← Book details Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 8 OF 31

BABI NA HAMSIN DA UKU DA NA HAMSIN DA HUD'U

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

***Umma ta jima tana rarrashin Hamza a d'akin sa,Wanda yake cikin tashin hankali da tsananin kuka kamar ba zai bari ba,da k'yar ya yi shiru saboda yadda Zuciyar sa ta fara sanyi a bisa innalillahin da ya dinga karantawa,tabbas k'addarar sa ce ta zo,jarrabawar sa ce ta zo,idan yana son ya cinye ta kuma dole sai yayi hak'uri akan duk wata k'addara da ta same shi Mummuna ko kyakkyawa,tun da Allah da kan sa yake fad'a a cikin alk'ur'anin sa mai girma cewar ya halicci komai da k'addara.


"إنا کل شیء خلقنہٰ بقدر"


Ma'ana(Mun halicci komai da k'addara).

"و خلق کل شیء فقدرہ تقدیر"

(Kuma ya halicci kowane Abu,kuma ya k'addara shi k'addarawa).

Haka nan duk wani D'an Adam ba abin da yake so ne yake kasance wa ba,sai abin da Allah ya nufa,domin fad'in Allah ta'ala.


"و ما تشاءون إلا أن یشاء اللہ رب العلٰمین"


Ma'ana(Kuma ba abin da kuka so ne yake kasance wa ba,sai abin da Allah ubangijin talikai ya so wakanarsa).


Ayoyin da Umman sa ta karanta masa,da wad'anda suka zo Zuciyar sa a yanzu,sun isa su sa ya gane cewar hak'uri da wannan k'addara da ta same shi tilas ne,idan har yana so ya cinye jarrabawar sa,haka nan Allah ya gani bai so kansa akan D'an uwansa abokin sa Khaleel ba,ya tabbatar sakamako mai kyau zai iske shi watarana,shiyasa yaji k'arfin imani da k'addara ya shige shi.


Umma ta bar d'akin sa cike da tausayin sa,ta koma d'akin ta ta tarar da Hidaya har bacci ya kwasheta akan daddumar da tayi sallah,hawayen da ta zubar duk ya bushe akan kyakkyawar fuskar ta,sai Umma taji tausayin ta ya cika Zuciyar ta,ta san baccin da bata samu jiya da daddare ba take ramawa,shiyasa bata yi yunk'urin tashin ta ba ta barta ta cigaba da baccin ta kawai…..

Har wajen misalin k'arfe goma na safe Hidaya na bacci,Tuni Umma ta gama aikace aikacen ta tayi break fast,Wanda ta d'auka da kanta ta kaiwa Hamza har d'akin sa, ta tarar da shi yana karatun alk'ur'ani cikin kamala da nutsuwa,sai ta ji dad'i a ranta.

Bata bar d'akin ba kuma sai da ta saka shi a gaba ya ci abincin,duk da ta lura cusawa kawai yake ba don yana masa dad'i ba,sai lokacin Umma ke tambayar sa ya ya jikin nasa? Ko za su je asibiti ne a duba shi,nan ya tabbatar mata ba ma sai sun je asibiti ba da sauk'i, har ma yake tambayar ta jikin Hidaya,ta tabbatar masa Hidayan har zuwa lokacin bacci take yi,sai ya D'an yi murmushi kawai ya sunkuyar da kan sa k'asa.


K'arfe sha d'aya da mintuna biyar muryar Khaleel ta kwarara sallama a tsakar gidan,lokacin Hidaya ta farka tana toilet tana wanka,Umma kuma na zaune a parlour'n ta,yayin da Hamza ke kwance a d'akin sa yana baccin ramuwa shi ma,Umma taji kamar muryar Khaleel, gaban ta ya D'an fad'i,ta mik'e da sauri tana d'aga labule, sai kuwa tayi arba da shi tsaye a tsakar gida fuskar sa cike da murmushi,Kwarjinin sa ya cika wa Umma idanu,ta ga ya k'ara wani girma da kyau tamkar wani balaraben misra,bata san lokacin da ta washe baki ba tana fad'in.


"Lale marhabin da Ibraheem, barka da zuwa bak'on turai"

Khaleel yaji farinciki sosai da ganin Umma, da sauri ya k'ara so gaban ta ya zube gwiwoyi a k'asa,cikin matuk'ar ladabi yake gaishe ta cike da fara'a,Umma cikin jin dad'i take amsawa tana fad'in.

"Wannan ba don nayi maka kyakkyawan sani ba ai ba zan ganeka ba Ibraheem,sai na d'auka wani bak'on balarabe muka yi daga k'asashen larabawa"

Yayi dariya cike da k'aunar Umman a ransa,Umma kam cewa take"shigo ciki Ibraheem, shigo mu k'ara gaisawa na ganka sosai"

Ya cire takalman sa ya bita har cikin parlour'n, Umma ta kasa zaune ta nufi kitchen ta kawo masa lemo da cincin,haka kawai taji tana murna da ganinsa,shi kansa Khaleel yana jin Umma a ransa ne tamkar mahaifiyar sa,ko domin yadda ta d'auke shi tamkar Hamza..

Umma ta zauna suna ta hira ita da Khaleel, tana tambayar sa Abubuwa da dama game da karatun sa da rayuwar sa,shi kuma yana bata amsa cike da ladabi,haka nan yake cin cincin da lemon duk da basu kasance masu tsada ba kamar abincin da ya saba ci,shi sai yake jin dad'in na Umman ma fiye da kowanne,Umma halayyar Khaleel tana birgeta,saboda baya k'yamatar su ko abin hannun su duk da kasancewar mai abin duniya.

Nan Umma ke masa k'orafin me yasa ba zai zauna ya gama hutawa ba?jiya jiyan nan daga dawowarsa amma har ya d'akko k'afa ya tawo Kaduna? Sai yayi murmushi kawai yace.

"Umma ina son na zo na ganki na gaishe ki ne,Sannan na duba jikin Aboki,saboda jiya mun rabu baya jin dad'in jikinsa,kuma tun jiyan nake Neman wayar sa a kashe,shine na kasa zama nayo sammako na tawo"

Umma ta jinjina kai tace.

"Allah sarki!ai jikin na sa da sauk'i ma,yanzu ma bacci yake yi a d'akin sa"

Tana rufe baki sai ga Hidaya ta fito parlour'n daga cikin bedroom, wadda ta fito daga wanka d'aure da babban towel a jikinta,sai k'arami da ta lullub'a a saman kanta,ta fito parlour'n ne da niyyar tambayar Umma in da ta ajiye mata wata doguwar rigar ta da Hamza ya siyo mata,tana son ta saka ta a lokacin,kwata kwata ma bata san Khaleel ya zo ba balle taji muryar sa a parlour'n, har sai da ta fito parlour'n tana wa Umman magana sannan ta Ankara da shi..

K'irjinta yayi bala'in bugawa da k'arfi,yayin da Khaleel ya bita da wani sumammen kallo tamkar ya mik'e ya cafkota yake ji,shauk'in amsar da ta rubuta masa Daren jiya na k'ayata ruhinsa,baki sake yake kallon ta yana jin yadda take zagaye jinin jikinsa,ita kuwa tamkar a tsorace take kallon sa,domin da ta san yana nan babu abin da zai fito da ita parlour'n ko cikakkun kaya ne a jikinta balle towel,k'afafuwan ta suka soma rawa,da wani irin hanzari ta juya ta shige bedroom d'in da gudu tana nishi.

Shi kam cikin mutuwar jiki ya bita da kallo,kafin ya sauke ajiyar zuciya yana shafa gashin kansa,ya juya a hankali yaga Umma na kallon sa,wata kunya ta kamashi,da sauri ya sunkuyar da kai k'asa,sai kuma ya mik'e da sauri yana fad'in.

"Umma bari na duba Aboki a d'akin sa"

Yana fad'in hakan yayi saurin ficewa,ya bar Umma zaune cikin tunanuwa barkatai.


********************


Da sauri Hamza ya bud'e narkakkun idanuwan sa jin Khaleel ya fad'o kansa yana dariya,kallon juna suka yi,Hamza yayi murmushi k'irjinsa na bugawa,Khaleel ya janyo hannunsa yana mik'ar da shi zaune,cikin Y'ar dariya yayi magana.

"Aboki ka wartsake gani na zo fa"


Hamza ya D'an yi Hamma yana lumshe idanuwan sa,kan sa na sarawa,cikin dusashewar murya ya dubi Khaleel yace.

"Khaleel me yasa ka tawo?kamata yayi fa ace ka zauna ka huta sosai"

Ya girgiza kai yana wani lumshe ido yace.

"Ni ba zan iya zama ba ne,na barka baka jin dad'i,na kwana da kai a raina,gashi ina son ganin Hidaya, ko domin nayi mata godiyar amincewar da tayi da soyayyata,Aboki jiya na yi kwanan farinciki da na riski sak'on Hidaya dangane da amincewa ga soyayya ta"

Hamza yaji wani Abu mai kama da bak'inciki a Zuciyar sa,da sauri ya fara addu'a yana korar shaid'anin da ke son kawo masa farmaki,yayi wani murmushi da ya k'ara masa kyawu ya dubi Khaleel yace.

"Amma na yi farinciki da jin hakan sosai,Aboki na ya samu mace ta gari,yayin da k'anwata ta dace da miji na gari"


Sai khaleel yayi murmushi ya rik'o hannun Hamza yace.


"Maganar da take cin raina kenan,har na ce maka idan na dawo za mu tattauna,sai gashi cikin ikon Allah Ubangiji ya kawo min mafita da wuri,na dace a karon farko,yanzu sai kai Aboki,ina son ka bani Labarin soyayyar ka,kuma ina son sanin wacece tayi sa'ar samun ka?domin da alamun kana tsananin sonta,bi sa ga yadda naji kana zazzaga kalamai a kanta…

Gaban Hamza ya fad'i,ya rasa abin cewa,ko giyar wake ya sha ai ba zai iya fad'awa Khaleel cewar Hidaya yake so ba,da k'yar ya samu abin cewa wajen fad'in.


" Wasa nake maka Khaleel, babu wata da nake so a raina"

Khaleel ya dube shi da hanzari cikin mamaki yace.

"Wasa kuma?daman ana wasa da So ne Aboki..!?

Hamza ya runtse idanu yana sakin numfashi ya kasa magana,Khaleel ya tsura masa idanu yace.

" Bana son k'aryataka ne Aboki,domin k'arya ba halayyarka ba ce,amma gaskiya zuciyata bata amince cewar wai wasa kake ba,domin yanayin ka yayi kama da Wanda soyayya ta yi masa mugun kamu.."


Shi kan sa Hamza ba jin dad'in k'aryar da ya zuba yake ba,kawai ya rasa abin fad'a ne,shiyasa yake ta istigfari cikin Zuciyar sa da Neman yafiyar Allah,a hankali ya dubi Khaleel da ya zuba masa idanu yace.

"Kai ma ka san bana b'oye maka komai,idan akwai wacce nake so kai ne mutum na farko da zan sanarwa,ka yarda wasa kawai nake maka,kalaman da kaji na yi a waya kawai a wani littafi na karanta,shine na kwaikwaya na fad'a maka,ina so ne na gane shin na iya soyayyar?idan na samu wacce nake so zan iya fad'amata irin kalaman?dalilin da yasa kenan fa,amma ba wai don na samu wadda nake so d'in ba,ka yarda da ni Khaleel…!


Khaleel yayi ajiyar zuciya tare da murmushi yace.

" Na fahimta Aboki,kuma na gasgata ka,amma na so ace zuwa yanzu kaima kana da taka masoyiyar a Hannu,domin na so ranar Auren mu ta kasance rana d'aya,amma da alamun a yanzu zan rigaka shiga daga ciki,don yadda Hidaya ta mamaye ruhina ina jin ko wata biyu ba zan iya jira ba tare da ta zama mata ta ba,domin a lissafina saura wata d'aya ta kammala secondary school ko..?"

Hamza ya gyad'a kai yana D'an murmushi yace.

"Eh hakane Khaleel, amma da wuri haka?me ya sa kake hanzari?

Khaleel shi ma yayi murmushi me kama da dariya yace.

" To menene abin jira Aboki?tunda har ta amsa min tana sona ai kawai ta zama mata ta a kurkusa shine tabbacin cikar soyayyar mu,ni yanzu ma please ka tashi kaje ka kawo min ita d'akin nan,sosai nake mararin ganin ta,ina jin kunyar Umma ba zan iya kiran Hidaya a gaban ta ba.."

Sai Hamza ya jijjiga kai,ya zame hannun sa daga na Khaleel yana k'ok'arin sakkowa daga gadon,Khaleel ya matsa,shi kuma ya sakko jiki ba k'wari ya fice daga d'akin,yayin da Khaleel ya bi shi da idanu yana jin sabuwar k'aunarsa a ransa .


******************


Umma zaune kan kujera,yayin da Hidayan ke zaune a k'asa Umma na yi mata Kalba a kanta,Umma tana so tayi wa Hidaya zancen Hamza amma tana tsoron kar ta tono Zuciyar Hidayan har tayi kuka,a gefe guda kuma ita kanta Hidayan tambayoyi ne fal a ranta da take so tayi wa Umman,musamman akan abotar Ya Hamza da Uncle Khaleel, tana son jin yadda aka yi suka san juna har suka shak'u haka,alhali shi Khaleel gidan su yana abuja,shi kuma Ya Hamza Kaduna,to ta ya ya suka had'u har suka yi wannan shak'uwar tamkar y'an uwa na jini?wad'annan tambayoyin da ma wasu sune suka addabi Hidaya a Zuciyar ta me cike da rauni…


Hamza ya shigo parlour'n Umma da sallama cikin siririyar murya,kallo d'aya yayi wa Hidaya da kanta ke sukuye yayi saurin d'auke idanun sa,kullum k'ara kyau take a idanuwan sa,shi sai yaga yau d'in har gashin kanta ya sauya masa,kamar ba shi ne kusan yake gyara mata kan ba ma kan ta girma sosai ya daina,Dan a can baya har tsifar kai shine yake mata,wataran har wankin kan ma shine yake mata,da ta fara girma ya daina yi mata kam an sha daru,yace Umma ce za ta cigaba da yi mata,in dai za a yi kuwa to da kukan ta ake yi, shi kam Hamza sai dai yayi ta lallashin ta.

Zama yayi kan kujera kusa da Umma, yana wani lumshe idanuwan sa,Umma ba tayi magana ba sai shine ya sake duban Hidaya a karo na biyu sannan ya kawar da kai,a hankali yace.

"Keh…ki tashi kije Khaleel yana son magana da ke"

Hatta Umma sai da ta kalleshi,balle Hidaya da ta d'ago a hanzarce ta k'ura masa idanu cikin bugawar zuciya,kallon da take masa yana son saka shi wani hali,shiyasa yayi saurin d'auke kansa daga gareta yace.

"Baki ji abin da nace ba ne…!?

Cikin marairaicewa da shagwab'a ta amsa da cewa.

" Ya Hamza kitso fa Umma take min"

Ya amsa yana Jan hanci.

"Abar kitson,idan kin dawo a k'arasa"

Zumb'ura baki tayi cike da haushi,shikam sai ya kashingid'a ma yana lumshe idanuwan sa,da yaga bata tashi ba sai ya bud'e idanunsa kad'an yayi mata kallon k'asan ido,cikin wata irin murya mai kama da fad'a yace…

"Kar ki bari na tashi baki rigani tashi ba,Allah zan mareki ne Hidaya,kin san bana son taurin kai ko…?

Da hanzari ta tashi tana hawaye,ta figi hijabin ta da ke kusa da Umma ta zumbula sannan ta fice da sauri.

Ya bita da kallo har ta fice,kafin ya d'auke kansa yana D'an sakin tsaki kad'an,a hankali yayi magana bayan ficewar ta,gabad'aya ma ya manta da Umma da ke zaune a wajen..

" Gulma kawai…an ce kije Khaleel na kiranki kin tsaya wata gardama…kamar ba ke ce kika amsa masa kina son shi ba"

Kawai muryar Umma yaji tana magana.

"Lallab'ata fa ya kamata ka yi Hamza,ni banga abin fad'a ba,yanzu gashi nan kasa ta ta fi tana Kuka"

Shiru yayi yana ajiyar zuciya,ya kwanta lamo kan kujerar yana takurewa kamar mai jin sanyi,Umma ta girgiza kai cike da tausayin sa,sannan ta tashi ta nufi kitchen domin d'ora abincin rana.


****************


Ta d'aga labulen d'akin ta na sallama cikin siririyar murya,Khaleel da ke kwance rigingine yayi saurin mik'ewa cike da farincikin ganin ta, a bakin k'ofar ta tsaya ta kasa k'arasowa kanta a sunkuye,ga hawaye sai sharara suke yi ta kasa tsayar da su,da sassarfa ya k'araso gaban ta ya tsaya yana ambatar sunan ta cikin wata daddad'ar murya mara amo.

"Hidayaaaaa….

Wani irin yarrrr taji a sassan jikinta,kawai sai ta durk'ushe a wajen ta k'udundune kanta cikin Hijab tana shesshek'ar kuka,hankalin Khaleel a tashe shi ma ya bita ya durk'ushe gaban ta,ji yake tamkar ya kamata ya rungume a k'irjinsa,wata irin k'aunarta yake ji tana tsumashi,jikinsa har rawa yake,sunkuyawa yayi saman kanta yana k'ara ambatar sunan ta.

" Hidaya….tashi ki gani….d'ago kanki ki kalleni kinji"

Ta k'i d'agowa ta kalleshi, illa ma k'ara k'udundune kanta da tayi,yayi yayi ta d'ago amma tak'i,cikin wata irin murya ya sake matsarta sosai yace.

"Zan rungumeki Hidaya,wallahi zan rungumeki idan baki d'ago kin tashi ba"

A zabure ta d'ago ta na k'walalo idanu,ganin sa dab da ita yana mata wani kallo sai tayi maza ta runtse idanuwan ta tana sakin ajiyar zuciya,ya k'urawa fuskar ta ido yana bin hawayen ta da kallo,ya narke murya cike da soyayya yace.

"Ina ma na aureki,da wad'annan hawayen naki sun zamo Ruwan sha na a yau,kwad'ayin su nake Hidaya"

Maganar da yayi ta saka ta bud'e idanuwa ta kalleshi, k'irjinta ya nata bugawa da k'arfin gaske,ya wani lumshe ido yana gyad'a kai alamar tabbatar mata da abin da yake nufi.

Sai ta sunkuyar da kai kawai tana jin wani Abu na zagayawa da ita,ya sake rage murya kamar mai rad'a.


"Na kwana cikin farincikin da ban tab'a riskar kaina a ciki ba Daren jiya,kin faranta min a bisa amincewar ki ga soyayya ta,ina sonki Hidaya,ina tsananin k'aunarki masoyiyata,Allah ya cika min burina na mallakeki a matsayin mata ta"

Tayi shiru ba magana,duk a takure take jin ta,shi kuma Khaleel ya dage sai ta amsa da Ameen,tilas ba don ta so ba ta bud'e baki da k'yar tace"Ameen".

Haka Khaleel ya saka ta a gaba da surutu da ambata mata soyayya,ita mamakin sa ma take,daman haka ya k'ware a magana? Duk ya kanainayeta ta rasa yadda zata yi,tun ba ta amsa masa magana har ta soma amsawa kad'an kad'an,wannan yafi komai yi masa dad'i.….

Bai barta ba sai da yaji an fara kiran sallar azahar,sannan yace ta shiga gida tayi sallah,ta turo masa Aboki su ta fi masallaci,kasa ma mik'ewa tayi saboda yadda k'afafuwanta suka yi sanyi,sai da yace ko ya d'aga ta ne?sannan ta mik'e da hanzari,ya tuntsire da dariya yana bin ta da wani shu'umin kallo,yana fatan Allah ya kai damo ga harawa…

Da sassarfa ta fito daga d'akin,suka yi kacib'us da Ya Hamza shi kuma yana k'ok'arin shiga,kallon sa tayi fuskar sa da danshin ruwa alamun alwala ya d'aura,idanunsa sun yi ja sun koma ciki,a sanyaye take duban sa kamar ta rik'e shi take ji,wallahi tana son Ya Hamza,babu yadda zata yi ne kawai,shi kam d'auke kansa yayi kamar bai ganta ba.

Wata irin juyowa yayi yayi a slow jin ta rik'o hannunsa k'am,idanuwan ta sun ciko da hawaye ta ambaci sunan sa.

"Ya Hamza……

Khaleel ya d'aga labulen d'akin yana kallon su tsaye suna kallon juna,ga hannuwan su a sark'afe….


Comments
Share
Vote
Pls


*GARKUWA BIYU*


BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter 8 · 0% Book details