← Book details Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 2 OF 31

BABI NA ARBA'IN DA D'AYA DA NA ARBA'IN DA BIYU

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

***Wani irin mamaki ya cika Zuciyar Umma,yanzu daman abin da Hidaya take b'oye mata kenan?amma shine har ta iya fad'awa Hamza a matsayin sa na Namiji?Kawai sai Umma ta mik'e da hanzari ta nufi d'akin da ledar a hannun ta.

Tana shiga ta tarar da Hidayan a tsaye tana niyyar shiga toilet,Umma ta D'an harareta kad'an ta ambaci sunanta.

"Fatima….!

Hidaya ta amsa gaban ta na fad'uwa,duk lokacin da Umma ta kira ta da Fatima to tabbas tana cikin fushi ne ko b'acin rai,Umma ta ta zauna gefen gado tace.

" Zo nan…!

K'arasowa ta yi a hankali ta durk'usa a gaban Umman kanta a sunkuye,fuskar Umma a d'aure ta fara magana.

"Me yasa baki da cikakken hankali ne,yanzu ki rasa wa zaki fad'awa kina haila sai Hamza?Hamza fa namiji ne amma kina mantawa da hakan,ba kowace magana ya kamata ki tattauna da shi ba,ni menene amfani na da ba zaki gaya min damuwarki ba?a matsayin mahaifiyarki nake Hidaya,kuma ciwon y'a mace na y'a mace ne,wannan rayuwar ba komai kake sakin jiki ka fad'awa Namiji ba,ko da kuwa uwarku d'aya ubanku d'aya,saboda yadda zamani ya lalace,na san kyakkyawan tarbiyyar da na Baku daga ke har Hamza,amma akwai rud'in zamani,Wanda nake addu'ar Allah ya kare ku daga shi,Hidaya ki dawo cikin hayyacin ki!duk wani abin da ya shafe ki in dai na kunya ne to ki dai na fad'awa Hamza,ki sameni ki fad'a min,ko kuma ki fad'awa Hansa'u ko Sumayya,duk za su baki shawara ta gari,amma ke a ce baki da abokin shawara da fad'awa sirrinki sai Hamza,ina jin kina mantawa da cewar Hamza Namiji ne,kuma bai kamata ya san wasu Abubuwa da suka shafi sirrin ki ba ko…!?

Haka Umma tai ta yi wa Hidaya fad'a,ita kam kanta a k'asa idanuwanta sun cicciko da hawaye,tabbas babu wada take fad'awa damuwar ta sai Ya Hamza,to amma gaskiyar magana wannan rud'ewa ta yi,shiyasa bata fahimci yanayin da take ciki ba ma kwata kwata,shirun da ta yi yasa Umma ta sake k'are mata kallo,rigar jikinta kanta bai kamata Hamza ya ganta da ita ba,ko ba komai a kwai shaid'an ,ga kuma sharrin zuciya,duk da kullum ana addu'a.Hakan yasa Umma ta k'ara ce mata.

"Irin wad'annan kayan ma bai kamata kina saka su ba matuk'ar Hamza na gidannan,ba wai takura miki nake son yi ba,ina k'ok'arin sauke nauyin hak'k'in tarbiyyar ku da ke kaina ne,zuciya bata da k'ashi Hidaya,duk tarbiyyar mutum da kaucewa sharrinta wani zubin tana kai mutum ta baro,Dan haka ki tattara ire iren wad'annan kayan duk ki Adana su ki daina sakawa,duk lokacin da Allah ya sa na aurar da ke sai ki sanya su a d'akin mijin ki"

Sai lokacin Hidaya ta d'ago kanta cikin shagwab'a tana dafa cinyar Umma,ta shagwab'e fuska tace.

"Aure kuma Umma?wane irin Aure?ni babu wani aure da zan yi Umma, domin ba zan iya rabuwa da ku ba..!

Umma ta yi murmushi tana duban ta tace.

" Aure kam ya zama dole Hidaya,domin idan ba a aure da ke kanki ba a sameki ba,Dan haka ki shirya kin kusa aure kina kammala secondary school zan miki aure"

Hidaya ta zaro idanu,sosai ta cigaba da yi wa Umman shagwab'a jin maganar ta,to ita da wa za su yi Auren?ita da bata da saurayi ko farinjini bata da shi?haka nan bata hango yadda zata iya rayuwa ba tare da Umma da Ya Hamza ta ba,tana ji a ranta mutuwa kad'ai za ta iya rabata da wad'annan mutane a rayuwar ta.

Haka Umma tai ta tsokanar ta ita kuma Hidaya na shagwab'a,sai da Umma taga Hidaya ta fara hawaye sannan ta k'yaleta tana dariya,lallai abin na Hidaya azimun ne,tun ma kafin Auren ya zo har an fara daru da ita?to ina ga Auren kuma ya zo?duk da bata fatan rabuwa da Hidayan ita ma,akwai abin da take sak'awa a ranta Wanda take fatan ya tabbata,za ta fi kowa murna da farinciki.

Umma da kanta ta nunawa Hidaya yadda za ta yi amfani da (Always)d'in,sannan ta zaunar da ita tana karanta mata yadda zata tsare kanta da jikinta,da yadda zata kaucewa kula maza da yawan wasa da su,duk da ta san Hidayan ba kula maza take ba idan ba Hamza ba,ko su Faisal abokan Hamza sai dai kawai su gaisa,amma bata hira da su ko kula su,da zarar ma sun fara janta da magana ko wasa Hamza zai yi kicin kicin da fuska,shi bai yarda wani namiji ya kula Hidaya ba,ban da Khaleel babu Wanda Hamza yake bari yayi hira da Hidayan, Dan Khaleel har waya ya siyawa Hidaya,wadda kullum suke hira ko Hamza baya nan,Hamza bai tab'a damuwa da hakan ba,saboda ya yarda da Khaleel fiye da komai.

Sannan Umma tace mata ta lura da iya kwanakin farawar ta da gamawar ta,ta sake koya mata wankan tsarki duk da sun karanta a makaranta,sannan tace da zarar ta ji alamun zuwan sa kar ta dinga bari ana sani,saboda shi wannan abin b'oyeshi ake ba bayyana shi ba.

Hidaya taji dad'in bayanan Umman, ta kuma yi mata alk'awarin zata kiyaye da yardar Allah.

Tun daga wannan kuma sai aka shiga Y'ar kunya tsananin Hidaya da Hamza,da k'yar suke iya had'a idanu,Umma dai tana lura da su bata ce musu kanzil ba,daga baya kuma sai suka ware suka koma kamar da.

Hamza ya soma zuwa Aiki cikin nasara da Sa'a,Ranar da Hidaya ta ji muryar Ya Hamzan ta a redio yana karanto labarai cikin harshen turanci kamar ta suma don murna,ta dinga k'yalk'yala dariya tana tsallen murna,Umma dai dariya kawai take mata ganin murnar ta har ta yi yawa.

A lokacin ne kuma Khaleel ya siyawa Hamza mota dalleliya,duk yadda Umma ta so hanawa k'i yayi,wai Hamza ya wuce hawa mashin yanzu,tunda ya samu aiki tilas a siya masa mota ya dinga zuwa gun aiki da ita,haka nan yasa ma'aikata masu gini suka zo k'ofar gidan aka ja baranda aka katange aka saka get,wai domin Hamza ya samu wajen ajiye motar sa.

Su dai sukan rasa bakin magana ma akan hidimar Khaleel, Hidaya kam yawan ci ma kayan da take sakawa shine yake turo mata,wasu ma duk bata saka ba saboda k'anana ne kuma d'amammu,hakan yasa Umma duk ta d'ebe ta Adana mata wai sai ta yi Aure za ta saka"

Tun daga wannan lokacin kuma Hamza ya rik'e lokacin fara al'adar Hidaya,da zarar lokacin yayi zai siyo mata pad ya kai mata har d'akin Umma ya ajiye mata ba tare da magana ba,in ta gani sai ta d'auka,ko Umma ta d'auka ta bata.

Hidaya ce mai bud'ewa Hamza get da zarar ya dawo daga Aiki,duk yadda yaso hanata tak'i,da ta ji k'arar motar sa za ta yi sauri ta fito ta zuge masa get,sai ta fita ta shiga motar su shigo barandar tare,sannan ta fita ta rufe get d'in,kullum haka take yi,Hamza yana jinjina k'aunar da Hidaya ke masa,duk da yana ganin k'aunar da yake mata ta ninninka wadda take masa.


********************


Ranan litinin da safe Hidaya ta fito daga wanka,da sauri sauri take shiryawa domin tafiya makaranta don kar ta yi latti,gogaggun uniform d'in ta ta d'auko ta fara sanya wa a gurguje,Umma ta shigo d'akin da Kofi a hannun ta cike da kunun gyad'a da ya sha madara, a dai dai lokacin da Hidayan ta zame towel d'in jikinta tana k'ok'arin zura riga a jikin ta,idanuwan ta suka sauka a k'irjin Hidaya da suka cicciko sosai suka fara girma,daman tunda al'ada ta zo mata ta fuskanci wani irin girma da Hidayan take yi,musamman k'irjinta da bayan ta,ga kwankwason ta ya k'ara fad'i, jikinta kuma sai k'ara murjewa yake yi,hakan yasa Umma ta ji a ranta ya kamata ta siyawa Hidaya brezia ta dinga sanya wa,kar ta dinga ragaje ragaje a cikin riga tunda sun fara girma sosai.

Hidaya ta waiwayo jin motsin Umma bayan ta saka riga da wandon,ta d'au hijabin ta tana cewa.


"Yau dai na makara Umma,ban ma san lokacin da bacci ya d'aukeni ba bayan nayi sallar Asuba,sai farkawa nayi naga lokaci ya k'ure haka,ni da wuya ma na zauna nayi break fast,na sayi wani Abu a school kawai"

Umma ta mik'a mata kofin hannun ta tana zama bakin gado tace.

"Ungo nan maza zauna ki shanye,ba zaki tafi makaranta da yunwa ba,yau dai gabad'ayan mu makara muka yi,shi ma Hamza Ashe bai farka ba,ina ktcheen na jiyo motsin sa a d'akin sa."


Hidaya ta amshi kofin ta zauna ta fara kurb'a a hankali,ji take kamar ta tashi sama,bata cika son makara a makaranta ba,ta kusa shan rabin Kofi Hamza ya shigo d'akin,k'amshin turaren sa duk ya baibaye su,yayi matuk'ar kyau cikin shigar shadda Ruwan siminti,ya d'ora hular da ta dace da kayan,sosai yayi kyau kamar wata D'an Daren goma sha biyu…

Durk'usawa yayi yana gaida Umma,ta amsa fuska a sake,Hidaya ma ta gaishe shi,ya amsa yana dubanta sannan ya kalli agogo yace.

"Ke daman har yanzu baki wuce makaranta ba?

Ta dire kofin kunun gyad'a tana cewa.

" Ya Hamza wallahi makara nayi yau,ban san me yasa ma Sumayya bata biyo min ba,ko k'ila tayi gaba"

Ya gyad'a kai yana kallon kofin da ta ajiye da ragowar kunun a ciki.

"Menene wannan…!? Ya fad'a yana kallon kofin.

Tayi dariya da fad'in.
" Kunun gyad'a ne Ya Hamza"

Umma ta dubeshi tace.

"Ko za ka sha a zubo maka?na sanka baka fiye sonsa ba shiyasa,amma ga tea can na dafa maka"
dubi Hidaya da ke gyara zaman hijab d'in ta tana rataya jaka,yace.

"Mik'o min ragowar kunun naki na sha"

Ta D'an zaro idanu tace.

"Ya Hamza ragowata ne fa,shi zaka sha..!?

Yayi mata wani kallo sannan ya dubi Umma yace.

" Umma ji wannan yarinyar da wani zance fa,to yau na saba shan ragowar ki,dalla ni mik'o min kawai"

Ta yi dariya kawai ta mik'a masa,ta in da ta sa bakinta nan ya mayar da na sa bakin ya shanye kunun tas ya dire kofin,Hidaya na ta kallonsa tana murmushi, ya mik'e tsaye ya kalleta yace.

"Wuce muje na direki,daman na san ragin hanya kike so shiyasa kika k'i tafiya,ba wata makara da kika yi"

Hidaya da Umma suka yi dariya,suka yi wa Umma sallama tana ta yi musu addu'ar dawowa lafiya,sannan ta cewa Hidaya idan ta dawo ta shiga mak'ota gidan su Salma ta karb'i mukullin gida,ita za ta je Unguwar sarki gidan wata k'awarta ta dubata bata da lafiya.

Hidaya ta amsa da "To" Sannan suka wace ita da Hamza.

Har k'ofar makaranta ya kaita,sai da yaga shigarta tana ta d'aga masa Hannu sannan ya lumshe idanu duk jikin sa yayi wani la'asar,wani Abu na mintsinin sa a Zuciyar sa game da Hidaya,sai dai har lokacin ya gagara tabbatar da abin da yake ji d'in…gani yake tamkar shak'uwa da tausayi ne kawai ,ba abin da Zuciyar take sak'a masa ba….!


Comments
Share
Vote
Pls


*GARKUWA BIYU*


BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter 2 · 0% Book details