Sashe 9
Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daddy ya san kai makaho ne kuma kurma ne sannan baka da seti ya saka ka tuka ni a mota?
Sai lokacin Mukhy ya dan juyo a gicciye a dube ta, da idanun sa masu kalar silver, duban da sai da yasa hantar Amani da hanjin cikin ta karkadawa domin ta yi zaton kwada mata mari zai yi, don ko da bai yi magana ba ta san kallo ne na zazzafan gargadi ya yi mata, wato ta san irin maganar da zata dinga furta masa.
He is not that stupid as she thinks.
Suka isa Goruba Estate wato inda boutique din Amani yake.
Nan ma jira take ya fito ya bude mata kofar mota ta fito amma ya bude yayi ficewar sa ya bar ta a zaune.
Masu kula da wajen sai gaishe shi suke yi don su a tunanin su shine mamallakin shagon, sabida duk wani shige da fice shi ya dinga yin sa har komai na boutique din ya kammala, tankareren shagon yana daga jerin farko-farko na shagunan da ke cikin plaza din.
Mai gadi ya kawo masa mukullan hannun sa ya bude ya shiga ciki.
Da Amani ta tabbatar ba zai bude mata kofa ba sai tayi kyacci ta bude ta fito ta bi bayan sa.
Ta tara shi fal a ranta har da karin gishiri da maggi na abubuwan wulakanci da zata gayawa Daddy ya yi mata, tana shiga shagon ita kanta ta girgiza da irin dukiyar da mahaifin nata ya narkar mata, takalma ne da jaka na mata na zamani na yayi da sittiru
yan waje na yara da manya, shi kansa wanda ya zabo kayan ta sara masa wajen iya investing kayayyakin da zasu dauki hankalin kwastoma, a rashin sanin ta ba kowa bane dan mutanen Diffa ne amanar Alhaji Usman Faskari.
Duk kushen ta da high taste din ta ta kasa kushe tsarin da Mukhy ya yi wa shagon nan.
Ko da suka gama dubawa abubuwa kadan ta iya cewa a kara.
Shi din ma rubutawa ta yi aka takarda ba da fatar baki ta gaya masa ba.
Yayi gabas ita kuma ta yi yamma a cikin shagon don kada ma ta hada hanya da shi.
Ta rubuta iya abubuwan da take bukata a kara sannan ta fice daga shagon ba tare da ta ce masa ta gama ba, shi kuma yana can zaune bisa wata kujerar roba a cikin shagon yana jira ta gama gatsine-gatsinen ta tana kallon komai tamkar ta ga kashi, nan kuwa can a kasan ran ta yabawa take yi komai ya yi mata, ta kuma jinjinawa fasahar wanda ya tsara shagon nan.
Wasu kayan ma da aka zuba duk gayun ta bata san da irin su ba farkon shigowar su Katsina kenan.
Da ta gama abinda zata yi mota ta koma ta shige ta zauna ta hau danna horn ji kake biiiiii
..biiiii
..kamar mai kiran kare.
Yana jin ta ya yi kamar bai san tana yi ba, ya gama danne dannen sa a wayar sa ya mike ya haura zuwa upstairs na shagon yayi zaman sa.
Ya rantse a kasan ran sa sai ya rama shanya shin data yi a gida cikin mota kafin ta fito.
In bai manta ba ai jiran awa biyu kwakkwara yayi cikin mota yana jiran ta, to itama sai ta yi shi yanzu.
Bakin ciki da bacin rai a wurin Amani abun ba
a cewa komai, data gaji da zama sai ta kira Daddy a waya yana dagawa ta hau kuka da balbalin masifa tamkar mai magana da kanin ta.
Daddy kuwa cewa yake me ya faru ne Tafisu?
Daga ina kike magana?
Tace.
Daddy daga cikin motar da wannan Dirty Human Being din ya shanya ni, tukun nama Daddy ka taba zaunar da shi ka gaya masa ko ni wace ce a wurin ka?
Shi ba kurma ba shi ba makaho ba amma wallahi sun fi shi ji da gani, mutum dunkumkum sai kace dankali ba um ba um um sai bakar zuciya zaka hada hanyata da shi?
Ko bude min mota fa bai yi ba, yanzu haka zaman sama da awanni biyu nake cikin mota har baya na ya fara ciwo
sai ta koma kukan shagwaba wanda Daddyn kadai take yi wa irin sa.
Tace.
Daddy in baka zo ka dauke ni da kan ka ba ba zai san matsayi na a wurin ka ba, idan baka kore shi ba dauka zai yi ni
yar aikin gidan ka ce, babu wanda ya taba yi min wulakancin da mutumin nan naka yayi min
Amani ta tsinke da fada kamar tsinkakken carbi duk a kan kunnen Mukhy da bata ma san yaushe ya bude motar ya shigo ya zauna ba, bayan ya duba agogo ya tabbata awa biyu ta cika, kuma ko da take ma Daddy wannan balbalin kara fusata shi abun yayi because he respects Alhaji so much, ba zai iya jurar jin ana masa wannan rainin ba.
Don haka ya fizgi motar a gujen gaske saida Amani ta zunkuda ta koma ta bugu da kujerar data ke zaune.
Amani ta zuga salati tana cewa
Daddy ka cece ni zai kashe ni
Daddy ya ce
bani Mukhtar din
tace
Daddy Allah ya sawwake ya taba min waya ya shafa mata bakin hali irin nasa
abin nata sai ya koma baiwa Alhaji dariya, ya ce
alright, bari in kira shi
ya katse kiran nasu ya soma kiran Mukhtar.
Yana ganin kiran Alhaji amma kuma yana tuki don haka saida kiran ya katse.
Ya gangara gefen titi ya kashe motar sannan cikin nutsuwa ya bi bayan kiran Alhajin.
A yadda ya tausasa murya ya kuma russunar da kai duk da Alhajin baya ganin sa sai kayi tsammanin da mahaifin sa ya ke magana, ya ce
Alhaji muna hanyar dawowa kana son wani abu ne?
Alhaji cike da damuwa ya ce
No Mukhy, karar ka aka kawo min kala-kala, ka bi ta a hankali ka ji?
Ka san wani lokacin haka take abu na
yan fari
.
Mukhtar ya saci kallon ta sai kumburi take kamar zata fashe ya ce
Alhaji ai babu damuwa ina iyawa da ita, musamman da wani lokacin tana abu zayyal majnunah (kamar mahaukaciya), abinda bazan lamunta daga gare ta ba shine rashin kunyar da take maka, ka gaya mata ta dinga maka magana with respect irin yadda
ya suke yi wa iyaye, saboda kai ne gaba da ita ba ita ba.
Idan ta cigaba da yi maka magana irin haka bazan kara daukan ta a mota ba
Alhaji ya ji dadi, ya ce
Mukhtar kada ka damu da shirmen Tafisu ka ji?
Ka san wanda baida mahaifiya a kusa sai ana masa uzuri
Mukhtar yace
ni ba zan yi ma ta uzuri da wannan ba, babu uzuri a cikin biyayyar iyaye, in dai a kan daga sautin ta sama da naka ne zan iya bubbuge bakin ta Alhaji
Alhaji yayi murmushi yace to shari
ar taku ta fi karfin waya, ku dawo gida sai mu yi ta a zaune.
Kuna ina yanzu?
Yace
muna hanya ko rabin isowa gida bamu yi ba.
Ni gaskiya Alhaji a gate zan sauke ta, ni kadai zan je na dauko Hajiya, daga can ina da inda za ni
Alhaji ya ji wani iri ya ce
Mukhtar ban san ka da rashin kirki ba kada ka fara akan kanwar ka
ya ce
Alhaji sai ta daina yi maka fada zan yi kanwa da ita, in ba haka ba kowa ya yi rayuwar sa cikin gidan nan ba ruwan Yaya da kanwar, bani da zuciyar da zata iya daukan ana raina min kai
Daga haka ya kashe wayar sa Alhaji na fadin ka dai shigo da ita kada ka sauke ta a gate don Allah ba don halin ta ba
Duk abinda suke fada a kunnen Amani, mamaki da haushi ya hana ta ko kwakkwaran motsi, anya wannan mutumin bai taki komai ba?
Yaya kana zaman yaron gida kake ma uban gidan ka Gadara irin haka shi kuma yana biye maka sai kace uban da ya haife ka?
Amani ta saci kallon sa sai suka hada ido, ya kashe ta da harara, yana kokarin cire farin gilashin idon sa don ya sha round din da zai kai su unguwar su.
Wani irin kyau ya yi a idanun ta mutum tamkar shi yayi kan sa, kai kace wani balaraben Madinah ne idan yana magana, tsafta da wanka sun kama jikin sa radam.
Sai ta tuno alfarmar da take so yayi mata duk da ya bakanta mata rai yadda bata zato amma wannan ce dama ta karshe da zata iya rokon sa don ba haduwa suke yi ba, sai dai ta hange shi a harabar gidan daga balcony din ta yana shiga mota zai fita ko ya shigo gidan.
Ko ya zo daukan Alhaji su fita.
Ta rasa ta ina zata fara don kwata kwata babu fuska daga Mukhy, yama kara daure fuska tamau da suka hada ido don kada ta kawo masa wargi, ya lura da kallon kurillar da ta ke masa wanda ya wuce shari
ah.
Shikuma baya son ko kalma guda ta hada shi da Amani don kada raini ya shiga takanin su irin wanda takewa kowa da ke karkashin ta.
Ya Allah ya zata yi da wannan mutum mara sakin fuska?
Sai kawai tayi kundumbala tace,
Man, ina son fidda kudi ne daga corporate account dina?
Mukhtar bai san cewa magana take da shi ba, ya dauka ma a wayar ta take magana da wani daban don haka ko juyowa bai yi ba.
Amani ta daga murya da dan amo tace
na tabbata kai ba kurma bane, but you are acting kamar baka ji!
Sai yanzu ya san da shi ta ke, ya kuwa kara daure fuska yaci gaba da tukin sa.
Amani sai ta fara hawaye don abun yayi mata ciwo mai yawa, ba
a saba yi mata irin haka ba, kowa na gidan girmama ta yake yi yana nan-nan da ita yana rawar jiki idan ta bada umarni, balle wanda ke matsayin yaron Baban ta ya yi mata irin wann funfurus din.