BABI NA SITTIN DA UKU DA NA SITTIN DA HUD'U
Garkuwa Biyu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
***Hidaya kam tsoro ne ya kamata Dan har firgita ta D'an yi tana zaro idanu,shi kam Hamza sai ya mik'e da k'warin gwiwa ya nufi k'ofar ya bud'e a hankali,Umma ta shigo d'akin tana duban sa da idanuwan ta masu cike da barci,Sunkuyar da kan sa yayi a k'asa Zuciyar sa na harbawa,ta waiwaya ta kalli Hidaya da ke durk'ushe k'asa hannayen ta rik'e da takarda,ga hawaye na zuba a idanuwan ta, taka wa tayi a hankali ta nufi gefen gadon Hamzan ta zauna,shi ma tura k'ofar d'akin yayi sannan ya ta ko ya biyo ta a hankali ya tsuguna a gaban ta kamar yadda Hidayan ke tsugune, Umma ta cigaba da dubansu cikin rauni tana tausayawa halin da suka samu kansu a ciki,a hankali Umma ta bud'e baki ta fara magana cikin wata irin murya mai sanyi.
"Hamza me yake faruwa ne na same ku kai da K'anwar ta ka cikin Daren nan a muhalli d'aya?
Cikin dukan Zuciya ya d'ago ya kalli Umma,Sannan ya ce.
" Na kasa bacci ne Umma,sai kawai naji zuciyata na ingizani kan na fita daga d'akin nan ko zan ji sauk'i,fitar da nayi ita ce silar cin karo da ita a tsakar gida cikin talatainin dare tana kuka,shine na kasa jurewa na janyo ta d'akin nan domin na rarrasheta na kwantar mata da hankali,Sannan na bata wani sak'o mai tsananin Girma a gare ta "
"Wane Sak'o ne…!? Umma ta tambaya idanuwan ta a kan sa.
Ya amsa yana kallon Hidaya da kanta ke sunkuye hawayen ta na d'isa a k'asa.
" Sak'on Mahaifiya zuwa ga y'arta Umma,A yau ne na Isar da Sak'on Mahaifiyar Hidaya zuwa ga Hidayan,gata nan a hannun ta na bata"
Hidaya ta d'ago a hanzarce tana kallon sa fuskarta cike da tambayoyi kala kala,domin bata fahimci abin da yake nufi ba,Sai ya jijjiga mata kai fuskarsa d'auke da murmushi yace mata.
"Ranar da Mahaifiyar ki ta dank'amin amanarki ta bani wannan muhimmin sak'on domin na isar da shi gareki da zarar kin Girma kin kai munzali irin wannan ,shiyasa ni……
Hamza ya dakata da magana ganin yadda Hidaya ta mik'e da Hanzari ta cillar da takardar da ke hannunta a k'asa,sannan ta fashe da kuka ta na goge hannayen na ta a rigar da ke jikin ta,cikin kuka take fad'in.
" Ba na buk'atar duk wani Abu da ya fito daga hannun wannan matar,ni ba mahaifiyata ba ce!ban santa ba!bana sonta bana k'aunarta!bana k'aunar duk wani Abu da ya danganceta! Ya Hamza kalli nan !Umma ita ce Mahaifiyata! ita ce wadda na Sani !ita nake so ita nake k'auna ! Amma ba wannan matar da ta gudu ta barni ba !bata San ci na ba!bata San sha na ba!bata San suttura ta ba !bata San karatuna ba balle batun lafiya ta! Ya Hamza kar ka sake kusanta ni da wannan matar da bata yi min komai a rayuwa ba…..
Kafin Umma tayi wani yunk'uri tuni Hamza ya aiwatar da abin da ya niyyata cikin matuk'ar fushi da rawar jiki,wani irin gigitaccen mari ya sakarwa Hidaya Wanda ya sakata kifewa a cinyar Umma cikin d'aukewar numfashi na wucin gadi,Fuskar sa d'auke da mummunan fushi da tashin hankali mara misali ya fara nuna ta da yatsan sa hannuwansa da jikinsa na rawa,Hidaya kam k'ank'ame Umma tayi ta na wani irin nishi saboda yadda Marin ya gigita k'wak'walwar kanta,abin da bata tab'a ji bane a rayuwar ta,yanzu da ta ji shi shiyasa ta gigice ta rasa in da za ta sa kuncinta domin ta ji dad'i.
Umma ma a gigice take da jin k'ak'k'arfan Marin da ya sauka a fuskar Hidaya Wanda bata tab'a tsammanin Hamzan zai iya ba,bata tab'a tsammanin shi da yake matsayin GARKUWAR Hidayan zai iya kai Hannu jikinta da sunan duka ba,d'agowa tayi da hanzari ta na shirin magana,kafin ta kai ga yin magana Hamza ya riga ta farawa a fusace,gabad'aya ya manta da cewar lokacin tsakiyar dare ne.
"Kin bani matuk'ar mamaki!yanzu na san cewa tsawon shekarun da nayi ina d'oraki kan tarbiyya basu amfaneki da komai ba!Hidaya wace irin Halittar zuciya ce da ke haka?wane irin taurin kai ne da ke?Mahaifiyar da ta tsuguna ta haifeki ita kike fad'awa wannan kalaman?har kike ambatar cewa bata tab'a yi miki komai a rayuwa ba ! Kin manta ita ce wadda ta d'auki tsawon cikin ki wata Tara a jikinta?ta sha fama da laulayin ki da rashin lafiya kala kala,tayi nak'uda mai zafi yayin haihuwarki! Duk da wahalar da kika bata amma ta haifeki tana mai tsananin sonki da k'aunarki!daga lokacin da ta haifeki take kula da ke da lamarin ki ko k'uda bata son ya tab'aki,ki hanata barci!ki hana ta cin abinci!idan kika yi kuka ita ma sai tayi kuka!idan baki da lafiya ta shiga damuwa!ki mata kashi ki mata fitsari!bata dukan ki bata hantarar ki a dukkanin wani laifi da za ki yi mata,sai dai tayi miki addu'a! Ta kan hak'ura da farincikin ta domin ta sama miki naki farincikin!ta kan gwammace ta shiga damuwa da K'unci akan ke ki shiga! Wannan ita ake kira uwa !Mahaifiya!dukannin wad'annan abubuwan da tayi miki baki gani ba?har kike fad'ar munanan kalamai a kanta? Idan baki yi hanzarin tuba ba za ki tab'e,domin Allah zai yi fushi da ke akan tsauraran kalaman da kike fad'i akan mahaifiyar da ta tsuguna ta haifeki,Girman iyaye ya wuce gaban wasa!Allah ya umarci a girmamasu !kada ayi tir da su!a fad'a musu kalamai masu dad'i.Allah ta'ala yana cewa a cikin littafinsa mai girma.
"فلا تقل لھما أف ولا تنھرھما وقل لھما قولا کریما"
Ma'ana(kada kace musu tir,kada ka yi musu tsawa,ka fad'a musu magana mai girma"mai dad'i").
Matuk'ar kina fad'in kalamai masu zafi akan Mahaifiyar ki zan raba hanya da ke Hidaya!Zan gujeki kwatankwacin yadda b'era ke gudu idan yaga mage!zan nisanta kai na da ke da duk wani Abu…….
Ya kasa k'arasa maganar sa saboda wani hawaye mai zafi da ya tsinke masa,Hidaya ta kuma fashewa da kuka tana rik'e Umma GAM cikin fitar hayyaci,tausayin ta ya kama Umma ganin yadda kumatun ta ya kumbura yatsun Hamzan rad'a rad'a a fuskarta, amma ta san laifin Hidayan ne,duk maganganun da Hamzan ya fad'a gaskiya ne,rik'o Hidayan tayi sosai tana rufe mata baki ganin gunjin kukan da take yi a tsakar Daren nan,Hidaya ta girgiza kai tana cire hannun Umma daga bakin ta,sannan ta fara magana cikin shesshek'a da hawaye.
"Umma ki tayani baiwa Ya Hamza hak'uri, yau nayi masa babban laifin da har duka ya shiga tsakani na da shi!abin da bai tab'a yi min ba a rayuwata!Don Allah ki bashi hak'uri ba zan kuma ba!ba zan sake fad'in munanan kalamai akan Mummyna ba!
Umma tayi murmushi idanunta cikin na Hidaya ta ce.
" Ban da shirme irin na ki Hidaya wanene ya fad'a miki ana fad'awa iyaye mugwayen kalamai?wallahi tallahi na tabbatar muhimmin Abu ne ya saka mahaifiyar ki ta rabu da ke a wancan lokacin!babu Wanda ya kai Uwa son D'an ta!kinga kuwa ba zata tab'a gudunki domin son ranta ba,Mahaifiyar ki tana k'aunarki!kuma komai Daren dad'ewa zata nemeki idan har tana da rai a filin duniya"
Hidaya ta gazgata kalaman Umma,kuma tayi nadamar furucin da ta yi,a hankali ta ja jiki ta matsa kusa da Hamza da ya kau da kai daga gareta,cikin muryar kuka take bashi hak'uri tana ta fad'in.
"Ka yi hak'uri Ya Hamza na tuba!
Sai da ya jima kafin ya dubeta idanuwan sa jajir!sannan yayi magana a hankali.
" Shikenan ya wuce amma ki kiyaye gaba!
Sosai taji dad'in yafe matan da yayi,ta rarrafa ta d'auko envelope d'in da ta cillar ta rungume a k'irjinta,sai taji wata k'aunar Mummyn ta da bata tab'a ji ba ta ratsa k'irjinta,lumshe idanuwa tayi tare da gangarowar hawaye mai zafi kan fuskarta.
Hamza da Umma suka k'ura mata idanuwa cikin tunanuka barkatai da ya cika zuciyar su…..!
***************
Daddy ya kwana cikin fargaba da dukan zuciya har zuwa wayewar gari da ya rasa tudun dafawa,kuma a safiyar ALHAJI Maude ya ishe shi da waya akan dakatar da d'aurin Auren,ya dinga yi masa Famfo yana tunzira shi da maganganu marasa dad'i akan Hidaya,hankalin Daddy ya sake tashi sosai har yaji kome zai faru ba zai bari Auren Khaleel da Hidaya ya kasance ba.,Saboda baya son sunan sa ya b'aci ko kad'an,sai dai kuma rayuwar D'an Sa fa?akwai buk'atar ya zurfafa tunani akan hakan……
Yayi matuk'ar namijin k'ok'ari wajen b'oye damuwar sa har zuwa lokacin da aka hallara wajen d'aurin Auren, idanuwan sa akan Khaleel yana hango wani mad'aukakin farinciki a fuskar sa da bai tab'a cin karo da shi ba,sai yaji K'unci ya mamaye ruhinsa,a lokacin da ake shirin d'aura Auren Alhaji Maude ya bayyana a wajen a gigice,Mutane dank'am kamar tsaki kowa ka gani cikin walwala,haka ya dinga tsallake mutane har ya isa inda Daddy ke zaune,zuwan sa yayi dai dai da Shafa fatihar D'aurin Auren…..!
Shin da wa aka d'aura…..?Da Khaleel d'in ne ko kuwa…?
Comments
share
vote
Pls
*GARKUWA BIYU*
BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️