← Book details Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 23 OF 31

BABI NA TAMANIN DA UKU DA NA TAMANIN DA HUD'U

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

***Dukkansu zuba wa Mummy idanu suka yi,wasu na hawaye,yayin da wasu suke kukan zuci wanda yafi na fili ciwo da mak'ak'i a zuciya,Mummy ta juya a sanyaye ta shige cikin parlour'n Umma tana kuka sosai,yayin da d'aya bayan d'aya suka dinga rufa mata baya suna bin ta,babu wanda aka bari a tsakar gidan sai Daddy da ke sandare a tsaye cikin firgici da tsoro,sai kuma Aunty Kubra da ke kallonsa cikin wani yanayi mara fassaruwa.

A hankali ta taka har in da yake tsaye jikinsa na mugun rawa,k'ura masa idanuwa tayi tana kallon yadda jikinsa ke mazari,ga wani uban gumi da yake yanko masa kamar wanda ya had'iyi kunama ko maciji,wani murmushin takaici Aunty Kubra ta saki tana cigaba da kallonsa,a hankali ta nuna masa hanyar parlour'n Umma kafin ta bud'e baki cikin b'atacciyar murya ta ce.


"Ya kamata wannan zaman ya kasance har da kai aka yi shi,domin kai ma muna son jin abubuwa masu yawa daga gareka Alhaji Mudassir,dan haka wuce muje"

Kamar wata uwarsa haka ta bashi umarni! ba kuma yadda zaiyi dole yabi umarnin na ta,shi ma kuma yana buk'atar hakan a ransa,gara a warware komai ya zo k'arshe,ko da hakan na nufin zai bar duniyar gabad'aya ne.

A gaba Aunty Kubra ta saka shi har parlour'n Umma,suna shiga suka tarar kowa ya zauna,neman guri suka yi suma suka zauna,Daddy sai sab'a babbar riga yake yana share gumin da yake yanko masa,a lokacin ne kuma Hamza ya mik'e ya shige cikin bedroom d'in Umma domin fitowa da Hidaya,wadda sautin kukan da take fitarwa duk ya cika gidan,yana shiga shiga ya tarar da ita bakin window rik'e da k'arafan da ke jikin window d'in,waiwayowa tayi tana dubansa,tsayawa yayi kawai yana kallon yadda uban hawaye yake saraftu a fuskarta,tana ganinsa ta sake fashewa da wani irin kuka,sannan cikin rawar murya tace da shi.


"Ya Hamza wace irin rayuwa ce wannan?wace irin k'addara ce ke bibiyata?haka daman mutum yake ji idan wata k'addara ta same shi?Ya Hamza zuciyata za ta buga saboda k'uncin da yake damunta"

Takawa ya soma yi har ya isa gabanta in da take tsaye,hannu ya zura a aljihu ya fito da wani hankici me kyau da k'amshi ya mik'a mata,bin sa tayi da kallo tana ta faman kuka,girgiza mata kai yayi alamar ta karb'a ta share hawayen ta,a hankali ta mik'a hannu ta amsa,sannan ta fara share hawayen wasu na k'ok'arin fitowa,tana cikin sharewar tayi ya fara magana cikin murya me tsananin taushi da laushi.

"Ba zan fasa fad'a miki cewar kiyi hak'uri da k'addararki ba,sannan ki godewa Allah a bisa duk wata jarrabawa da zai yi miki,wasu suna nan da yawa a duniya jarrabawarsu tafi taki zafi,k'addararsu ta ninninka ta ki sau ba adadi amma sun yi hak'uri sun jure,saboda shi hak'uri tamkar wata madogara ce da babu yadda bawa ya iya dole sai ya dogara da shi,babu imani cikakke ga wanda ba shi da hak'uri Hidaya,bana son ki zamo daga cikin wasu irin mutane gafalallu,wad'anda lokacin da farinciki ya same su sai suyi ta murna,idan akasin hakan ya same su sai su juya baya,irin wad'annan mutanen Allah ya ambace su cikin littafinsa mai girma,cikin suratul hajji,in da ya ke ce wa.


"و من الناس من يعبد الله على حرف فإن أصابه خيراطمأن به وإن أصبته فتنة انقلب على وجھه خسرالدنياوالأخرة ذلك ھوالخسران المبين"


(Daga cikin mutane akwai wanda yake bauta wa Allah a kan gab'a,idan alheri ya same shi sai ya gamsu da shi,idan kuma wata musiba ta same shi sai ya juya baya,to ya tab'e duniya da lahira,wannan ita ce hasara mabayyaniya).

"Shin Hidaya kina so kiyi hasara mabayyaniya ne?kina so ki zama cikin wad'anda suka tab'e?"

Da sauri ta girgiza kanta,sannan ta ce.

"Bana so Ya Hamza,kullum ina so na kasance mai godiya ga Allah ne,kuma mai hak'uri"

Yayi murmushi yana karb'an hankicinsa da ta kammala share hawayen ta da shi,sannan ya ce.

"Idan kuwa haka ne sai kin daina yawan kokawa a bisa k'addararki,sai kin zama Jaruma mai tawakkali,kuma sai kin k'arfafa zuciyar ki munje kinji abin da zai fito daga bakin mahaifiyarki a yanzu"

Jijjiga kai tayi cike da gamsuwa,ta juya ta d'auki Hijab d'in ta da ke gefen gado ta sanya,sannan Hamza yayi gaba,ita kuma ta biyo shi a baya cike da k'arfin zuciya.

Zuciyarta sai da taso sake karyewa,a yayin da idanuwan Uncle Khaleel suka shiga cikin na ta,da sauri ta sake aro jarumta ta afkawa ruhinta,tana son kallonsa amma haka ta kawar da kai ta samu gefe guda kusa da Aunty Sajida ta zauna kanta a sunkuye,yayin da take jin yadda idanuwan Uncle Khaleel ke mamaye ilahirin jikinta,wani irin kallo yake mata tamkar ya janyo ta jikinsa,sai dai inah! sama tayi wa yaro nisa!

Tsit kake jin Parlour'n babu motsin komai sai saukar numfashin mutanen da ke zazzaune,kowa da bitar da zuciyarsa take yi,sai da Mummy taga kowa ya nutsu,Sannan ta share hawayen ta tayi gyaran murya ta soma labarta musu labarin kamar haka.


***************


"Bani da k'warin gwiwar da zance zan tsawaita muku wannan labari a yanzu,zan bayyana muku shi ne a gajar ce,amma ta yadda kowa daga cikin ku zai iya fahimta.

" Suna na ZAINAB ,sunan mahaifina SANI. A wani lokaci mai tsawo da ya gabata,munyi aure ni da mahaifin Hidaya mai suna SULAIMAN,duk da kasancewar ba garin mu d'aya ba,ni y'ar garin (GOMBE STATE) ce,shi kuma yana garin (ABUJA),dalilin had'uwata da shi ya samo asali ne a lokacin da uban gidansa mai suna( TAUFIK') ya turo shi garin mu domin ya duba wata ma'aikata,wadda yake son yayi irin ta ko mai kama da ita a Kaduna,saboda shi Taufik' d'an kwangila ne,kuma mutum ne mai rik'o da gaskiya da amana,shiyasa yake samun kwangila sosai domin bashi da ha'inci da son zuciya a lamuran sa.

A ranar da na had'u da Sulaiman mun taso daga makarantar islamiyya ne,mun biyo ta jikin ma'aikatar da yazo takanas garin mu domin duba ta,a lokacin ne idanuwan sa suka yi arba da ni cikin shigar mutunci da kamala,nan take zuciyar Sulaiman ta afka cikin tsananin sona da k'aunata.

A daren ranar sai ga Sulaiman gidan mu,ya aiko yana sallama da ni,ban fita ba sai mahaifina ne ya fita domin ya ga wanene yake sallama da ni,domin ni ko zance bana yi duk da yawan masoyan da nake da su,cikin girmamawa Sulaiman ya gaida Babana,sannan ya shaidawa mahaifina wajena ya zo,sona yake yi,kuma shi aure na yake son yi,Babana ya tambaye shi yadda akayi ya sanni har ya zo gareni,sai ya shaida masa ya ganni ne d'azu da yammaci na dawo daga makaranta ,shine yayi tambaya akaina har aka kwatanta masa gidanmu shine yazo,Mahaifina yayi masa tambayoyi da dama kasancewar ya gane Sulaiman ba d'an gari ba ne,shi kuma Sulaiman yayi ta bashi amsa cikin ladabi da nutsuwa,nan Babana yace da shi ya tashi ya tafi,bayan kwana uku ya dawo.

Haka kuwa akayi,Babana bai min zancen ba ban ma san abin da ke faruwa ba,kawai bayan kwana uku sai ga Sulaiman ya sake zuwa,shi Babana ma ya manta da batun sa,kawai yace masa ya tafi ne a zaton sa ma ba dawowa zaiyi ba,ganinsa kamar ba aurena zaiyi ba,sai gashi Sulaiman yayi masa bazata ya dawo,kuma Sulaiman tun kwana biyu da suka shige ya kamata ya koma Abuja,amma ya kasa komawa saboda tsananin sona da ya kama shi,yana ji shifa yayi matar aure kawai.

A ranar ma Babana ce masa yayi akwai abin da yake yi,dan haka ya k'ara komawa bayan sati d'aya ya dawo,haka Sulaiman ya tafi duk da zuciyarsa babu dad'i,shi ko ganina ma abarshi yayi amma hakan ya gagara,kullum da tunanina yake kwana yake tashi,amma haka ya daure,ya k'ara share wuri ya zauna har tsawon sati d'aya,sai dai yayi wa Oga Taufik' waya akan wasu matsaloli sun tare shi amma yana hanyar dawowa da zarar komai ya daidaita.

Sati na cika cif Sulaiman bai yi k'asa a gwiwa ba ya dawo gidan mu,Babana ya cika da mamaki,nan ya san cewar tabbas Sulaiman da gaske yake yi,haka nan daman yana ta istihara kan lamarina da Sulaiman d'in,sai yake jin abin ya kwanta masa sosai a ransa.

A ranar Babana ya bawa Sulaiman damar ganina,sosai hakan ya faranta ran Sulaiman,ya dinga yiwa Baba godiya da addu'a.

A ganina na farko da Sulaiman naji ya kwanta min a raina,saboda kana ganinsa kaga mutum mai addini da cikar kamala,munyi hira a lokacin duk da ban cika magana sosai ba,sai dai zantukan soyayya da k'auna da Sulaiman ya cika ni da su sun haskaka ruhina k'warai da gaske,take naji na afka kogin soyayyarsa ni ma.

In tak'aice muku daga wannan ranar sai Gombe ta zame wa Sulaiman gida,domin ba a cikakken sati sai yazo ya ganni,da Babana yaga zirga zirgar tayi yawa sai ya umarci Sulaiman da ya turo danginsa ayi maganar aure kawai,tunda mun aminta da junan mu,Sulaiman kamar ya zuba ruwa a k'asa ya sha don murna,sai dai kuma zuciyarsa cike take da tarin fargaba saboda k'alubalen da ke tattare da shi.

Haka ya samu Oga Taufik' da maganar,nan take ya goya masa baya cikin murna da farinciki,saboda ba k'aramin so Oga Taufik' yake wa Sulaiman ba,domin yaso ace yana da y'a mace,to da wallahi ita zai bawa Sulaiman ya aura,sai dai kash! shi Oga Taufik' bai tab'a haihuwa ba,asali ma shi d'in ko mata bai da ita,duk wadda ya aura gudunsa take saboda baya haihuwa,duk da tarin dukiya da Allah yayi masa.

Sanda Oga Taufik' yazo suka gana da Mahaifina kan lamarina ni da Sulaiman,Babana ya girgiza da jin batun da Oga Taufik' d'in ya zo da shi,domin ya sanar da shi gaskiyar lamari akan Sulaiman babu b'oye b'oye,in da yake ce masa Sulaiman ba shi da kowa ! bai da iyaye,a gidan marayu ya d'akko shi ya raine shi har ya girma,saboda bai tab'a haihuwa ba,sannan ya sanar da shi cewar Sulaiman tun yana yaro suka yi had'ari shi da iyayen sa,cikin hukuncin Allah iyayen sa suka k'one k'urmus amma Sulaiman ko tabo bai samu ba,kamar cilloshi ma akayi daga motar,kuma an jima ana neman dangi da y'an uwan mahaifansa amma ba a samu ba,shine dalilin da hukuma ta bada shi a gidan marayu,sai daga baya Oga Taufik' ya karb'e shi dalilin bai da d'a ko guda d'aya.

Wannan jawabi ya girgiza Babana,ya cewa Oga Taufik' zaiyi nazari akan batun ya bashi sati biyu,Oga Taufik' yayi godiya sosai ya bar Gombe ya koma Abuja,ya zayyanawa Sulaiman duk yadda suka yi da Babana,sannan ya dinga tausar sa akan duk sakamakon da ya fito to ya karb'a yayi hak'uri da shi,haka Sulaiman ya amsa,sannan ya dage da addu'a.

Mahaifina ya kira ni yayi shawara da ni akan maganar,na nuna masa ni dai ina son Sulaiman a haka,tun da dai musulmi ne,kuma an tabbatar iyayensa mutuwa suka yi ba wai jefar da shi akayi ba dalilin an same shi ta gurb'atacciyar hanya,jin hakan sai mahaifina ya goya min baya,duk da mahaifiyata ta so hanawa,amma da Babana ya zaunar da ita ya fad'akar da ita da maganganu masu dad'i sai ta amince ta sanya albarka a lamarin,sai dai tana ji a zuciyarta za ta yi kewata,saboda mu biyu kacal ta haifa,daga ni sai k'anwata Sajida,kuma ni ce babba,saboda suma iyayena Allah bai basu haihuwa da wuri ba.

Wannan shine tsanin Soyayyata da Sulaiman,kuma turbar da ta kaimu ga auren juna ni da shi,munyi aure na soyayya da k'auna,Sulaiman na sona nima ina son sa,cikin lokaci k'ank'ani komai ya kammala aka d'aura aure na da Sulaiman,aka kaini dank'areren gidan Oga Taufik' da ke Abuja,wanda ya bamu part guda domin mu zauna ni da Sulaiman,kuma ya k'awata mana ko ina da kayan more rayuwa da kayan cima kala kala.

Mun yi zaman aure mai tsananin dad'i da nagarta ni da Sulaiman,baya son b'acin raina ko kad'an,yayin da nake masa ladabi da biyayya sosai da sosai,haka nan ina tsananin girma ma Oga Taufik' wanda muke kiransa da (ABBA) ni da mijina,ko abinci zan dafa tare da shi nake dafawa na zuba Sulaiman ya kai masa,da farko ma Oga Taufik' cewa yayi in daina wahalar da kaina ina dafa masa abinci,amma nak'i dainawa,saboda ni a uban miji na d'auke shi,uban miji kuwa kamata yayi ka kyautata masa yadda za ka kyautatawa naka mahaifin,kullum Oga Taufik' saka mun albarka yake ni da mijina,ya kan ce muna wawashe masa takaicinsa na rashin haihuwar da baiyi ba,a kullum kuma Sulaiman bai fasa rok'on Oga Taufik' akan yayi aure ba,ya kan ce "Abba don Allah kayi aure,zaman ka haka babu dad'i" sai Oga Taufik' yayi murmushi ya ce,"Sulaiman kenan! tunda dai kai kayi ai shikenan,ni bana sha'awar yin auren ne,babu wacce za ta zauna dani ta san bana haihuwa,ni mata ma tsoro suke bani wallahi,duk wadda zata aureni yanzu sai dai ta aureni don dukiyata amma ba don soyayya ba"

Sulaiman ya sha zuwa yace min shifa yana so Abban sa yayi aure,sai in yi murmushi in ce"Idan da rabo zai yi".

Haka rayuwar mu ta kasance cikin jin dad'i,duk wata hidima ta Oga Taufik' a hannun Sulaiman take,babu wanda ya san sirrin Oga Taufik' sama da mijina Sulaiman,haka nan babu mutumin da Sulaiman ya fi so a duniya irin Oga Taufik',domin ko hira nake ni da shi bai da zance sai na Abban sa da yabon sa,ya kan rok'e ni akan nima na cigaba da girmama masa Abban sa da yi masa hidima.

Wata ranar Asabar lokacin watan mu shida da aure,ina kwance ina baccin rana saboda yadda nake jin kasala sosai a jikina,sakamakon shigar ciki k'arami da na samu,sai ga Sulaiman ya dawo gida katsahan,ina d'an baccina amma sai da ya tasheni da wasannin sa ya wartsakar da ni,sai da na wanko idanuwana a toilet na dawo gare shi sannan nake tambayar sa me ya dawo da shi gida a dai dai wannan lokacin?

Sai yake ce min "Zainab Abbana ne zaiyi bak'i abokanan aikin kwangilar sa,kuma gida za su zo su ziyarce shi,shine ya ce min in je restaurant in siyo musu abinci da abubuwan sha da za a tarbe su da su,ni kuma sai nake ganin tunda gaki ai babu abin da ba zaki iya ba,yanzu so nake ki tashi muje ktcheen muyi girki kala kala domin mu fitar da abbana kunya ko?"

Jijjiga kai nayi ina murmushi,duk da ko ktcheen din bana son dosa saboda abin da ke cikina baya son k'amshin ktcheen,amma haka na daure muka shiga ni da Sulaiman muka fara harhad'a abubuwan da zamu buk'ata,nan da nan muka fara girki Sulaiman na tayani da yanka abubuwa,yana ta min dariya ganin nasa yanki na d'aure hancina dalilin bana son k'amshin abincin,a haka har muka kammala,Sulaiman na ta azalzalata wai muyi sauri saboda bak'in daga Kaduna za su tawo,kuma yanzu dab suke da isowa.

Ko awa d'aya bamu yi da kammalawa ba sai ga Abba yayi wa Sulaiman waya kan cewa bak'in fa sun iso,ganin kayan da yawa sai Sulaiman ya umarceni da na sanya hijabina na tayashi d'aukar wasu kayan domin mu kai,haka kuwa akayi,ya d'auki basket d'in da na jera abinci,ni kuma na d'auki wanda na jera drink da su ruwa,muka nufi sashen Oga Taufik' (Abba).

Bak'in su biyu ne kacal,har k'asa na durk'usa na gaishe su,Abba yana ta fara'a yana nuna musu ni a matsayin surukarsa matar d'an sa,ganin abincin da yawa kala kala nan Abba ya fahimci ni ce na girka,nan ya dinga yiwa Sulaiman fad'a wai ya wahalar da ni,shi dai Sulaiman dariya yake kawai,Abba ya min godiya sosai,abokanan sa ma suka yi min godiya,wad'anda na rik'e sunan su sosai a raina,lokacin da naji Abba na fad'awa Sulaiman sunan su,wato ALHAJI MUDASSIR DA ALHAJI MAUDE.


Comments
share
vote
pls


*GARKUWA BIYU*


BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter 23 · 0% Book details