← Book details Amani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 25

Sashe 16

Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji ya so a ce yana da baki, ya yi sulhun alkhairi tsakanin Mukhtar da Amani, baya son wannan rashin jituwar tasu wanda zaman su waje daya tsayin sati biyu bai saka sun shaku da juna ko sun daina kyarar juna ba, su daina hamayyar nan mara dalili da shi take sakawa a damuwa da tantamar cikar burin sa a kan su.

Shi dai kullum kunnen sa sa
in sar su ke tada shi daga barci, idanuwan sa basa ganin komai cikin idanun su sai tsanar juna, da rashin jin dadin zama da juna da hantara da kyarar juna.

Bai taba jin sun yi maganar arziki a tsakanin su ba tun zuwan su asibitin, ko sentence daya balle a je ga batun gaida juna.

Basa amsa sallamar junan su sai a cikin cikin su.

B
abu mai ragawa dan uwan sa.

Gara shi Mukhy yana rage uzzura mata a dalilin kaifin idon Alhaji.

Data fito daga toilet ficewa ta yi ta bar musu dakin ta koma reception din asibitin ta zauna a kujera nesa da jama
a ta kira Hamida Balewa.

Hamida ta ce
mutuniyas ina kika shiga ne? kwana biyu ban ji complain din dan Alhaji ba
Da 'yar damuwa a muryar tace tana asibiti tare da Daddy a France,
Daddy na ya samu stroke Hamdy ki yi masa addu
a na san ke mai addu
a ce mai yawan sallah ce da tsayuwar dare
Hamida ta shiga juyayi, a karshe ta jajantawa aminiyar ta, ta ce
ke da Haj.

Rabi kuke jinyar kenan?

Wani mikakken tsaki ya fito kai tsaye daga bakin Amani, tace cikin dan daga murya
kema kin san ko da waye, ko baki tambaye ni ba, ni da waye kuwa banda bare ka fi dan gida, yana nan ya hana ni sakat, ya hana ni samun ladan uba na, masifar yau daban ta gobe daban, ke sai ki rantse da Allah yana da gadon Daddy ko tare Alhaji ya haife mu, tare kuma yake so mu rayu dole, ya shiga komai na gidan mu yayi kane-kane ya fi ni iko da uba na yanzu
sai ta kama matsar kwallah, Hamida tana so ta yi dariya sabida wannan sakalci na Amani, amma ta san Amani bata cikin mood din da take bukatar a yi mata dariya, don tsakanin ta da Allah take sharing mata damuwar ta, don bata da inda zata je ta fada ta ji sanyi, wannan Mukhy!

Ya addabi aminiyar ta, ita kuma haka nan yake burge ta, bata ganin laifin sa ko kankani, da kullum Amanin ke nanatawa, wanda duk ciki in ka saurareta zaka fahimci ba komai ke damun ta ba sai kishin son da mahaifin ta ke ma Mukhtar din.

Hamida ta nisa tace
kin san Allah Amani, idan har na isa in baki shawara ki dauka to ki koma girmama Mukhtar, ki kaunace shi matsayin dan uwan dake taimakawa Daddyn ki, ki bashi gurbin Yayan da baki da shi, ku zamawa Alhaji Yaya da kanwar sa.

I'm sure duk da ban sani ba Alhaji haka yake so ya gan ku, musamman a yanzu da bashi da lafiya ku biyu ne a kans a kuke jinyar sa.

Idan ya bar miki jinyar bazaki iya ke kadai ba dole sai namiji dan uwan sa idan ana maganan stroke.

Kuma kin ga wannan fadan da kuke ta yi a kan idon Alhaji yana saka shi a damuwa musamman cikin yanayin da yake a yanzu, shi fa Daddy in na fahimta saboda Allah yake son Mukhtar din nan.

Hayagagar ki bata isa tasa ya kore shi ba, da zai kore shi da tuntuni ya kora don gudun bacin ran ki.

To fadan da yafi karfin ka hausawa suka ce ka maida shi wasa, sai ka zauna lafiya.

My friend I want you to stay cool and healthy, kada Mukhy yasa jinin ki ya hau, zuciyar ki ta buga a banza ya yi wa Alhaji da kan sa asara
.

Ta karasa cikin dariya ta kuma yi maza ta kashe wayar ta.

Amani na kururuwar sai tagaya mata me take nufi da hawan jinin ta ta ko bugawar zuciyar ta zata zamo asara ga Mukhtar.

Meye manufar ta?

Hamida nata dariya ita kadai ta tura mata text.

Ga abinda ta rubuta mata.
kan ki ake ji kullum a kan sa, kin hana kan ki zaman lafiya saboda shi, watch your actions over him, you care too much for him, listen to your heart and understand the actual feelings.
-Yours Hamdy.

Amani ta kusa zagin Hamida, ta kira ta back yafi sau biyar Hamida ta ki dauka, kamar ta yi hauka ita kadai wai Hamida ta zageta, zagin da ba
a taba yi mata irin sa ba, ta rasa wanda zata ce ta saurari zuciyar ta a kan sa sai Mukhtar?

Me zata saurara din banda bugun zuciyar ta dake karuwa kullum a kan bacin ran da yake sanya ta kullum?

Hamida daga inda take sai murmushi take yi rike da wayar hannun ta, ta dubi fuskar wayar kamar Amani take kallo tana mata murmushin karfafa guiwa, haka kawai ta samu kan ta tana ma aminiyar ta sha
awar auren Mukhy din nan, duk da kasancewar sa a karkashin mahaifin ta, ta shiga yi ma Amani addu
ar samun daidaiton ra
ayi da fahimtar juna tsakanin ta da wanda take ganin ya shige gabanta.

A ganin Hamida ba wanda zai iya da ita da halayen ta duk duniya sai wannan Mukhtar din, da tun yanzu yake juya Amani wanda hakan ke nuna zai iya jarumtakar zama da Amani da dukkan halayen ta, ta san zama da Amani sai jarumin mutum, duk kawayen su na makaranta babu wadda Amani bata yi fada da ita ba itama don ta zame mata kamar 'yar uwa ne ko sun yi fada ita da kanta Amanin zata zo ta nemo ta su shirya.

A ganin Hamida babu mai iya auren Amani ya juya ta sai jarumin namiji saboda izzar ta.

Ta kuma yabawa Mukhtar wajen jure rayuwa kusa da Amani alhali kullum tana kyarar sa da gori kala-kala.

To amma Alhaji ya riga ya karbi maganar abokin sa ta kuma ce mata ta yi masa biyayya a kan maganar Alhaji Sadi, yanzu kam ta fi mata sha
awar auren Mukhtar yaro dan uwan ta mai halin manya.

Zata dukufa taya Amani addu
ar samun zabi mafi alkhairi a matsayin ta na aminiya ta kwarai.

Miji wanda zai taimaka ya saita musu hankalin ta, tarbiyyar ta, addinin ta da nutsuwar ta.

Wadanda duk ta rasa a dalilin rashin tashi gaban mahaifiya.

Sanda ta koma dakin maghriba ta kawo kai, Mukhtar na yima Alhaji alwallah zai yi sallah yadda yake yi daga kwance, sai ya tabbatar Alhajin ya tada sallah sannan ya shiga ya dauro tasa ya fito, sai ya tadda Amani ta ja ledar nashi abincin tana ci ba kunya ba tsoron Allah fuska tamke, an ce yunwa ba kanwar uwa bace.

Girgiza kai yayi ya shimfida dardumar da yake sallah a kai ya tada sallah a gefen gadon Alhaji.

Ko da ya idar da sallah bai ce mata don me ta ci masa abinci ba, ya san dama in yunwar cikin ta ta kama ta zata ci ne kullum haka take masa, ba don komai ba sai don kada tace ta gode a duk lokacin da ya sayo masu abinci.

A haka sauki ke ta samuwa ga Alhaji Usman, bakin sa da ake ta gasawa ya fara fidda magana sosai, likitocin sa sun ce duk bayan watanni shida zasu dinga zuwa check up, duk da tafiya da kafafu bata samu ba don haka suka ce Alhaji zai dinga amfani da wheelchair.

Watan su guda kenan suna jinyar Alhaji amma ba abinda ya canza a alaqar su.

Yau suka sauka a gida Mukhtar na turo Alhaji a wheelchair inda Haj.

Rabi taje ta taho dasu daga filin jirgi tareda sauran ma'aikatan kamfanin Faskari.

Kowa ya zo falo ya jajantawa Alhaji yayi masa sannu da dawowa.

Malam Tajuddeen shi ya gaya musu zuwan Alhaji Sadi Talle uku bai samu Alhajin ba, yace kuma layin Alhajin da yake da shi baya tafiya, sun gaya masa Alhaji asibiti yaje babu lafiya, ya ce duk ranar da suka dawo Malam Tajuddeen ya sanar da shi.

Ba Alhaji ne kadai fuskar sa ta sauya ba har da ta Mukhtar.

Amani tunda ta haura sama ta bar su bata kara saukowa ba.
**** **** ****
Washegari kuwa tunda safe Alhaji Sadi ya zo cikin rantsatstsiyar motar sa Acura, kai da ganin irin kwalliyar da ya caba cikin sassalkar shadda fara kal, zaka san ba dubiya kadai ya zo ba har da zance na saurayi ga budurwa don fara kafa gwamnatin sa.

Mukhtar baya gida yana company don gudanar da ayyukan da suke jiran sa duk da cewa yana rage ayyukan sa daga can asibiti ta kwamfuta wadanda sakataren sa ke tura masa, musamman in Alhaji na barci, zaka same shi yana aiki cikin kwamfuta yayin da zaka samu Amani na harkokin ta cikin wayar ta cikin dakin ba ya ko daga ido ya dube ta, amma a zuciyar sa ya na takaicin ace mace bata da abun yi sai shiga social media, babu lazimi sam babu karatun Al
ani, Amani fa ko addu
a take son yi sai dai ta roki Hamida tayi mata don a cewar ta bata iya hana idon ta barci, kuma Hamida ta fi ta juriyar tsayuwar dare.

A hakan da yake yi ya samu ya rarrage ayyukan kamfani da yawa ta yadda yanzu da ya dawo ayyukan basu cude masa ba, ko da yake yanzu ayyuka sun karu masa tunda shi yake gudanar da duk wanda Alhaji ke yi da kan sa a lokacin da yake da lafiya.

Aka yi wa Alhaji Sadi iso falon Alhajin, bisa umarnin Alhajin.

Yana shiga ya ga Alhaji cikin wheelchair a zaune yana kallon talabijin.

Alhaji Sadi ya ce
Ya salamu sallim, ashe ciwon babba ne haka?

Yanzu da wadanne kafafu zaka yi takara?

Kai bana jin ma jam
iyya zata yarda in tsayar da mai shanyayyen barin jiki kan kujerar gwamna tunda ba ni kadai ke da jam
iyyar ba
Sannan ya zauna gefen sa ya bashi hannu yana fadin
sannu, sannu yaya jikin naka?
Chapter 16 · 0% Book details