Sashe 13
Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya ta ci karfin ta in ta tuno kamannin Alhaji Sadi, har ya fi Daddyn ta muni da tsufa, da kyar ta tsahirta dariyar ta ce
wato Daddy kawai kace ka sayarwa da abokin ka
yar ka Amani bisa yarjejeniyar siyasa, to wallahi ko shugaban kasa zai tsaya maka ka samu bazan aure shi ba.
Ai ba mijin aure na rasa a duniya ba, da sani na nake korar su, don lokacin aure na bai yi ba.
Duk duniya ban ga mijin da zan iya so ba Daddy, mai yiwuwa ma ba
a haife shi ba, saboda ba kowa zan iya aure ba sai wanda zuciya ta take matukar so.
Alhaji ya ce
Amani kada ki yi min rashin kunya, tsakani na da Alhaji Sadi amana ce
. abota ce ta kwarai, yafi karfin ya nemi alfarmar auren ki in hana shi
Amani da yake kunyar ta ragagga ce sai cewa tayi
Daddy ka rage son duniya, na rantse da Allah ba don abota ka amshi wannan maganar ba sai don son Mulki, ka manta cewa (power is transient), ammma farin cikin
yar ka guda daya (has to be eternal), ban san me kake nema kuma a duniya ba, da zaka mayar da ni hajar siyasar ka
Ta soma kukan ta na halitta na shagwaba kamar marainiyar da aka fadawa mutuwar iyayen ta, na yau har da sheshshekar kukan gaske.
Kukan da ya fi komai dagawa Alhaji hankali.
Cikin kukan ta ce
wallahi Daddy bana so, bazan aura ba, ta yaya recently na gaya maka na samu admission ina so ka yi min izni in wuce Masters dina zaka kawo wannan maganar?
Alhaji ya soma fusata yace
to in ke kika haifi kan ki sai ki tafi Masters din mu gani, magana na gama, na baiwa Alhaji Sadi auren ki, don kin ga ina sakar miki da yawa shi yasa kika raina ni, karatu kin gama shi daga kwalin digiri ba kari, dama ana ta cewa na barki babu aure
.
Amani ta mike tana cewa
to Daddy sai ka zaba ko ni ko abokin ka, idan aka takura min kan maganar nan na rantse zan sha poison in mutu ka huta, da dai in auri wannan mummunan tsohon
Gaban Alhaji ne yayi mummunar faduwa, exactly irin kalaman da mahaifiyar ta Jal
an ta furtawa nata mahaifin a gaban sa, ranar da ya bashi auren ta.
Kuma tabbas ta sha poison din bayan haihuwar Amani, bashi da tabbacin tana raye ko ta mutu, don tun ranar da ya kai ta asibiti ya damka wa mahaifin ta takardar sakin ta, bayan ya dauke jaririyar
yar sa, bai kara waiwayar ta ba, a dalilin ta dade tana kunsa masa bakin ciki mai yawa saboda kawai ita kyakkyawa ce shi ba kyakkyawa ba.
Allah wadaran masu aure don kyau
, Alhaji ya fada a fili cikin tuno dararen da suka shude tsakanin sa da Jal'an.
Allah yasa kada Amani ta yo halin mahaifiyar ta tarihi ya maimaita kansa tsakanin ta da Alhaji Sadi Talle, don shi aure da Alhaji Sadi ya riga ya gama zartar da hukuncin yin sa ba zai fasa ba.
Amani ta wuce zuwa sama ba tare da ta san halin tunanin data jefa mahaifin ta a ciki ba.
Ya dade a zaune a wajen yana tunanin mafita ko ta inda zai bullo mata ta yarda da auren Alhaji Sadi, ba abinda yake hangowa kansa sai gashi a kan kujerar gwamna, ya tuna Mukhy ma yace zai taya shi lallashin ta, da wannan tunanin ya shiga bayan gida toilet na dakin sa domin ya yi wanka ya kwanta, yana sanya kafa cikin kwamin wankan ya zame ya fadi a ciki, wata irin muguwar faduwa da ta yi sanadin kai Alhaji Usman asibiti cikin daren, Allah ne ya kawo Haj.
Rabi dakin taji karar da ya saki, ta fado bandakin tana salati.
Maigadi da mai ban ruwan shukoki ta kira suka kinkimi Alhaji suka sa a mota, Malam Tajuddeen ya tuka motar suka yi asibiti da shi.
Sai da suka isa asibitin Malam Tajuddeen ya kira Mukhtar.
A gigice Mukhtar ya zo asibitin, shi yasa hannu ya biya komai likitoci suka soma baiwa Alhaji taimakon gaggawa.
Zuwa safe babban likitan da ke duba Alhajin ya tabbatar ma Mukhtar Alhaji ya samu stroke wato rabin jikin sa ya daina aiki.
Kasancewar dama yana da hawan jini da suga masu tsanani.
Mukhtar ya saka fuskar sa cikin tafukan sa ya na ambaton
innalillahi wainna ilaihi raji
.
Tabbas dan Adam ba a bakin komai yake ba.
Jiya jiyan nan suna tare da Alhaji lafiyar Allah yana kasafta yadda zasu ci duniya da tsinke da kudin talakawa idan ya zama gwamna yau a ce rabin jikin sa ya mutu?
Amani tana gida bata san abinda ke faruwa ba, tun dare take waya da Hamidah tana kuka tana gaya mata Daddy ya daina son ta, zai aurar da ita auren dole ga tsoho, kuma sa
an sa saboda siyasa.
Tace
Hamida na tabbata ba zugar kowa bane wannan aikin annamimi Mukhtar ne, don ni Daddy bai taba yi min zancen aure ba, na tabbata shi ya zuga shi tunda yanzu baya jin maganar kowa sai tasa, kuma na tsole masa ido a gidan yana so a kawar da ni ya ji dadin cuta ma uba na
.
Ta fyace hanci ta ce
Hamdy na shiga damuwa don ban ga alamar Daddy da wasa yake maganar nan ba, kamar auren da yake son yi min din is based on political aspiration din sa.
Hamidah yarinya mai hankali tace "wato Bestie ba zaki daina tsanar bawan Allan nan ba babu gaira babu dalili?
Zato zunubi ne, how sure are you shi ya zuga Daddy?
Ke da kan ki kin ce is based on his political aspirations sai ki cire Mukhtar a ciki tunda shi ba dan siyasa bane.
Ba lallai ya zama Daddy bai da ra'ayi sai nasa ba, kamar kina exaggerating alaqar tasu.
Sabida kin damu da shi, kuma ba kya son sa".
Amani ta saki tsaki tace "na damu da shi a gidan wa?
Ai ni kawai so nake ya bar gidan mu" Hamida tace "ki ji da matsalar ki ta auren tsoho ki kyale bawan Allan nan ya sarara" "shawara zaki bani ko zagi na za ki yi Balewa?" Hamidah na dariya tace "duk wanda kika zaba shi zamu yi" ta ce "to shawara ta gaskiya nake so ki bani" "shawara ta itace ki yi wa mahaifin ki biyayya whatsoever hujjar sa na aurar da ke ga abokin sa, wanda yayiwa iyayensa biyayya baya taba tabewa.
A karshe ina so ni da ke duka muyi istikhara mu nemi dacewa da zabin Ubangiji ba abinda zuciyar mu tafi karkata ba".
"Menene istikhara!" Amani ta tambayi Hamidah.
"Sallah ce ta nafila da Annabi SAW ya koyar ta neman zabin Allah kan kowanne al'amari da sulusin dare" Hamidah ta gaya mata yadda zata yi.
Ta kuma daure ta yi din.
Ita da kan ta tayi mamaki ganin cewa zuwa washegari data tashi sai taji ta wasai babu damuwa a dalilin istikharar data yi.
Har jira take Alhaji Talle ya zo yayi mata bayanin dalilin sa na kutsowa rayuwar ta.
Da abinda yake nufi da Baban ta, na cewa wani suyi yarjejeniya sai kace an gaya masa ita hajar sayarwa ce.
Mai aikin ta ce ta kwankwasa mata kofa.
Tana budewa a fusace tace "lafiya da sassafe haka kike damuna da bugun kofa?"
Rakiya ta karya wuya ta langabe cikin lallashi ta ce "kiyi hakuri, Haj.
Ce tace in gaya miki ki fito ku tafi asibiti Alhaji na can babu lafiya".
Gaban Amani yayi mummunan faduwa, abinda ya zo ran ta shine irin rabuwar da suka yi ita da Daddy din daren jiya, kada dai shi ya saka a ran sa har ya kwantar da shi rashin lafiya?
In haka ne kuwa zata yi masa biyayya iyakar iyawar ta ba Alhaji Sadi ba, ko kuturu ya kawo ya aura mata zata yi biyayya da dai a ce wani abu ya faru da Daddyn ta a kan ta.
Sabida gigicewa a haka ta fito da kayan barci a jikin ta, sai Rakiya ce ta biyo ta da mayafi bakin mota.
A yadda ta ga Mukhtar zaune a reception din asibitin ya hada kai da gwiwa, yayi jajawur abun ki da farin mutum ainun, hatta idanun sa sun yi jawur ya tabbatar mata condition din na Alhaji ba mai dadin ji bane.
Ita ta sani ko Uban sa sai haka, a irin halin da ta gan shi a ciki.
Suna hada ido ya sunkuyar da kai, ta karasa da sauri tana tambayar sa me ya samu mahaifin ta?
Mukhtar ba baki sai ido ya bi ta da shi.
Ta koma ga Haj Rabi tana tambaya.
Babu wata damuwa a tare da ita tace "sun ce ya samu stroke ne, barin jikin sa ya shanye, Amma zasu dinga yi masa gashin kashi har ya samu lafiya".
Daidai lokacin da aka gangaro Alhajin a kan gadon marassa lafiya aka bashi daki na musamman.
Amani ta rasa inda zata tsoma ran ta, sai kuka take yi a dakin.
Haushin ta ya ishi Mukhtar yace "ko ki yi shiru ki yi masa addu'a, ko ki koma gida" ta galla masa harara da jajayen idanun ta tace "Uban ka ko nawa?" Ya ce "to zage ni" ta yi tsaki ta ce "in aka zage ka din me za'a yi?" Kai tsaye yace "banida lokacin ki yanzu, amma ranar da kika kuskura kika zagenin, zaki ga me za'a yin".
Haj Rabi ta yi salati tace "Amma ku kuwa an yi sakarkaru, ta yaya mutun yana kwance rai kwakwai mutu kwakwai kuna neman dambe da juna a kan sa?
Ku kuma irin naku hankalin kenan maimakon ku dukufa yi masa addu'a?"
Mukhtar ya juya ya fita daga dakin ya bar su.
Amani ta nufi Alhajin da sauri ta kura masa ido yana barci kamar ba abinda ya faru da shi.
Hawaye fal idonta ta soma magana.
"Daddy in dai a kan auren da kake son yi min ne ka saka kan ka a wannan yanayin na roke ka ka tashi mu tafi gida, na amince ka aura min duk wanda ka ga dama, don Allah Daddy".