Sashe 5
Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko a satin da wuce ya kori ma
aikata biyar daga kamfanin sa, da ya kama su da yi masa sama da fadi da wasu
yan kalilan kudade.
Bayan kuma kudaden ma bata suka yi cikin lissafi amma a hannun su.
Ya iso kofar dakin ya danna kararrawa, Alhajin ya bude masa yana lale marhabin da shi, sanye yake da farar shirt an rubuta
Fred Perry
da bakin wandon
CK Jeans
.
Dogon matashi, kakkarfa, farin ba
abzinen usli, mai wani irin sassanyan kyau, hancin sa kamar an sa ruler an ja masa shi an saka masa shi a tsakanin idanun sa, komai na halittar sa ya zauna a inda Allah Subhana ya ajiye shi, kamar shi ya zaba wa kan sa zati da kamala, ga wata lallausar suma da ta taru a saman goshin sa ta abzinawan usli, har ta dan kalmaso a kan goshin sa, ta maida shi tamkar Ba
indiyen nan mai farin jini (Shahrukh Khan).
Alhaji ya bashi kujera ya zauna suka gaisa sannan ya nade hannun riga yace ya sauko kasa su ci abinci tare.
Ko kadan rashin walwalar yaron da shan kamshin sa baya damun sa.
Kamar ba zai ci ba, amma ganin Alhajin da an sa yayi serving din su a plate guda, sai ya kasa tankwabe kulawar wannan dattijon, wanda ke ta haba-haba da shi cike da kauna, sai ya sauko kasa ya kalmashe kafafun sa, suka fara cin abincin a plate daya.
Suna ci, Alhaji Usman na hilatar shi da hira cikin dabara irin ta manya, har yaji abinda yake son ji, wato inda ya fito da kuma abinda ya kawo shi birnin Paris.
Nan yake gaya masa cewa daga wani yanki na jamhuriyyar Niger ya zo nan, ana kiran yankin nasu Diffa Region, yau watan sa uku da kammala karatun digirin sa na biyu a nan kasar, daga jami
Paris Saclay University
.
Ya gayawa Alhajin tun baya kammala masters din sa ya nemi ayyuka na wucin gadi har uku bai samu ba, kasancewar shi ba dan kasa ba, don haka zai koma Hong-Kong yanzu ya nema a can.
An ce suna bada ayyuka sosai ga
yan Afrika, shi neman na kan sa ya fito, ba yanzu zai koma gida ba.
Kasancewar a lokacin kasar Nijar na fama da matsalar durkushewar tattalin arziki babu ayyukan yi ga matasa masu ilmi kamar sa a Nijar.
Alhaji Usman ya tambaye shi ko me ya karanta da level din karatun sa duk ya gaya masa, cewa daga digirin sa har master first class ne.
Alhaji Usman became highly impressed da jin hakan, sai kawai Alhajin ya ce,
ina ma za ka iya zaman kasar Najeriya, da mun tafi tare na baka ragamar kamfani na, in ya so sai ka dinga zuwa gida kana ganin iyayen ka lokaci-lokaci, saboda ni din bani da Da namiji, sai mace tilo, ina neman mataimaki a kan harkoki na wanda zan iya ja a jiki na in sakar masa ragamar kamfani na.
Na kuma yaba da halayen ka
Mukhtar ya ce
ban taba zuwa kasar Najeriya ba Baba, amma ina jin labarin ta, kuma ina son aikin yi kwakkwara wand azan tsaya a kan sa da kafafu na, musamman wanda ya shafi kasuwancin kamfani, a nan buga-buga kawai nake babu permanent job ga wadanda ba
yan kasa ba, ni kuma ba yanzu zan koma gida ba.
Don haka zan bi ka in gwada in gani, idan naji dadin kasar, zan zauna, don bani da abun yi ko na koma Diffa.
Kuma babu wanda ke jira na a can
Cikin mamaki Alhaji Usman ya ce
ina iyayen ka?
Nan da nan fuskar Mukhtar din ta wani irin sauya, ta rine ta yi jajir abin ki da farin mutum.
Wani yanayi ya shiga na kokawa da numfashin sa da Alhaji Usman ya kasa karanta.
Shi da kan sa ya baiwa kan sa amsa da basa raye kawai.
Sai ya shiga yi musu addu
a ba tare da shi Mukhtar din ya ce masa komai a kan su ba
Amana ce ta hada mu, naji ina kaunar ka kamar dan da na haifa saboda halayen ka da suka burge ni, ina fatan wannan amanar tayi ta yado da yabanya a tarayyar mu
**** **** ****
Mafarin zuwan Mukhtar Diffa kenan gidan su Amani, tarayyar da ta zamewa Alhaji Usman sanadin alkhairori masu yawa.
Bai sakar ma Mukhtar ayyukan sa na sirri ba sai da ya cigaba da gwada shi iyakar gwadawa ta hanyar yawan aiken shi kai kudade banki, domin da farko kamfani ya kai shi, ya bashi ofis, a matsayin Chief Operating Officer (COO) ya kuma bashi gidan zama a kusa da gidan sa wanda babu nisa da kamfanin Faskari Investment cikin birnin Katsinan Dikko.
Excellent Performance din da Mukhtar Diffa ya soma nunawa daga zuwan sa ya razana kowa, domin yana zuwa ya canza akalar komai zuwa na zamani, ya kawo sababbin innovations masu tafiya da zamani na yadda za
a bunkasa hanyoyin da kamfanin ke amfani da su wajen shigo da kayayyakin da kamfanin ke shigo dasu Najeriya daga Faransa da sauran kasashen Europe irin Mexico.
Har ila yau, COO Mukhtar Diffa, ya kawo hanyoyin samun cigaba ga ma
aikata ta hanyar karawa ma
aikata sani da dabarun kasuwanci a zamanance, ta hanyar shirya (capacity building programs) iri-iri da yake shiryawa a kai-a kai ga kananan ma
aikatan Faskari.
Ya tsame masu lalaci daga ciki ya kai su kasa, ya maye gurbin su da masu hobbasar cikin su.
Ya kuma takura wa Alhaji a kan kara albashi da welfare din ma
aikata da yake kankamewa.
Kan ka ce meye wannan hakan ya sayo ma Mukhtar farin jini gun kananan ma
aikata, ya kuma kara musu himma da maida hankali, sannan ya kawo conducive working atmosphere ga dukkan ma
aikatan Faskari Investment.
Shi ba hausa ce ta ishe shi ba, amma da zuwan sa Katsina ba jimawa sabida cudanya da hausawa da ma
aikata a company, da kuma shi kan sa Alhajin da ke masa magana kullum da hausa don ya kware, a sannu bakin sa ya fara iyawa sosai, a hankali a hankali kuma accent dinsa na Francaise da abzinanci ya fara barin bakin sa sabida rashin abokin yi.
Mukhtar Diffa, ya soma rikidewa yana koma wa zallan Ba-katsine, in ka cire nannadaddiyar sumar kansa da launin jar fatar sa da ke fallasa shi, matsayin kyakkyawan Ba
abzinen mutum dan hutu kuma dan zamani, hatta hausar bakin sa kafin shekara guda ta koma ta Katsinawa.
****** ****** ******
Sanda Alhaji Usman ya kawo shi gidan tana makarantar kwana aji daya a Ulul Albaab, ya dade a gidan ma bata san da shi ba, a lokacin Alhaji bai mayar da kamfanin da sunan ta ba, so ko ta zo hutu ba wani haduwa suke ba ko a ce bata san shi ba ko da ta hange shi, don bai cika zuwa gidan ba a Kamfani yake rayuwar sa, daga gida sai ofis, Mukhtar ko aboki bai da shi, sai Malam Tajuddeen mai gadin gidan Alhajin.
Ranar da ya fara ganin ta wata asabar ce, direba ya dauko ta daga makaranta yana cikin motar Alhaji a harabar gidan yana jiran fitowar Alhajin zasu wuce duba wata gona da Alhajin ya saya a garin Bindawa, ji yayi yarinyar wadda fitowar ta Kenan daga mota tana zagin direban ta cikin daga murya wai yayi parking ba a kofar shifa falo ba, yana nufin da kafar ta zata taka har kofar falon ko yaya?
Ga zakin murya cau ga zare ido kamar tana yi wa dan ta fada, shi kuma Malam Sirajo yah au rawar jiki yana bata hakuri tare da cewa Mukhy ne yayi parking a kofar falon yana jiran fitowar Alhaji, amma duk da yadda ya kwantar da kai ya bata hakuri data fito sai da ta tsarta masa miyau a fuska ta ce
donkey, monkey, idiot!
Mukhtar na shirin fitowa ya dauke yarinyar nan da mari sai ga Alhaji ya fito hanzari yan cewa
yi hakuri Mukhy, ina jiran isowar TAFISU ne kada ta dawo bana nan an tafi dauko ta
yana daga ido kuma ya gan ta cikin uiform din ta ta doso shi da gudu, Alhaji ya bude hannu yana
Oyoyo!
Da Tafisu na
.
Ta rungume Alhaji duk da ta fara kirgen dangi ma a lokacin suka yi ta murnar su kafin Alhaji ya ce mata ta shiga ciki, ya sa an shirya mata komai, gobe sabuwar matar da auro zata tare bazatayi kadaici ba wannan hutun
.
Direban data tsartawa miyau shi ya dauko jakar ta ya shigar mata da ita bayan yasa hankici ya goge fuskar sa, a ranar kuma ya ajiye aiki a gidan su Amani.
Mukhy da Alhaji suka kama hanyar Bindawa, Mukhtar ke tukin Alhaji na gefen sa yana bashi labarin itace tilon
yar sa Amani da yake bashi labarin tana makarantar kwana, ya ce ka gan ta Tafisu akwai rigima ga kyuya, nikadai nake iya mata.
Ai komai nata na uwarta ta debo, yadda Jal
an haka Tafisu take, kullum ina godewa Allah da bata debo kannina ba
Mukhy dai tuki yake bai ce komai ba, amma a ran sa ya ce
ai gara da kamannin naka ta debo, da wannan halin nata na rashin kunya,
yar karama da ita da raina na sama da ita.
Shi bai taba ganin rashin tarbiyya irin na yau ba.
Imagine in shi ta yi wa abinda ta yiwa Malam Sirajo, wallahi sai ya mare ta, kuma daga ranar ko nawa ake biyan shi bai kara aiki a gidan su.
Basu kuma kara haduwa ba har ta koma hutu, don shi ba wani zuwa gidan yake ba sosai, idan ba Alhaji ya neme shi a gida ba, duk harkokin su a kamfani suke yin su.