← Book details Amani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 25

Sashe 10

Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuka ta soma yi sosai har da sheshsheka da fyace hanci, tace tunda dai na san kana ji na, halin ka ne shariya da wulakaci, to bari in fadi sako na, ya rage naka ka yi min alfarmar ko kada ka yi.

Ina so zan cire kudi 5 million zan yi amfani da su bana son Daddy na ya tuhume ni, idan ka ga alert dinnan alfarma ce kada ka fada masa tunda dai kudi nawa ne, ba na wani ba
Mukhtar ya rage gudun motar ya dan juyo kadan ya saci kallon ta, sai kuka take tana fyatar hanci kamar wadda aka yi ma wani mugun duka, kada ya je ta daura masa sharri, don ya ji an ce masa mata makirai ne.

Ya kashe motar gaba daya a gefen titi ya ce.

Da ni kike?

Amani ta ce
a da sitiyarin motar ka nake
.

Karo na farko da Mukhtar ya yi wani miskilin murmushi, ya ce
to kai sitiyarin mota ana maka magana!

Amani ta kara rushewa da kuka tace
Allah yasa ayi maka irin wulakancin da kake yi min.

Allah ya hada ka da daidai kai, Allah ya sakawa mahaifina amana ta da ya baka kake ci don ka san ka asirce shi
Mukhtar ya bugi sitiyarin sa ya ce
ban da muguwar addu
a ga wanda baki sani ba Ma
am, you will never know what a man like me is going through, I hate hayaniya, ki gaya min wace alfarma ce kike so?

Bana son koke-koken banza me na yi miki?

Wane kudi kike magana a kai?

Kuma me zaki yi da su?

Ban fahimce ki ba anymore
Amani ta dan ji dadi, at least hargagin ta ya sa ya kula ta, ta share hawayen ta da gefen mayafin ta, ta ce
ba damuwar ka bane abun da zanyi da kudi na, kawai bana so Daddy ya ji ne, da ba zaka san ma na cire ba
to kin san ba damuwa ta bane kuma bai shafe ni ba don me zaki sako ni ciki?

An gaya miki ina shiga abunda ba
a sa ni bane?

Ai kawai ki yi abinda kika ga dama nima in yi aiki na na daukar zance in kai gaba, tunda shi aka sa ni, ba sai kin saka ni cikin sha
anin ki ba, mind your own business and leave me alone
Ya ja motar suka cigaba da tafiya Amani na gayawa kanta ta gara ta canza taku, tunda har kuka yana karya zuciyar sa ya saurare ta, ko baya so, ya bata amsa ko yaki Allah to zata rage izza tunda ta lura izzar ta ke tunzura shi ya ki sauraron ta.

Tabbas yau ta gamu da wani sabon mutum a cikin rayuwar ta, wanda bata taba ganin mai hali irin nasa ba.

Bawan Allah ko wa kake da suna?

Na yi rantsuwa ba ta hanyar banza zan kashe kudin nan ba, kawai bana so Daddy na ya san da fitar su
Ta sassauta murya ta ce
kayi min wannan alfarmar, ba don ni ba ba don hali na ba
Mukhtar ya yi mata kallon kin ishe ni haka kafin yace
zan yi miki only in kin gaya min gaskiyar ko me zaki yi da kudin nan, bana backing munafurci da rashin gaskiya komai kankantar su, in kina da gaskiya ba zaki nemi a boyewa mahaifin ki wani abu da zaki aikata ba
Amani ta share ido da bayan hannun ta ta marairaice, sai ta dan bashi tausayi, ta ce
wallahi ina da gaskiya ta, trust me, kuma ta hanya mai kyau zan yi amfani da su yanda ba zai gane ba, don bai san irin ciwon da na ke ji in naga kowa a jikin uwar sa ba
Ta cigaba da cewa
Malam COO (Chief Operating Officer) ni din ban taba ganin uwa ta ba sai a hoto, ban rasa komai ba amma ina so in je gare ta, ba don kuma na raina kulawar Daddy na a kaina ba, sai don kowannen su matsayin sa daban a gare ni
Zuciyar Mukhtar ta dan yi laushi, laushin da shi kan sa bai zaci tana da shi ba, yafi zaton zuciyar sa tafi dutse tauri amma ashe akwai sauran tausayi a cikin ta, akalla ya gamsu, tunda ba shaye-shaye zata yi da kudin ba don tafi masa kama da masu banka kwaya, yace
I will think over it.

But remember always zaman Alhaji nake ba zaman wata Amani ba!

Maganar shi ta karshe bata yi mata dadi ba.

Ta yi kuta ta ce
kai a rayuwar ka baka da humanity ne? baka da concern?

Baka da sabo da mutane kuma baka daukar kowa da muhimmanci sai Daddy?

Ya murmusa kadan, har beauty point din fuskar sa ya lotsa ciki sosai yace
ban san ta ba humanity din, concern kuwa ko ma
anar ta ban sani ba, mai yuwuwa sanda ake rabon su ni ina Diffa.

Kin san ni dan Diffa ne, Diffa region, ta kasar Nijar
Amani ta kulu iya kuluwa, ta yaya ba zai dauki abinda ta gaya masa da muhimmanci ba bayan sirrin ta ne da bai kamata ma ta gaya masa ba?

Zai bi ta da bakar magana bayan ta bude masa sirrin ta?

Maganar mahaifiyar ta fa take masa, wadda bata taba gani ba, yana mata maganar wani garin su.

Daidai lokacin da suka iso tangamemen gate din gidan su Amani.

Dama bata son zuwa dauko Hajiya Rabi.

Ba tun yau ba ta fahimci matar zal wajahaini ce (mai fuska biyu) a gaban Daddy kawai take nuna kaunar ta, a bayan idon sa kuwa kashi ya fi ta daraja a gidan nan.

Shi yasa itama ta kama kan ta, sam bata shiga sha
anin Haj.

Rabi ko hanyar sassanta bata bi, ta kuma yi wa kanta alkawarin bazata bari Daddy ya sake ta ko ya san halin ta a kan ta ba, don ta gaji da aure-auren sa da ake faman kirga masa akan ta.

Mace ta karshe da Alhaji ya saka wai ita Zaibi, ta fadi maganar data tsaya mata a rai har gobe ta kasa mantawa, kuma daga kanta ne ta kudiri aniyar hana Daddy kara sakin kowacce mata duk mugun halin ta.

Gara ta bar su da halin su ta nemo tata mahaifiyar.

Cewa matar ta yi
ga gidan nan ta bar mata, karshen soyayya Alhaji ya auri Amani ya maye gurbin ta da ita
Don haka tun kafin ya gama daidaita parking ta soma kokarin bude kofar don ta fice kada ma ya ce suje dauko Hajiya Rabi tare, sai ta ji ta gadagau wato ya rufe ta automatically.

Kallon tambayar dalili Amani tayi masa.

Idanun ta fal hawaye.

Mukhy ya daure fuska sannan ya shafa sumar kan sa ya ce da ita
as a brother, zan hore ki da abu daya, duk rintsi kada ki kasance mai munafuntar mahaifin ki, domin mahaifin ki extraordinary Uba ne, musamman a kan ki, ban taba ganin uban da ke son
yar sa irin son da mahaifin ki ke yi miki ba.

Don haka bai cancanci ki boye masa komai da ya shafe ki ba.

Mai zai hana ki same shi officially ki gaya masa damuwar ki, akan son ganin Maman naki?

I
m sure yadda Alhaji ke son ki da girmama lamarin ki ba zai ki kai ki ga mahaifiyar ki ba.

Wane irin bincike ne saboda Allah har miliyan biyar?

A kasa ake hako kudin?

In gaya miki gaskiya an doki hancin ki, don an ga baki da wayau, kuma you are desperate, a kan bukatar ki, ni ki bar ni zan lallaba Alhaji ya kai ki gun Maman naki on koboless (babu ko sisin ki) ba kuma don ke ba sai saboda Alhaji ne ya haife ki.

Wani kwayan mutum guda daya da nake matukar kauna da girmamawa.

Alhaji da kan sa ya fi dacewa ya gaya miki inda take, ba sai kin bi ta karkashin kasa kin sha wahala ba
Amani ta yi ajiyar zuciya tana jin wani irin relief na zagayeta a zuciyar ta, yau Mukhy kamar ba shi ba, yana magana ne ta hanyar bata dukkan attention din sa da concern as a brother, duk da ba kallon ta yake ba wayar sa ya ke dannawa a duka maganar da yake yi, amma kuma ya dauki zancen yanzu da muhimmanci, ba don komai ba sai don ya tuno tasa UMMAMIn.

Yadda yake son Ummami da yadda yake son zama kusa da ita bai samu ba, ba don komai ba sai dalilin norms, culture and traditions irin na gidan su.

Ya yarda rashin kulawar ta a tare da shi ne duk yayi mujazar matsalolin sa a rayuwa da a yau suka saka shi garanranba a duniya.

Amani na bukatar tallafin uwa da gaske.

Musamman a kan dabi
un ta da tarbiyyar ta, kai har addinin ta ma yana bukatar gyara, in yayi duba da irin dressing din da take fita da shi da rashin kunya ga na gaba da irin tabarar data ke yi wa mahaifin ta.

Amani ta ce
I wish Daddy din zai saurare ni a kan damuwa ta irin yadda ka saurare ni yanzu, to ba zai saurare ni ba, ban san abinda ya raba su ba amma ko zancen ta baya so na yi masa, ya dauki gaba mai tsanani da mahaifiya ta yana fadin muddin na zabi zuwa gare ta to shikuma zai sallama mata ni ne
Ta share hawayen ta tace
and I love my Daddy more than everybody, saboda da shi kadai na taso, da kaunar sa gare ni na budi ido.

Ban san kowa sama da shi ba ko
yan uwan mu na Faskari sama-sama na san wasu daga cikin su, bani da wa bani da kanwa
Cikin tausayi Mukhtar yace
me yasa ba zaki neme su ba?
Chapter 10 · 0% Book details