gaya mata dai dai ba,gara ma tun wuri ta cireshi a ranta ta maidashi matsayin sa na baya wato yayanta,tunda shi ma a k'anwa ya d'auke ta.


Da taji Zuciyar ta ta dameta da tunani sai ta kife kanta a kan cinyar ta kawai tana sakin ajiyar zuciya,hawaye na son tawo mata,ita kuma bata son ya gani balle ya fuskanci yanayin da take ciki

A b'angaren Hamza shi ma tuk'in kawai yake yi,amma Zuciyar sa na ga Hidayan,ji yake tamkar ya d'auke ta ya tsaga k'irjinsa ya cillata filin Zuciyar sa ya rufe,yau yake son ya kawo k'arshen komai!burinsa ya had'u da Khaleel ya fallasa masa sirrin Ruhin sa domin ya samu sauk'i,daga nan kuma sai ya tunkari Hidayan,ya jinkirta bai sanar da ita bane saboda bai ma san ta yadda zai fad'a mata ba,ya tabbatar Khaleel zai bashi shawarar hanyar da zai bi domin ya sanar da itan,shi kuma Khaleel sai ya sanar wa Umma,saboda yana jin kunyar kallon tsabar idanun Umma ya fad'a mata cewar yana son ta bashi Hidaya ya Aura….

Har suka isa Abuja babu Wanda ya kula wani a tsakanin su,su Kansu suna mamakin yadda suke share junansu kamar wasu abokan gaba.babu abin da ke tashi a motar sai saukar numfashin su da kuma karatun alk'ur'ani da Hamza ya saka a motar,shiyasa ma suka sami Kansu cikin nutsuwa sosai.

A hankali ya shiga da motarsa airport d'in ya faka ta,ya kalli agogon hannunsa sai yaga lokaci har ya k'ure,tuni jirgin da Khaleel ya hau ya sauka,hanzari kawai yake domin yayi ido biyu da Khaleel, amma dole ya fara Neman toilet ya rage mararsa saboda wani fitsari da ya matse shi sosai,ya kashe motar yana wani lumshe idanu da fad'in"Alhamdulillah "Sannan ya waiwaya ya dubi Hidaya da sai lokacin ta d'ago kanta,ya D'an tsura mata idanuwan sa yana duban ta,ita kam sai ta sunkuyar da kai tana wasa da zoben hannun ta,saboda bata son kallon tsakiyar idanuwan sa,ya sauke ajiyar zuciya ya ambaci sunanta a hankali.

" Hidayaaaaaa….!

Kanta a k'asa ta amsa tana muskutawa,taji kiran har cikin tsakiyar kanta,tsigar jikinta na mik'ewa yarrrrr !

Ya D'an yi baya da hular kansa ya shafa goshinsa,sannan ya sake kallon ta yace.

"Ki D'an yi min hak'uri kad'an ki zauna cikin motar,zan je na gabatar da wani uzuri ko da minti biyar ne,idan na dawo sai mu shiga ciki,don na san tuni Khaleel ya sauka yana jiran mu.

Gyad'a kai tayi kawai,murya a sark'afe tace.

" To Ya Hamza……!

Yayi murmushi sannan ya b'alle murfin motar ya fita,sai lokacin ta sake d'aga idanu ta bi bayansa da kallo,tafiyar sa kan ta abar Sha'awa ce,yana tafe a nutse cikin wani irin kwarjini da Allah yayi masa baiwarsa,baki sake take kallon sa har ya shige wata kwana,sai lokacin ta d'auke idanuwan ta ta runtse su tana sauke ajiyar zuciya, sai ta samu bakin ta da furta cewar.

"Ya Allah na! Ina rok'on ka ka bani Ya Hamza a matsayin mijin Aure na,Ya Allah kai ne ka halicci zuciyata da sonsa tun ban san menene son ba !Ya Ubangiji na mamallakin komai da kowa ina son Ya Hamza,ina k'aunar sa,shi kad'ai nake so Ya Allah !sarki na ina Neman taimako gareka ka cika min burina,kasa Ya Hamza ya zama alkairi a gareni…..!

Ta share k'wallarta da gefen hannun ta,ta koma ta jingina da kujerar ta tana lumshe idanuwanta, kusan minti goma tana a haka ba taji dawowar Ya Hamza ba,a hankali ta bud'e idanuwan ta,tana hangen mutane jefi jefi suna kai kawo a harabar airport d'in,bata san me yasa ba,kawai sai ta tsinci kanta da bud'e murfin motar ta fito,ta shak'i wata iska mai dad'i ta lumshe ido,rufe motar tayi ta jingina da ita tana gyara lullub'in gyalen da ke jikinta,mutane na wucewa wasu na kallon ta ,musamman maza,sai taji ina ma bata fito ba,sai dai ta gaji da zaman motar ne gabad'aya, shi kuma Ya Hamza daga minti biyar yanzu kusan inti goma sha biyar kenan amma shiru bai dawoba,haka dai ta cigaba da tsayuwa jikin motar tana son ganin ta in da Ya Hamzan zai b'ullo.


*****************


Shi kam Hamza ya samu ya rage mararsa sai yaji sakayau,ya fito daga toilet d'in Wanda ya kasance na maza(male).

Yana fitowa zai karya kwana in da zai samu Hidaya kawai sai idanuwan sa suka kai kan wata mata,k'irjinsa yayi bala'in bugawa saboda yadda matar tayi masa mugun kama da Mummyn Hidaya,domin ko daga barci ya tashi zai iya shaidata,ya bita da kallo bakin sa a sake k'irjinsa na dokawa,ganin tana shirin b'ace masa da hanzari ya taka yabi bayan ta,sai dai yadda jikinsa ya mutu sai ya kasa sauri,illa d'aga mata Hannu da ya dinga yi yana ambatar .

"Mummy…Mummy…Mummy….!

Ko waiwayowa bata yi ba,domin bata san ma yana yi ba,yana biye da ita yana k'wala kiranta har suka je wajen wasu dandazon mutane da kowa yake harkokinsa,tana shigewa cikin mutanen nan ya nemeta tsaf ya rasa,nan da nan ya rud'e shi ma ya kutsa tsakanin su yana ta dube dube idanuwan sa a warwaje,Iya duban da zai yi baiyi nasarar ganin ta ba,a rikice ya fara bin mutane yana tambayar su wai basu ga wata mata sanye da bak'ar doguwar riga ba,wasu suce basu ganta ba,wasu kam kallon tab'ab'b'e suke masa duk da gashi nan tsaf da shi,amma yadda yake magana a rikice jikinsa na rawa sai suke ganin yana da matsala k'ila…

Hamza haka ya dinga zagaye gurin yana fatan idanuwan sa suyi katarin ganin ta,amma ko mai kama da ita bai gani ba,kamar yayi kuka haka yaji,ya dafe kansa yana ambaton Allah.


*****************


A hankali yake tako steps d'in jirgin domin sakkowa,cikin jerin mutanen da suke k'ok'arin sakkowa,sanye yake da suite bak'a wadda ta amshe shi,idanuwan sa sanye da bak'in glass da ya k'ara masa kyau kasancewar sa fari tas,sai da ya sakko k'asa sannan ya kai Hannu ya zare glass d'in yana kallon mutanen da ke warwatse a wajen…

Mutane ne dank'am a wajen,wasu a zaune wasu a tsaye,wad'anda suka zo taren y'an uwan su,daga gefe ALHAJI Mudassir (Daddy)ne tsaye rungume da Hannu a k'irji,daga gefensa matarsa ce Anty Kubra,sai y'ay'anta guda biyu mace da namiji ,Sameera da Sameer,wad'anda ba za su wuce shekara takwas zuwa goma sha d'aya ba,dukkanin su fuskar su d'auke da murmushi da zumud'in hango Khaleel yana isowa wajen su….


Tun ma kafin ya k'araso daddy ya d'aga k'afa ya isa gareshi,yana zuwa suka rungume juna cikin kewa da murna,daddy sai shafa kan Khaleel yake yana jin wata matsananciyar k'aunar sa a ransa,musamman da daddyn na sa ya zama wani mutumin kirki sab'anin baya,kuma ya san addu'ar da Hamza yasa yake masa ne tayi tasiri,tare da k'ok'arin Anty Kubra mace mai kirki da d'ora mijinta akan dai dai.


Sun jima rungume da juna kafin Khaleel ya zame jikinsa ya nufi Anty Kubra da ke ta kallonsa tana murmushi,yana zuwa ya durk'usa yana gaishe ta,cikin fara'a da kulawa take amsawa da.

"Lafiya k'alau ibraheemul Khaleel dafatan ka dawo lafiya?ina fatan kuma ka dawo da shirin Aure,domin tuni na gama shirin aurar da kai yadda kayi girman nan ya kamata ace zuwa yanzu ina da suruka a Hannu."

Wani irin murmushi ya saki yana janyo hannun k'annensa yana shafa Kansu,cikin karsashi ya amsa mata yana kallon daddyn sa yace.

"Karki damu Anty,ban sauka k'asar nan ba sai da shiri na,a yau zan gabatar muku da wadda nake so insha Allah,kuma ko cikin sati d'aya kuke buk'atar ta zama matata ina da yak'inin hakan zai tabbata insha Allah…


Daddy da Anty Kubra farinciki ya ka ma su,cikin zumud'i suke fatan ganin matar da Khaleel ya zab'o a matsayin matar da zai aura,Khaleel ya d'aga kai ya fara hange hange kamar mai Neman wani Abu,har suka lura da shi,daddy ya dube shi yace…

" Kana Neman wani Abu ne…!?

Ya gyad'a kai yana yamutsa fuska yace.

"Eh daddy ina Neman Aboki ne,mun yi da shi zuwa wannan lokacin zai zo airport d'in nan,amma kuma har yanzu shiru.."

"Wai Hamza kake nufi…!?

Anty ta ambata tana kallon sa.

Ya amsa da cewa.

" Eh Anty,naga security nan ba kowa suke bari ya shigo nan ba,k'ila a waje ya tsaya,ku D'an jira ni na duba shi please"

"OK ka hanzarta" Daddy ya ambata yana dafa kafad'ar sa.

Khaleel yayi murmushi ya gyad'a kai,sannan ya juya da hanzari ya nufi harabar airport d'in har da D'an gudun sa.


*****************


Har lokacin tana tsaye jikin motar,kamar ta fashe da kuka saboda jiran Ya Hamza,ya tafi ya shanyata ya manta da ita.


Wata irin iska ce mai k'arfi ta taso kamar guguwa,Hidaya taji iskar na shirin d'auke ta ta jefar da ita,tunda ba k'iba ce da ita ba,da hanzari ta juya tana shirin bud'e motar ta shige,sai iskar ta janye mayafin jikinta ta tafi da shi,a rud'e Hidaya ta kuma juyawa tana k'ok'arin kamo mayafin ta da iska ta d'auke,amma ina yayi mata nisa,da hanzari ta D'an taka da gudu tana mik'a Hannu da niyyar kamowa,a dai dai lokacin da iskar ta soma lafawa,mayafin ya fara yin k'asa,ya sauka a fuskar Khaleel da ya k'araso wajen domin duba Hamza,ruf ya rufe masa fuska.


Hidaya ta tsaya tana maida numfashin tsoro,tana kallon yadda mayafin ta ya fad'a jikin wani namiji Wanda bata san ko wanene bane,saboda yadda k'ura ta cika mata idanuwan ta,shi kam Khaleel k'amshin da ke jikin mayafin ya soma shak'a yana lumshe idanu,kafin yasa hannun sa a hankali ya soma zareshi shi daga fuskar sa ya rik'e a hannun sa,sannan ya dubi Hidaya da ke tsaye,ya sakar mata murmushi me tafiya da hankalin mutum,yana mata wani kallo tamkar idanuwan sa za su tsiyaye…


Zaro idanuwa Hidaya tayi sosai saboda ta shaida fuskar sa,wani irin murmushi ya sub'uce mata bata shirya ba,cikin tsananin murna ta rufe bakin ta idanuwa warwaje ta ambaci.


"Uncle Khaleel kai ne…!?da gaske kai ne…!?wayyoo your highly welcome Uncle Khaleel…..!


Wani irin taku ya fara yi tamkar d'awisu zuwa gabanta,baki sake take kallonsa tana wani irin murmushin farinciki,shi kam yanayin fuskar sa ta had'a Abubuwa da dama,kamar fata,d'oki,shauk'i,soyayyah,k'auna,bege,kewa,da sauran su.


Yana zuwa gaban ta ya ci burki ya wani tsura mata idanu,mik'a mata mayafin hannunsa yayi,ta mik'a Hannu a hankali tana shirin karb'a,ta d'ora hannun ta a gefen mayafin ta rik'e,yayin da shi yake rik'e da d'aya gefen,idanuwan sa a kanta tamkar ya narke,suna kallon juna ya bud'e baki da k'yar yace.


" Zahrahhhhhhh…..!

Hidaya ta waiwaya gefen ta domin taga Zahran da Khaleel ya ambata,amma bata ga kowa ba,dawo da kallonta tayi zuwa gareshi,tana juya idanuwa a hankali da tambayar sa ina Zahra …!?


Cikin wani yanayi ya rangwad'a kai gefe ya k'urawa Hidaya idanu ya fara magana cikin wata k'ayatacciyar murya.


"Kalli cikin idanuwa na Zahra….za ki samu Labarin abin da yake cikin zuciya ta…..!


Sai Hidaya ta samu kanta da kallon sa,da sauri ta rintse idanuwan ta tsigar jikinta na mik'ewa saboda wani Abu da yake fitowa ta cikin idanuwan sa…cikin wata murya ya sake cewa.


" Kin gani Zahraaa..!?kinga abin da ke ciki ko…!?


Girgiza kai tayi cikin rawar jiki,har lokacin kuma suna rik'e da mayafin a tare,da k'yar ta fizgo magana cikin rawar murya..

"Wai wacece Zahra Uncle Khaleel…!?ban ga Zahran da kake ta ambata ba…!

Kawai sai ya zare mayafin daga hannun ta, ya warware shi yana yafa mata a kanta,sannan ya lek'a fuskar ta yana murmushi yace.


" Ai babu wata Zahra bayan Hidaya….idan har baki gano abin da yake cikin zuciyata ta idanuwana ba, bari na fassara miki……ILOVE YOU WITH ALL MY HEART HIDAYA…..!


A razane ta d'ago idanuwa cikin fitar hayyaci tana duban sa,a dai dai lokacin da Hamza ya iso gaban su yana duban su cikin wani yanayi,kunnuwan sa kuma suka jiye masa gingimemiyar Kalmar da Khaleel ya furtawa Hidaya……..!


Comments
Share
Vote
Pls


*GARKUWA BIYU*


BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter 5 · 0% Book details