← Book details Amani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 25

Sashe 22

Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ni da kai na na yi mata alkawarin ni zan kai ta da kaina, zan nemo adireshin daga gare ka.

Na tsara in mun gama da Faskari, in roke ka mu bi jirgi zuwa Sierra Leone din mu dangana ta da mahaifiyar ta.

Ta yanke wannan hukunci cikin fushi, don haka ka bi ta a hankali ka rarrashe ta mu tafi Faskari tare, sauran ka bar komai a hannu na
Alhaji ya nisa, ba ya son kai
yar sa ga Jal
an da iyayen ta, don ya san Jal
an bata son sa, kuma bazata taba son sa ba, don haka bazata so jinin sa ba, amma ya ya zai yi da Mukhtar tunda ya dage ya tsaya wa Amani a kan hakan?

Jal
an ta taya shi rainon diyar sa ne ko ko ta taba tunanin ta tako ta zo ta gan ta ko sau daya?

Ai ta san inda ta bar
yar in dai ba kiyayyar da ta ke masa ce ta shafe ta ba, ya ci a ce ko sau daya ta waiwaye ta ta ga cewa ta rayu ko ta mutu?

Alhaji ya manta cewa shi ya raba tsakanin uwar da
yar tun ranar da ta kawo ta duniya, shi y araba wannan kaunar da hannun sa, ya bar Jal
an a halin da ita ma ba shi da tabbacin ta wuce ko ta rayu, Hausawa suka ce,
laifi tudu
Alhaji ya ce,
Kada ka damu, I will take care of her
kafar mu kafar ta zuwa Faskari, in ka ga ta je wani waje bayan Faskari, to sai tana a matsayin matar ka, bisa yardar ka da amincewar ka.

Biyayyar da ka yi min da kyautatawar ka gare ni Allah ya ba ka masu yi maka kai ma.

Allah ya sa Amani ta zamo alkhairi gare ka da addinin ka.

Allah ya ba ku zuri
a masu irin halin ka, ba masu irin nata halin ba
Dan murmushin mamaki Mukhtar ya yi, yana so ya ce,
Alhaji na furta maka na amince ne?

Amma kunya ta hana shi cewa komai, don karamcin Alhaji gare shi ya zama abin kwatance, tunda har ya amince ya ba shi auren tilon
yar sa ba tare da ya san asalin sa ba, ba tare da ya san iyayen sa ko wani nasa ba, ba kuma tare da ya ga mahaifar sa ba.

Sannan ba tare da amincewar
yar tasa ba, wadda kowa ya san ba ya son bacin ran ta amma a kan sa ya yarda ya bata wa Amani karshen batawa da kan sa.

Ko don wadannan dalilan, da wasu da dama, sai ya ji ba zai iya badawa Alhaji Usman kasa a ido ba.

Zai rike masa amanar
yar sa da dukkan halayen ta ababen ki, da dukkan tijarar ta da rashin kaunar ta gare shi.

Zai iya rantsewa cewa zuciyar sa ta dade tana son AMANI, ita kuma ba ta son sa da alaqar aminci dake tsakanin sa da mahaifin ta, wanda ya san shi ya fi komai sayo masa bakin jini, kishi da tsana a idanun ta.

Alhaji ya soma kokarin kiran Amani bayan sun rabu da Mukhtar a waya.

Tana kallon kiran Daddy nata shigo mata amma ta kai zuciya nesa ta ki dagawa har ta katse, ya sake kira.

Amani sai hada kaya ta ke tana kuka, amma ba ta amsa ba.

Alhaji ya kira Malam Tajuddeen ya ce masa a rufe gate kada a bar Amani ta je ko ina in ba tare da su ba.

Daidai lokacin Mukhtar ya shigo gidan, misalin karfe bakwai na safe, suka gaisa da Malam Tajuddeen da sauran ma
aikatan gidan, ya wuce ma
adanar motoci ya fiddo wadda za su tafi a cikin ta ya zuba mata mai da kan sa, sannan ya ce da Ali ya wanke motar amma wajen ta ba cikin ta ba, sannan ya karasa sassan Alhajin.

Da sallama ya shiga falon, Alhaji ya amsa ya ce,
Yanzu nake so in kira ka ka je ka turo min AMANI, tana can side dinta a saman bene.

Na kira na kira ta ki dagawa
Mukhtar ya ce,
Alhaji ka fara yin wanka tukunna, ka karya kumallo, ka kwantar da hankalin ka, everything will be alright, in sha Allahu
Ya taimaka wa Alhaji ya yi wanka, ya fiddo masa manyan kaya ya saka, ya tambayi Alhaji ina Hajiya Rabi don bai ga ta kawo breakfast ba har yanzu.

Alhaji ya ce,
Na ba ta tikitin ta daren jiya ta tafi, tana barazanar danne ni da filo in ban sake ta ba, daga kan ta na rufe aure in sha Allahu, zan zauna cikin kujerar
nakasa
in nemi lahira ta, har zuwa ranar da wa
adi zai cika, kai dai ka rike min Amani da gaskiya, ka bunkasa mata dukiyar ta har Allah ya baku zurri
Dan ku ya girma ya gaje ka kan sha
anin kasuwancin mu.

Idan na samu wannan na gama samun duk wani farin cikin rayuwa
A wannan lokacin Mukhtar ya jona kettle ya hada wa Alhaji coffee mai zafi ya bashi yana sha, ya yi waya kitchen ya ce Rakiya ta shiryo karin kumallo ta kawo wa Alhaji, kuma ta kai wa Amani.

Ta lallashe ta ta tabbatar ta ci ko kadan ne, don fita za su yi.

Alhaji na kurbar coffee dinsa yana jin abin da Mukhtar ke ce wa Rakiya, sai ya ji wani irin dadi ya lullube ran sa.

At least Mukhtar bai ba shi matsalar da Amani ta ba shi a kan hukuncin sa ba.

Ya tabbatar wa kan sa ko Mukhtar ba ya son Amani, to fa ba zai wulakanta masa ita ba duk irin halin fitsarar ta, wanda a yau ya yarda rashin tashi da uwa ne ya janyo mata, ko wata kwakkwarar uwar riko a gare ta.

Kuma duk hakan ya faru ne bisa kuskuren sa da munanan halayen sa.

Tun farko me yasa ya rabo ta da Sahura?

Don kada ta sha wahala da rayuwar kauye.

Me yasa bai barta ta rayu a Funtuwa ta samu tarbiyyar data dace a hannun kanwar sa ba da cikakken ilmin addini wanda zai sa ta san muhimmancin iyaye da girman da Allah ya yi musu?

Rakiya ta shigo ta kawo musu karin kumallo mai rai da motsi, sinasir ne da miyar ganye da ta ji naman talo-talo, sai kunun gyada fari sal mai gardi.

Mukhtar ya cikawa Alhaji plate ya tura masa gaban sa yana ta yi masa hirar abubuwan da ke faruwa a company kwana biyunnan don dai ya samu ya dauke damuwar da ke kwance kan fuskar Alhajin.

Amma sai ya ji Alhaji ya ce,
Na yi maka izinin hawa sama, har dakin TAFISU.

Ka je ka zo min da ita nan cikin lallashi mu ci abincin nan tare da ita
Mukhtar ya rasa yadda zai yi da wannan umarni mai nauyi a gare shi na ubangidan sa, amma ganin irin damuwar da ke kwance a fuskar Alhajin sai ya ce.

To Alhaji, amma idan ta ki fa?

Zan dauko ta a ka ne?

Ka san fa babu shiri irin wannan tsakanina da ita
Alhaji ya ce,
Da irin haka ne za ku saba da juna.

Har watarana ku kaunaci juna.

Yanzu Amani matsayin matar ka ta ke, shaidu kawai ya rage su shaida
Mukhtar duk sai ya ji maganar ta Alhaji wani irin banbarakwai wai namiji da suna Hajara.

Alhaji ya kira Rakiya a waya ya ce ta zo ta raka Mukhtar sassan Amani.

Rakiya na gaba, Mukhtar na bayanta har dakin Amani.

Ta kwankwasa kamar yadda ta saba yi wa Amani.

Amani na can abu goma da ashirin ya ishe ta don har zuwa lokacin da ta tura wa Mr.

Balogun kudi da awanni biyu babu adireshi babu lambar waya na Maman ta da ya turo mata.

Ta yi ta gwada kiran wayar sa tun tana shiga yana kin dagawa har ta daina shiga kwata-kwata.

Ko dai an daina amfani da layin, ko an kashe wayar gabadaya.

Sai ta dora hannuwa bibbiyu a kanta tana son rusa ihu ko ta samu sa
idah.

Sai ga Rakiya ta murda kofar ta shigo, jin ta yi ta kwankwasawar Amani ba ta ba ta izinin shiga kamar yadda ta saba ba, sai kawai ta shigo kan ta tsaye don ta ga ko lafiya.

Amani ta zuba wa Rakiya idanun ta da suka yi jazir da bacin rai, tana kallon ta tamkar ita ce Balogun.

Rakiya ta karyar da kai gefe ta ce,
Afuwan uwardaki na, Alhaji Mukhtar aka ce na rako wurin ki.

Alhaji da kan sa ya ce in rako shi
Kafin Rakiya ra rufe baki, Amani ta samu zarafin ci mata mutunci, ko kunduma mata ashar, Mukhtar din ya shigo dakin kan sa tsaye.

Daga jikin kofa ya tsaya hannuwan sa harde da kirjin sa yana kallon Amani da yadda a cikin dare guda duk ta zabure ta fice a hayyacin ta.

Rakiya ta juya ta fita har da rufo kofar dakin, tana fadin
a fito lafiya Alhaji
Mukhtar kallon ta kawai yake daga sama har kasa, wani irin kallo da bai taba yi mata ba.

Duk da cewa kayan barci ne a jikin ta gashin kan ta babu rufi, gashin duk ya tarwatse duk ya yi buyaya da shi kamar sabon kamun hauka, shi a idon sa gani ya yi kamar an kara mata kyau da kwarjini, duk da idanun ta sun jeme sun yi zuru-zuru din.

Kallon-kallo aka tsaya ana yi tsakanin Mukhy da Amani, kallon da su duka suka kasa fassara yanayin sa yayin da Mukhtar ya ji wani abu mai kama da tausayi ya darsu a ran sa game da ita, ganin yadda duk ta sauya kamanni da appearance a kwana daya.

Amma ya riga ya san Amani zuma ce sai da wuta ake iya sarrafa ta.

Kamar ba zai yi magana ba don ya san kiris ta ke jira ta saki tantrum, amma sai ya tuna damuwar da mahaifin ta ke ciki a kan ta.

Ya tuna rokon da ya yi masa a kan ya lallaso ta ta zo ta karya kumallo tare da shi sannan su wuce Faskari.
Chapter 22 · 0% Book details