← Book details Amani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 25

Sashe 7

Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni wallahi ta ko
ina ya yi min, kin ga dai daga nesa kawai kika taba nuna min shi last zuwa na KT, kuma ban ga fuskar sa sosai ba sai bayan sa yana shiga mota, amma ko daga tsayuwar sa da zatin bayan sa kadai mutum ya gani ya san Allah ya ajiye namijin duniya a nan, haibar sa da kamalar sa sun tafi da ni, da duk nutsuwa ta, kyawun sa ya tafi da Imani na na dade ban daina tuna shi ba.

Ki ga min mutum kamar shi ya yi kan sa don kyau, ga iya daukar wanka, ga iya dressing, ga jan aji nna karshe, da iya takun tafiya, yana tafiya gib-gib tamkar basarake, ga wani
special class
(aji na musamman), na kasaitattun maza
.

Watakila saboda idon ki ya rufe da kishin sa da kiyayyar sa saboda son da Daddy ke masa ne yasa baki hango abubuwan da ni na hango a tare da shi ba
Babu shiri Amani ta katse wayar ta, bayan ta lailayo ashar ta yarfawa Hamida.

Haka kwana ta yi tana tsinewa furucin Hamida da Hamidar kan ta a zuciyar ta.

Washegari tun da Amani tayi sallahr asubah bata koma barci ba, ta zauna bisa dardumar sallahr ta tana tunanin yadda zata yi ta fidda wadannan kudade daga corporate account din, wanda Daddy ya bude mata shi ne don ajiyar jarin kasuwancin ta kadai, ya kuma bude shi tare da sunan Mukhtar ne a matsayin Director kuma sakataren ta, sannan kuma mai kaso daya bisa uku na abinda ke cikin asusun, Hon.

Usman yayi haka ne kawai ba don da gaske ya mallakawa Mukhtar din wannan kason ba a
a, komai na Amani ne, ya yi ne kawai don Mukhtar din ya zama spy din sa a kan duk wani transaction na Amani da kuma sunan wanda ta turawa, ba don komai ba sai don ya san ta da almubazzaranci da saurin mika wuya wa mutane, shikuma ga shi da son abun hannun sa, bai yarda a ci da gumin sa ba.

Tun bayan zuwan Mukhtar wajen sa Hon.

Usman ya fito da wannan idea din, ta joining account din Amani da Mukhtar a matsayin
corporate account
na kasuwanci, yardar da ya yi masa mai yawa ce, don ko dan sa na cikin sa ba zai sakarwa sirrikan sa irin yadda ya sakar wa Mukhtar ba, yana jin takaicin almubazzarancin Amani don shi ko wane sisi da kowanne kobo abu mai daraja ne a wurin sa, kashe kudin Amani ya yi yawa, musamman ga dangin sa na Faskari, inda wani abu mai kyau guda daya tak cikin halayen Amani to
kyauta
ce.

Amani tana da hannun kyauta wa na kasa da ita kasancewar bata san zafin kudin ba, abun duniya bai taba rufe mata ido ba kullum hannun ta a mike yake cikin yin kyauta ga wanda Alllah ya tsaga da rabon sa.

Wani zubin tana sanin an cuce ta ko an dafketa wajen sayen abu, amma bata damuwa don Alhaji kullum kara tara mata yake.

Babbar damuwarta a yanzu tana so ne ta turawa dan sandan cikin dake mata bincike a kan inda Mama Jal
an take a kasar Sierra Leone.

Dan sandan ya bukaci wadannan makudan kudaden da suka wuce hankali ne ganin yarinyar ta zama desperate a kan neman mahaifiyar ta, kuma ya ga alamar akwai kudin tare da ita sannan bata son shigar da kowa cikin maganar tasu.

A karshe Amani ta ga cewa babu mafita fa dole sai Mukhtar ya ga debit alert dinnan, wanda ke nufin sanin Daddy, domin tabbas ne Mukhtar sai ya gayawa Daddy a irin amanar da ke tsakanin su cewa ta fidda miliyoyin kudi don ta san dalilin hadasu a account guda Kenan, don ko sau daya Mukhtar bai taba daukar wani abu a ciki ba.

Don haka ta kai azahar a daki tana qulubi, tana bacin rai, ga shi dan sandan cikin wato DSS din da ke mata aikin ya tabbatar mata data tura masa kudin da ya bukatan a take zai turo mata adireshin Maman ta da ke Freetown wato babban birnin Sierra Leone.

Kai har ma da lambar wayar ta ya ce duk ya samo.

Amma sai ta fara biyan sa wadannan kudaden da ya kayyade mata tukunna.
**** **** ****
Abu daya da ta san bazata taba iyawa ba shine rokon Mukhtar alfarma, don tana ganin bai yi wannan isar a idanun ta ba.

Ba don haka ba da ta roke shi ya yi mata alfarma ya rufa mata asiri sau daya a rayuwa, kada ya gawa Daddynta ta fidda 5 millions ta baiwa wani a boye domin ya nemo mata Innar ta.

Idan Daddy yasa ta gaba da tambaya da kwakkwafi (query) tabbas zai gano shirin da ta ke yi ta karkashin kasa na son ziyartar mahaifiyar ta a boye.

Tana cikin wannan tunanin wayar ta ta hau ruri.

Ganin sunan Daddy a daidai lokacin da take tunanin sa sai da gaban ta ya fadi.

Ta amsa a sanyaye.

My Daddy!

Daga can barin sa Hon.

Usman ya ce
Tafisu ki sauko falo na yanzun nan
Iya abinda ya fada kenan ya kashe wayar sa.

Ta zura siraran kafafun ta cikin silifas din bakin gado sannan ta fita ba tare da ta canza kayan barci farare samfurin
Calvin Klien
da ke jikin ta ba.

Falon Alhaji Hon.

Usman Faskari, wani irin makeken falo ne wanda sai da ya ci saitin kujeru uku iri daban-daban saboda girman sa.

Ya kawatu da kayan alatu da
air condition
ta tsaitsaye a kowacce kusurwa, komai na jin dadin rayuwa yaji a wannan falo mai kama da
palace
, din wani gwamnan kai ka ce babu ranar mutuwa a zuciyar mamallakin sa.

Amani ta shiga tako matattakala tana saukowa daga saman benen ta tana tafiyar nan tata tamkar bata so.

Kallo daya Mukhtar da ke zaune gefen Alhaji ya iya yi mata a lokacin tana saukowa daga stairs din, cikin takun nan nata tamkar na macen Dawisu mai ji da kasaita, ya yi maza ya sunkuyar da kai cikin jin faduwar gaba don bai taba yi mata kyakkyawan kallo ba, yau din ma kamar kullum, a sace ya kalle ta, amma ya ga surar jikin ta sosai a cikin kayan barcin, sai ya samu kan sa cikin jin takaicin wadannan sharasharan kuma bingilallun kayan dake jikin ta a matsayin ta na mace kuma Musulma a cikin mutane, domin kamar kanwar sa ya ke kallon ta.

Har ga Allah Amani bata san da shi a falon ba ta riga ta saba gaida mahaifin ta da kayan barci in har tana son su gaisa kafin ya fita, kasancewar sa ma
abocin sammako.

Tana cigaba da saukowar bugun zuciyar Mukhtar na dada karuwa, ba tun yau ba hakan ce take kasancewa da shi a duk a lokacin da ya hangi Amani ko daga nesa ne.

Duk da dai wata kalmar fatar baki bata taba hada su ba.

Amma Tafisun tun dawowar ta daga ATBU take yi masa kwarjini sosai.

Tafisu na dauka tuntuni kin shirya jiran isowar Mukhy kike ya zo ku wuce ki duba Boutique din naki?

Amani ta yi kicin-kicin da fuska cikin sakalci irin nata tace
Daddy ai ba sai mun tafi tare ba, yayi gaba, tunda yana da mota a hannun sa, ni inna kintsa na gama breakfast na yi wanka sai in zo mu hadu a can
A zuciyar ta kuwa fadi take
Allah ya tsare ni da shiga motar sa, Allah tsare ni hada hanya da shi
Don dai ita Amani fisabilillah bata yarda hakanan Mukhtar ya bar baban ta ba, tafi yarda da cewa asirin su na Diffawa yayi masa yake son sa irin haka, kada ta je itama ya hada da ita ya dinga juyata yadda yake juya Daddyn ta.

Daddy ya ce cikin lallashi,
amma kin san bana so kike tuki da kan ki ko Amani?

Tunda duk kin kori direbobin saboda masifar ki sai ki shiryo Mukhy yana jiran ki ku tafi tare, ban yarda ki kara tuki daga yau ba, kada ki manta sau uku kenan kina yin
accident
din da sai na biya diyya ga wadanda kike bugawa mota ta baya, tunda tukin bai karbe ki ba, to a hakura da shi babu dole.

Duk inda kike son zuwa ki kira Mukhy a waya ya zo ya kai ki.

Amani ta hau tumami da kafa cikin shagwaba tana fadin "Ni gaskiya bazan daina tuki ba, da koyo akan iya Daddy.

Kuma da haka ne zan kware da tukin".

Hon.

Yace "duk ba na ki ba, ina nufin for the mean time zuwa kafin ki koya din nake magana, daga yanzu duk inda zaki Mukhy na yarda ya kai ki.

Shi kin ga bayan iya tuki na hankali, harda nutsuwa da sanin ciwon kai a tare da shi.

Maza shiryo ki zo ku tafi kin ji Tafisu na?

Bana son musu.

TA FI SU KIN FI SAURAN MATA!

Ya fadi kirarin da ya san da shi yake lallashin ta, duk da tana cewa bata son kirarin amma sosai mahaifin nata yake ciyo kan ta da shi ta yi masa abu idan ta yi gardama, kamar wata karamar yarinya.

Fuskar nan ta Amani kamar hadarin da ya nausa yayi gabas ya juya yayi yamma.

Wato Daddy na nufin ita bata san ciwon kan ta ba kenan kuma bata da nutsuwa sai Mukhy din sa.

A fusace ta juya zuwa hanyar data fito, bayan ta zabgawa Mukhtar wata hadaddiyar harara tamkar manyan idanun nata zasu fado kasa.

Mukhtar wanda kansa ke sunkuye yana danna wayar hannun sa bai san tana yi ba, ya yi sallama da Daddy yana fadin
zan jira ta a mota
Daddy ya ce
ka dai tabbatar da lafiyar motar da za ku hau din ko Mukhy?

Kuma Amani zata so hawan wadda ka zabo din?

Bata so tana tafiya a hanya mota ta samu matsala, kuma bata son dindimemiyar mota.
Chapter 7 · 0% Book details