← Book details Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 26 OF 31

BABI NA TAMANIN DA TARA DA NA CASA'IN

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

*SADAUKARWA GA MUTANE GUDA BIYU*👇

GAREKI MISS FLOWER KE CE TA FARKO,MARUBUTA NA GODIYA DA YABAWARKI GARESU,ALLAH YA BAR ZUMUNCI,MU MA MUNA K'AUNARKI SOSAI🥰


TA BIYUN KUMA BAN SANKI BA,AMMA SAK'ONKI YA ISO ZUWA GARENI TARE DA SAURAN MARUBUTA,KAMAR YADDA KIKA CE NICE A FARKON FARI,TO NIMA NACE KE CE A FARKON FARI 😅KUMA INA NEMANKI DOMIN KI KARB'I TUKUICIN K'AUNA,HASSANA D'AN LARABAWA NA MIKI SON SO FISABILILLAH,KUMA MUNA GODIYA SOSAI ALLAH YA BAR ZUMUNCI.🤝🥰


***Ruwa suka yayyafa min na farfad'o,a lokacin bani da buri illa nima su kasheni domin nabi Sulaiman d'ina,hakan yasa na dinga kallon gawar Sulaiman da ke kwance,ina rok'onsu akan nima su kasheni kawai na shirya mutuwa,Ogansu ya sake fashewa da dariya yana kallon wuk'ar hannunsa sannan ya dube ni ya ce dani.

"A cikin tsarin mu babu aika ki lahira a yanzu y'ammata,ki bari idan buk'atar hakan ta taso ba ma sai kin rok'emu ba,da kanmu za mu aika ki lahira domin ki bi d'an masu taurin kai"
Daga nan ya juya ya dubi mutanen da suka rik'e Sulaiman,ya umarce su da su d'auki gawar Sulaiman suje su sakata a motar da suka zo da ita,duk fizge fizge na akan su bar min mijina kar su fita gawarsa k'in saurarata suka yi,suka d'auke shi jini na yarari suka fice da shi akan idanuwa na,wannan shine gani na k'arshe da Sulaiman d'ina.

Akwai ragowar mutum d'aya a cikinsu wanda na lura shi tunda suka zo baiyi magana ba,kuma baiyi motsi ba yana k'ame yana kallon dukkan abinda ke faruwa,sai a lokacin Ogansu ya dube shi yayi masa sigina,Sannan ya juya ya fice ragowar d'ayan ya bishi a baya,daman su biyar ne.

Shi wanda aka yiwa siginan shine ya k'araso gareni inda nake tsugune ina wani irin kuka na tashin hankali,yana zuwa gabana ya dubeni ya ce min "Tashi" yanayin muryar da yayi amfani da ita babu fad'a da tsawa,sai naji kawai dan karan kaina na bi umarninsa na tashi tsaye,kallon fuskarsa nake ina kuka,amma da yake akwai mask a tasa fuskar bana ganin komai sai idanuwan sa,nuna min d'akin yayi sannan ya sake ce min.

"Ki duba d'akin nan ki d'auki duk abinda za ki d'auka kizo mu tafi"

Na cigaba da kallonsa kawai,to ina zamu tafi?ina za su kaini?tambayoyin da nake wa zuciyata kenan babu mai bani amsa,sai naji kawai ban tsorata ba,gara na bisu in ma kashenin ne suyi zan fi son hakan ma,me zan zauna nayi a duniyar da babu Sulaiman a cikinta?

Juyawa nayi nabi ta k'ofar da ke cikin d'akina zuwa d'akin da Hidaya take,Allah sarki baiwar Allah duk abinda ake ita baccin asara take,ana can an kashe mata mahaifi tana bacci,yana biye da ni har inda take kwance,ban san abinda ya k'arfafa min zuciyata ba kawai dai naji na daina jin tsoro zuciyata ta dake sosai,sai naji hawayen ma ya k'afe min illa azabar suya da k'irjina yake yi.

Yana ta kallona har na d'auki Hidaya duk girmanta na sab'a a bayana,na d'auki zani na goyata,sannan na tsaya ina kallonsa,sai naji ya sake ce min.

"Y'arki kawai za ki d'auka?ki sake dubawa dai idan da wani abin da za ki d'auka,amma ki hanzarta kada lokaci ya k'ure mana"

Nayi duru duru na rasa me zan d'auka,gani nake babu wani abu da zai min amfani,amma da na tuna da maganar Sulaiman akan na kula da d'iyar mu,kawai sai na juya na d'auko wata jaka,na d'ibarwa Hidaya y'an kayayyakinta da takalma,sai kuma idanuwana suka fad'a kan Sark'ok'in gwal d'in mu da Abba ya siya mana ni da ita,suma na d'auke su,sai kuma wani littafi da biro da na d'auka,duk na had'a a cikin jakar yana tsaye yana kallona.

Karb'ar jakar yayi ya rik'e,sannan ya nuna min hanya na wuce ya biyo ni a baya har zuwa waje,ina ta kallon gidan da nayi rayuwa a cikinshi tsawon shekaru,muna zuwa harabar gidan na kalli inda mai gadi yake sai naga ban ganshi ba,k'ila shima sun kasheshi ne,sai dai naga ragowar mutanen da suka fara fita suna shisshiga mota,sai Ogansu ya nufo mu ya tsaya dab da mu,cikin wata kakkausar murya yace da wanda ya fito da ni.

"Ka aikata abinda aka umarceka,kar ka sab'a mana k'aidar aiki,idan har aka samu matsala kaima ka san sauran"

Jijjiga kai yayi yana sara masa,sannan ya nuna masa wata mota yace ita za mu shiga,agaba mutumin ya sanya ni ina goye da Hidaya a bayana,so nake na tambayesu gawar Sulaiman amma bakina ya b'ame,haka aka bud'e min k'ofa na shiga bayan motar na zauna,sannan wnnan mutumin ya shiga gaban motar ya tayar ya figeta muka bar harabar gidan.

Muna fita ya tsayar da motar,banyi aune ba naga ya juyo ya busa min wata hoda,take kaina ya juye,ban san lokacin da wani bacci mai nauyi ya d'auke ni ba.


*****************


Bud'e idanuwa na nayi a hankali,sakamakon wani abu da naji an fesa min wanda ban san ko menene ba,a hankali muka had'a idanuwa da mutumin da ya d'akkoni a mota,sai a lokacin naji Hidaya ma ta farka tana ta motsi a bayana jin na matseta,kuma daman ni ba goyata nake ba kasancewar ta girma sosai,idanuwana a kansa na tsura masa idanu,sai naga ya sa hannu a aljihun rigarsa ya fito da biro da takarda yayi rubutu a jiki,sannan kuma ya d'auko wata envelope ya had'a da takardar hannun na sa ya mik'o min,hannu na kai na amsa,ban san me yasa nake masa ladabi kan duk abinda ya umarceni ba,ina karb'a naga ya fita daga motar sannan ya zo ya bud'e min ta inda nake zaune, "Fito"abinda yace da ni kenan bayan ya bud'e min k'ofar,a hankali na janyo jikina na fito Hidaya na a bayana tana ta k'ok'arin na saukota,lek'awa yayi cikin motar ya fito min da jakar da na zubo kayan Hidaya ya mik'o min,nan ma na karb'a babu bakin magana,sai naga ya koma cikin motar ya zauna bayan ya rufe k'ofofin,kafin in ce me har yaja motar da gudu ya bar inda nake.


Motar na bi da wani irin kallo har ya b'ace a wajen na rasa tunanin me k'wak'walwata take,nidai na san tuni hankalina ma ya gushe daga jikina tun sa'ar da aka kashe min Sulaiman akan idanuwana,nafi minti goma ina kallon in da yabi da motar na kasa d'auke idanu,kukan da Hidaya ta soma shine ya ankarar da ni na dawo hayyacina,a hankali na sakkota daga bayana ina kallonta,sai lokacin wani hawaye ya sake zubo min,shikenan an mayar da ni bazawara!sannan an mayar min da y'ata marainiya! rungumeta nayi a k'irjina na fashe da wani irin kuka mai cin rai,ita ma Hidaya ta rungumeni tayi luf a jikina,kiran Assalatu da naji an fara yi shine ya ankarar da ni ashe fa talatainin dare ne a lokacin,gurin yayi tsit babu motsin kowa,hakan yasa na ja gefe d'aya daga wani loko na ajiye jakarmu a gefe,sannan na zauna na d'ora Hidaya akan cinyoyina na cigaba da kuka ina salati,Hidaya kam luf tayi a jikina ta kwantar da kanta,sai bacci ma ya sake kwasheta.

Muna wajen har gari ya waye rana ta fara fitowa,da yake ina daga d'an loko babu wanda ya ankara da mu,sai da rana ta dallewa Hidaya idanu sannan ta farka tana muttsike idanuwa,ni ko dama babu alamun wani barci a idanuwana,hankalina yana ga gawar Sulaiman,ko ya suka yi da ita oho,Allah masani.

Hidaya ce ta fara kukan yunwa,dan lokacin kusan goma na safe ne,hakan yasa tilas na mik'e jiri na kwasata,na k'ara sab'ata a bayana na d'au jakar na rik'e a hannuna na fito daga lokon da muke,har lokacin kuma wannan takarda da envelope da wannan mutumi ya bani suna hannuna,mun fito daga lokon na kama waige waigen in da zan samarwa Hidaya abin da zata ci,tunda shi yaro bai san hak'uri da yunwa ba,ni kuwa ko yunwar ma bana ji,a haka na dinga tafiya ban san ina nake tsoma k'afata ba,dan ban ma san a ina nake ba a halin da nake ciki.

Cikin ikon Allah na b'ullo wata kwana na dinga jin k'amshin suyar wainar k'wai,ashe me saida shayi ne a wajen,hakan yasa na tsaya a gefe duk ga maza nan akan benci sun jeru masu zuwa su siya,sai lokacin na tuna ai ban d'akko kud'i ba,banda ko sisi a jikina,hankalina ya tashi na rasa ya zanyi,me shayin ne ma ya lura da ni ya k'ura min idanu kamar zai cinyeni,sai kuma yace da ni.

"Hajiya lafiya kuwa?ko wani abin za a baki?"

Daurewa nayi cikin wata irin murya nace.

"Don Allah taimako nake nema,shayi da bread za ka sammin zan bawa y'ata tana jin yunwa gashi bani da kud'in siya mata"

K'are min kallo yayi,ya kalli suturar jikina ya tabbatar me tsada ce,sai dai daga gani bana cikin nutsuwata,hakan yasa ya b'ata rai kamar yaga kashi sannan yace min.

"To angaya miki ni kayan Shayin zuwa nake a sammin balle nima nazo nayi ta sanwa mutane?dalla malama wuce kibawa mutane guri kayana na kud'i ne ba na alakoro ba,ke ni gabad'aya ma ban yarda dake ba"

Hawaye ne ya tawo min,har na juya zan tafi sai naji wani daga cikin mutanen da ke zaune ya kirani,na juyo na dawo,sai ya kalli me shayin ya ce.

"Haba Rabilu,taimako fa ta nema,idan ba zaka taimaka mata ba bai kamata ka muzantata ba,kuma duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimaka masa in dai da zuciya d'aya yayi,kuma in dai don zatin Allah yayi,dan haka ka had'a mata shayi ka bata bredi ta bawa y'ar ta ta ,ni kayi min lissafi da kud'i na sai na had'a na baka"

Godiya nai tayi wa mutumin,sannan na ja gefe na zauna kan wani dandamali,har aka had'o min shayin aka mik'o min tare da bread,na karb'a na sakko Hidaya kan cinyata na fara bata,nan da nan kuwa ta karb'a taci bread ta sha shayi ta k'oshi tayi gyatsa,ni ko ko sha'awa bai bani ba ma,ko ruwa bana jin zan iya kaiwa bakina,mutumin da ya siya mana shayin yana zaune har Hidaya ya dinga yiwa wasa,na sake yi masa godiya sosai sannan na mik'e,ya zaro kud'i a lokacin ban san ko nawa ba ne ya mik'o min wai na siyawa Baby abincin rana,kamar ba zan amsa ba sai kuma na amsa na sake yi masa godiya na wuce Hidaya na d'aga masa hannu,mutanen wajen suka bini da kallo,a haka har na fita daga layin na shiga wani layin,sai na had'u da wani d'an mata shi haka yana motsa jiki,na tsaya na tambaye shi shin nan ina ne?sai ya tsaya yana kallona kafin yace min.

"Nan tudun wada ne"

Na tsaya nayi kasak'e,ya sake kallona yace min.

"Ko baki gane ba ne?Nan fa unguwar tudun wada ne,cikin jihar KADUNA"

Sai mamaki ya kamani,kenan wannan mutumin a daren jiya da ya d'akkoni daga Abuja kaduna ya kawoni kenan?godiya nayi wa matashin kafin na wuce shi ma ya bini da kallo.

Ina ta tafiya har nazo wani layi da babu hayaniya sosai,lokacin sha biyu na rana har ta wuce,na fara gajiya gashi na rasa in da zan dosa,hakan yasa na tsaya cak ! sai kuma idanuwana suka fad'a kan wani kango da ke gefena,sai kawai naji zuciyata ta aminta da shiga cikin kangon na fake kafin in san abin yi,ganin kangon a bud'e yake hakan ya sa na turmutsa kaina rik'e da Hidaya da jakar kayan ta.

Muna shiga na samu wajen zama,na sauke Hidaya,sai ta k'ara matsowa jikina ta kwanta,kafin wani lokaci bacci ya sake d'auketa,ni kuwa ina zaune dangwargwar tunani da sak'e sak'e ya cika zuciyata,kawai sai na d'akko wannan takarda da wannan mutumi ya bani na bud'eta,sai naga rubutu kamar haka a jiki


*Ba wani ba ne ya umarcemu da mu kashe mijinki illa Alhaji Mudassir,kuma shine yace bayan mun kashe shi ke kuma mu b'atar da ke yadda ba za a sake jin d'uriyarki ba ke da y'arki,a yanzu haka ni aka bawa kwangilar b'atar da ke,amma sai naji wani abu mai kama da tausayinki,dan haka na kawo ki kaduna,abinda yasa na kawoki kaduna kuwa shine,nan ce mahaifar Alhaji Mudassir,ina so ke da y'arki kuyi rayuwa a garin ta yadda zaku san komai nasa,duk da yanzu baya garin yana Abuja,ta haka ne zaku iya d'aukar fansar abinda yayi muku a tsawon rayuwarku,ko kuma ita y'arki ki barta ta rayu a kaduna ke kiyi nesa da ita,amma ki bar mata sak'o wanda ko da ta girma zai zame mata jagora wajen gane wanda ya kashe mata mahaifinta,saboda shi Alhaji Mudassir yafi saninki a kanta,muddin yasan kuna wannan gari zai iya lallab'owa kuma ya sa a kashe ku,dan haka kisan yanda zakiyi ki bar kaduna a yau domin zai iya bibiyarki,amma ita y'arki ki barta a kaduna*


Nayi kuka sosai bayan kammala karanta wannan takarda,sai naji a zuciyata na aminta da duk abinda wannan mutumi yace min,tabbas ba abinda nake ji a zuciyata sai son d'aukar fansa,hakan yasa naji a zuciya zan rabu da Hidaya,zan barta gidan marayu ko dan watarana burin zuciyata ya cika,bud'e envelope d'in nayi,sai naci karo da hoton Alhaji Mudassir,na dinga kallon hoton ina kuka ina jin matuk'ar k'iyayyar wannan mutumi a zuciyata,a haka na bud'e jakar nan na zaro biron da na sako da littafin,na yagi paper na fara rubutawa Hidaya takardar cikin kuka,bayan na gama sai na had'a ta a cikin envelope d'innan tare da hoton Alhaji Mudassir,sai kuma na yagi wata paper nayi rubutu da zummar zanje gidan marayu na Kaduna in faki ido,ko a k'ofar wajen ne na ajiye Hidaya da kayanta in tafi in barta,k'ark'ari dai na san zanyi kewa,na rasa ubanta ita ma na rasa ta,amma zan bita da addu'a,saboda nidai zuciyata ta k'ek'ashe akan d'aukar fansa,kuma Hidayan nake so ta d'aukar min fansar bayan ta girma.

A wannan kangon muka wuni,har Hidaya ta farka ta cigaba da wasanninta,kuma bata ce min tana jin yunwa ba,ni kuwa halinda nake ciki ma ya isheni,musamman da Hidaya ta tambayeni Abbanta sai na b'oye fuskata na dinga kuka,ita kam sai ta cigaba da wasanninta tana tsalle tsalle,burina na nemi ruwa nayi alwala nayi sallah,amma bani da nutsuwar da zan iya yin sallar,so nake duhun magariba kawai yayi in samu in fita daga kangon in kai Hidaya gidan marayu ni kuma na wuce duk inda Allah ya nufe ni da zuwa,ina kwance lamo cikin mawuyacin hali har Hidaya ta gaji da wasan ta zo tana cewa in tashi mu tafi,ni kuwa ko mik'ewa na kasa yi,nan ta lura da bushewar da bakina yayi,shine ta ce zata fita ta samomin ruwa,ina niyyar hanata fitan ma amma tuni ta ruga ta fice daga kangon ta barni kwance nan,wanda dalilin fitar ta ne gamuwar ta da HAMZA,wanda ya zame mata GARKUWA.

A lokacin da naga Hamza kallo d'aya nayi masa kawai naji ya kwanta min a zuciyata,sai naji ina ma dai zai iya rik'e min Hidaya duk da dai shima ba wani girma ne da shi ba,amma tun lokacin na fahimci shi yaro ne mai matuk'ar hankali,kuma Allah yayi masa wata baiwa da shi kansa bai san yana da ita ba,shiyasa lokacin da na bashi takardar da zai kai gidan marayu ina kallo ta fad'i daga hannunsa lokacin da zai cusa a aljihu,kafin ya ankara na janyeta na b'oye,na san ba zai tab'a iya kai Hidaya gidan marayun ba idan ba wannan takarda tunda ita ce shaida,tilas zai rik'e min Hidaya da shi da iyayensa,sai gashi kuwa yayi mata rik'o irin wanda ma ban tab'a zata ba,lallai Hamza ya cika GARKUWAR HIDAYA.


Mummy ta sauke ajiyar zuciya tana kallon mutanen da ke sauraren ta,a hankali hawaye ke cigaba da kwarara a idanuwan ta kafin ta bud'e baki don cigaba da magana.


Comments
Share
Vote
Pls


*GARKUWA BIYU*


BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter 26 · 0% Book details