← Book details Amani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 25

Sashe 6

Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya zama cewa in tazo hutu sau tari ya kan gan ta ko daga nesa ne, a harabar gidan ko a falon Alhaji, itama ta kan hango shi daga can saman balcony na saman benen ta, ko a falon Alhaji in suna ganawa ta sirri, wani lokacin ta kan shigo, in ta gan shi sai ta koma, bata taba gaishe shi ko yi masa magana ba, shi dai ko gaisuwa bata hada su tun da ya gane bata da kwalli a idon ta, sannan Alhaji baya kwabar ta, ta raina duk wani ma
aikaci na gidan, aka ce hanyar lafiya a bi ta da shekara, sosai ya kama kan sa, ko ya ganta zai bar wuri shima, don ya san zuciyar sa ba irin ta sauran ma
aikatan Alhaji bace, da suke iya shanye duk wani rainin ta da wulakancin ta saboda Alhaji.

A haka suka rayu tsayin lokaci a gidan Hon.

Usman, ko in ce tsayin shekaru, har Amani ta soma zama budurwa sosai, babu wata sanayya ko wani
cordial relationship
a tsakanin ta da Mukhy.

Tana gama sakandire ba jimawa ta samu gurbi a Jami
ar Bauchi, da taimakon Baban Hamida, suka fara karatun su ita da Hamida Hashim Balewa a ATBU, sai rayuwar ta ta koma Bauchi gabadaya, ko an yi musu hutun karshen zango ba koyaushe take zuwa Katsina ba saboda bata shiri da Haj.

Laura ko kadan, wato sabuwar amaryar gidan su matar da Alhaji ya auro a lokacin, sai tayi zaman ta gidan su Hamidah sai dai shi Alhaji da kan sa yayi ta zaryar zuwa ganin ta, don harr aba su dambe aka yi kwanaki tuni Alhaji ya yanke shawarar sallamar Haj.

Laura don itama kamrar sauran, ta kasa da Amani sabida rashin tarbiyyar ta.

A haka Amani ta kammala jami
a ta yi hidimar kasa duk a Bauchi din.

Daga lokacin ne Alhaji ya maida
Faskari Investment
ya koma da suna
Amani Faskari Investment
ya maida hakkin mallakar komai nasa da sunan ta.
**** **** ****
Ta haura sama inda dakin ta yake tana gaya wa kan ta in har Daddy ya dage lallai sai Mukhtar ne zai taimaka mata wajen gudanar da tafiyar shagon ta, to kuwa zata hakura da shagon.

Ita ta san kasuwanci ai ba sai mutum ya karanta shi ba ne zai iya tafiyar da abun sa, karatun ta na
International Relation and Diplomacy
ya ishe ta komai, kawai Daddy ya bar ta ya ga iyawar ta, ya daina underestimating din ta don tana mace, bata bukatar taimakon Mukhtar a dukkan sha
anonin ta.

Shi kuma Daddy abun nasa kamar wanda aka camfa, ko aka sihirce, from all indications, baya samun gamsuwa idan ba ya hada sha
anin kasuwancin sa kowanne iri ne da Mukhtar din ba.

Idan Mukhtar yana tsaye akan abu, ji yake kamar shi da kan sa ne ya tsaya ya kula da abun sa.

Tsabar yarda da aminci.

Don haka ta san ko me zata fada a yanzu ba zai yi tasiri ba, kowanne irin bore zata yi Daddy ba zai saurare ta ba, in dai a kan kada Mukhtar ya saka mata hannu ne a ragamar Boutique din ta.

Tunda shi Ya riga ya yi amanna cewa komai nasa sai Mukhtar ya saka hannu ne zai tafi dai-dai.

To ita bata son taimakon nasa a kan komai nata, a bar ta tayi irin tata iyawar da kokarin, a boko-akida irin nata
what man can do, a woman can do better
Ta shaki iska cikin fushi sannan ta furzar ta bakin ta.

Ba wanda zata gaya wa damuwar ta a kan mutumin nan ya fahimce ta sai Hamida Balewa.

Aminiya daya kwal da bata da tamkar ta, duk da nisan gari da ya raba su yanzu, kullum suna tare a waya, hakannan suna ziyartar juna lokaci lokaci su yi kwanaki a gidajen juna, dama an ce garin masoyi ba shi da nisa.

Zamantowar Hamida a Bauchi Amani a Katsina bai rage komai na karfin amincin dake tsakanin su ba.

Har abinda ba zata iya gaya wa Daddy ba tana iya gaya wa Hamida kasancewar bata da
yar uwa mace, musamman matsalar matar sa ta yanzu wato Hajiya Rabi idan ta saka ta gaba.

Ta san Hamida mai fadin gaskiya ce a kullum, kuma mai yi wa kowa adalci.

Duk da ra
ayin su baya zuwa daya.

Amma zata yi adalci tsakanin ta da Daddy a kan mutumin nan, ta kuma bata shawara ta gaskiya na yadda zata yi da zaman sa a gidan su.

Wani banbanci dake takanin ta da Hamida shine an ce sai hali ya zo daya ake abota, amma ita Hamida kowa dake tare da su ya san ba halin su daya ba, haduwar jini ce ta mikar da abotar su domin Hamida Hashim, bata da girma kai, bata da dagawa sannan bata raina kowa duk da kasancewar ta diyar tsohon gwamna.

Wayar ta ta dauka ta kira Hamida Balewa tana tsaye daga can saman balcony na sassan ta dake saman gidan su.

Daga inda take tsaye tana iya hango duk abinda ke faruwa a yalwatacciyar harabar gidan nasu mai cike da korran shuke-shuke.

Yaya aka yi mutuniyas?

Kwana biyu ban ji duriyar ki ba, halan kin fara shirin tafiya Sierra Leone dinne?

Hamida Balewa, ta fada bayan ta daga kiran aminiyar tata.

Amani ta yi tsaki tana fadin
Hamdy, ba ta wannan nake ba tukunna.

Don wanda ke min binciken inda Maman nawa take ta karkashin kasa ya bukaci wasu kudade masu yawa a hannu na, wadanda ban san yadda zan fidda su ba a yanzu haka, ina nufin, ba zan iya fidda su ba tare da shaidanin nan ya ga alert ba, kuma tabbas zai gayawa Daddy a sanda ya gani din, idan kuma ya tambaye ni me nayi dasu bani da amsa don ya sha ce min in na zabi bin Mama na ko neman inda take, to tabbas in manta cewa ya haife ni, zai bar mata ni a kowanne hali na same ta, zai yafe soyayyar da yake yi mun komai girmanta, tunda bai rage ni da komai ba na duka soyayyar UWA da UBA.

Actually har gobe ban san me yayi zafi haka tsakanin Daddy da Mama na ba, kuma ina so in sani, sama da komai ina so in ga uwata nima kamar kowa in ji dumin jikin ta tunda dai tana raye
Amani ta soma hawaye tana fadin
Hamdy, I want to see my Mum, ko sau daya ne a rayuwa ta, koda a bukka take rayuwa a Sierra Leone din zan je gare ta zan kuma iya zama da ita, ba kuma don Daddy ya min komai ba, ko ya gaza da kulawa da ni ta wani bangaren, ba kuma don bana son cigaba da zama da mahaifi na ba, a
ah, shaukin soyayyar uwa da ban taba samu ba ke diba na, so nake kawai in gan ta a gefe na, nima in san cewa uwa da uba ne suka haife ni ba Uba namiji shi kadai ba
Hamida ta ce
Da yardar Allah zamu je ga Mama bada jimawa ba duk inda take, amma bisa yarda da amincewar Daddy.

Amma kamar yaya kike nufi in kika fidda kudi masu yawa daga account dinki Mukhtar din Daddyn ki zai ga alert?

Amani ta numfasa tana fadin
ba zaki gane ba Hamdy, Daddy na wani irin SMART ne, mutane ne ke ganin yana sangarta ni, yana min duk abinda nake so, baya hada kaunata data kowa haka babu abunda ya kai ni muhimmmanci a gun sa.

Eh, hakane da gaske amma kuma bai yarda da sakin rayuwata sakaka in yi abunda na ga dama ba, musamman bayan haduwar sa da shaidanin mataimakin nan nasa, kullum sai kin gan shi da sababbin dabaru na kiyaye dukiyar sa.

Zancen dana ke miki yanzu ko me nake so Daddy zai min, amma dole yaron nan ya sani, kuma yana saka ido sosai akai na da abinda nake kashewa kullum ranar Allah ta hanyar wannan fitinannen yaron, mai kwakwalwar huda-huda da ya hada account dina da lambar wayar sa (corporate account).

Wallahi Hamdy na tsane shi bana ko son ganin shi, ba don komai ba sai don yadda Daddy ya daukake shi yake girmama shi, yake fifita shi da daukaka sha
anin sa a kan kowa a gidan nan yanzu.

Karo na farko kenan dana kasa samun abinda nake so a gun Daddy; wato yaki yi min abunda nake so kamar koyaushe na bukaci ya kori ma
aikacin da bai yi min ba, wannan karon ya nuna min bai iya rayuwa sai da wannan mutumin, ya shiga gabana da yawa a gun Daddy Hamdy, ko asiri yayi masa ni ban sani ba, I
m extremely jealous of him!

Hamida ta soma dariya, dariyar da ta kara kular da Amani don ita tsakanin ta da Allah take fada mata damuwar ta, damuwar da tafi kowacce girma yanzu a gun Amani wato zaman MUKHTAR DIFFA tare da mahaifin ta Hon.

Usman, Hamida ta hadiye dariyar ta jin Amani na kwafa, tana fadin
Amani ki taka a sannu fa, ki bi abin a hankali, you are complaining too much about this guy, Kaman kina
exaggerating
abun ma, in ban manta ba duk ranar da kika kira ni complain din sa kike fara yi min, baki saka comma baki saka full stop, anya?

Baki fa san inda rana zata fadi ba, shaaah!

This dislike and hatered you have on him are beyond my understanding (kiyayyar ki a kan sa ta yi yawa har ta wuce fahimta ta) kuma na rasa dalilin ta, ina laifin mai son Baban ka, da taimaka masa kan dukiyar sa da sha
anonin kasuwancin sa da zuciya daya irin wannan mutumin, calm, cool and reserve da shi?
Chapter 6 · 0% Book details