Sashe 4
Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi Alhajin ya yi, maimakon ran sa ya baci ya kwabeta a kan rashin kunyar da ta yi masa, amma sai ya buge da rubuta mata text message din lallashi da wayar hannun sa.
Zuwa shekaru kadan a gaba, idan Allah ya raya mu, Tafisu zaki zo ki gode min, for making MUKHTAR DIFFA your Business Mentor, ranar da kika ga Mukhtar ya maida dan Boutique din nan naki ya rubanya zuwa PLAZA guda.
Domin Allah SWA ya huwwace da ya halicce shi yayi masa hikimar maida taro ya koma sisi.
Trust him my daughter, work with him for a while, give him a try as your business mentor!
**** **** ****
Sai da Amani ta zo kwanciya ta ga wannan sakon na Daddy, zumburo baki tayi tana tunanin mutumin nan ba haka ya bar mahaifin ta ba.
Yardar ta isa.
Kaunar ta yi yawa.
Ko shi ya haife shi sai haka.
Iya shaidar arziki da zai iya masa kenan.
Daddyn ta da duk wanda ta nuna bata ra
ayi nan take zai yanke alaqa da shi ko waye kuwa, ko da zai kasance jinin sa ne, amma banda MUKHTAR DIFFA.
Farin ba
abzinen data taso ta gani tare da mahaifin ta, yana rayuwa karkashin sa matsayin mataimakin sa, kuma yana tare da shi kullum a gida ko ofis.
Dan asalin garin Diffa, ta kasar Nijar, wanda ko asalin sa basu sani ba har shi Daddyn kuwa, banda sunan garin sa da yake amfani da shi a gaban sunan sa
DIFFA
Daddy dai ya dauke shi aiki ne da farko a dalilin haduwar jini kawai, ta sanadin wani halin amanar sa da ya bayyana gare shi, rashin zalama da rashin kwadayin abun duniya, in kana da wadannan halayen, tabbas zaka zauna lafiya da Hon.
Usman Faskari tunda shi bay a so wani ya more shi ko yayi arziki da shi, sannan ga kyawawan kwalayen ilmi (educational qualifications) din sa masu nagarta, domin Mukhtar Diffa, ya fitar da kwalayen boko biyu masu darajar farko (B.
Sc & M.
Sc in Business Administration) daga jami
ar Paris wato (Paris Saclay University).
***** ***** ****
FARKON HADUWAR HON.
USMAN DA MUKHTAR DIFFA
Asalin haduwar su da Alh.
Usman Faskari a wata tafiya da ya yi birnin Paris ne, lokacin da ya je shigo da wasu kayan assasa kamfanin sa na farko wasu shekaru kusan goma a baya.
Cikin tsautsayi Alhajin ya yarda wallet din sa a cikin jirgin kasa, wanda ke dauke da dukkan katunan sa na banki daban-daban (credit cards), fasfo, ID cards, da duk wasu muhimman abubuwa da ake sakawa a cikin wallet.
Bayan ya sauka daga jirgin kasan, ya shiga motar da zata maida shi masaukin sa ne ya lura babu wallet din sa a tare da shi, wadda ba katunan bankin sa kadai ta kunsa ba, akwai kudade (Euros) masu yawan gaske a ciki.
Alhaji da kudi, ko sadakar dubu guda baya iya yi in ba ta hanyar siyasa ba.
Yayi salati a gigice yana kara laluba aljihun sa yana gayawa direban da dauko shi su koma, ya yar da abubuwa masu muhimmanci su koma tashar jirgin kasa.
Komawar da bata haifar da komai ba sai bata lokaci, domin train din tuni ya dade da barin Paris, ya nausa wata jihar dake gaba da Paris wai ita Bourdeaux.
Ya dai bar report a ofishin jirgin kasan da wajen
yan sanda.
Hon.
Ya shiga damuwa ba
yar kadan ba a daren, domin a cikin wallet dinnan kusan duka sirrin rayuwar sa ne gabadaya.
Ga tsabar kudaden da ke ciki wadanda ya fitar dasu daga banki ne da zummar zai yi amfani dasu wajen accommodation na tsayin zaman sa a kasar da cuku-cukun clearance na kayan sa har zuwa komawar sa gida.
Damuwar sa tana karuwa in ya tuna
identity cards
din sa daban-daban na siyasa da na kasuwanci duk a cikin wallet din sa.
Alhaji kamar ya zare.
Amma ko minti goma bai yi da shiga masaukin sa ba ya samu kira a wayar sa, a lokacin yana kokarin revoking katunan sa na banki don kada a samu damar yashe shi.
Duk da iya abinda ya mallaka ba wai a bankuna suka kare ba, yana da hannayen jari da kadarori masu yawa da kamfanin sa na FASKARI INVESTMENT LTD.
Yana dagawa ya ji an yi masa sallama da hausar da bata fita yadda ya kamata, ko dai Francaise ya rinjayeta ko harshen Espanol, ko
kuma abzinanci.
Cikin ukun dai.
Duk da haka a kan gane hausar idan aka saurara, kasancewar cikin nutsuwa mai kiran yake yin ta.
Ina Magana da mai wannan layin ne?
In sha Allahu kana tare da mai wannan layin
Engnr.
Othman Fass
Ya kasa furta sauran da accent din sa.
Amma Alhajin ya gane yana son cewa Faskari ne.
Sai ya karasa masa da cewa
Eh nine Engnr.
Usman Faskari
Alhmdulillah, ina zan sameka in baka wallet din ka yanzu?
Na tsince ta a jirgin kasan da ya taho daga Bordeaux zuwa Paris.
Na samu wannan lambar a jikin daya daga cikin identity cards din ka
Alhaji a zaune yake amma bai san lokacin da ya mike tsaye ba yana hamdala, yana hailala, ya gaya masa sunan Hotel din da yake, yace ya kira shi in ya zo reception.
Cikin daren ba
a kwana ba saurayin ya zo hotel din, suka hadu da Alhajin.
Ya dauko wallet din sa ya bashi.
Ya tsaya har Alhajin ya bude ya duba sosai ya kuma kirga kudin sa ya ga suna nan cif, a jere yadda ya jera su, ko kwarzane basu yi ba, ya tabbatar ba abinda aka cire.
Babban abun mamakin Alhajin, kudin sa na nan yadda ya bar su ko guda daya ba
a cire ba.
Har yaron ya juya ya tafi, Alhaji Usman ya kasa daure mamakin sa.
Sai ya bi bayan sa.
Ganin cewa dan Afrika ne ga hausa kadan ya iya, duk da dai alamu sun nuna ba bahaushe bane Ba
abzine ko dai dan kasar Nijar ne, wato irin matasan nan na Nijar wadanda ke tahowa karatun boko kasar goyon su wato Faransa, daga Jamhuriyyar Nijar, kasancewar kasar Faransa ce ta goya kasar Nijar.
Amanar yaron, exceptional personality, da kuma bravity din sa kai har ma da character da attitude din sa sun yi matukar impressing din sa.
Alhaji Usman ya bi bayan sa da sauri yana fadin;
Ya ka Da na, dakata don Allah, yaya sunan ka?
Cikin halin sauri-sauri don kada ya rasa jirgin kasan komawainda ya fito, da ko
in kula irin nasa, kuma ba tare da ya juyo ba, cikin rashin sakin fuska da rashin annuri ya ce da Alhaji Usman,
suna na Mukhtar
Daure ka tsaya ka ji Da na Mukhtar in maka godiya don Allah
Amma bai tsaya din ba sai tafiya yake, Alhajin kuma bai fasa bin bayan sa ba, yana rokon sa Allah Annabi ya tsaya ya bashi tukuici.
Ya dan tsaya har Alhajin ya cimmasa, juyin duniya Hon.
Usman yayi a kan ya karbi kudin dake cikin wallet din bakidaya don farin cikin taimakon da yayi masa, amma kyakkyawan matashin ba
abzinen ya ki, duk kuwa da cewa a lokacin neman kudin jirgin da zai koma Hong-Kong din China yake yi, saboda ya nemi wani aikin a can, kasancewar interview din da ya yi ta neman aiki da wani kamfanin turaruka a nan Paris din bayan kammala karatun sa, bai yi nasara ba.
To na ji bazaka karba ba, na kuma gode da karamcin ka, na kuma yabawa nagartar ka, samun irin ka a cikin matasa is a blessing.
Ka cigaba da wannan halin na taimako da amana zai kai ka har inda baka taba zato ba.
Na sha gwada samari kamar ka, ban samu wanda ya san amana ba.
Ni kuma mutum ne mai son mutane masu amana.
Don ta yi karanci a wannan zamanin
Still fuska ba walwala ya ce
na gode
Sannan ya juya da sassarfa ya bar reception din.
Tafiyar sa kadai abin a bi da kallo ne, saboda taku yake da sassarfa, amma kamar na kasaita.
Yaron ya tsaya masa a rai har wayewar gari.
Don haka washegari ya kira shi da layin da ya kira shi jiya, suka gaisa.
Alhaji Othman ne ko?
Ya fada da kakkaurar muryar sa bayan sun gaisa.
Ni ne Da na Mukhtar, ya ka je gida?
Alhamdulillah
ya bashi amsa.
In ba damuwa ina so in zo in gan ka kafin na wuce gida Nijeriya gobe
.
Yace
babu mishkilah, Allah ya kaimu, amma ka bari ni zan zo in same ka kasancewar daga Clermont-Ferrand City zan taho, bana so ka sha wahala har nan Baba
.
Murmushi Alhajin yayi yace
na gode Da na sai ka zo, don Allah ina jiran ka
Lokacin da yayi masa waya yace ya taso a train daga Clermont Ferrand, Alhajin yasa aka shirya abinci na alfarma a dakin sa na hotel, dama kuma yayi sayayya ta sutturu masu tsada, agogon maza na (Swatch) da takalma da turaruka ga Mukhtar din, da niyyar ya je ya kai masa har gida a matsayin godiya, tunda ya ki karbar makudan kudin da ya barma shin.
Wannan ya nuna ba karamar alfarma da haduwar jini Mukhtar ya samu a gun Hon.
Usman ba.
Kasancewar shi mutum ne mai tsananin kankamo, bi ma
ana, ba kowa ke cin arzikin sa ba bayan tilon
yar sa AMANI sai wanda rabon sa ya rantse, mutum ne mai rowa kwarai.
Tsakanin sa da duk wani ma
aikacin sa albashi kadai, babu ihsani.
Amma shi wannan yaron ya nuna masa akwai sauran masu amana da rashin kwadayi a duniya, sabanin daukar da yake yiwa kowa, cewa mutanen yanzu duk kwadayayyu ne masu neman gasashshen tsuntsu daga sama, shi yasa yake so ko yaya ya gode masa.
Don yana yawan gaya wa Amani yanzu duk mutanen duniya makwadaita ne, shi yasa suke cewa ya fiya rowa, ya dauki kowa a irin dabi
ar da yake kai, wato son ci daga haram ko halak kamar sa.
Sannan a ganin sa mutaen yanzu basa ganin kudi su kyale balle irin wadannan Euros dake dankare cikin wallet din sa.