← Book details Amani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 25

Sashe 12

Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai shi bai ma yarda Alhaji Sadisu zai sa a bashi takara a PRC ba duk da matsayin sa na shugaban jam
iyya, don ya san bashi da farin jini yafi yarda da cewa kudin sa zai ci ya wofintar da shi.

Duk da cewa ba yau suke tare ba duk da banbancin jam
iyya dake tsakanin su.

Abota ce tsakanin su tun ta kuruciya.

Ai Alhaji Sadi kamar jira yake Mukhtar ya bar wurin ya muskuta cikin kujerar sa bakin sa nata motsi yace
shin Hon.

Usman wannan kyakkyawar diya taka ce ko
yar riko ce?

Hon yayi dariya yace
Amani ce fa, Amani Faskari, ita kenan
yar daya jallin jal dana mallaka duniya da lahira
Sai a lokacin Alhaji Sadi ya hau tuna komai na Alhaji Usman yana bearing wannan sunan ne wato
Amani Faskari
, bai taba sanin sunan
yar sa ne Amani din ba, don bai taba jin irin wannan sunan ba.

Alhaji Sadisu ya shafa gemun sa da sajen sa yana murmushi yace
ai kawai Hon.

Ka ce ta zo gidan sauki tuwo na mai na, abu nawa maganin a kwabe ni.

Ka bani auren ta ni kuma na maka alkawarin kujerar gwamnatin Katsina sau biyu, ko ana ha maza ha mata sai ka yi
Hon.

Usman a matsayin sa na uban da bai taba jin wani ya tare shi yace yana son Amani ba, saboda kowa cewa yake tafi karfin sa saboda izzar ta da irin rainon da yayi mata, sai ya ji dadin maganar kwarai, ya ga cewa tabbas Alhaji Sadi zai iya da Amani ba tare da yace tafi karfin sa ba shi, tunda in dukiya da mukamin siyasa ne da take takama yana da su ne shima Sadi a cikin su yake dumu-dumu har ya dara shi komai yanzu, in ka dauke yawan shekarun sa da suka zarta nasa, da furfurar data soma samun muhalli tsilli-tsilli a saman kansa, sai ya ga cewa zai iya bashi auren Amani muddin zai taimaka masa ya zama gwamnan jihar su.

Babban burin sa na yanzu kenan wato zama gwamnan jihar Katsina.

Alhaji Sadi bai bar gidan ba sai da suka kulla yarjejeniya a rubuce da shi da Alhaji Usman cewa zai tsaya masa a matsayin sa na shugaban jam
iyyar PRC a bashi takarar kujerar gwamna shi kuma kafin nan ya aura masa
yar sa Amani.

Ya so a yi magan
ar nan a gaban Mukhy, amma Mukhtar din tunda ya zame da sunan zai je yayi sallah ya ki dawowa.

Haka kawai ya kasa jure mayataccen kallon da Alhaji Sadi ke bin Amani da shi, kuma in za
a kashe shi bazai ce ga dalili ba.

Shi kawai yana ganin ba girman Alhajin bane.

Basu kara haduwa da Alhaji ba sai washegari.

Lokacin da Alhaji ya gaya masa yarjejeniyar da suka yi da Alh.

Sadi washegari suna hanyar zuwa ofishin Alhajin, Mukhtar suman zaune yayi.

Ya yarda neman Mulki yana fidda wasu dattijan a hankalin su.

Ina Amani
yar shekaru 20 ina tsoho dan shekaru 65 banda kwadayin Mulki da neman sa ido rufe irin na Honourable Usman?

Kai bama wannan ba wani dunkulallen abu ne ya zo ya tokare shi a makogaron sa ya kasa cewa Alhajin sa komai, sai kawai ya maida hankali ga tukin da yake yi zuciyar sa na wani irin bugawa fat-fat.

Alhaji Usman yace
baka ce komai ba Mukhy, ko shawarar tawa bata yi bane?

Na san ka da tsinkaye, amma nima ina da amfanin da zan samu a cikin auren, ai wato komai mutum zai yi a rayuwa yanzu ya fara hangawa ya auna ya gano ribar da zai samu a cikin sa.

Kaga in ya auri Amani zai taimakamin na zama gwamna, zai tsaya min kan duk mai son taka ni a jam
iyya, abinda na tsara shine sai in nada ka mataimaki na amma ko shi ban gayawa hakan ba, ka nemo mata kayi aure kai ma mu tara dukiya iyakar tarawa, mu Mulki Katsina tare, mu ci duniyar mu da tsinke, amma na yi rantsuwa ba mijin da zai ci min dukiyar Amani, don ita na tara mawa, komai nata zai koma karkashin kulawar ka da amanar ka ko da ta auri Alhaji Sadi.

Hatta kayan daki ka ga ba sai mun yi mata ba gidan Alhaji Sadi duniya ne; babu abinda babu cikin sa.

Kudin komai dana tanada don auren ta sai a kara jari dasu a boutique din ta ka ga dadin auren mai akwai kenan.

Gashi babu mace yanzu tare da shi tun rasuwar uwar yaran sa bai kara aure ba, yaran bakwai duk sun manyanta, biyar daga ciki sun yi aure.

Don haka Amani bazata yi masa rainon yara ba.

Ya ka gani?

Mukhtar Diffa dai ya zama mutum-mutumi a zaune.

Tuki kawai yake ya rasa amsar da zai baiwa Alhaji.

Bai san cewa ya bar hanyar da zata kai su company ba ya dauki wata daban da bai san inda zata kai su ba, har sai da Alhajin ya ankarar da shi, sannan ya koma da baya ya dauki hanya daidai.

Da Alhajin ya takura sai ya ji ta bakin sa sai ya ce
ni me zan ce Alhaji?

Banda Allah yayi zabi mafi alkhairi?.

Tunda kun riga kun rubuta yarjejeniyar a rubuce ai bani da say.

Kome zan ce is too late.

Sai dai naso ace Amani din da yardar ta aka zartar da komai.

Saboda ina tsoron maka halin yaran zamani, kada ta baka kunya Alhaji.

Yaran yau ba
a sha musu alwashi irin wannan
Shima sai a lokacin yayi wannan tunanin na cewa ba lallai Amani ta yarda ta auri Alhaji Sadi ba in aka yi la
akari da yawan shekarun sa.

A sanin da yayi wa Amani bata taba nuna tana sha
awar a yi mata aure ba, tafi sha
awar cigaba da rayuwar ta cikin hutu a gidan su, cigaba da tabara da wadaka da dukiyar mahaifin ta, ta hanyar yin kwalliya ta kece raini da sanya sitturu masu karshen tsada da hawa duk kalar motar data ke so wato yawan canza mota new mdel duk shekara, burin ta kenan.

Rana daya azo a ce an bada auren ta ga tsoho abokin baban ta don cimma wani kuduri na siyasa, abin zai zo mata banbarakwai, shima ya san ya daukowa kan sa Dala babu gammo.

Dama Amanin ga ta nan ga kamar ta wajen hankali da tarbiyya.

Har suka iso ofishin Alhajin babu wanda ya kara magana a cikin su, Alhaji na cikin taraddadin yadda zai fuskanci Amani da maganar.

Mukhtar da ke tuki na kokawa da numfashin sa dake faman kai kawo a tsakanin kirji da zuciyar sa.

Kwana biyu a tsakani Alhaji na ta nan nan da Amani, ya rasa ta inda zai bullo mata da zancen Alhaji Sadi, ya tuna lokacin canza motar ta yayi bari ya nemo motar da take mafarki in yaso yace mata Alhaji Sadi ne ya kawo mata a matsayin goron na gani ina so, ga Alhaji Sadin ya takura yana so ya bashi izni ya fara zuwa zance.

Ya san in bay a yi da gake ba zai sha kunya idan Alhaji Sadi ya tare ta da zancen kafin shi.

Don haka yau dai yayi kundumbala ya kira Mukhtar falon sa.

Suka zauna shi da Alhajin cikin dakin sirrin Alhaji, Alhaji Usman yace
Mukhtar na yi abinda ya zo ya dame ni, har yanzu na kasa gaya mata zancen nan, jiya ta zo min da admission na son tafiya karatu a jami
ar Queen Mary, ta ce tana so in yi mata iznin tafiya karatun digiri na biyu, ga Alhaji Sadi na maganar aure nan kurkusa, so yake in bashi izni ya fara zuwa ganin ta na rasa ta inda zan bullo mata
Mukhtar kamar yayi dariya ya dai gintse ya ce
Alhaji Amani
yar ka ce, me yasa kake shayin ta?

Hakan bai dace ba ko kadan
Alhaji yace
rikicin ta nake tsoro, baka san ta bane, wanizubin kamar sarka take fadi ki rikice ta fannin rikici, sau da dama in ta rikice min kamar mahaifiyar ta take komawa, bana sanin ta ina zan shawo kan ta
.

Mukhtar na so ya ce
ita siyasar dole ce da za
a saida farin cikin
ya domin ta?

A fili kuma yace
Alhaji kamata yayi ka kirawo ta ka zaunar da ita ka gaya mata hujjojin ka kamar yadda ka gaya mini, na tabbata bayan rikicin, zata zo ta fahimta tunda dai kana son takarar nan, in ya so daga baya in ta gama rikicin zata yi biyayya, zan taya ka tausar ta
Da wannan shawarar ta Mukhtar ya dogara, washegari ya kira Amani, ya kawo takardar sabuwar mota da mukullin ta ya bata, ya ce
Tafisu na ji kina korafin injin motar ki yana kara, nace bari kawai a sake wata, kafin ki zama Amarya
.

Amani ta karbe mukulli da murna tace
My Daddy like no other, godiya nake, kamar ka san na dade ina son Lamborghini, Allah ya bar mini kai Baba na
yace
ai yau kyautar ba daga ni ta fito ba, daga Alhaji Sadi ne, ai kin san shi ko?

Wannan abokin nawa da yazo satin da ya wuce?

Amani ta ce
ni kuwa na san shi, wannan mai katon cikin kamar kwaryar kindirmo, da idanu kamar na soyayyar gyada, yana kallon mutane tamkar mage ta ga bera
.

Alhaji ya kama baki yace
Amani ban san ki da cin zarafin na gaba ba, shi da ya gan ki ya yaba da ke ya nemi auren ki cikin girma da daraja a hannu na da alkawarin zai tsaya min sai inda karfin sa ya kare in samu takara.

Idan na samu kujerar ai ke zaki fi kowa morewa da jin dadi
Amani tayi sakale!

Tana kallon bakin Alhaji tana cewa a ranta
ko Daddy ya fara shaye-shaye ne?

A fili tace
Daddy ban gane komai cikin maganar ka ba, wace Amanin?

Ni?

Kuma takarar me ka ke magana?

Alhaji ya sassauta murya cikin lallashi ya shiga yi mata bayanin yarjejeniyar su yadda zata fahimta.

Sai Amani ta sunkuya ta rike ciki ta daddage ta hau zuba dariya tana cewa,
Daddy!
Chapter 12 · 0% Book details