← Book details Amani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 25

Sashe 21

Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amani ta yi maza ta ce,
kada ki daure ni da jijiyoyin jiki na.

Ai hakkin sa ne ya so ni ya kula da ni, amma banda auren dole.

Da ne Daddy yake so na Hamida, yake kauna ta, yake tattalin farin ciki na da gudun bacin rai na amma banda yanzu.

Idan har zaki lura da kyau zaki gane Mukhtar kadai yake so yanzu, tunda har yana fadin bai iya hada jinin jikokin sa da na kowa sai nashi
Ta sake rushewa da kuka, ta ce,
Hamdy, ina cikin tashin hankalin da Allah kadai zai iya fidda ni.

Tunda har Daddy ya yi wannan tunanin.

Kin sani na ki jinin mutumin nan da duk abin da ya shafe shi, tun yanzu sai abin da ya ce ma Daddy, ina ga ya zama son inlaw din sa ko ya haifa masa jikokin da baya da su?

Ai shikenan kuma Daddy cewa zai yi ba ni ya haifa ba shi ya haifa
Hamida na ta guntse dariya, ta ce,
Fisabilillahi Habeebty me ye abun tashin hankali a wannan abun arziki?

Cewa nake da tsoho zai aura miki sa
an sa?

Da ki ka yi hakuri kika fawwalawa Allah kika kuma bashi zabi, nima kuma nayi ta taya ki da addu
a ba gashi Allah ya amsa ya dube mu ba?

Shi da kan sa Daddyn ya fasa ba tareda rayuka sun baci ba, ya zabo yaro santalele ya baki, son kowa, yaro sabon jini mai ilmi da nagarta, kuma mafi soyuwa a zuciyar sa?

Ai kawai Amani ki manta da wata kiyayyar ki maras hujja, maras madafa maras dalili face envy dake damun ki a kan sa, ki bawa Mukhtar dama ki san ko shi waye a wannan fannin, ta hanyar yi wa mahaifin ki biyayya.

This man is a treasure!

Hamida ta karasa fadi kasa-kasa ba tare da ta san lokacin da kalaman suka fito ba, tana jin dan wani kishi-kishi a ran ta.

Domin tun ganin ta da Mukhtar na farko ya tsaya mata a rai, ya kuma shiga zuciyar ta.

Har Allah-Allah ta ke Amani ta kira ta ta bata complain din sa don ita haka nan abun yana saka ta nishadi.

Wato tana son hirar Mukhy da Amani ke yawan yi mata duk da cewa bata arziki bace.

Amma daga ranar yau insha Allahu ba za ta kara saka komai a ran ta a kan Mukhtar ba, sai fatan daidaita tsakanin sa da sahibar ta.

A tata fahimtar sun yi bala
in dacewa da juna, kuma ita ma kamar Alhajin tana ganin ba wanda ya dace da Amani sai shi, ba kowa ne zai iya auren Amani ya kuma jure zama da ita ba.

Sai mai jan wuya.

Gara shi Mukhtar din, tunda ya san mutuncin mahaifin ta, mai yiwuwa kuma ya san duka halayen ta tunda ba yau suke tare ba.

Don haka zai iya hakuri da jure zama da ita.

Ban gane me ki ke kokarin fada min ba Hamida?

Hamida ta ce,
Eh, ina nufin Mukhtar is a treasure ga duk macen da tayi sa
ar samun sa a matsayin miji kuma abokin rayuwa, he
s a rare gem, sannan gashi mutum na musamman a halayya da dabi
a mai dauke da dukkan attributes na cikar mazantaka.

Ina nufin. mutum ne daya cikin dubu, wanda kafin ki samu kamar sa a wannan zamanin sai an tona.

Kamata ya yi ki gode wa Baban ki
for giving you this treasure
.

Amani ta yi maza ta katse ta da cewa,
Ai sai ki zo ke a ba shi ke sadakar.

Na yi rantsuwa duk yadda zan yi in fidda kudin nan daga yau zuwa gobe zan yi in komawa mai binciken nan ya ba ni adireshi da lambar wayar Mama na.

Na rantse guduwa zan yi Hamida, da in auri yaron Baba na kuma wanda ban san asalin sa ba, sannan mai mugun hali irin na Mukhtar gara na gudu gun uwa ta ko a bukka take mu rayu tare
Dama can na ki tafiya ne sabida Daddy da tunanin kaunar sa gareni, amma yanzu na tabbata wallahi ya fi son bare a kaina
Hamida ta kama kai, cikin cewa,
Ki daina rantsewa Amani, Uban da ya haife ka baya hada kaunar ka data kowa sai dai kawaici.

Ba zan gaji da ce miki a kowanne al
amari da ya tunkaro ki, ki dinga neman zabin Allah ba, hakan shine daidai, kullum ina gaya miki haka.

Yanke hukunci cikin fushi kuskure ne babba, ki yi sallah raka
a biyu ki nemi zabin Allah ta hanyar istikhara da Annabi SAW ya koyar, idan Mukhtar alheri ne a gare ki da addinin ki, Allah ya sanyaya zuciyar ki ki karbi zabin mahaifin ki da hannu bibbiyu.

Idan babu alkhairi Allah ya sa Daddy ya janye da kan sa, ba tare da kin bata da mahaifin ki ba
Amani ta ce cikin hargagi.

Daman na san ba za ki taba bin bayana ba a nan, ke kadai ki ka rage min da zan ji sanyi daga gare ta.

Ba irin bayanin da ban miki a kan waye Mukhtar din nan ba, da rashin mutuncin da yake yi min, kamar ba a karkashi na yake ci ba.

Amma kin ki ganewa da gangan, kullum sai dai ki yabe shi, saboda farar fata da bakin gashin kan sa na rudar ki.

Insha Allahu daga yau ba zan sake kiran ki in kawo miki kuka na ba, don na san ba za ki share min hawaye ba in dai a kan Mukhtar ne.

Zan nemo mahaifiya ta da kaina in koma inda ta ke duk yanayin da zan same ta, na san ita ba za ta taba yarda a yi min auren dole da wanda ba na so kuma ba zan taba so ba, har duniya ta nade
Ta kashe wayar ta tana kuka ta bar Hamida da mutuwar jiki.

Ta fara yarda da gaske Amani ba ta kaunar Mukhtar, ba yin kanta bane, tunda yau ta zabi ta koma gun mahaifiyar ta bayan duk gatan da Daddyn ta ya yi mata a rayuwa.

Yau ta zabi ta bar shi.

Ba ta san ya za ta yi ta ceto kawar ta daga fadawa fushin iyaye ba.

Ko kadan Hon.

Usman ba irin uban da
ya za su bijirewa umarnin su ba ne domin bai ragi Amani da komai ba, sai ma dai a ce soyayyar sa gare ta tayi yawa, har babu kawaici a cikin ta.

Ta yanke shawarar tahowa Katsina don ta taimaki kawar ta, don da gaske tana kan dokin fushi wanda zai iya saka ta aikata da na sani ko ya raba ta da mahaifin ta dungurungum.

A daren Hamida ta hau shirin tafiya Katsina a washegari.

Amani ta manta shaf da maganar tafiyar su Faskari, kuma ba ta san Daddyn ta ya saki Haj.

Rabi ba, ta bar gidan tun daren jiya.

Ta kwana cikin mawuyacin hali da tunanin Daddy ya daina son ta.

A daren ta cire wadannan kudade naira miliyan biyar, ba tare da tunanin komai ba, sai na son ganin mahaifiyar ta, ta tura wa mai binciken kwakkwafin ta.

Ta tura masa shaidar receipt ta layin wayar sa, tana yi tana tuna alkawarin bogi da Mukhy ya taba yi mata na cewa shi da kan sa zai nemo mata mahaifiyar ta on koboless.

Amma ya nemo din?

Tun daga lokacin har zuwa inda yau ke motsi bai kara tada zancen ba, saboda ashe sun hada baki da Daddy za su nakasta farin cikinta ta hanyar aura masa ita.

Allah Sarki rashin sani, domin kuwa ko a daren bayan ya koma gida, duk da halin da yake ciki ya rubuta cikin schedules din sa na gobe cewa daga Faskari zai saka Daddy a gaba da magiya da lallashi da ban baki irin nasa, ya yarda su wuce su kai Amani ga mahaifiyar ta.

Ba zai yarda Daddy ya yi mata aure ba da sani da sanya albarkar Innar ta ba, in har tana raye.

Wannan wani alkawari ne da ya yi wa Amani, da yake da kyakyawar niyyar cika shi, duk da rashin jituwar da ke tsakanin su.

Ba ya daukar al
amarin mahaifiya da sauki, ko don irin son da yake yi wa tasa Ummamin, wadda bai samu tata soyayyar ba shima, so he can feel for Amani, a kan rashin soyayyar uwa, wannan wani abu ne da ba ya son tunawa a yanzu.

Cikin kurakuran da yake so ya taimaka wa Alhaji ya gyara ko hakki ya ragu a kan sa, har da kai Amani ga mahaifiyar ta.

Kuma alhamdulillahi tunda ya yi sa
a Alhaji ya amince, a lokacin da nadamar abubuwan da yake aikatawa na kuskure ta zo masa.

To amma me?

A washegarin ranar da asubahi yana kunna wayar sa da alert din banki ya fara cin karo, mai nuna an cire kudi miliyan biyar, zuwa akawun din wani
Balogun Sunday
.

A take ya gane me Amani ke shirin yi, da ya tuna maganar su ta rannan a mota.

Mukhtar ya kama kai cikin mamakin taurin kan ta.

Wato ta yanke hukuncin data ke ganin ya fi mata.

Tafiya Sierra Leone ko ta halin kaka, da dai ta amince Alhaji ya hada ta rayuwa da shi, don su kula da shi tare a kan lalurar sa har muddin ran sa.

A fili ya ce.

Why Amani?

Gaggawa daga shaidan ne!

Ya kuma tabbata don ta guje wa auren sa ne da mahaifin ta ya furta ta yanke shawarar guduwa any how, ba ta kuma da inda za ta je da nisa in ba can din ba.

A take ya kira Alhaji, wanda a lokacin yana sallar asubahi a kan gadon sa daga zaune kamar yadda yake yi.

Ganin kiran Mukhy a daidai wannan lokacin ya san ba lafiya ba, sai da wayar ta tsinke ya kuma idar da sallah, sannan ya kira shi da kan sa.

Alhaji ka kula da takun Amani, kada a bar ta ta fita, ka sa ta a gaba mu tafi Faskari tare da taki da ta so.

Ta fidda kudin nan da na gaya maka tana son fiddawa don a nemo mata Maman ta.

She is desperate Alhaji.

A taimaka mata.
Chapter 21 · 0% Book details