← Book details Amani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 25

Sashe 2

Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Faskari, yana da shekaru hamsin da biyar amma in ka gan shi arba
in zaka bashi sabida jin dadi da kula da lafiyar sa, bashi da wani buri da yasa a gaba yanzu irin diyar sa Amani da rayuwar ta, babban burin sa kullum shi ne farin cikin ta, jin dadin ta da walwalar ta.

Hon.

Usman ya wadata Amani fiye da kima, tun a kananan shekarun ta Amani ta san tafi sauran tsararrakin ta gatan aljihu dana Uba, ya kuma fifita ta ya sangartata wanda hakan ya shafi tarbiyya da mu
amalar ta da mutane, saboda ya jika ta da komai na jin dadi da bukatun rayuwa ba tare da ta yi maraicin mahaifiyar ta ba, wadda Amani bata taba gani ba ko a hoto, alhalin tana raye ba wai ta mutu ba.

Iyayen ta sun rabu tun tana tsumman haihuwa, a cewar sa saboda munin sa ne Jal
an ta ki zama da shi, wanda kullum take cewa yana firgita ta, a zahiri shi yake tunanin hakan, amma dalilai da yawa ne suka hana Jal
an iya zama da shi, ciki har da halayen sa na kankamo da rowa, dama kuma auren dole iyayen ta suka yi mata da shi a dalilin ya saye mahaifin ta da dukiya.

Tunda ta koma kasar su (Sierra Leone) bata kara dawowa Najeriya ba, wai da sunan ganin
yar da ta Haifa ta tafi ta bari bata ko shayar ba, shi kuma bai kara bin bayan ta ba, bai ma san tana raye kota rasu ba.

Sai ya maida hankali a kan rainon kyakkyawar diyar data bar masa wato
AMANI
, ya kuma maida kafatanin soyayyar da yake yi wa Jal
an a kan ta, bai yarda ta nemi wani abu a rayuwar ta ta rasa ba, komai darajar sa, bai yarda ta yi kukan babu ba, ba ya ko tunanin ya dace ya aurar da ita haka, kullum kallon
yar kankanuwar yarinya yake mata, yadda take shekaru ashirin a baya sanda yake goya ta da kan sa a bayan sa.

Shi kan sa bai san iya son da ya kewa
yar sa Amani ba, ko iyakar adadin abinda ya mallaka, kuma komai nasa da sunan tilon
yar sa AMANI yake rubuta hakkin mallakar sa.

Wato ita yake sanyawa hakkin mallaka a rubuce gaban lauyoyin sa.

Wannan ne kuma babban abinda ya assasa bakar kiyayya tsakanin Amani da matar sa Hajiya Rabi, saboda ita bata taba haihuwa da shi ba.

Kafin Hajiya Rabi ya auri mata kusan tara yana sakin su, duk ba a kan komai ba sai a kan rikon Amani, don sun kasa yi mata irin rikon da yake so na gaskiya da amana, kankanin laifi zasu yi, ya basu takardar saki in dai a kan
yar sa Amani ne, da ya sakawa suna TAFISU.

Yake mata kirari da
Kin fi sauran mata
Haka masu aiki ma basu tsira ba, kullum cikin canzawa Amani su ake, saboda a cewar sa basa kula masa da ita yadda yake so.

Wannan yasa Amani ta tashi yarinya sangartatta, hamshakiya, mai girman kai, mai yawan alfahari, mai raini ga mutane, kuma mai izzah da dagawa da son a bata girma koda kuwa mutum ya haife ta.

Ga rashin tauna magana da kowa take Magana, har shi mahaifin nata kuwa wani lokacin bata masa magana da girmamawa, ka yi mata magana ta mayar maka da harara.

Yadda duk magana ta zo bakin ta haka take furzar da ita ga kowa cikin raini da gatsali, bazata yi la
akari da yawan shekarun da ka bata ba zata iya marin ka ko ta tofa maka miyau a fuska muddin ka shiga gonar ta.

Sabida girman kai irin na Amani ko kawaye cikin tsararrakin ta bata da su domin ta raina ajawalin kowa, da an fara kawancen za
a babe, saboda ba kowa ke jure halin ta na raini da dagawa ba.

Kawar ta daya ce da suka yi karatun sakandire tare a (Ulul Albaab Science Secondary School Katsina) wato Hamida Balewa wadda itama Baban ta tsohon dan siyasa ne, da ya rike har mukamin gwamna a jihar Baucin Yakubu.

Hamida ta iya da ita da halin ta, don ta fi ta hankali da hakuri kuma tana son Amani kamar
yar uwar ta, shiyasa suka rayu tsayin lokacin nan basu rabu ba, har zuwa yanzu suna tare a shekarar nan da suka kammala karatun Jami
a tare a jami
ar Tafawa Balewa.

Har zuwa lokacin da mahaifin ta ya auri Haj.

Rabi, ita da kan ta Amani ta roke shi ya rufe aure-aure daga kan Haj.

Rabi saboda mutuncin siyasar sa, da kuma kasancewar tana son ya zama akwai mace tare da su, duk da dai in ya saki baya jimawa yake kara aurowa, kafin ya auri Haj.

Rabi ya dade babu mata, don ta karshe ta kusa kashe Amani da duka don haushi sabida ta tofa mata miyau a fuska, ita kuma Haj.

Rabi ganin inda raunin Alh.

Usman yake wato (son a taya shi kula da Amani da taya shi soyayyar tilon diyar tasa), sai ta saka kaimi a kai, ta kama Amanin ta rungume a farkon zuwan ta, har fiye da kima, da ta gan ta zata hau rawar jiki da hidima da ita a gaban Alhajin, irin yadda Hon.

Din yake so matar duk da ya aura ta yi wa Amani, Haj.

Rabi ta shiga nuna mata soyayya har fiye da shi.

Hakan yasa ta shiga ran Alhaji.

Amma ba haka abin yake a zuciyar ta ba.

Wannan ne yasa tayi dan nisan zango a gidan Hon.

Usman, domin a kalla zuwa yanzu tayi shekaru kusan hudu a gidan su Amani, sauran matan da ya aura a baya babu wadda ta rufa shekaru biyu.

Amma a zahiri Haj.

Rabi ba wanda ta tsana data bude ido ta gani a duniya irin Amanin.

Babban tashin hankalin ta ranar data fahimci cewa komai na dukiyar Alhajin sunan Amani yake bearing, mai nufin ya gama mallaka mata komai nasa, duk wadda zata zo sai dai ta jira dan tumunin takaba (idan ma ta yi nasarar dadewa a gidan kenan).

Musamman hankalin ta ya kara tashi da likita ya tabbatar mata shekarun ta sun wuce na daukar ciki wato ta isa
menopause
ba matsalar haihuwa ce da ita ba yadda take zato.

Haj.

Rabi tana da yara biyu mace da namiji da tsohon mijin ta na baya.

Ta aurar da macen, namijin kuma yana jami
a yana hannun mahaifin sa a garin su Minna jihar Neja.
**** ***** *****
Amani ta karasa saukowa daga matattakalar benen, ta karaso ta zauna a jikin mahaifin nata yadda ta saba duk girman ta, kai ka ce yarinyar goye ce a yadda take masa magana cikin shagwaba.

Daddy, saboda Allah ba zaka daina kira na da sunan tsofaffi ba ko, bana son wannan Tafisun da kake kira na da shi, kullum sai na gaya maka ka bari bana so, amma ba dama ka ga na yi ado sai ka sake kira na da Tafisu-Tafisu
.

Amani ta fada cikin zumburo baki, tana kallon takardun da ya kammala sakawa hannu, sakamakon ganin sunanta baro-baro a kan takardar shaidar mallakar boutique na kayan sanyawa na mata mai suna
AMANI COLLECTION
In bata manta ba tun shekarar data gabata Daddy yake shirye-shiryen bude mata boutique din nan, wato sai yanzu Allah yasa aka kammala kenan.

Alhaji ya ce
ba sunan da ya dace da ke irin
Tafisu
, saboda ai kin fi sun ne da gaske, ina nufin kin fi tsararrakin ki gata, kin fi sauran
ya gatan Uba, kin fi su komai tunda kina da Uba iri na, wanda ke tsaye a kan duk abinda kike so, da son tsaya miki kan duk mai son shiga hancin ki
.

Ya fada babu wasa a maganar sa, ita ta san Daddy yana nufin abinda yake fadi, a shirye yake ya tsaya mata a kan kowa da komai.

Shi yasa itama bata hada kaunar sa da ta kowa a rayuwar ta.

Hon.

Usman Ya mika mata takardun yana fadin
amshi ki duba Tafisu.

Boutique din ki da na dade da yi miki alkawarin bude miki a nan Katsina ya kammala, yana nan a jerin shagunan Goruba Road, gobe sai kuje da
MUKHY
ki gani, idan da abinda bai yi ba, ko ba
a kawo ba, ko za
a canza cikin kayan da kika bada list aka yi odar su, sai ki fada masa, in ya so sai a kara yin sabuwar order, don yana da wata tafiyar dama nan da watanni biyu zuwa Mexico, ina saka ran zai shigo min da wasu samfurin marbles, sai ya karo miki abunda babu din.

In yaso sai ku je tare ki gani, kina dubawa kina fada masa yana rubuta min komai a tsanake
Ai kuwa nan da nan fuskar Amani ta yi kicin-kicin, ta zama kamar hadarin da ya nausa ya yi gabas, ta yi mugun bata rai kamar bata taba far
a a rayuwar ta ba, ta kirne kyakkyawar fuskar nan tata ta wani irin yamutse ta, fuskar ta a wannan lokacin sai ta koma masa exactly ta Jal
an, wato mahaifiyar ta, idan kiyayyar ta ta motsa a kan sa; wata kwayar mace guda daya da ya taba so a rayuwar sa, kuma daga kan ta bai kara son kowacce mace ba, yanzun da Amani tayi hakan sai ya ga ta rikide ta koma masa Jal
an har sai da gaban sa ya fadi sosai.

Yanayin ta a irin wannan lokacin yafi kama da na
yan nan da ba
a kwaba, ba
a hantara, wadanda saidai iyayen su su bi abinda suke so ko basa so, fadi take cikin shagwaba, hassala da zumburo baki.

Allah ya tsare ni hada hanya da shi, Allah ya raba gatari da saran kuka, shin Daddy sau nawa zan gaya maka ka manta ne?

Magana ta gaskiya ka daina hada sabga ta da ta wannan mai cunkusashshiyar fuskar da halin sumumu-kasau din.

Ina dalili mutum kullum yana faman kirnewa mutane fuska kamar mala
ikan daukan rai, alhalin da bazar su yake rawa?
Chapter 2 · 0% Book details