BABI NA ARBA'IN DA UKU DA NA ARBA'IN DA HUD'U
Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
K'arfe biyu na rana Hidaya ta taso daga makaranta,tare suka tawo da Sumayya wadda ta kasance k'anwa ga Faisal abokin Hamza,da yake gidan su Sumayyan ya fi kusa da kan hanya a k'ofar Gidan suka tarar da Faisal da wasu abokanan sa guda biyu,zaune kan dandamalin k'ofar gidan suna hira,suna ganin su Hidaya suka bi su da kallo har suka k'araso suka dab da su,Faisal ya washe baki yana kallon Hidaya tamkar ya cinyeta D'an ya,ita kam sunkuyar da kai ta yi cikin kunya ta gaida shi tare da abokanan sa,da hanzari suka dubeta suna amsawa,Sumayya ma ta gaishe su suka amsa.
Suka yi sallama Sumayya ta shige gida,ita kuma Hidaya ta wuce domin k'arasawa gida.
Tana wucewa Faisal ya sauke gwauruwar ajiyar zuciya ya girgiza kai yana lumshe idanuwan sa,Habib ya lura da shi,Dan haka ya dafa kafad'ar sa cikin shakiyanci yace.
"Abokina ya dai?na lura duk sanda ka ci karo da yarinyar nan sai ka fita hayyacin ka,ko dai sonta kake ne..!?
Faisal yayi murmushi yace.
" idan ma sonta nake son bashi da amfani,domin na san na zan tab'a samun ta ba "
"Me yasa kace haka?ka san abin da Allah zai yi a gaba ne? Cewar Habib.
Kan Faisal yayi magana d'aya abokin na su mai suna Shazali yayi magana cikin tab'e baki.
" Ai dole ya fad'i haka Habib,waye zai auri Y'ar tsuntuwa wadda ba a san asalinta ba?duk wannan kyan na ta kyaun D'an maciji ne bashi da wani amfani,Sannan a yadda wannan Hamzan yake kaffa kaffa da ita ka san kansa yake wa tanadi,wa ya sani ma ko tun yanzu yana amfana da ita?domin kulawar da yake bata ta yi yawa wallahi"
A fusace Faisal ya dubi Shazali cikin b'acin rai yace.
"Amma Shazali ka bani mamaki wallahi,ka rasa wa za ka yi wa mummunan zato sai mutumin kirki irin Hamza,Wanda kowa ya san halayen sa na gari a unguwar nan,to idan ma kansa yake wa tanadi ai ba laifi bane,domin duk duniya babu ma Wanda ya cancanta ya kasance miji ga Hidaya sai Hamza,domin shine ya santa fiye da kowa,babu wani namiji da zai bata kulawa fiye da shi,sai dai kuma idan Allah bai k'addari ya zama mijinta ba,Wallahi Shazali ka yi gaggawar yin istigfari,domin ka fad'i magana mara dad'i akan D'an uwanka musulmi Wanda ba hakan ba ne,Manzon Allah (S A W)Yace.
" idan zaka fad'i magana to ka fad'i alkairi ko ka yi shiru…" Don haka ka kiyaye.
Habib yace.
"Tabbas baka kyauta ba Shazali,Ai ko wani kaji ya fad'i irin wannan maganar akan Hamza sai in da k'arfin ka ya k'are,Hamza mutumin kirki ne mai ilimin addini da kiyaye dokokin Allah,Hamza ko nasiha zai maka ya kan kafa maka hujja da ayoyin alk'ur'ani mai girma,Dan Allah ka daina aibata shi Shazali,hakan bashi da kyau ko kad'an"
Shazali ya sauke numfashi cike da nadamar furucin sa,magana zarar bunu,kuma yayi danasanin furtawa,duban su Faisal yayi cikin muzanta yace.
"Insha Allahu ba zan sake ba,sharrin zuciya ne ya saka ni furta hakan da zugar shaid'an,kun san shi shaid'an duk in da yake ba ya son a zauna lafiya,burinsa ya ga ka aikata wani Abu na sab'on Allah,amma ni da kaina na tabbatar da Hamza mutumin kirki ne,Na gode da tunasarwar ku gareni abokai na"
Faisal da Habib suka ji dad'in nadamar furucin da Shazali yayi,nan suka cigaba da hirar su da suke yi akan yadda siyasar Nigeria take garawa.
************
Bayan ta karb'i mukulli ta bud'e gidan abin da ta fara yi bayan cire unifoam shine Sallar azahar,tana idar wa ta duba ktcheen ta tarar da abinci cikin kula Umma ta dafa musu kafin ta fita,jalop d'in macaroni da kayan lambu sai k'amshi take,nan da nan ta zuba ta nufi parlour ta hard'e ta fara ci,a Zuciyar ta tana wa Umma addu'a da jinjina fannin iya girki,shiyasa a kullum Umma cikin koya mata girki take kala kala,haka nan idan suka je kano gidan K'anwar Umma Anty Salamatu anan ma tana koyar na zamani,domin Anty Salamatu har makaranta ce da ita ta koyawa mata girkuna na gargajiya da na zamani.
Da ta kammala cin abincin ta mike ta fita da plate d'in ta d'aura ye ta mayar da shi muhallin sa,mukullin d'akin Hamza ta d'auko ta je ta bud'e,gyaran d'aki take so tayi masa,nan ta fara ta gyara tsaf duk da babu wata k'ura kasancewar sa mai tsafta,ta d'ebi singlet d'in sa da gajerun wanduna da ta lura ya saka duk ta wanke masa ta shanya su a toilet d'in d'akin sa,ta kunna burner ta zuba turaren wuta,nan da nan d'akin ya d'auki k'amshi mai dad'i,har zata fita ta lura da wani hoto D'an k'arami a jikin bed side drawer a mak'ale,dawowa tayi ta d'auki hoton tana kallo tana murmushi, mutum uku ne a jikin hoton,gefe da gefe Hamza da Khaleel ne,sai ita a tsakiya,Hamza zaune a cikin studio na gidan redio,ya mak'ala abin saurare a kunnuwan sa,hannayen sa d'auke da takarda yana kallo alamar labarai yake karantawa,fuskar sa d'auke da murmushi,Khaleel kuma zaune cikin wani lambu mai kyau,yana sanye da k'ananan kaya kamar yadda yafi saka su a kowane lokaci,ya hard'e hannuwan sa a kan gwiwoyin k'afafun sa,ya karkata kai ya kanne ido d'aya yana wani smile mai kyau Wanda ya bayyana fararen hak'oran sa farare tas, sai na ta hoton Wanda tayi kyau duk da babu kwalliya a fuskar ta,don lokacin ma shagwab'a take wa Hamza ta turo baki,kanta ko D'an kwali babu,shine ya d'auke ta hoton da wayar sa a lokacin,Hamza yana son hoton Sosai, idan ya kalla yana saka shi nishad'i.
Zama tayi ta na k'arewa hoton kallo,da alamun zuwa yayi aka fitar masa da shi aka had'a da na sa da na Khaleel, ta kai Hannu tana shafa hoton domin duk sun yi kyau sosai,sai da ta kwashe tsawon lokaci kafin ta fito ta rufe masa d'akin.
Kafin Umma ta dawo har ta k'ara gyara gidan Sosai, tayi girkin dare tuwon shinkafa miyar Agushi da taji wadataccen busasshen kifi,sai k'amshi ke tashi,wanka ta fad'a,bayan ta fito tayi hanzarin saka kayanta tayi sallar la'asar ,Dan har lokacin ta ya d'an gota,ta san da Ya Hamza na nan da ta sha fad'an k'etare lokacin sallah,domin baya wasa da sallah kuma baya shiri da mai wasa da ita.
Akwai lokacin da ya sameta tana kallo a TV har akayi sallah bata tashi ba saboda yadda film d'in da take kallo ya d'auke mata hankali,ranar ma Umma bata nan,yana shigowa ya tambaye ta ta yi sallah ta zauna tana kallo?ta fara Sosa kai tana cewa ah ah yanzu za ta tashi tayi,ya kalli agogo yaga tuni lokaci ya k'ure,ai bata tab'a ganin b'acin ransa irin ranar ba,ya dinga zazzaga mata fad'a kamar ya doketa,yace muddin za ta dinga wasa da sallah to za su b'ata,shi kansa yayi mamakin yawan fad'an da ya dinga surfa mata,sai da yaga tana kuka sosai tana bashi hak'uri sannan ya koma yi mata nasiha akan kiyaye sallah da tsananin girman ta a gun Allah (S W A),Bata manta lokacin ba,kanta a k'asa durk'ushe a gabansa tana hawaye,shi ma ya tsuguna yana kallon ta,murya cike da kyautatawa ya fara magana.
"Hidaya a ko ina kika kasance to ki zama mai tsai da sallah akan lokaci da kulawa da sharad'in ta,domin ita ce mafificin Abu,in ji manzon Rahama Alaihis salatu wassalam,haka nan sallah tana sadarwa tsakanin bawa da ubangijinsa,sallah ta kasance ita ce abin faranta ran masana Allah,kuma hutun zukatan su,gata kuma tana hani ga aikata alfasha da mummunan aiki,Allah ta'ala ya ce:
"إن الصلوٰة تنھیٰ عن الفحشاء والمنکر"
(Hak'ik'a sallah tana hana alfasha da mummunan aiki).
Haka nan Allah mai tsarki da d'aukaka yayi kira zuwa kiyaye ta,yace:
"حفٰظوا علی الصلوٰت والصلٰوة الوسطی وقومواللہ قنٰتین"
(Ku kiyaye salloli,da kuma Sallah ta tsakiya,kuma ku tsaya kuna masu biyayya ga Allah)
Hidaya sallah ita ce maraba tsakanin kafirci da imani,domin jabir ya rawaito cewar,manzon Allah (S A W)Yace,"Hak'ik'a abin da ke tsakanin mutumin da kafirci ba wani Abu bane face barin sallah"
Akwai ayoyi da hadisai da yawa da suka yi magana akan Sallah da kiyaye ta akan lokacin ta,farkon abin da za a yi wa bawa hisabi da shi ranar Lahira shine sallah,idan ta cika tayi kyau to dukkanin wasu ayyukan bawa sun yi kyau ,idan aka samu akasin haka kuma sai innalillahi wa inna ilaihir raji'un,Dan haka Hidaya ina yi miki wasiyya da ki kiyaye sallah!ki gabatar da ita yadda Allah yace ayi,kuma ki yi ta akan lokacin ta,sannan ki kyautata ta"
Sallamar Umma ce ta katse Hidaya daga tunanin ta,ta sauke ajiyar zuciya a hankali tana amsawa,Zuciyar ta cike da k'aunar Ya Hamza saboda kyawawan d'abi'un sa da kiyaye dokokin Allah.
*****************
Da daddare tana kwance akan kujerar parlourn Umma da wayar ta a hannun ta tana chatting, hira suke ita da Khaleel cikin Annashuwa da jin dad'i,Hidaya sai k'yalk'yala dariya take yi,har Umma ta gaji da jiyo dariyarta daga d'aki ta leko tana kallon ta tace.
"Wai ke lafiyar ki kuwa kika ishi mutane da dariya..!?"
Hidaya ta d'ago kai ta kalli Umma fuskar ta d'auke da murmushi sosai tace.
"Wallahi Umma Uncle Khaleel ne yake ta saka ni dariya fa,kin san shi da zaulaya"
Umma ta girgiza kai ta na cewa.
"Ai shikenan Allah ya shirye ku" Ta juya da nufin komawa d'aki,da sauri Hidaya ta tare ta da cewa.
"Umma wai ina Ya Hamza ya shiga ne?tun d'azu banji shigowar sa ba"
"Ya tafi zance wajen budurwar sa….!
Umma ta ambata kai tsaye tare da shigewa bedroom.
Hidaya da ke kwance taji saukar maganar tamkar aradu,ta mik'e da hanzari a gigice tana zare idanuwa ta,mik'ewa tayi da sauri ta bi Umma d'akin,ta tarar da ita tana shirin tub'e kayan ta domin shiga wanka,Hidaya ta k'arasa da sauri ta rik'o hannun Umma tana firfito da idanu,cikin rawar murya tace.
" Umma me kika ce?kamar naji kince Ya Hamza ya tafi zance gun budurwar sa?kamar haka kunnuwana suka ji ko…!?
Umma ta dubeta tace.
"Eh haka nace,tad'i ya tafi,daman bai gaya miki bane?
Haka kawai Hidaya taji k'irjinta na tsananin bugawa kamar ya fad'o,taji Zuciyar ta ta yi zafi Sosai,hawaye ya ciko idanuwan ta jikin ta ya kama rawa,a sanyaye ta saki hannun Umma ta juya baya,bata son Umma taga hawayen ta,cikin wata irin murya da saura kad'an ta fashe da kuka tace " bai gaya min ba Umma,ban ma san yana da wata budurwa ba…"
Umma ta kalli bayanta da ta juya d'anyi murmushi sannan tace.
"Ayya!ni na zaci ma ya fad'a miki saboda naga ke ce abokiyar shawarar sa,sai ku hak'a ku binne ba tare da na sani ba,to amma ya naga kamar ranki ya b'aci da maganar?ko baki yi farincikin jin cewar yayanki yana da budurwa zai yi Aure ba?
Tamkar an cakawa Zuciyar ta mashi haka taji,a lokacin tuni hawaye ya fara gangarowa kan kumatun ta,cikin k'ank'anuwar murya tayi magana.
" ina farinciki Umma,kawai dai nayi mamaki ne da bai fad'a min ba…..
Ta kasa k'arasawa saboda yadda muryar ta ke shak'ewa,Umma ta girgiza kai ganin yadda Hidaya ta rud'e sosai,sai kawai ta share zancen ta mik'a Hannu ta d'auko wata bak'ar leda tana cilla mata sannan tace.
"Hmmm wannan kuma ita ku ke da shi,ba mai shiga tsananin ku ku bashi kunya, ni ga tsaraba nan na siyo miki da na fita d'azu,ki d'auka ki bud'e sai ki ga idan sunyi miki"
Tana fad'in hakan ta shige bathroom ta bar Hidaya tsaye k'ik'am cikin fitar hayyaci da sarawar kai,a dai dai lokacin ne kuma Hamzan ya d'aga labulen d'akin ya shigo da sallama,Hidaya ta kasa amsawa ta bi shi da kallo tamkar idanuwan ta su fad'o,ita sai taga ma bai tab'a yi mata kyawu kamar lokacin ba,sai k'amshi yake zubawa ya d'au wanka,sai ta ji wani bak'inciki a ranta tamkar Zuciyar ta ta babbake,ta tabbata daga gun budurwar shi yake kenan?shine har da gayu haka,duk da dai kowane lokaci cikin gayun yake.
Kallon juna suka fara yi cikin wani yanayi,tsugunawa yayi a hankali ya d'auki ledar da Umma ta cillo mata ya rik'e a hannun sa yana kallon ta,ya matso dab da ita yana fad'in.
"Hidaya me ye wannan…!?
Ta kautar da kai tana Jan hanci,ya sake karkata kansa in da ta mayar da na ta kan yana kallon fuskar ta da ta sunkuyar yace.
" Zan shigo kenan naji Umma na cewa ga tsabar da ta siyo miki,ni gaskiya Hidaya ban yarda ba kullum idan Umma ta fita ke take siyawa tsaraba,amma ni ba a min kara a D'an siyo min,yau dai ko me Umman ta siyo miki sai dai mu raba tare ni da ke aha"
Wani takaici ya kamata,yaje ya dawo daga wajen budurwa tad'i zai zo ya dame ta da zance,karo na farko a rayuwar ta da ta tab'a jin zafin Ya Hamzan ta a ranta kenan,Hannu ta kai cike da haushi za ta fizge ledar ,yayi saurin d'agawa sama yana matsawa,fuskar sa d'auke da murmushi yana girgiza kai yace.
"Ah ah K'anwata,ki bari na kwance sai a raba biyu ki d'au rabi na d'au rabi"
Hidaya ta shagwab'e fuska sosai,ta fara tsalle tana son cafko ledar,shi kuma ya k'i bata damar hakan,idan ya d'aga sama sai ya sauke hannunsa k'asa ya b'oye a bayan sa,yana zagaye d'akin yana dariya,ita kuma sai bin sa take tana son ya bata,ganin sai wahalar da ita yake yi sai ta kama dira k'afafu a k'asa cike da shagwab'a tana son yin kuka tana cewa.
"Ya Hamza ni ka bani Abu na mana ….
Mak'e ka fad'a yayi kamar yaro,yana murmushi yace.
" Na k'i,ni fa yau sai mun raba ko menene a cikin ledar nan…!
Da taga ba zai bata ba wahalar da ita yake yi kawai sai ta tsaya cak tana duban sa,shi kam a hankali ya fara warware k'ullin ledar yana bud'ewa,yana kammala bud'ewa ya zazzago abin da ke ciki,kawai sai ga brezia kusan guda shida masu soso,sababbi dal y'an k'anana dai dai Brest d'in Hidaya….da sauri Hamza ya sake su a k'asa suka tarwatse tamkar ya tsorata,ya d'ago kansa suna kallon juna shi da Hidaya ,dukkan su cikin zare idanuwa da dukan k'irji………!
Comments
Share
Vote
Pls
*GARKUWA BIYU*
BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️