← Book details Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 25 OF 31

BABI NA TAMANIN DA BAKWAI DA NA TAMANIN DA TAKWAS

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

*SADAUKARWA GA* 👇

SA'ADATU TIJJANI D'AHEER
RUMAISA GWARZO
AMEERA ABUBAKAR
KADIJA D'ANGUDE
SAFIYA UBA WADA
NANA AISHA
MOMYN IFFAH
SADIYA Y'AR AMANA
FA'IZA GOMBE

DA SAURAN SU

*Kuna bawa GARKUWA BIYU Hak'k'insa na Sharhi yadda ya kamata,godiya nake muku tare da Jinjina*🥰🤝👍


***Gida ya cika taf da mutane y'an jaje,haka nan ga police da suka zo bincike akan lamarin,kuma sunyi wa mai gadi tambayoyi sosai bayan ya dawo hayyacinsa,in da ya sanar da su cewar shi dai bai san komai ba,abin da ya sani shine, Ya kulle get kuma ya dawo wajen zamansa ya zauna,can gyangyad'i ya fara d'ibansa yaji alamun kamar ana bud'e get d'in ta waje da mukulli,da sauri ya zabura ya mik'e ya nufi bakin get d'in,sai ya lura ashe bai sa sakata ba,ya kai hannu kenan zai sa sakatar kawai yaji an turo k'ofar get d'in da k'arfin tsiya an doka masa ita a fuska,yayi baya ya fad'i,wasu mutane suka shigo da bai tantance ko su wanene ba,suka murk'usheshi suka shak'a masa wata hoda da ta fitar da shi daga hayyacinsa take ya suma,daga nan bai sake sanin inda kansa yake ba har zuwa safiya da ya farka yaji ana batun ba a ga Oga Taufik' ba.

Mai gadi yana bayani yana kuka da sharar hawaye,y'an sanda suka d'auki bayanansa sannan suka zo kan Sulaiman shima,da farko ma kasa magana yayi saboda halin da yake ciki,duk wanda yaga Sulaiman a lokacin dole ya tausaya masa,yayi kuka yayi kuka har hawayensa ya k'afe,burinsa yaga Abbansa kawai,abinda yake dad'a tayar masa da hankali rashin sanin wane hali Abban yake a halin yanzu,da k'yar ya iya bud'e baki yayi wa y'an sanda bayanin da suke so,bayan haka y'an sanda sun dudduba gidan tare da d'aukar bayanin komai da komai,sannan suka ce mu jira su za su gudanar da bincike kuma in sha Allahu za a dace.

Sai yamma lik'is y'an jaje sun fara bajewa sai ga Alhaji Mudassir da Alhaji Maude a gigice sun zo,suka samu a gaba har da kukansu na munafunci,suna tsinewa duk wanda wa sace Oga Taufik',shi dai Sulaiman ko kallonsu bai yi ba ma har suka gama maganganunsu na rainin hankali,sai kuma suka koma yiwa Sulaiman yarfe,wai da alamun tambaya a kansa,saboda shine yake kula da shi har ya kwana da shi,to yana ina har hakan ta faru?to in ma shi ya b'atar da Oga Taufik' dan ya cinye dukiyarsa to yayi gaggawar fitowa da shi,in ba haka zai fuskanci masifa da bala'i a rayuwar sa,Ina zaune a gefen Sulaiman ina jin duk cin mutuncin da suke masa,hawaye na zubar mana ni da Sulaiman amma basu daina ba,haka suka gama rashin mutuncinsu sannan suka mik'e suka fice suna ta yab'awa Sulaiman bak'ak'en maganganu.

Sai da suka fita sannan Sulaiman ya mik'e da hanzari zai bi su,na mik'e na rik'e shi ina had'ashi da girman Allah akan ya rabu da su ya tura musu aniyarsu,amma Sulaiman ya fizge jikinsa daga nawa,ya dubeni a haukace yace min.

"Zainab wallahi ba zan k'yalesu ba,basu isa suci bulus ba,sai na bisu na mayar musu da amsoshin maganganun da suka yi a kaina"

Ina ji ina gani Sulaiman ya fice ya barni a gun a tsaye,yana fita ya hango su sun nufi motar su za su shiga sai shewa suke yi suna tafawa,Alhaji Mudassira na cewa.

"Wai shikenan Maude kana nufin mun gama da babin Taufik' kenan?"

Alhaji Maude ya k'yalk'yale da dariya ya ce.

"K'warai kuwa Mudan,har duniya ta nad'e ba za a sake jin d'uriyar Taufik' ba,saboda kurciya me dogon zango na sa akayi masa"

Suka sake kwashewa da wata mahaukaciyar dariya,shi kam Sulaiman ilahirin jikinsa rawa yake da jin zantukan su,daman yana zargin su! gashi kuwa zarginsa ya tabbata daga jin kalaman da suke furtawa,hannu ya sa aka ya rafka wani salati tare da ambatar"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un".

A gigice suka waiwayo suka zubawa Sulaiman ido ganinsa a bayansu,domin su basu ma san yana bayansu ba,kuma sun tabbatar yaji duk maganganun da suka furta,matsanancin tsoro ne ya kamasu,suka fara waige waige dan ganin ko wani yaji maganarsu bayan Sulaiman,ganin babu kowa a wajen sai suka saki ajiyar zuciya suka fad'a motar su suka fizgeta suka bar harabar gidan,suka bar Sulaiman tsaye a wajen a sandare yana zubar da hawaye.

Shiru shiru bai shigoba hakan yasa na biyo shi dan ganin meke faruwa,tunda na ganshi yana kuka naji hankalina ya tashi,jansa nayi har cikin gida na zaunar da shi,na rik'e hannayensa a rud'e ina ta tambayar sa dalilin kukan da yake,Sulaiman ya kasa magana,illa jikina da ya fad'o ya dinga wani irin kuka kamar zai had'iyi zuciya,ganin halin da yake ciki ban san lokacin da nima na fashe da kukan ba,Hidaya ma ganin muna Kuka sai ita ma ta zo ta rungume mu ta fara kukan,haka muka kasance cikin kuka babu mai rarrashin wani a cikin mu.

Sai dare sannan na samu Sulaiman ya fara nutsuwa,shima sai da muka d'auki alk'ur'ani ni da Hidaya muka dinga karantawa,har muka kammala,lokacin ne ya janyo Hidaya jikinsa yana jin dad'i ya dinga sanya mata albarka,Hidaya kuma ganin Abban ta ya fara warewa sai ta shiga yi masa surutu da tambayoyi irin na yarinta,har ya dinga murmushi yana tambayat wai yanzu shekarar Hidayan nawa?take na bashi amsa da cewar ta shiga shekara ta takwas a wannan watan.

Sai da Hidaya tayi bacci sannan Sulaiman ya iya fad'a min abinda yaji su Alhaji Mudassir suke tattaunawa akai,take hankalina nima ya tashi,nace yanzu menene abinyi?Sulaiman ya ce min.

"Gobe zan kai wa y'an sanda report akan abinda naji,duk da dai bani da wata sheda akan hakan,amma na tabbatar idan suka tsaurara bincike za su tarar da abinda nake gaya musu,Zainab wallahi tunda Abba ya fara rashin lafiyar nan nake zargin mutanen nan,ashe kuwa sune azzaluman da suka aikata komai,shin daman Zainab a duniya sakamakon alkairi da sharri mutane suke saka shi?babu abinda Abba bai wa mutanennan na kyautatawa ba,amma ga da abin da suka saka masa,lallai na yarda d'an adam butulu ne Zainab,kuma sharrin mutum yafi na sharrin tsohuwar mota,amma in sha Allahu k'arshen zaluncinsu ya zo,gobe da wurwuri zan tafi police station na kai report d'in su".

Ni dai azabar mamaki ta cikani,lallai mutum mugun ice ne,sharrin mutum na da yawa,haka muka dinga tattaunawa da Sulaiman a daren nan,har za mu kwanta bacci ma sai naga ya mik'e,ya tafi ya d'auko wannan jakar da Abba ya bashi mai d'auke da kadarorinsa,dawowa yayi ya dank'amin jakar,sannan yace min.

"Zainab ki ajiye wannan jakar a hannunki,ki kula da ita sosai,na zab'i in damk'a miki ne saboda ni na san rayuwata za ta iya shiga garari a hannun wad'annan azzaluman mutanen,duk da Allah ya fi su,amma dai gara ki barta a gunki ki kula da ita sosai,na san duk wani abu da suke hank'oro ba zai wuce dukiyar Abbana ba,kuma babu rabonsu a cikinta,domin bai ambace su cikin wad'anda za a raba da su ba"

karb'a nayi ina jinjina batunsa,yace min in tashi in je in yi mata b'oyo na musamman,haka na tashi jikina a salub'e,shima sai naga ya tashi ya fice zuwa d'akin sa wai zaiyi wanka zafi yake ji.

Da na shiga bedroom d'ina sai na rasa in da zan b'oye wannan jakar,nai ta kallen wurare da dama a d'akin amma na rasa inda zan saka ta,duk inda idona ya kai sai naga ai jakar bata dace da wurin ba,a hankali sai naja jiki na nufi Vantlation d'in cikin d'aki na jakar na hannuna,ina zuwa na tsaya ina kallon k'asan gurin,siminti ne shimfid'e a wurin ba tayel ba,kawai sai naji zuciyata ta amince da gurin a matsayin in da zan b'oye jakar.

Ajiye jakar nayi na fita na koma store d'in mu na d'akko guduma,sannan na tawo da ruwa a kofi,sai na dawo na kulle d'akin na wuce Vantlation d'in,tsugunawa nayi daga gefe nasa guduma na fara fasa k'asan gurin sosai da k'arfi,sai da naga yayi rami sosai nasa hannu na fito da k'asar wajen,sannan na saka wannan jakar tayi dai dai a wajen,sai kuma na mayan da k'asar na dandab'e,nasa ruwa na k'ara dandab'ewa,ma'ana na binne jakar kenan,da na gama komai sai na janyo k'ofar vantlation d'in na kulle,na nufi toilet na wanke hannaye na,sannan na fito parlour.

A dai dai wannan lokacin da na kammala komai sai ga Sulaiman ya shigo,ya dube ni yana tambaya ta.

"Kin adana jakar inda ya dace ko?"

Na gyad'a kaina tare da cewa.

"Na adanata inda babu wani mahaluk'i da ya isa ya ganta"

Jinjina yayi min tare da murmushi,sannan ya ce min.

"Allah yayi miki Albarka Zainab,Na gode".

Naji dad'in addu'ar sosai a zuciyata,na amsa ina murmushi,sai ya dubeni ya sake cewa.

"Kije kiyi wa Hidaya addu'a a d'akinta,ni zanyi wasu salloli ne"

Na amsa tare da mik'ewa na fice zuwa d'akin Hidaya da ke jikin na mu d'akin,dan akwai k'ofa ma cikin d'akinmu da zata kaika d'akin Hidaya kai tsaye ba sai ka bi ta parlour ba,ina wucewa shi kuma ya shimfid'a darduma ya tayar da Sallah.

Da na je na dawo sai na tarar har lokacin sallolinsa yake ta yi,na zauna ina jiran ya kammala mu kwanta,amma shiru da yayi sallama sai ya kabbara wata har na fara hamma bacci na d'iba na,hakan yasa na kashingid'a ina ta kallonsa,idan yayi sujjada ya kan d'au tsawon lokaci bai d'ago ba,a haka har bacci ya kwashe ni yana ta sallar sa.

Har bacci na yayi nisa sosai sai naji Sulaiman na bubbugani yana tashina,na bud'e idanuwana da suka zama k'ananu saboda bacci ina dubansa,sai naji yana cewa.

"Zainab tashi kinji,motsi nake ji kamar ana shigowa gidannan fa"

Nan da nan na wartsake,na nemi baccin na rasa jin abinda yace,a firgice na mik'e zaune,muka yi kasak'e muna jin alamar motsin tafiya sosai,a tsorace muka sake duban junan mu,kafin muyi wani yunk'uri muka ji an banko k'ofar d'akinmu da k'arfi an shigo.

Wasu mutane ne za su kai kimanin su biyar,sanye da bak'ak'en kaya da mask bak'ak'e sun b'oye fuskokin su,wata irin tsawa d'aya daga cikinsu ya daka mana,sai da y'an hajin cikinmu suka kad'a take muka durk'ushe a k'asa ganin manya manyan makamai da bindigogi a hannun su,wani irin matsanancin tsoro ne ya kama mu,yayin da muke ta ambatar "La ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimina"

Babbansu ne ya k'yalk'yale da wata irin dariya kafin ya dubi Sulaiman,cikin kakkausar murya ya nuna shi yace da shi.

"Kai k'aramin d'an iska k'aramin k'waro,kai har ka isa ka ja da manyan alhajoji kamar Alhaji Mudassir da Alhaji Maude?to uban gidan naka ma mun gama da babinsa balle kai k'aramin matsiyaci,yanzu muna so ka fara fito mana da duk wasu kadarori da Alhaji Taufik' ya mallaka,domin mun san cewar suna hannunka,idan kuma ba haka ba kasan ya yadda ake sara rake?to billahillazi haka za mu sassaraka mu feraye naman jikinka"

Tashin hankali kenan wanda yafi k'arfin tunanin mu,take na nemi hawaye ma na rasa tsabar bala'in da ya same mu,addu'a kawai nake bankawa a zuciyata Allah ya rabamu da sharrin wad'annan mutane azzalumai,ganin Sulaiman yayi shiru bai amsa musu ba yana ta dai kallonsu,sai wani da ke gefe ya d'aga bindigar sa ya kwad'awa Sulaiman a gefen kansa da k'arfi,wata irin k'ara Sulaiman ya saki ya fad'i kwance a k'asa jini ya fara zubowa ta kansa,cikin matuk'ar tashin hankali na nufe shi a razane na kamoshi jikina ina kukan da babu hawaye,sai ihu nake cikin gigicewa har ban san lokacin da na dinga k'unduma musu zagi ba,Marin da aka gaura min shine ya tsayar da maganata,saboda azabar da ta ratsani kamar wadda aka saukewa guduma a kumatu,jikin gigicewa Sulaiman ya rungumoni jikinsa yana hawaye,take ya fara rok'on su da cewa.

"Dan Allah na rok'e ku kar ku tab'a min matata ! duk abin da za ku yi min ni na fanshe ta kuyi a kaina,amma don Allah ita mace ce kar ku tab'a min iyali na,komai za ku yi to kuyi a kaina na amince"

Wata dariya dukkan su suka bushe da ita,kafin babban na sau ya sake magana cikin shakiyanci.

"Eh lallai soyayya ruwan zuma! tabbas akwai k'auna a tsakani,to babu laifi tunda soyayya gaskiya ce,kuma muma walidan mu ita suka yi har aka samar da mu,za mu k'yale matarka darajar soyayya,amma fa kai wallahi ko ka bamu abinda muke so ko ka bar duniya a yanzu ba da b'ata lokaci ba"

Har zanyi magana domin d'auko musu jakar sai naji Sulaiman ya zuro hannunsa na baya ya kama hannuna da k'arfi ya matsa alamar in yi shiru,sannan ya dube su har lokacin jini na fita ta goshinsa,yace musu.

"Babu mahalukin da a duniya yasan inda na b'oye abinda kuke nema,ko matata bata sani ba,ni kad'ai na sani,kuma na rantse da ubangijina ba zan fad'a muku ba, ba zan baku ba,sai dai ku kasheni har lahira,na san cewa daman kwanaki na na duniya ne suka k'are,amma ba zan taimakawa azzalumai irinku ba"

A haukace Babban nasu yayi ball da Sulaiman yana dukansa da wata sanda,ihu na saka nayi kansa ina tunkud'e shi ina cewa"Ka daina dukar min mijina,kar ka kashe min mijina,zan ...."

Katseni Sulaiman yayi da mugun sauri ya fizgo hannayena,bai damu da dukan da ake masa ba ya tsura min idanu cikin firgici ya ce.

"Idan har kika yi magana ba zan tab'a yafe miki ba Zainab,ki barsu suyi duk abinda za su yi,komai yana da farko kuma yana da k'arshe,idan sun kasheni suma za su je inda na tafi,ba za su tab'a dawwama a duniya ba"

Inaji ina gani a gabana suka cigaba da dukan Sulaiman,wani irin duka da har ya fara fita daga hayyacin sa,ni dai kuka kawai nake mai cike da firgici,ba don maganar da Sulaiman ya fad'amin ba da tuni na basu abinda suke so,jin hannun Sulaiman nayi yana janyo ni da alamar magana yake son yi min amma muryarsa ta kasa fita tsabar wahala,da hanzari na ture na kusa da shi da yake dukan sa na matsa jikinsa,kunnena na kai dai dai bakinsa ina kuka sosai,sai naji yana ce min.

"Zainab duk wuya kar ki basu wannan jakar,idan har kika basu sun ci nasara a kanmu,kuma na san ko na basu ko ban basu ba kasheni za su yi,gara suyi nasara guda d'aya,bana son su samu nasara guda biyu,Zainab ki rik'e mana y'ar mu da kyau,ki kula da tarbiyyarta da lalurarta,ke kad'ai kika rage mata yanzu da danginki,kinga ni dai bani da dangi,Abba ne kawai dangina kuma a yanzu shima babu shi,nima kuma zan tafi,don Allah Zainab ki rik'e amana kar ki bari azzalumai suyi nasara a kanki Zainab....

Iya nan maganarsa ta tsaya saboda fizgata da akayi daga jikinsa akayi cilli da ni gefe,a lokacin ne kuma wayar Ogan na su tayi k'ara,d'agawa yayi yana fad'in.

"Hellow,ALHAJI MUDASSIR"

Banji maganar da akayi masa daga can ba,sai dai naji ogan na bada amsa da cewa.

"D'an taurin kaine wannan shegen mutumin yak'i bamu abinda muke so fa"

Yayi shiru yana sauraren abinda ake cewa,sai ya kwashe da wata muguwar dariya.

"Hahaha! kar ka damu ALHAJI MUDASSIR,yanzu za mu aika da shi BARZAHU kamar yadda ka umarce mu,suma iyalin na sa za mu yi abinda ya dace a kansu" ya sake bushewa da dariya sannan ya kashe wayar ya mayar aljihu.

Ni dai matsanancin kuka nake ganin har Sulaiman ya daina motsi,ina kallo ogan na su ya sa mutane guda biyu suka zo suka d'aga Sulaiman da ya gama fita daga hayyacin sa,suka mik'ar da shi tsaye,ni kuma ya umar ci d'ayan da yazo ya rik'eni,ina fizge fizge amma haka ya rik'eni gam ya toshe min baki na,Lokaci guda naga Ogan ya fito da wata zabgegiyar wuk'a sai k'alli take yi tana d'aukar ido,zaro idanuwa nayi ina shirin sume wa a sanda naga ya nufi gaban Sulaiman da ita ya tsaya,sannan ya sa hannu ya d'ago kan Sulaiman da k'arfi ya dube shi,cikin wata kakkausar murya ya nuna masa wuk'ar da ke faman k'yalli ya ce.

"Za ka bamu ko ba za ka bamu ba?"

Sulaiman da ya kasa magana ya girgiza masa kai alamar ba zai basu ba,bakinsa na motsi yana ta kallona alamar salati yake yi da shahada,wani mugun murmushi Ogan yayi kafin ya d'aga wuk'ar ya sokawa Sulaiman a k'irji da k'arfi😭Wani irin ihu na saka duk da bakina a rufe yake sai da gidan ya amsa,fizgo wuk'ar yayi ya sake luma masa a cikinsa😭 take wani irin jini yayi tsartuwa ya fara malala a k'asa,a lokacin tuni rai ya bar gangar jikin Mijina Sulaiman😭,sun kashe min shi😭,duhu ne kawai ya mamaye min idanuwa na,sanda na riski muryar Ogan na su na magana da alama waya ya buga.

"ALHAJI MUDASSIR mun cika aikin ka ! a yanzu haka ran Sulaiman ya tafi Lahira...!

Daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba😭


Comments
share
vote
pls


*GARKUWA BIYU*


BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter 25 · 0% Book details