← Book details Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 21 OF 31

BABI NA SABA'IN DA TARA DA NA TAMANIN

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

****A sanyaye ya juya ya fasa shiga d'akin,domin bai ma san ta ya ya zai fuskanceta tana wannan kukan ba,a yanzun ma ba k'aramin motsa masa mikin da ke zuciyarsa tayi ba,gabad'aya ta taso masa da wata irin kewar Khaleel shi ma.


Umma da Mummy suka waiwayo suna kallonsa lokacin da ya k'araso parlour'n,da hanzari ya aro jarumta dan kar su gane yanayin sa,Umma ce ta cigaba da kallonsa sannan tayi magana.

"Wai har ka bata maganin kenan?"

Girgiza kai yayi yana shirin zama kan kujerar da ke gefensa,a hankali ya dubi Umma yayi magana.

"Ah ah ban bata ba,da alamun kamar barci ta fara yi shiyasa na k'yaleta zuwa lokacin da za ta farka"

Umma ta d'an murmusa ta ce.

"Ai gara ta samu tayi barcin zai rage mata damuwa,tunda muka dawo daga asibitin nan na lura tana cikin damuwa,na san k'ila sakin da Khaleel yayi mata ne yake damun zuciyarta,to amma ya zata yi ?haka Allah ya k'addara zai faru"

Shiru Hamza yayi baice komai ba,sai can ya dubi Mummy da tayi shiru tana jin maganganunsu kawai,har zaiyi magana kuma sai ya fasa ya sake maida kansa k'asa yana sakin ajiyar zuciya. Mummy ta lura da shi shiyasa tayi murmushi ta kalleshi ta ce.

"Ya dai GARKUWAR HIDAYA akwai wata magana ne?"

Girgiza kai kawai yayi cikin k'aramin murmushi,yayi shiru ya kuma yin k'asa da kansa.

Mummy ta dubi Umma suka had'a ido suka yi murmushi,sannan ta dawo da ganinta kan Hamzan,cikin muryar kyautatawa ta ce.


"Labarin zuciya a tambayi fuska! akan fuskarka na hango tarin maganganun da ke zuciyar ka GARKUWA,don haka bud'e bakinka ka fito da komai,kar ka bar komai a ranka,domin barin kashi a ciki baya maganin yunwa"

kafin ma yayi magana Ummansa ta cafe zancen tana kallon Mummy.

"Aikam dai gara ki fad'a masa,domin wannan GARKUWAR ta ki bashi da wani hali sai barin kashi a cikin,wanda barin da yayi masa har yayi masa babbar illa cikin cikinsa"

Mummy bata gane zancen Umma ba,amma shi Hamza sarai ya fuskanci abin da take nufi,murmushi kawai yayi bai ce komai ba,illa duban Mummy da yayi ya fara magana cikin nutsuwa.

"Mummy daga ni har Hidaya zuciyoyinmu cike suke da son sanin abubuwa da dama daga gareki,na farko sanin alak'ar Daddy da mahaifin Hidaya,na biyu tabbacin Daddy ne ya kashe shi da kuma dalilin yin kisan,na uku dalilin gujewarki a rayuwar Hidaya tsawon lokaci,na hud'u son sanin yadda akayi kike bibiyarmu da sanin halin da muke ciki,na biyar dalilin bayyanarki garemu a dai dai wannan lokaci,na shida....

"Dakata GARKUWA" Mummy ta katseshi cikin k'aramin murmushi,sannan ta cigaba da ce wa.

"Duk wad'annan tambayoyin ni zan amsa muku su? Lallai kun had'ani da aiki babba" Cikin sigar zaulaya tayi maganar,Hamza ya d'an shafa kwantacciyar sumar kansa yana jingina da bayan kujerar da yake zaune,cikin wani irin murmushi shi ma ya dubeta ya ce.

"Eh Mummy,duka muke so har ma da k'arin wasu tambayoyin,don Allah a taimaka ko dan mu san yadda za mu tunkari lamarin Daddy wajen shari'a"

Ambatar sunan Daddy ma bata so,amma hakan ta cije bata bayyana ba,illa murmushi da ta sake yi wanda ya zamto na takaici a gareta,sannan ta cewa Hamza.

"To kar ka damu GARKUWA,da yardar Allah za ku ji komai da kuke buk'atar ji daga gareni,akwai dalilin da ya saka har yanzun ban gaya muku ba"

Gyad'a kai yayi tare da ce wa.

"To shikenan Mummy Allah ya nuna mana lokacin"

"Ameen ya Allah" Mummy ta fad'a,sannan ta d'auke kanta daga gareshi ta mayar da hankalin ta kan Umma suka cigaba da hirar duniya da abubuwan da suke faruwa a wannan zamanin.

Hamza yana zaune yana sauraren su shiru da shi,can ya d'auko wayarsa yana d'an danne danne har ya shiga gallery,da hoton su ya fara cin karo shi da Khaleel,wanda suka d'auka ranar d'aurin aure,Khaleel ya dafo kafad'arsa suna murmushi,sunyi matuk'ar kyawu mara misali,k'urawa fuskar Khaleel idanuwa yayi kamar ya ciroshi daga jikin hoton,wata k'walla na taruwa a idanunsa,a hankali ya danne wayar ya kashe ta ma gabad'aya ya jefa cikin aljaihunsa,sai kuma ya mik'e a sanyaye ya dubi Umma,yayi magana a hankali.

"Umma bari na d'an fita gun su Faisal"

Umma ta amsa,ya nufi k'ofa ya fice yana jan k'afa,gabad'aya baya jin dad'in yanayin jikinsa,shi kansa idan aka bashi gado a asibiti tabbas zai kwanta ne,saboda yanayin da yake jin jikinsa da zuciyar sa,a tsakar gida ya tadda Aunty Sajida tana aiki,yayi mata sannu sannan ya wuce ya fice daga gidan ma gabad'aya,Aunty Sajida ta bishi da idanuwa har ya k'urewa ganinta.


A can parlour ma Mummy da kallo ta bishi,sai da ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya,cikin murmushi ta ce .

"GARKUWA kenan"

Umma ta d'anyi dariya kad'an tana duban Mummy ta ce.

"Wato dai kin sakawa Hamza suna GARKUWA ko? to wai shin GARKUWAR Hidaya kike nufi ko kuwa?"

Mummy ta jingina da bayan kujerar da take kai tana duban Umma,tayi murmushi mai kyau ta ce.

"Ki godewa Allah ki k'ara godewa Allah da ya baki Hamza a matsayin d'a,Hamza ba iya GARKUWAR Hidaya ya tsaya ba ! shi d'in GARKUWA NE a komai !

Sai Umma tayi murmushi tana jin dad'in yabon da d'anta yake samu a kullum.


****************


Wannan magana da Khaleel ya fad'awa Aunty Kubra ita ce magana mafi muni da ta tab'a ji a kunnuwanta,wai mijinta ne yayi kisan kai! tayi kuka a ranar kuka mara misali,har ta dinga danasanin kasancewa a matsayin matar Daddy,duk da yanzu alamu sun nuna ya shiryu,amma kisan kai babban tabo ne da zai iya shafar rayuwar y'ay'anta ko a gaba.

A maimakon ta cigaba da rarrashin Khaleel sai ita ma take neman me rarrashinta,har sai da taga kukan bashi da wani amfani a gareta sannan ta hak'ura ta daina,sai dai lokaci zuwa lokaci ta kan ji hawayen ya zubo mata,ta kai hannu ta share.

Ko wayar Daddy k'in d'agawa tayi,saboda ko muryarsa bata k'aunar ji,abu d'aya kawai take son sani,shine yadda akayi Daddyn ya kashe mahaifin Hidaya,a yaushe hakan ta faru?kuma menene dalilin kisan?duk yadda zuciyarta ke zakwad'in samun wad'annan amsoshi bata kai Khaleel ba,ji yake tamkar yayi fiffike ya tafi gurin Hidaya ta warware masa komai,hakan yasa ya dinga yiwa likitansa magiya yana kuka akan ya sallameshi,iya rarrashi likitan yayi masa akan ya bari ya sake murmurewa amma Khaleel ya k'i amincewa,tilas likitan ba don ya so ba a washe gari ya rubuta takardar sallama ya basu,tare da kafa sharud'a masu yawa wajen kulawa da lafiyar Khaleel d'in.

Suna shirin tafiya sai ga Daddy ya zo,daga Khaleel d'in har Aunty Kubra babu wanda ya dubeshi,dan wani mugun kallo ma da Aunty Kubran tayi masa sai da ya yamutsa masa y'an hanjin sa,tsoro ya kamashi dan ya san tabbas Khaleel ya fad'a mata komai,kuma ya san in zai kwana dubu yana nufin kare kansa ba za su saurare shi ba.

Ya na ji Khaleel yana cewa da Aunty Kubra shifa ba zai shiga motar sa ba,gara ya hau motar haya ta mai dashi gida ko ya tafi da k'afarsa,bai k'ara jin mamaki ba sai da yaji Aunty Kubran ta mayar masa da amsar cewa"Ni ma ba zan hau motar Daddynka ba Khaleel,ni yanzu tsoronsa ma nake yi,mutumin da yayi kisan kai ai abun tsoro ne,muje mu shiga tawa motar mu tafi,daman da ita na zo asibitin nan randa muka kawo ka"

Daddy yana tsaye kamar gunki yana duban su,har Aunty Kubra ta gama ficewa da kayansu ta saka a mota,sannan ta dawo tana tambayar Khaleel shin zai iya tafiya ko sai ta rik'eshi,Khaleel yace zai iya,saboda jikinsa babu k'wari garin mik'ewa har yana shirin fad'uwa,Daddy ya zaburo zai rik'e shi,Khaleel ya janye jikinsa da sauri yana d'auke kai gefe guda,sannan ya gyara tsayuwar sa ya fara takawa a hankali kamar mai tausayin k'asa,ya rame sosai duk ya zurma,yayi fari fat dogon hancinsa ya k'ara fitowa,leb'ensa yayi jajur,yayin da idanuwan sa suka k'ara fitowa da wata irin kala.

Yana tafe Aunty Kubra na biye da shi har zuwa wajen mota,Daddy yana tsaye suka tafi suka barshi a d'akin,ya rasa ma mai zaiyi,haka shima ya janyo jiki ya fito a salub'e,yana kallo Aunty Kubra ta bud'ewa Khaleel k'ofa ya shiga ya zauna,ita ma ta zagaya ta shiga ta rufe,sannan ta tayar da motar suka fice daga harabar asibitin,A sanyaye Daddy ya k'arasa wajen tasa motar ya shiga ya tayar ya rufa musu baya,gara ya bisu gida ayi ta ta k'are kawai.

Sun fara tafiya kan titi Khaleel yana ta takure jikinsa yana lumshe idanu,sanyi yake ji sosai,har sai da ya waiwayo ya dubi Aunty yayi magana a hankali.

"Aunty a kashe A C d'in motar nan,sanyi nake ji"

Aunty ta kai hannu ta kashe tana cigaba da tuk'i,fuska babu walwala ta ce.

"Don dai kawai ka damu a sallameka ne Khaleel,amma ni na san baka gama warkewa ba,har yanzu jikinka baiyi k'warin da ake so ba"

Murmushi yayi mai ciwo,kafin ya girgiza kai yayi magana.

"Ai Aunty jikina ba zai tab'a dawowa yadda ake so ba,balle kuma zuciyata da ta riga ta gama raunata gabad'aya"

Hanzarin dubansa tayi ta d'an harareshi,sannan ta ce.

"Kar ka kuma fad'in hakan Khaleel,Ai Allah (S W A)shine yake d'orawa bayinsa cuta,kuma shine yake yaye musu,kar ka cire rai da rahamar Allah,sai kaga ka warke sumul kamar baka tab'a wata cuta ba"

Murmushi ya sake yi,sannan ya ce.

"Haka ne Aunty,tunda kin ambaci Allah" Sai kuma yayi shiru ya d'an rufe idanuwansa yana maida numfashi,Aunty ta cigaba da tuk'in ta kowa yayi shiru.

Sun d'an yi tafiya mai nisa suna dab da zuwa wata kwana sai Khaleel ya bud'e idanuwan sa,gyara zamansa yayi sannan ya waiwaya ya kalli Aunty Kubra ya ce.

"Ba gida zaki kaini ba fa Aunty"

A d'an sace tayi masa kallon mamaki ita ma ta tambaye shi.

"Ina zan kai ka?"

Kai tsaye ya amsa.

"Gun Hidaya da Aboki"

Sai da Aunty ta sake rik'e sitiyarin motar sosai saboda yadda ya so kufcewa daga hannunta tsabar mamakin maganar da Khaleel ya fad'a,cikin wata irin murya ta ce.

"Khaleel me kace?na kaika gun Hidaya?nufinka in kaika gidansu yanzu fa! kai kuwa wane k'warin gwiwa ke gareka da har za ka iya tunkarar wad'annan mutanen bayan manyan laifukan da ka aikata musu?"da wane ido za ka kallesu Khaleel?"

Wani hawaye ne ya ciko idanuwan sa har ya zubo kan kyakkyawar fuskarsa,ya ja numfashi ya runtse idanu yayi magana cikin rauni.

"Ko ma da wane ido ne zan kallesu Aunty....ni dai fatana ki kaini gare su yanzu...ina son sanin komai...ina son fita daga duhu zuwa cikin haske...ina son komai ya bayyana gareni kafin raina ya bar gangar jikina,ina son yin ido hud'u da manyan masoyan da zuciyata ke so kafin k'asa ta rufe idanuwa na,ki kaini Aunty,yau nake da dama tun kafin damar ta kufce min na rasa....

Sai tausayin Khaleel ya tsirgawa Aunty Kubra,taji ita ma hawayen ya tawo mata,a hankali ta karkatar da motar ta suka nufi gidan su Hamza kamar yadda Khaleel ya buk'ata.

Daddy da ke bin su a baya ganin sun sauya hanya kawai shi ma sai ya sauya,ya rufa musu baya domin bin su in da za su je,a zuciyar sa yana fad'in gara ya bisu koma ina ne,komai ta fanjama fanjammmmm.....!


*TIRK'ASHI*!!!


Comments
share
vote
pls


*GARKUWA BIYU*


BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter 21 · 0% Book details