← Book details Amani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 25

Sashe 23

Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji yana da hope na cewa, shi kadai zai iya hakuri da tilon
yar sa, mai tarin nakasu a halayya da dabi
a, shi ya sa ya damka masa ragamar rayuwar ta ta hanyar da ta fi kowacce muhimmanci ga dan adam, wato aure.

Kuma a istikharar da ya yi daren jiya shi kam bai ji yana kin al
amarin nan ba, ya dai san zai sha wahala iyakar sha a hannun Amani, tunda Allah bai halicci zuciyar ta da kaunar sa ba.

Mukhtar ya nisa, ya kira sunan Amani, ba cikin yanayin da yake mata magana da shi a baya ba, na nuna halin ko in kula da al
amarin ta.

Wannan karon akwai kulawa da dan lallashi acikin sautin sa.

Ya ce,
Ki sani cewa komai ya yi zafi ga bawa bai fi karfin Ubangiji ba.

Iyaye suna gaba da komai a rayuwar dan Adam.

Mahaifin ki ba yaron ki ba ne, ba kuma dan ki ba ne da za ki dinga yi masa duk abin da ki ka ga dama ba.

Ya kira ki kin ki amsa kiran sa, kin bar shi a damuwa, anya Amani kina son gamawa da duniya lafiya?

A hakan kuma ki ke so Allah ya ji tausayin ki ya hada ki da mahaifiyar taki?

Alhalin shi din da ya maye miki gurbin ta ba ki tsaya kin kyautata masa yadda yake kyautata miki ba?

Me ki ka dauki kan ki Amani da ki ka zabi yin fito-na-fito da mahaifin ki?

Ni da bai haifa ba na zabi in masa biyayya a kan umarnin sa, don na san ba zai ba ni matar da za ta cutar da ni ba.

Sannan yana cikin hali na rashin lafiya yanzu, wanda kyautatawa da tausasawa kadai yake bukata daga gare mu.

Yau in aka ce babu Alhaji sai kin fi kowa zama abun tausayi, ba ki ga tsuntsu ba ki ga tarko, baki rabauta daga biyayyar uba ba, sannan uwar ma ba za ki san inda za ki gan ta ba.

Na zaunar da ke na ce ki bi shi a hankali, ki bar komai a hannu na, amma ki ka yi kan gaban kan ki saboda ke ba ki da mafadi kuma ba ki yarda kina da na gaba da ke ba.

Zan iya rantsuwa da Allah kan cewa
yan damfara ki ka tura wa kudi, bayan na gaya miki kada ki tura, gaggawar ta mece ce tunda na ce ni da kaina na yi alkawarin kai ki ga mahaifiyar ki amma karkashin umarni da amincewar mahaifin ki?

Yanzu ina adireshin da ki ka sayo miliyan biyar sai ki ba ni in gani
Kuka ya kubucewa Amani, ba kukan shagwaba ta ke yi ba yau, kuka ne na kubucewar azanci da tausayin kai.

In ta ce maganganun Mukhtar ba su yi tasiri a zuciyar ta ba ta san ta yi karya.

Da gaske Daddy ya wuce komai a gare ta, kuma bai cancanci reactions din da ta ke yi mishi ba, amma zabin da ya yi mata ne ba za ta taba karba ba, domin ya kaskantata, ya sayar da ajin ta ya zubar mata da ego din ta, muddin Mukhtar zai bai wa auren ta.

Daga nan har kotun koli za ta je don neman hakkin ta a kan hakan, bazata taba yarda tayi auren kaskanci ba, auren yaron Alhaji mara asali, mai halayen da ta ki jini, wato musamman girman kai, da kin yarda a taka shi, ita kuma ta saba taka kowa da ke kasan ta, tunda ta yi kokarin riskar mahaifiyar ta don ta samu mafaka a gun ta abun ya ci tura.

Tana ta kuka tana fyace hanci da share ido da gyalen ta, Mukhtar ya ce,
Taso ki biyo ni, mahaifin ki na son ganin ki, in kuma kin ki tashi ko a ka ne zan dauke ki in kai masa ke, na rantse
A yadda ta ga idanun sa sun rikide cikin bacin rai ta san sarai zai iya aikata abin da ya furta, sai kawai ta mike, ta na so ta ce ya ba ta wuri ta canza kaya, amma ya kasa ya tsare a kofar dakin yana muzurai na ko ta wuce ko ya ciccibe ta.

To ka je zan canza kaya
.

Ta fada a turbune, fuskar kamar wani kauye wai shi Durbunde saboda turbunewa.

Mukhtar sai ya ga akwai bukatar ta canza kayan, bai kamata ta tafi har Faskari da kayan barci ba, sai ya juya yana fadin,
Na ba ki five minutes, in ban gan ki a falon Alhaji ba da jakar fita unguwa da trolley din matafiya da kayan ki da zasu yi miki a kalla kwana bakwai a ciki zan dawo.

Don tafiyar tamu ba mu san har yaushe za ta kai mu ba, tunda neman sulhu da gyara zumunci ne zai kai mu
Ya fice a dakin ya bar mata daddaddan turaren sa na sirnanawa a kofofin hancin ta.

Tana kuka tana komai ta canza kayan jikin ta, ta sanya doguwar riga sannan ta yi maza ta yayibo mayafi ta jefa kaya kala uku da man shafawa da deo spray a trolley da
yan sauran abubuwan bukatar ta.

A gurguje ta rufo dakin ta fito kada ya kara dawo mata daki, don ko turaren sa ba ta son ji, balle ganin cunkusasshiyar fuskar sa mara annuri da rashin walwala.

Sai da ya taimaka wa Alhaji ya gama kintsawa ya debar masa duk abin da zai iya bukata har nan da kwanaki bakwai kama daga magungunan sa da kayan sanyawa ya kai komai mota.

Ya dawo kenan ya tadda ita a falon na Alhaji, da jakar tafiya a gaban ta.

Alhaji na ta faman lallashin ta kamar shi ne
yar ita uban, yana gaya mata duk abin da ta ga ya yi mata soyayya ce, idan kuma har ta zabi ta bijirewa umarnin sa ta hanyar tozarta shi a idon Mukhtar, to kuwa zai yi hakuri da duk son da yake mata ya sallama ta, zai kwace komai da ya mallaka mata ya kai ta wajen mahaifiyar tata su karata.

Mukhtar ya yi kamar bai ji me Alhaji ke fada ba a karshe, ya ce,
Alhaji komai ya kammala, mota an mata full tank an kuma wanke ta sai tafiya ya rage
Allah ya yi maka albarka Mukhtar, dauki kayan ta ka sa mata a mota, jakar hannun ma karba mata
Yar murmusawa ya yi, a ran sa yana fadin, Alhaji ke kara lalata yarinyar nan, ya karba mata jakar hannunta wato ga mijin Hajiyar Faskari ko?

Ko Alhaji ba ya karba wa briefcase in za su fita balle wannan fitsararriyar.

Tana jira ya daukar mata har jakar hannu kamar yadda Alhaji ya yi masa umarni, sai kawai ta ga ya dauki trolley dinta da hannu daya ya bar falon.

Ita ta kai zuciya nesa ta dauki jakar ta rataya sannan ta turo Alhaji a kan keken sa.

Ita da Mukhtar din suka yi kici-kicin saka Alhaji a mota, ya nade keken nasa ya saka a boot din motar.

Gidan baya ta shiga ta zauna gefen Alhaji don tana ganin ta fi karfin ta jera kafada da Mukhtar a gaban mota, alhalin yana matsayin yaron Alhaji ko kuwa ta ce direban ta.

Zuciyar ta ba za ta taba ba shi wani matsayi bayan wadannan ba.

Alhaji zai yi korafin muhallin da ta zaba don zama sai gani ya yi Mukhtar ya tada motar, ko a jikin sa, shima baya so ya hada kafada da ita, ko ba komai ta kula da Alhaji a bayan motar wanda suka yi masa kujera ta musamman suka sanya mishi belt sosai.

Kamar ya san a karkashin zuciyar ta ta so ya yi magana ta gaya masa mara dadi, ta gaya masa har abada shi yaron gidan su ne, kada wani zancen aure da Alhaji ya furta ya rude shi.

Sai aka yi sa
a bai tanka mata ba, ya ja mota cikin tukin sa na nutsuwa, na kwarewa da kamala suka yi reverse, wanda ba haka ta so ba.

Mukhtar ya sa a ran sa ba zai dinga biye mata ba yanzu kamar da, saboda jiya da ya yi wa Alhaji b.p ya ga ya hau sosai.

In ta rasa wanda za ta yi wa rashin kunyar dole za ta yi shiru ta bar su su ji da abin da suka fuskanta yanzu, wato gyara tsakanin Alhaji da
yan uwan sa.

Malam Tajuddeen ya bude musu kofa tare da daga musu hannu yana fadin,
a sauka lafiya
.

Mukhtar ya dan daga masa hannu shima, sannan suka fita gate din gidan.

Sannu a hankali ya hau bisa kwalta, sannan ya soma shimfida gudu da su kamar zai tashi sama dasu, abin da ya san Amani ba ta so, wato gudu da mota musamman a babban titi irin wannan, ba
a cikin gari ba.
**** ***** ****
Suna tafe kan titin da zai shiga garin Faskari Mukhtar ya kunna karatun Alqur
ani mai tsarki ya kure a radiyon motar cikin Suratul Baqarah, duk yadda ta ke so ta yi masa korafin gudun da mota da yake yi da su albark
ar wannan karatun da ya kure sai ta kasa, ta samu kan ta da nutsuwa tana sauraron ayoyin na karshe na suratul Baqarah da taji sun mata dadi, kasancewar ita bata saba sauraren karatu ba sai music.

Mukhtar na tafe yana tambayar kan sa shin ko Amani ta taba yin islamiyya?

Balle a je ga batun sauke Alqur
ani?

Ya nisa, umh.

A lokaci guda Alhaji na tuhumar kan sa da ka sa a ran sa da sakaci mai yawa da ya yi a kan tarbiyya da kuma upbringing din Amani in general.

Ya tuna ko hizfi biyar ba ta da shi a kan ta, don tun tana karama da ya dauki wani bayerabe yake zuwa gida yana koya mata karatun Alqur
ani, da ta yi wayo ta kai munzali sai ta nuna ba ta ra
ayin koyarwar malamin.

Dole Alhaji ya sallame shi.

Daga wancan lokacin kuma Amani ba ta kara sha
awar tahfiz ba, dan wanda ta samu a gun bayeraben nan da shi ta ke karatun sallah har yau.
Chapter 23 · 0% Book details