BABI NA TAMANIN DA D'AYA DA NA TAMANIN DA BIYU
Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read
***Dai dai k'ofar gidan Aunty Kubra ta tsaya da motar ta,ta juya tana kallon fuskar Khaleel,fuskarta cike da da damuwa ta ce.
"Ga shi mun zo Khaleel,ta ya ya za mu fuskance su?"
Shi ma cikin tarin damuwar ya dube ta,a hankali ya ce.
"Shiga kawai za mu yi Aunty"
Tayi ajiyar zuciya tana jinjina kai,a hankali ta b'alle murfin motar ta fito k'irjinta na tsananin bugawa,Khaleel ma ya fito yana jan numfashi,idanuwan sa k'ur akan k'ofar gidan,zagayowa Aunty tayi gefen da yake tana kallonsa,shi ma kallonta yayi idanuwansa narai narai sannan ya ce.
"K'irjina bugawa yake sosai Aunty....Zuciyata na rawa"
Aunty tayi kasak'e,kafin kuma tayi ajiyar zuciya ta ce.
"Kayi addu'a Khaleel,in sha Allahu komai zai zo da sauk'i"
Jinjina kai yayi,ya fara addu'o'i cikin zuciyar sa,daga nan suka jera shi da Aunty suka nufi zauren gidan domin shiga.
***************
Da d'an gudunta ta biyo su zuwa zauren gidan tana rik'o hannayen su suna fizgewa,da sauri ta sha gaban su tana nishi,fuska babu walwala Hansa'u ta dube ta ta zabga mata harara ta ce.
"Malama matsa mu wuce,domin magana da ke bata da wani amfani wallahi"
Summaya tayi k'aramin tsaki ita ma tana hararar Hidayan,sannan cikin takaici ta ce.
"K'warai kuwa Hansa'u,gaskiya yanzu na k'ara tabbatar da cewar Hidaya bata da hankali,kuma bata san in da yake mata ciwo ba"
Hidaya ta marairaice kamar tayi kuka,tana duban su ta fara magana cikin rauni.
"Ya kamata ku fuskanceni k'awayena,menene abin fushi dan na fad'a muku sirrin zuciyata,wallahi ba laifina ba ne,kawai na tsinci zuciyata ne da tausayawa Uncle Khaleel,ga kuma tsananin soyayyarsa da take addabata kamar ta faso k'irjina,yanzu haka ji nake idanuwana tamkar su makance saboda rashin ganinsa....
Wani mugun tsaki da Hansa'u ta saki sai da ya tsorata Hidaya,cikin matuk'ar fushi Hansa'u ta dubi Sumayya ta ce.
"Sumayya ina jin kamar nayi ta dukan Hidaya wallahi,ina ji kamar nai ta kikkifa mata mari saboda b'acin ran da take saka ni,wai an ya kuwa lafiyar Hidaya k'alau?an ya kuwa bata da aljanu?"
Summaya ta keb'e baki tsananin takaici na cinta,tana dank'arawa Hidaya harara ta yi magana.
"Ai ni Sister Hansa'u ji nake kamar in shak'eta dan bak'inciki,ban da hauka da rashin zuciya duk wulak'ancin da Khaleel d'in yayi mata amma wai har yanzu yana zuciyarta bata fincike d'an iska ba! shege asararre mai kama da nunar rana! ina ganinsa mai hankali da ilimi ashe dak'ik'i ne mara hankali,an gaya masa har yanzu muna cikin zamanin da maza suke dukan mata ne da zai kama ki yayi ta jibgarki kamar jaka?daman duk soyayyar da yake ambata miki ta k'arya ce shigo shigo ba zurfi yayi miki kenan?"
Da sauri Hansa'u ta katseta da ce wa.
"Ke Sumayya ma ta duka kike,ai ba dukan ne abin ji ba,sakin wulak'ancin da yayi mata shine abin dubawa,kwana d'aya da aure,Allah dai yasa bai gama kwashe miki albarkatun jiki ba bak'in d'an iska,wallahi ni dai da zanga Khaleel d'innan a yanzu mai rabani da shi sai Allah,domin zan iya rufe idanuwa na na ci zarafin matsiyaci"
"Ya isa ! ya isheku haka!!"
Hidaya ta daka musu wata muguwar tsawa tana rik'e kanta,wasu hawaye masu zafi suka zubo mata suna bin kumatun ta,cikin matuk'ar fushi da b'acin rai take duban su tana shesshek'ar kuka ta ce.
"Gaskiya baku da kirki ! har ku tsaya a gabana kuna zagin Uncle Khaleel,shin baku san matsayinsa a guna bane?mijinah ne fa,wanda ya nuna min soyayyah! wanda ya zame min GARKUWA,saboda me dan yayi wani kuskure da ya zama k'addararsa za ku dinga aibata min shi?ni bana fushi da shi! kuma ba zan tab'a fushi da shi ba! Uncle Khaleel martabar mahaifinsa ya kare kamar yadda na kare martabar nawa mahaifin duk da baya raye,akan me za ku ga bak'insa?akan me za ku dinga zagin shi?bana buk'atar hakan,idan har za ku zo gabana ku zagar min Uncle Khaleel to gara baku zo ba"
Cikin fushi Summaya ta ce.
"Ni idan kina ambatar Soyayyar nan ji nake kamar na mutu dan takaici,Hidaya in dai haka Soyayya take to Allah ya tsinewa Soyayyah ! Allah ya kwashe mata albarka,domin bata amfaneki da komai ba tunda gashi cikin kwana d'aya da d'abbak'ata an ci mutuncinta,ashe kuwa Soyayya bata da rana,bata yi wani tasiri da amfani ba,kuma ko za ki mutu,ko za ki tsanemu ba za mu fasa zagin Khaleel ba,ba za mu fasa ambatarsa da mugu azzalumi da ya zalunci maraici ba,kuma Allah ba zai barshi ba sai ya ga sakayya da wurwuri"
Kuka Hidaya ta sake fashewa da shi,ta sa hannu ta ture su daga kusa da ita,sannan cikin kuka ta ce.
"Shikenan ku tafi ku barni,tunda ba za ku gane abin da nake nufi ba,ba za ku daina aibata min Uncle Khaleel d'ina ba! bana son ganinku Hansa'u da Sumayya ku tafi gu bani guri,kuma ni har abada zan cigaba da ganin k'imar Uncle Khaleel tare da girmama shi,saboda INA SON SA,INA K'AUNAR SA,SHINE FARIN CIKINA....!
Tana fad'in hakan ta juya ta shige cikin gidan da gudu tana kuka me tab'a zuciya,yayin da ta barsu a tsaye a wajen suna bin ta da kallon mamaki da takaici,tana shigewa a tare suka saki mugun tsaki,sannan Hansa'u ta ce.
"Za ma ki hankalta ki gane nufinmu,kuma dole ne ki cire wani Khaleel daga ranki,Khaleel d'in banza Khaleel d'in wofi,Shege mara rabo kawai"
Fizgar hannun Sumayya Hansa'u tayi suka nufi k'ofar fita daga gidan,suna kai kansu waje suka yi wata muguwar razana suka yi turus jikinsu na mugun rawa da karkarwa,wata muguwar kunya da basu tab'a ji ba ta lullub'esu,basu tab'a jin muzanta ba irin haka,ba komai ya janyo hakan ba illa Khaleel da ke tsaye yana kallon su cikin wani yanayi,ga Aunty Kubra a gefensa a tsaye ita ma sai kallon su take yi,kallon kuma da suke musu ya nuna alamar cewa sunji duk zagi da aibatawar da suke wa Khaleel d'in.
Wani mugun kwarjini Khaleel d'in yayi musu da basu tab'a gani ba,da hanzari suka sunkuyar da kansu suna jin kamar su nutse dan kunya da muzanta,shi kam Khaleel kallonsu kawai yake yi ya kasa d'auke idanu daga kansu,basu b'ata masa rai ba,illah ma jin tsanar kansa da ya k'ara yi,musamman da yaji kalamai masu dad'i da Hidaya take fad'a a kansa,tabbas yayi rashi,rashi mai girma wanda ba zai maida makamancinsa ba ma balle irin sa,wayyo rayuwa ! bai aune ba sai hawaye suka soma sintiri akan fuskar sa.
Summaya ce ta fara jan hannun Hansa'u da sauri suka bar wajen cikin tsananin kunya,Khaleel ya bi su da kallo yana kuka,har suka k'urewa ganinsa,a hankali ya dawo da kallonsa kan Aunty,ita ma hawayen ne ya cicciko idanuwan ta,amma duk da hakan sai ta girgiza masa kai alamar ya daina kuka,a maimakon ya daina sai ya sake fashewa da wani irin kuka yana ambatar.
"Aunty wallahi da gaske su Sumayya suke,wallahi na cuci Hidaya cuta ta har abada! Aunty dubi kalaman da Hidaya take ambatawa a kaina...Aunty wannan ita ce masoyiya ta hak'ik'a mai yiwa masoyinta uzuri...Aunty nayi rashi...tabbas nayi rashi mafi girma a rayuwata....
Sai ya sake fashewa da kuka,yayin da Aunty ta runtse idanuwa tana jin yadda tausayin Khaleel ke ragargaza zuciyar ta.....!
*************
Shigarta cikin gida da gudu tana kuka suka yi kacib'us da Ya Hamza da yake fitowa daga d'akinsa,da kallo ya bita yana jin zuciyarsa na bugu har ta shige parlour'n Umma tana kuka,ta wuce su Umma da Mummy da Aunty Sajida da ke zaune suna hira,ta fad'a d'aki tana gurshek'en kuka.
Cikin tashin hankali Umma ta mik'e da niyyar bin ta d'akin,sai Mummy ta dakatar da ita da fad'in.
"Barta ta sha sharafinta kawai,komai da kika gani da lokacinsa,wataran ba za ta yi hakan ba"
A sanyaye Umma ta koma ta zauna ranta a jagule duk ba dad'i,tausayin Hidayan take ji sosai a ranta.
Shi kam Hamza ya d'auki mintoci a tsaye jikinsa a sanyaye,a hankali kuma ya saki ajiyar zuciya yana lumshe idanu,wai shin yaushe zai samu sauk'i a zuciyarsa ne?yaushe abubuwa za su yi masa sanyi zuciyarsa ta samu salama?ko har sai ya mutu hakan zai tabbata...
Motsin da yaji shine ya bashi damar bud'e idanuwansa ya d'ago kai,nan take idanuwansa suka yi arba da Khaleel,wata matsananciyar fad'uwa gabansu yayi a tare,suka tsurawa juna idanuwa jikinsu na mugun rawa,kowa da abin da yake zuciyar sa,sun d'auki kusan minti biyu suna kallon kallo a tsakanin su kowa ya kasa furta komai,yayin da hawaye yake bin fuskar Khaleel da gudu,Aunty Kubra ce ta katse mutuwar ido biyun da suka yi ta hanyar rafka sallama a tsakar gidan.
Daga cikin parlour'n su Umma suka had'a baki wajen amsawa,Umma a jikinta taji kamar ta san muryar da ke sallama,hakan yasa ta taso ta d'aga labule don dubawa,a take gabanta yayi tsananin fad'uwa da k'arfi ganin Khaleel da Aunty Kubra a tsakar gidan su,da wani irin sauri ta fito jikinta na rawa ta zubawa Khaleel idanu cikin wani yanayi,da k'arfi kuma Umma ta ambaci sunan sa cikin wani yanayi.
"Ibraheem....!
kiran har k'wak'walwar Hidaya ya shiga,a take tayi sufa daga kan gado ta mik'e da hanzari tayo wajen window da gudu tana d'aga labule domin ganin tsakar gidan na su,jikinta babu in da baya rawa,tunda taji muryar Umma na ambatar Ibraheem to ta san Uncle Khaleel ne,take kuwa idanuwan ta suka nuna mata gaskiyar zance,Uncle Khaleel d'in ta ta gani ya juyo da hanzari yana d'aga k'afa da k'yar ya nufo Umma da ke tsaye tana duban sa,idanuwan Hidaya a kansa tana kallon wata muguwar rama da yayi ya dawo kamar tsinke,shauk'i ya d'ebeta,sai taji kamar ta shek'o da gudu ta afka k'irjinsa mai dad'i ta rungume shi,runtse idanuwa tayi tana sakin wani marayan kuka zuciyarta na harbawa.
Lokacin da Khaleel ya iso gaban Umma zubewa kawai yayi akan gwiwoyinsa,hawayensa na kwarara kamar an bud'e famfo,murya na karkarwa ya d'aga tafukan hannunsa ya had'e su guri d'aya yana rok'on Umma cikin kuka.
"Afuwan...Afuwan....Afuwan Umma...don Allah kiyi hak'uri...don darajar manzon Allah ( S A W) kiyi hak'uri Umma....
Abin da yake nanatawa kenan cikin kuka kamar ya shid'e,Umma ta rasa ma me zata ce,ta fito ne da niyyar b'atawa Khaleel rai,sai dai yadda ta ganshi gabad'aya ya gama karya mata zuciya,ji take tamkar ta fashe da kukan ita ma,Hidaya kam tsananin kukan da take yi tana kallon Khaleel tamkar ta shid'e,yanzu shikenan ita da shi sai gani sai hange daga nesa?wannan wace irin k'addara ce?"
D'aga labulen parlour'n aka yi,Mummy ta fito ita da Aunty Sajida cikin wani yanayi,a hankali ta zo gefen Umma ta dafata,Umma ta d'ago ta dubeta suka had'a idanu,sai Mummy tayi murmushi tace da Umma.
"Wannan shine Khaleel ko?D'an gidan MUDASSIR?"
Da hanzari Khaleel ya d'ago idanuwa ya dubi Mummy suka had'a idanu,gabansa yayi mugun fad'uwa da kallon da tayi masa,matsowa Mummy tayi gabansa tana kallonsa,cikin wani yanayi ta k'ura masa idanu ta ce.
"Khaleel ko...?ka san ko ni wacece kuwa?"
A hankali ya girgiza kai kafin ya maida kallonsa kan Hamza,shi kam Ya Hamza kansa a sunkuye yake,baima san halin da zuciyarsa take ciki ba,ya shagala da kallon Hamza a sanda yaji muryar Mummy na ce masa.
"Heyyyy...Ni za ka kalla ba GARKUWA ba,ni zan maka bayanin ko wacece ni ka fahimta ko?"
Dawo da kallonsa yayi kanta yana had'iyar zuciya,tun kafin ya san ko wacece k'irjinsa ke bugawa.
Murmushi tayi mai ciwo kafin ta ce.
"Wannan lokacin nake jira...kuma na san za ka zo daman...jiran da nake kenan domin na bayyana maka yadda Mahaifinka ya kashe Mahaifin Hidaya...daga nan ku bayyana gaban ALK'ALIYA domin tuhumar ku kai da mahaifinka ! yayin da zai fuskanci tuhuma akan kisan kan da yayi tsawon shekaru ! kai kuma za ka fuskanci tuhuma kan wulak'anta aure da cin zarafin Y'a mace! saboda haka ina mai farincikin shaida maka cewar ni ce MAHAIFIYAR HIDAYA WADDA TA HAIFE TA...!"
A gigice Khaleel da Aunty Kubra suka dubi Mummy cikin firgici,a dai dai lokacin kuma da ALHAJI MUDASSIR (DADDY) ya sako kan sa cikin tsakar gidan a firgice,dukkanin su suka waiwaya suna duban sa,babu wanda bai razana ba kaf cikin su,idanuwan Mummy suka yi arangama da bak'ar fuska! a take wani hawaye mai tsananin zafi suka zubowa Mummy,ta bud'e baki yana karkarwa ta ambaci sunan sa.
"MUDASSIR....!
A gigice Daddy yake kallon ta yana nuna ta hannu,cikin masifaffiyar firgita ya d'ora hannu a ka bakinsa na rawa da karkarwa yake duban Mummy kafin yayi magana a rarrabe.
"Ke....ke...ke ce...?da ...daman....ki...kin...kina...nan...?"
Tana kuka amma sai da tayi murmushin takaici,sannan ta tsurawa Daddy idanu ta ce.
"K'warai ina nan Mudassir ! ban mutu ba kamar yadda ka kashe mijina! ni ma kuma kaso kasheni ni da y'ata amma Allah ya kub'utar da mu!
Ta maida kallonta kan Hamza da ke tsaye tamkar an dasa shi,ta girgiza kai hawaye na ambaliya ta ce.
"GARKUWA HAMZA yau za ka samu dukkanin amsoshin tambayoyin da kake min da kai da Hidaya,yau zan fito da ku cikin haske daga duhun da kuka afka! yau za ku san komai da ke b'oye! tabbas yau sirrin b'oye zai fito fili.....!
*RIGIJI GABJI*😳
Comments
share
vote
pls
*GARKUWA BIYU*
BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️