← Book details Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 28 OF 31

BABI NA CASA'IN DA UKU DA NA CASA'IN DA HUD'U

Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read

*Hassana D'an Larabawa Fan's,ina godiya gareku da sharhin ku akan wannan littafi tare da addu'o'i na fatan alkairi da nake samu daga gareku,Allah ya bar zumunci ya saka da alkairi,ku cigaba da hakan ni kuma in sha Allah zan cigaba da faranta muku,Na gode masoyana* 👏😅🥰


BARKA DA JUMA'A 😍


***Kafin ma Daddy ya k'arasa maganar da yake tuni Khaleel yayi wuf ya mik'e cikin tsananin tashin hankali da gigita ya rik'o kafad'un Daddyn sa,idanuwansa na zub da hawaye masu zafi da k'una,kallon Daddyn yake cikin fitar hayyaci numfashin sa na sama sama tamkar zai d'auke,k'ok'arin magana yake amma ya gaza hakan,tuni idanuwansa suka soma shirin k'ak'k'afewa,sai gashi yana niyyar zubewa k'asa,babu wanda ya fara isa gareshi sai HAMZA,ya taro shi da hanzari yana zubewa a jikinsa,a tare suka kai k'asa Hamza na rungume da Khaleel d'in yana ambatar sunan sa da k'arfi yana tallafo fuskar sa domin ya kalleshi.
"Khaleel...." abin da yake ta ambata kenan,yana k'ok'arin Khaleel d'in ya bud'e idanuwan sa da suke lumshewa za su rufe,"Open your eyes Khaleel,don Allah ka bud'e idanuwanka ka kalleni nan kaji.....Hamza ke magana...Hamza abokin ka..!" a wani slow Khaleel ya fara bud'e idanuwan ya zuba su a fuskar Hamza ya k'ura masa idanu,sai kuma ya sake lumshe idanuwan wasu hawaye suka kwararo masa tamkar ruwa,Hamza ne ya saka hannuwansa yana tare hawayen Khaleel,tare da girgiza masa kai,cikin taushin murya ya sake ce masa.

"Ka daina kuka,kayi hak'uri da K'addarar ka"

Runtse idanuwa Khaleel yayi,da k'yar ya iya d'aga hannu ya rik'o hannun Hamza ya runtse cikin nasa hannun,sai kuma ya fara magana a hankali wadda bata fita sosai,amma shi Hamzan yana jin abin da yake cewa.

"K'addara ko...? Tabbas haka ne,na had'u da k'addarori masu zafi a rayuwa ta,ciki kuwa har da fushin da Abokina Hamza yake da ni,wannan ma k'addara ne ko?"

Girgiza kai Hamza yayi sannan ya ce.
"Hamza baya fushi da Khaleel, wata ajiyar zuciya Khaleel ya saki mai k'arfi tare da kwararowar hawaye,sannan ya k'ok'arta ya d'ago da taimakon Hamza ya mik'e zaune,duk hankalin mutanen parlour'n a tashe yake,wasu ma har sun mimmik'e tsaye ganin fad'uwar da Khaleel yayi,musamman da Hidaya ta zabura tana kuka ta isa gaban Khaleel d'in da Hamza ta tsuguna,idanuwan ta akan Khaleel d'in,had'a ido kawai Khaleel yayi da Hidaya,sai ya fashe da kuka ya sa tafukan hannayen sa ya rufe fuskar sa,cikin kwararar hawaye da rauni yace wa Hidaya.

"Don Allah kiyi min afuwa...kiyi hak'uri...wallahi kunyarki nake ji ko idanuwa bana son had'awa da ke...hak'ika da ni da mahaifina mun cutar da ku...mun gigita duniyar ku....mahaifina ya kashe miki mahaifin ki...wayyo Allah na ...! Sai ya fad'a kafad'ar Khaleel yana wani irin kuka na tashin hankali yana dafe k'irjinsa da ke barazanar tarwatsewa.

Kowa na cikin palour'n kukan tausayin Khaleel yake yi,Hidaya kam ji take kamar ta janyo shi jikinta ta rungume shi,daren su na jiya na dawowa k'wak'walwarta da tarin soyayya da k'auna da ya gwada mata,kuka take sosai yayin da ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta tana jin ina ma mutuwa ta zo ta d'auke ta da wannan bak'ar rana da take gani a idanuwan ta.

Khaleel dai kuka yake mara misali,yayin da Hamza ke hawaye yana bubbuga bayansa alamar rarrashi,can Khaleel ya d'ago cikin hawaye ya dubi Hamza ya ce.

"Kaine fitilar da ke haskaka min gabana Aboki,duk wani duhu da zan fad'a k'ok'arin ka shine kaga ka fito da ni cikin haske,sannan kana yawan fad'a min girman iyaye da zaburarwa akan yi musu biyayya,wani lokaci kuma da ya sud'e kayi min nasiha akan GASKIYA,har ma kace min tana da matuk'ar amfani a duniya da lahira,domin ana shigar da masu yin gaskiya gidan aljanna,har kace min an tambayi Annabi ( S A W) menene aikin y'an aljanna?sai Annabi ya ce "GASKIYA" ,kuma kace min GASKIYA tana kub'utar da duk wani mai yin ta daga halaka,haka nan GASKIYA tana sa nagartar zuciya,tana gadarwa mai yin ta nutsuwa da kwanciyar rai,tana kub'utar da mai yinta daga afkawa cikin fitintunun rayuwa,ta kan zamewa mai yinta tushen aikata ayyukan alkairi,tana korewa mai yinta siffantuwa da munafurci,tana datar da mai yinta wajen hasashe da hangen nesa,tana k'arfafa hujjar mai rik'o da ita da kuma yinta,mai yinta yana samun yabo da kirari da kyakkyawan ambato daga mutane,duk wad'annan abubuwa mutum ba zai tab'a samunsu ba sai yayi rik'o da GASKIYA,Aboki ina so ka fito da ni Haske,shin Shin Mahaifina zan zab'a a wannan gab'ar ko kuma bayan GASKIYA zan bi?"

Hamza ya lumshe idanuwan sa,maganganun Khaleel sun tab'a ruhinsa,ya bud'e baki zai magana kawai suka ji muryar Daddy cikin kuka yana cewa.

"D'ana Khaleel kar ka bi bayana,ka bi bayan GASKIYA,domin ita za ta tseratar da kai,nima zan bi bayan GASKIYA,kuma ita za ta yi min jagora wajen sanar da ku dukkan wani abu da kuke son sani daga gareni,kuma na rantse da ubangijina zan fad'i GASKIYA,don haka kowa ya bud'e kunnuwan sa ya saurari wannan labari.


*******************


Na kasance mutum mai son zuciya da son abin duniya,wannan hali na wa munyi tarayya akansa ni da Abokina Alhaji Maude,domin shima haka yake,ko in ce har ya fini,duk abin da za mu yi bamu fiya saka Allah da GASKIYA a lamarin mu ,wannan shine ya janyo duk wasu ayyuka da za mu gabatar babu imani a cikin su.

Alhaji Taufik' yayi mana komai a rayuwa! duk wani abu da muke tak'ama da shi ta silar sa muka same shi,bawan Allahn nan ya kan hana kansa wani abun domin ya bud'a mana mu samu,amma maimakon mu tsayar da GASKIYA da AMANA a lamarinmu sai muka k'i,muka dinga bin son zuciya muna aikata b'arna kan duk wata kwangila da yake nemo mana,yayi mana uzuri babu adadi,kullum nasiha yake mana a k'ok'arin sa na mu zama mutanen kirki,amma muka shafawa idanuwan mu toka muka k'i saurarensa da Gasgata shi,ko ni na so nabi tsarinsa sai Maude ya dankwafeni,akan gara muyi abinda muke so,ko domin mu zo mufi Alhaji Taufik' d'in kud'i,tunda yayi mana zarra nesa ba kusa ba.

Babu wani mutum da ya tsaye mana a rai irin SULAIMAN,domin mun gane cewar da shawarwarinsa Taufik' yake amfani,shiyasa a lokacin har Taufik' d'in yake neman d'aga mana jan kati domin fatattakarmu cikin sha'aninsa,akan hakan muka nemi Sulaiman domin mu janyo ra'ayinsa ya goya mana baya,sai ya nuna mana cewar shifa ba zai bi bayan K'ARYA ba,bayan GASKIYA zai bi,wannan ta sa muka k'ara k'ullatarsa,musamman ni da na fito masa da tsanata a fili,sab'anin Maude da ya b'oye muguntarsa a zuciyar sa.

A wancan zamanin abubuwa sun cigaba da tafiya ne ba yadda muke so ba,tunda kuwa babu dad'ewa da Taufik' ya zare hannuwansa daga lamuran mu sai gashi mun fara fuskantar matsaloli,komai ya fara rincab'e mana,abubuwa suka fara yi mana zafi,babu ta in da muke samun kwangiloli Taufik' ya toshe mana duk wata k'ofa da zamu dinga samu,hujjarsa kuwa ita ce,bama yin aiki da GASKIYA,kuma duk abinda za mu samu cikin aikin da za mu yi kusan haramun muke ci,to shi yana karemu daga cin haram ne saboda haram ba zai cecemu a lahira ba,gara mu rasa a duniya da muyi asarar lahirar mu,wanda mu duk bamu fuskanci abinda yake nufi ba,idan ma mun fuskanta to mun take Gaskiya,gani muke kawai Hassada da bak'inciki yake mana,baya son cigabanmu ne.

Watarana Alhaji Maude ya kirani akan shifa ya fara gajiya da ganin Taufik' a doron k'asa,ya kamata mu san yadda zamu salwantar da rayuwarsa mu shafe babinsa,nan da nan na bashi goyon baya,sai dai na cewa Maude kar a kashe Taufik',ni duk zaluncina ba zan iya kashe mutum ba,a dai san yadda za a yi kawai a b'atar da shi a doron k'asa,amma ban da kisa,nan Maude yayi wani murmushi,yace min na bar komai a hannusa shi zaiyi maganin abun.

Kwana biyu da hakan na samu labarin Oga Taufik' ya kwanta rashin lafiya,wadda ya zama baya ji baya gani balle tafiya,ina jin wannan na san aikin Maude ne,ashe kuwa hakane,dan kirana yayi yana shek'a dariya yana ce min "Mudan mutuminka fa ya zama dukunu,kuma saura kad'an na k'are masa gudu" nima na shek'e da dariya sannan nace masa"Hakan ma yayi Maude,amma dai ba kashe shi za a yi ba ko?dan bana son kisa ya shigo lamarin mu,hakkin rai ba k'aramin abu bane"sai Maude ya ce min"Kar ka samu damuwa ba kashe shi za a yi ba,kurciya me dogon zango zan sa ayi masa,nan da kwanaki k'alilan za a manta da tarihin wani Taufik' gabad'aya" Muka kwashe da dariya muka tafa muna jin dad'i.

Kwanaki k'alilan da hakan kawai naji zancen an sace Taufik' ,ma'ana an neme shi an rasa,ina shirin kiran Maude a waya sai ga wayarsa ta shigo,da hanzari na d'aga ina tambayar sa abinda ke faruwa,sai ya shek'e da dariya yana fad'in"Mudassir na gama cika aiki,ka shirya yanzu zan zo na d'auke ka mu tafi gidan Taufik' yin Jaje,domin kurciya me dogon zango ta tabbata a gareshi" Wani irin dad'i ya mamayeni,na dinga shek'a dariyar murna,nan Maude yake ce min idan mukaje gidan mu dinga nunawa kamar Sulaiman ne ya b'atar da Taufik',domin shi ya kamata mu lik'awa sharrin tunda duk shine sanadin da yasa Taufik' yayi fushi damu,tunda da shawarar Sulaiman yake amfani.

Aikuwa hakan ce ta tabbata kamar yadda Zainab ta fad'a,tabbas mun fad'awa Sulaiman bak'ak'en maganganu a ranar,mun bi shi da sharruka kala kala akan muna zarginsa da sace Taufik',muka yi muka gama yana zaune yana kuka baice mana uffan ba,sai da muka juya muka fito muna dariya da hirar yadda aka yiwa Taufik' kurciya me dogon zango,ashe bamu sani ba Sulaiman na bayanmu kuma duk yaji abin da muka tattauna,wannan ya saka mu cikin tsananin tashin hankali da tunanin wace mafita garemu?domin komai zai iya faruwa idan muka yi sake.

Muna tafe a mota sai zufa nake yi,Alhaji Maude ne yake tuk'a motar amma shi sai na lura hankalinsa ma a kwance yake,cikin wani irin yanayi na fara fad'a masa cewar ni dai nayi danasanin abin da muka yi,yanzu gashi tun ba a je ko'ina ba asirinmu yana neman tonuwa,nan Maude yayi wani murmushi mai kama da na mugunta,sannan ya ce min" Haba Mudassir kar ka bani kunya mana,wannan d'an abin ne zai tashi hankalinka?kawai dan wannan k'aramin alhakin yaji sirrin mu?ka zuba idanu ka gani shima a yau d'innan zan sa a gama min da shi,domin ba zai kai labari ba"

A tsorace na dubr shi ina fad'in "Ba dai kashe shi zaka yi ba ko?nifa na fara tsorata Maude,gara mu ajiye makamanmu wallahi,idan ma asiri kasa aka yi wa Taufik' aka neme shi aka rasa to gara kaje ka sa a warware shi kawai ya dawo,gara mu hak'ura kawai saboda zuciyata ta fara rawa akan aikata wad'annan munanan ayyuka,iya rashin Gaskiyar mu da hassadarmu ta ishemu ba sai mun had'a da salwantar da rai ba Maude,mu fa musulmai ne,kar muje mu rasa imaninmu gabad'aya"

Nan da nan naga fuskar Maude ta sauya,hankalinsa ya fara tashi saboda ina neman in mana sakiyar da babu ruwa a wannan lamari,take ya sauya fuska ya fara karantomin dad'in baki,wai idan har na bijire a wannan gab'ar to k'arshen mu yazo,domin Sulaiman zai iya fallasa mu ga hukuma,kuma idan akayi bincike tilas a gano mune muka shirya komai,a likacin ne za mu kwashi kashinmu a hannu,dan haka na maida hankali kawai muyi abinda ya kamata,in yaso daga baya sai mu tubarwa Allah kawai,haka Maude ya isheni da dad'in baki har na aminta da maganarsa,yace min in bar komai a hannunsa,shi dai yayi min alk'awarin babu kisa alamarin,tunda bana so,amma zai bi duk hanyar da zai bi domin ganin komai ya wakana cikin sauk'i,a haka muka rabu,yaje ya saukeni a gidana shi kuma ya wuce domin tsara yadda zai tunkari lamarin.

Allah shine shaidata,kuma nayi alk'arin fad'in GASKIYA, duk da na san cewar ba lallaine ku aminta da abinda na fad'a ba ko wanda zan fad'a yanzu,amma ni dai na san GASKIYA zan fad'a,ko da za ta kasance min kalami na k'arshe da zanyi a rayuwata.

Daddy ya Numfasa cikin zubar da k'walla mai zafi,ya kalli Mummy da tunda ya fara magana idanuwanta na kansa cikin wani kallo na muguwar tsana,ba Mummy kad'ai ba kowa ma Daddyn yake kallo,shi kam Daddy cigaba yayi da kallon Mummy kafin ya sake bud'e baki ya cigaba da cewa.

"Zainab....Na rantse da Allah ba ni nasa aka kashe Mijinki ba...ba ni na kashe Sulaiman ba...hasalima ni ban san Sulaiman baya doron duniya ba...ban san an kashe Sulaiman ba duk tsawon wannan lokacin...
Na san duk wannan sharrin Alhaji Maude ne ya k'ullashi,ya aikata wannan abun da sunana domin ki tsaneni Zainab,domin duniya tayi Allah wadai dani,domin ba tun yau ba na fara fuskantar Maude ba don Allah yake sona ba,abotar da muke yi ba don ALLAH da GASKIYA da AMANA ya d'auketa ba,sai don shima ya cimma wani k'uduri na sa a kaina.Wallahi Zainab a washegarin da kika ce an kashe Sulaiman da kaina na samu Maude akan ya ake ciki?sai yace min in kwantar da hankalina angama komai,daga Sulaiman har iyalensaya sa an musu kurciya me dogon zango,ban tab'a fahimtar wannan yaren na sa na KURCIYA ME DOGON ZANGO ba sai yau,ashe abinda yake nufi ya kashe Sulaiman,kuma na tabbatar shima Taufik' ya sa an kashe shi ne,tunda har wa yau ban k'ara jin labarinsa ba,duk kuma lokacin da na cewa Maudw ina son ganin Taufik' domin na nemi afuwarsa sai dai yayi dariya ya share zancen baya bani amsar komai akan hakan,ashe ni ban sani ba Maude ya kashe Taufik' da Sulaiman,kuma yayi amfani da sunana wajen fad'in ni na aikata hakan,innalillahi wa inna ilaihir raji'un...Tabbas Maude ya ci amanata...sannan ya ci amanar abotar mu....!

Daddy yana zuwa nan ya fashe da wani irin kuka,fad'i yake "Wallahi Zainab ba ni na kashe miki Sulaiman ba...ban san me nayi wa Maude ba da ya nana min wannan sharri me girma haka...me yasa yayi min haka bayan ni na rik'eshi Aboki...ashe shi ba da zuciya d'aya yake zaune da ni ba...yanzu wannan shine sakayyar abotar da muka yi ni da shi kenan?"

Kafin kowa yayi magana HAMZA ne ya fara mik'ewa tsaye,idanuwan sa na zubar da hawaye ya dubi Daddy,sannan ya d'aga d'an yatsansa sama yayi magana da babbar murya,kowa ya zubawa Hamza idanu suna jin abinda yake cewa.

"Na rantse da ubangijina,Abota ta k'warai da tasirinta ga mutum tana tabbatuwa a gareshi muddin an ginata akan GASKIYA NE,ayoyi da yawa a cikin alk'ur'ani sun bayyana mana wajabcin rik'ar abokan k'warai da yin watsi da miyagun abokai,a ko yaushe mutum mai hankali ya kan gujewa miyagun abokai kamar yadda ake gujewa zaki saboda ya san babu alkairi a tare da shi,kuma duk wanda ke zama da miyagun abokai to ya had'u da tab'ewa,bisa ga misali,Daddy kalli fad'in Allah mad'aukakin sarki inda yake cewa.

"و يوم يعض الظالم على يديه يقول يليتنى اتخذت مع الرسول سبيلا. يويلتى ليتنى لم أتخذ فلانا خليلا. لقد أضلنى عن الذکر بعد إذ جاءنى وکان الشيطن للإنسن خذولا."
Fassarar ayar(Ranar da azzalumi zai rik'a cizon yatsansa yana cewa"kaicona ! ina ma na bi hanya tare da manzo! kaicona ! ina ma da ban rik'i wane aboki ba?hak'ik'a ya b'atar da ni daga bin Alk'ur'ani bayan ya zo min" kuma shaid'an ya kasance mai tab'ar da mutane ne).

Sannan Manzon Allah (S A W) ya tsawatar mana akan zama da miyagun abokai.Kamar hadisin da aka karb'o daga Abu musa Allah ya yarda da shi ya ce: Hak'ik'a Manzon Allah (S A W) ya ce: "Kwatankwacin zama da abokin k'warai da miyagun aboki kamar zama da mai sayar da turare ne da zama da mak'eri,shi dai mai sayar da turare ko dai ya sammaka,ko ka siya,ko kuma kaji k'amshi.shi kuwa mak'eri ko dai ya k'ona maka sutura,ko kuma ka ji k'auri" Bukhari da muslim ne suka rawaito shi.
Duk abubuwan da suka faru da kai Daddy babban tushensu shine rashin samun Aboki na gari,tarayya da mugun aboki ya janyo maka fad'awa cikin wannan yanayi,abota ta k'warai daga mutanen kirki take,masu hankali da nagarta wad'anda za su dinga taimaka maka akan GASKIYA kuma suna nuna maka ita,kai ne ka zalunci kanka Daddy,domin ubangiji ba mai zaluntar bayinsa ba ne.


"من عمل صلحا فلنفسه.و من أساء فعليھا .و ما ربك بظلم للعبيد"


(Duk wanda yayi aiki nagari ,to kansa ya yi wa,wanda kuma ya munana kansa yayi wa,ubangijinka ba mai zaluntar bayi ba ne).

Gabad'aya mutanen da ke zaune sun had'a baki ne wajen fad'in "ALLAHU AKBAR" tare da jinjinawa Hamza wajen fad'in GASKIYA.Sai Hamza ya cigaba da magana yana kallon kowa.

"Ni na gasgata Daddy...kuma kuma ina son ku gasgata dukkan abin da ya fad'a..na hangi tarin GASKIYA cikin idanuwan sa da kalamansa..magana ta k'arshe shine,za mu sa ayi bincike ta b'angaren Shari'a akan Alhaji Maude,kuma zai shiga hannun hukuma nan ba da jimawa ba,domin abi kadin duk wani abu da ya aikata,ni nayi Alk'awarin zan d'auki nauyin komai a hannuna"

Da hanzari Khaleel ya mik'e ya iso gaban Hamza ya kama hannuwansa ya rik'e,girgiza kansa yayi sannan yayi magana ya ce.

"Tun lokaci mai tsawo kake amsa Sunan GARKUWAR HIDAYA ABOKI,don Allah nima ka bani wannan damar ko sau d'aya,ni ma ina so na amsa sunan GARKUWAR HIDAYA ko sau d'aya ne"

Sai Hidaya ta taso ta tsaya a gabansu, cikin kuka take duban Ya Hamza da Uncle Khaleel,tayi magana cike da rauni.

"Uncle Khaleel kana so ka zama GARKUWATA kamar yadda Ya Hamza ya zama ko?"

Da sauri ya amsa mata da "Tabbas ina so" yana kwararar da hawaye.

Sai ta sunkuyar da kanta k'asa ta ce.


"To ina so duk inda Alhaji Maude yake ka sa a kamo shi,da duk wani mai hannu cikin kisan Mahaifina da Alhaji Taufik',a gurfanar da su gaban shari'ah,sannan ka tsaya min a matsayinka na LAUYA har mu samu nasara a yanke musu hukuncin da ya dace da su,muddin ka aikata haka to tabbas ka zama GARKUWAR HIDAYA"

Kafin ma Khaleel yayi magana sai suka ji muryar Daddy cikin tabbatarwa yana ce wa.

"Ni kuma zan baka goyon baya D'ana Khaleel,domin cikawa Hidaya burinta,duk da na sani har da ni cikin wad'anda hukunci zai hau kansu,amma na zab'i GASKIYA kuma ita zan bi,k'ila ita ce aikin da zan yi wanda zai zame min kaffarar laifukana na baya...!

Sai Khaleel ya matsa jikin mahaifinsa ya rungumeshi,take suka fashe da kuka mai cin rai,yayin da ragowar mutanen da ke zaune kowa ke kuka hawaye na zuba.


Comments
Share
Vote
Pls


*GARKUWA BIYU*


BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️
Chapter 28 · 0% Book details