BABI NA ARBA'IN DA BIYAR DA NA ARBA'IN DA SHIDA
Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read
***Wani irin kallo ya bita da shi kafin ya D'an sunkuyar da kai yana Sosa k'eya,ita kam Hidaya jikinta ne ya kama rawa kar kar ganin Abubuwan da suka zubo a ledar,tayi k'asa da kai cikin wata muguwar kunya da ta rufe ta,a dai dai lokacin kuma Umma ta bud'e k'ofar bathroom ta fito daga wanka,k'arar bud'e k'ofar ya k'ara firgita su suka wani zabura kamar su ruga da gudu,Umma ta bi su da kallo sannan ta dubi brezia d'in da ke zube a k'asa a watse,Hamza kamar ya nutse don kunya,cikin azama ya d'aga k'afafu yayi saurin ficewa daga d'akin har da had'awa da D'an gudun sa.
Yana fita Umma ta maida kallon ta kan Hidaya da ke tsaye tsamo tsamo kai a sunkuye,cikin alamun fad'a fad'a Umma ta fara magana.
"Yanzu ke Fad'imatul Hidaya baki da wani Sirri na kanki kenan?komai da ya shafeki sai kin fad'awa Hamza ko kin nuna masa?rigar nono ma da ake son sayata sai da kika nuna masa?to me kike so ya gani kenan?iya gejin girman da k'irjinki ya fara ko kuwa…!?
K'irjin Hidaya ya buga da k'arfi,Hawaye ya tawo mata,nan da nan ta fashe da wani irin kuka tana cewa.
" Ni wallahi Umma bai nuna masa nayi ba,shine fa ya k'wace wai sai dai mu raba abin da kika siyo min,ni dai wallahi ba ruwana ba laifi ba bane…!
Umma ta D'an yi mata gwalo yadda ba zata gani ba,ta juya baya tana D'an murmushi ta k'ara kunna Hidaya,domin cewa tayi.
"To shi da bashi da nonuwan saka brezia mai zai yi da ita?sai dai da yake ya kusa Aure sai ki bashi ko guda uku ya saka a lefe kawai,duk da k'ananu ne ina tunanin za ta yiwa matar da zai aura kad'an…"
Hidaya ta ji kamar Umma ta caka mata wuk'a a k'ahon zuciya,kawai sai ta sake rushewa da kuka ta fad'a gadon Umma tana jin zuciyar ta na ciwo,Umma ta tab'e baki ta nufi wardrobe tana cewa.
"Ai sai ki yi ta kukan…!tun da baya miki wahala…!"
******************
Duk ranar Hidaya haka ta kasance kamar mara lafiya babu walwala,hawaye kuwa har gajiya suka yi da zuba,haka kawai da ta tuna cewa Ya Hamza yaje zance wajen budurwa sai ta kama hawaye,ta rasa me yasa hakan,bata san me yasa take jin b'acin rai idan taga Hamza ya kula wata mace ba,duk da ma bashi da kule kulen y'ammata,duk abin da take Umma na lura da ita,Sosai taji dad'in yadda ta kunna Hidaya,a wani salo na ta na son cimma k'udurin ta,haka nan take tunanin saura Hamzan shi ma.
Washe gari Hidaya ta tafi gidan su Sumayya za su yi karatun jarrabawa,Umma ma ta D'an fita,sai Hamza kawai da bai fita Aiki ba,saboda ciwon kai da ya tashi da shi,yana kwance a parlour'n Umma akan doguwar kujera,idanuwan sa a lumshe,tunane tunane sun cika zuciyar sa,har Umma ta d'aga labulen d'akin ta shigo da sallama bai ji ba,sai da ta ambaci sunan sa da k'arfi sannan ya bud'e idanuwan sa da suka sauya kala,ya mik'e zaune yana dafe kansa,cikin kasalalliyar murya ya dubi umma da ke tsaye da k'atuwar Leda a hannun ta fal da kaya yace.
"Umma har kin dawo?sannu da dawowa."
Ta nemi gefen sa ta zauna,sannan ta amsa.
"Yawwa sannu ya kan na ka?ko har yanzu yana ciwon ne…!?
Ya lumshe idanuwan sa.
" yana yi Umma,amma dai ya ragu tunda na sha magani"
"Allah ya k'ara sauk'i,Allah ya sa ba maleria ba ne…..wai har yanzu Hidaya bata dawo ba ne…?
Ta zarce da tambayar sa.
Ya jijjiga kai ya jingina da bayan kujerar yana lumshe idanuwa,ambatar sunan Hidaya kad'ai na tab'a ruhin sa.
Umma ta D'an sa ci kallon sa tace.
" Aikuwa ya kamata ta dawo gida haka,ko Dan ta duba kayayyakin nan da na siyo mata idan sun yi mata ….
Ya bud'e idanu a hankali ya dubi Umma,sai Umma ta sake cewa cikin murmushi.
"Au!tunda ma gaka ai sai ka tayata dubawa,domin naga kusan ra'ayin ku ya zo d'aya,kayan Auren ta na fara siya domin na fara ragewa,kar lokacin ya zo Abubuwa suyi min ya…….
Maganar Umma ta katse saboda wata zabura da taga Hamza yayi cikin zare idanuwa yana kallon ta,a rikice yace.
" Aure kuma..!?wane irin Aure Umma..!?Hidayan za a yi wa Aure..!?
Ya jero tambayoyi.
Umma ta mik'e ta nufi hanyar d'aki tana cewa.
"Au wai ban gaya maka ba daman?Ai na kusa Aurar da Fatima,Auren wuri zan mata ba zan barta ta sangame ba..kai dai da ka zama tuzuru ka k'i Neman matar Aure kai ta zama Hamza…Hidaya kam nan da wani lokaci k'ank'ani za ka ganta a gidan mijinta"
Tana kammala magana ta shige d'akin ta ta barshi sake da baki da hanci da idanuwa,cikin wani yana yi na miliyoyin tashin hankali da firgitarwa…..!
Umma kam tunda ta shige d'aki take murmushi mai kama da dariya,tana ganin wasan da ta buga tsakanin Hamza da Hidaya zai yi tasiri kamar yadda take so….
****************
Kwana biyu da hakan Hamza da Hidaya suna cikin damuwa,ita Hidaya ma kam kullum sai ta yi kuka,a ganin ta Ya Hamza yayi mata babban laifi da har ya kasa sanar da ita ya samu matar Aure,sai dai taji maganar a bakin Umma,wannan babban laifi ne da take ganin yayi mata,saboda basa b'oyewa junansu sirrikan su,amma Ya Hamza ya b'oye mata wannan,haka nan kuma take jin tsanar wadda yake so d'in duk da bata san kowace ce ba.
Daga b'angaren sa shi ma hakan take!ko nace ma ya zarce hakan,domin Hamza ko bacci ba yayi sai yawan tunani,babu abin da ke cin Zuciyar sa irin idan ya tuna da kalaman Umma,wai zata aurar da Hidaya,to ga wa zata aurar da ita?ga wani haushin Hidayan da yake ji ganin ta b'oye masa,domin gani yake ai ta san komai,Hamza dai har wata rama yayi ta musamman saboda damuwa,sai suka zama sirikan juna shi da Hidayan,babu kulawa da juna da zama suyi hira da juna kamar yanda suka saba,ko cikakken kallon juna basa yi sai dai a dinga satar kallo,da an had'a idanuwa ayi saurin kau da kai ana basarwa,Hidaya na ganin Ya Hamzan ta ya daina yayin ta,tunda ya samu mai d'ebe masa kewa,ya bata matsayi fiye da na ta,in ta tuna hakan sai hawaye ya zubo mata,sai ta faki idanun Umma ta share.
Haka Hamza ma ke ganin Hidayan a matsayin wadda ta juya masa baya,a ganinsa ta samu Wanda ya fishi,shiyasa ta daina bashi kulawa kamar baya,duk da bata daina yi masa komai ba,kullum ita take dafa masa abinci,ta gyara masa d'aki,tayi wankin singlet da jallabiyoyin sa,da duk wani aiki da ya dangance shi,yawan zama suyi hira ne da magana kawai ta daina.
Umma na kallon takun su,tana murna tayi Abu domin su hankalta,sai taga Abu na neman zame mata D'an zani,yo D'an zani mana!ita a yadda ta lura tun Hamza da Hidaya na da matakin k'ananan shekaru suka fad'a tarkon Soyayya da K'aunar junan su,har kuma zuwa girman su,amma har izuwa wannan lokaci sun kasa yardar wa junan su cewa son juna suke so irin Wanda yake rikid'ewa ya zama Auratayya,a ganin su so irin na Yaya da k'anwa kawai suke yi,shine dalilin da ta jefa wannan game d'in a tsakanin su wai domin su Ankara su furtawa junan su Soyayya,amma inah!sai ta lura ma gabad'aya sun kaucewa tsarin,a maimakon k'udurin ta ya tabbata,sai wankin hula yake son kai ta dare.
Sai dai duk da hakan ta zuba musu ido domin taga gudun Ruwan su,sannan tana addu'ar idan da alkairi a lamarin Allah ya tabbatar.
Ko da Hamza suka yi waya da Khaleel sai da ya gane yana cikin damuwa,yayi ta tambayar sa dalilin damuwar amma ya kasa sanar da shi komai,to me zai ce masa?saboda za a aurar da Hidaya yake fushi ko me?tunda dai shi bai furta yana son Hidayan ba balle a ce kishi yake,tilas Khaleel ya k'yale shi,sai kuma ya wanke masa zuciya da albishir d'in dawowar sa Nigeria a cikin wannan satin,a matsayin cikakken Lauya me kare hak'k'in D'an Adam,musamman wad'anda aka zalinta.
Wannan albishir tamkar na zuwa aikin hajji ya zame wa Hamza,farinciki ya yawaita a Zuciyar sa Wanda ya jima bai ji irin sa ba ko makamancin sa,saboda murna ko kammala wayar basu yi ba ya katse ta ya ruga parlour'n Umma fuska kamar gonar auduga domin kai rahoto.
Umma na zaune k'afafuwan ta kan cinyar Hidaya tana yanke mata farce,ya fad'o d'akin kamar an jeho shi har sai da suka razana,Umma ta dubeshi tace.
"Kai lafiyar ka kuwa…!?
Ya k'arasa gaban ta ya tsuguna har kafad'ar sa na k'ok'arin gogar ta Hidaya,ta yi hanzarin matsawa,ya rik'o hannun Umma yana wata irin dariya yana fad'in.
" Umma na ki tayani murna,cikin satin nan Khaleel d'ina zai dawo k'asar nan gabad'aya…yanzu ya gama yi min albishir….
Wani irin farinciki ya kwarara a Zuciyar Umma,har ma da Hidaya da tsananin murna ya sa tamkar ta tashi ta buga tsalle,ta rufe bakin ta da hannayen ta tana zaro idanu cikin tsananin murna,Umma kam hamdala kawai take wa Allah da jin wannan magana,lallai tilas a taya Hamza murnar dawowar babban abokin sa Wanda ya zame masa D'an uwa….
Juyawa yayi yana duban Hidaya,suka had'a idanu,wasu kibiyoyi suka tsikari cikin idanuwan su,k'irjin su yayi wata irin bugawa,tsigar jikin su ta tashi,da sauri Hidaya ta kautar da idanuwan ta,ta mik'e da hanzari ta fad'a d'akin Umma,shi kam Hamza bin ta yayi da idanu tamkar dolo,yana lumshe idanuwa da sakin wata nannauyar ajiyar zuciya…..
Umma ta bi shi da kallo yayin da na sa idanuwan ke kan k'ofar d'akin Umma da Hidaya ta shige….!
****************
Cikin kwanakin sai Hidaya ta samu walwala sosai,ba domin komai ba sai yawan kiranta da Khaleel yake su sha hira,ko suyi video call har ta watsap hira suke sha,da yake Khaleel gwanin iya tsara zance ne,gashi da shagwab'a tamkar mace,yanayin yadda yake magana kad'ai wani zubin yana narkar da Zuciyar Hidaya.
Khaleel kam tuni yake son fallasa asirin Zuciyar sa game da Hidaya,wata soyayya yake mata wadda bai tab'a tunanin akwai ta a duniya ba,tun ranar da ya fara ganin ta yaji fad'uwar gaba sonta ya addabeshi,ya rayu da soyayyarta tsawon wannan lokaci,Wanda ko Hamza bai furtawa ba saboda yana jiran ya dawo k'asar sa gabad'aya sannan ya bayyana manufar sa,
Da gaske yake son Auren Hidaya domin ya taimaki rayuwar ta,ya inganta ta ta yadda zata zama d'aya daga cikin matan da duniya zata yi alfahari da su,yana son Hidaya,so mara misali,yana ji a ransa kuma ita ma zata so shi,haka nan kowa zaiyi alfahari da Auren su.
Hamza kam sai ya share ta,ganin yadda ta watsar da shi kawai sabgarta take,shi ma ya shiga sabgar shirye shiryen taron Jinin jikinsa wato Ibraheem Khaleel…
Saura kwana d'aya Khaleel ya dawo Hamza na zaune a d'akin sa,waya ce a kunnen sa,fuskarsa d'auke da murmushi suna hira da Khaleel,Khaleel d'in sai shagwab'a yake masa wai shi yake so yazo Abuja ya tarbeshi a airport, shi kam Hamza tsoron had'uwa da daddy yake yi,sai Khaleel ke ce masa kar ya ji komai in dai daddyn sa ne ya sauya,ya fara watsar da halayen sa mara sa kyau,Dan har ce masa yayi yana jin kunyar abin da yayi wa su Hamzan a rayuwa,kuma zai nemi afuwar su,nan da nan Hamza yaji farinciki ya kamashi,ya tabbatar wa Khaleel cewa insha Allah gobe da wurwuri zai tawo Abuja,domin yana son jirgin ma ya sauka a gaban sa,Khaleel yayi ta murna,daga k'arshe ya sanyaya murya yace da Hamza.
"Abokina ina son mu tattauna wata magana ni da kai,amma mu barta sai na dawo sai mu yi insha Allah…"
Hamza ya sauke ajiyar zuciya yace.
"Ni ma ina son yin magana da kai akan wani Abu da yake damuna,amma bari na bar maganar zuwa lokacin da zaka dawo sai mu tattauna gabad'aya ko….?
Khaleel yayi murmushi yace.
" Aboki ka san yanayin da muryarka take ciki kuwa…?
Hamza ya amsa da .
"Ah ,ah,wane yanayi take ciki..!?
Khaleel ya kwashe da dariya yace.
" Allah ta yi min kama da Wanda ya fad'a tarkon soyayya,Aboki ko ka fara soyayya ne ban sani ba…?
Hamza ya lumshe idanu,k'irjinsa na bugawa sosai yace.
"Ta ya ya kayi saurin d'agoni Khaleel? Ya ya akayi ka gane zuciyata ta fad'a tarkon soyayya?
Khaleel ya sauke numfashi ,a hankali yace.
" saboda ni ma ina cikin irin yanayin …..ni ma na fad'a tarkon Soyayya da K'auna…!
Hamza yayi k'asa da murya yana jin shauk'i kamar ya narke,ya lumshe idanuwan sa ya rufe su ruf sannan ya cewa Khaleel.
"Haka kawai ta addabi zuciyata Khaleel, yanzu haka da sonta nake rayuwa a jikina,raina na sonta,zuciyata na k'aunar ta,idanuwana na begenta,jikina na mararinta,bana bacci Khaleel ,saboda yadda tunanin ta yake tsinkamin zuciya,daman haka so yake Khaleel…!?haka yake da narkar da Zuciyar ma'abota Soyayyah…!?
Shi ma Khaleel ya sanyaya murya,cike da shauk'i ya fara bawa Hamza amsa da hanzari.
" Eh Aboki,tabbas duk abin kake ji akan wadda kake so nima haka nake ji akan wadda nake so,ko ma fiye da haka,ta makantar da idanuwana fa,ta to she kunnuwana daga jin duk wata dad'in magana idan na tata ba,ta kanainaye ruhina da sassan jikina gabad'aya,sai nake jin muddin ban sameta a duniyata ba zan iya rasa raina Aboki……fatana idan na ambata mata soyayya ta ta rik'e hannuwana ta kaini inuwarta,sannan……
Ya kasa k'arasawa saboda yadda shauk'in soyayya yake tab'a ruhinsa,shi kam Hamza idanuwan sa a lumshe suke,Ashe da shi da Khaleel d'in duk d'aya ne kenan!tunda duk cikin su babu Wanda ya bayyana wa wadda yake so soyayyar,idan kuwa hakane lallai suna ruwa…..
"Ina sonta Khaleel….ta shiga zuciyata saboda tarbiyyarta da nutsuwar ta,son da nake mata shine farincikin duniyata…ina samun lafiya ne idan har ina tare da ita….ruhina na fad'a min da ita na dace a zaman duniyata….zuciyata na martaba ta…ita ce mafarkina a kullum….ina sonta adadin yadda baki ba zai iya furtawa ba…….
Hamza ya furta wad'annan maganganun a lokacin da hawayen soyayya suka ratso fatar idanuwan sa.
" Wow…!Khaleel ya ambata cikin karad'i,sannan ya zarce da magana cikin wani yana yi.
"Lallai Aboki ka zarme da yawa,daman fa an ce irin ku Malamai kun fi kowa iya soyayya,zan so sanin wadda ta zama mai nasara,eh dole na kira ta mai nasara,domin sai mai nasara ce zata same ka a matsayin miji….don Allah Aboki wacece ….!?
Har lokacin idanuwan Hamza a lumshe suke,yayi ajiyar zuciya yace.
" H….
Maganar sa ta katse lokacin da yaji motsi a gabansa,ya bud'e idanu a hankali,sai ya ci karo da Hidaya a gabansa,wadda ke rik'e da flask a hannun ta ta kawo masa abinci,kuma tun kafin ta shigo d'akin take jin wasu irin kalamai da Ya Hamzan yake furtawa akan wacce yake so…kalaman da suka kusa fasa mata k'ok'on kanta,kalaman da ta ji tamkar zubar garwashin wuta a filin zuciyarta…bata san lokacin da k'afafuwan ta suka yi a zarb'ab'in shigewa d'akin ba tare da sallama ba,idanuwan ta cike da hawayen da ta rasa ko na menene…
Wani kallo Hamza ya bita da shi idanuwan sa na narkewa,da gasken gaske Hidaya ta gama da ruhinsa gabad'aya,ita kam wani haushin sa take ji,shiyasa kawai ta dire flask d'in abincin ta juya da hanzari gudun kar yaga hawayen ta…cikin wani yana yi bakin sa yayi azarb'ab'in kiran sunan ta da rawar murya….
"Hidayaaaaaaa…..!
Ta tsaya chak! Ba tare da ta juyo ba,k'afafuwan ta na rawa,tana fata da d'okin jin cewa akan ta yake furta wad'annan kalaman,sai dai ina!ta san da wata yake,Ya Hamza a matsayin K'anwa ya d'auke ta,ta rasa ma ta yadda aka yi zuciyarta ta fad'a kogin sonsa,duk da zuciya tana son mai kyautata mata…kuma Ya Hamza shine Wanda ya kyautata wa rayuwar ta tun daga yarinta zuwa girman ta ….tilas ya zama abin so a gareta….
A maimakon taji muryar sa ta ambata mata abin da take fatan ji !kawai sai ta tsinci muryar da ambata mata cewa.
" Ki shirya gobe da wurwuri za ki rakani Abuja domin mu tari Khaleel a airport…….!
Comment
Share
Vote
Pls
*GARKUWA BIYU*
BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️