← Book details Amani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 25

Sashe 8

Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mukhtar ya dan cije lebe cikin jin takaici, ya ce
Alhaji kai ka ce min farar Brabus ta fi son hawa, kuma ita na dauko, lafiyayyar mota ce
Yayi kyau, to sai kun dawo, kada ka manta ka yi tuki a hankali bata son gudu, ku dauko Hajiya a filin jirgi in zaku dawo, yau zata dawo daga Umrah da zarar kun gama da boutique din sai ku je ku dauko ta, na san kafin nan jirgin nasu ya yi landing don sai bayan azahar zasu sauka
Ba tare da ya ce komai ba yasa kai ya fita daga falon.

Takaicin yadda Alhaji ke sakalta yarinyar sa ya fi komai bata masa rai.

Amma shi ya isa yace wani abu?

Shi yasa take ma mutane kallon hadarin kaji kallon kowa banza ne saboda ta san Alhaji ya daure mata gindin sakarci.

Mukhtar Yafi karfin mintuna sittin zaune cikin motar yana jiran saukowar
yar mulki Amani, har aka rufa awa guda da rabi babu Amani ko inuwar ta, tun yana duba rantsatstsen agogon hannun sa
swatch' dama na motar as well, har ya gaji ya kishingida a kujerar direba, ya ware sautin radiyon motar yana sauraren waqar mutumin sa mai debe masa kewa a duk lokacin da yake tuki, wato fasihin mawakin nan Ba-sudane
Mahmoud AbdoulAzeez
.

A rayuwar sa ba abinda ya tsana irin jira, to amma ya zai yi?

Umarnin Alhaji ne, kuma in an bi salsala Amani itace kamar second Boss din sa bayan Alhaji.

Dole yayi zaman jiran ta a mota, ta shanya shi iya yadda ta ga dama.

Tun lokaci na farko da suka fara haduwa da Amani da ya fahimci dabi
un ta na sangartattu ne kuma bata ganin kan kowa da gashi yake taka-tsan-tsan da shiga sha
anin ta, yake kokarin kaucema haduwar su a yawancin lokuta, in kuma ta kure sun hadun baya yarda ya yi mata kallo na biyu, sabida yadda ta ke masa kwarjini da sanya shi faduwar gaba.

Ga harara kala_kala da yake sha daga kyawawan idanun ta.

Maigadin gidan Hon.

Usman wanda tasu ta zo daya wato Malam Tajuddeen Bafillace, ya sha yi masa fatawar cewa,
muddin kana son zaman lafiya da Alhaji, muddin kana son tafiyar ku tayi tsaho, muddin kana son fadar ka ta fadada a wurin sa kuma tauraruwar ka ta cigaba da haskawa a idanun sa, to ka kyautatawa mara kunyar
yar nan tasa mai soyayyun idanu a tsakar ka
Shima ya yarda da hakan don idan ya zauna da Alhaji na minti biyar to hirar sa ta mintina uku cikin biyar din a kan tilon 'yar sa Amani ne da irin tanade
tanaden da yake yi mata a rayuwa don baya so ko bayan ran sa ta sha wahala ko ta nemi wani abu ta rasa tunda bata samu soyayyar Uwa data dangi ba.

A irin haka watarana ya taba gaya masa cewa ya gina mata estates har guda biyu ya kuma mallaka mata su da sunan ta, karkashin idanun lauyoyin sa a cikin Birnin Katsina da babban birni, Abuja.

Watau AMANI FASKARI HOUSING ESTATES.

Wadanda dukkansu ya zub
a tenants 'yan haya duk shekara suna biyan Amani miliyoyin da shi kan sa bai san zai same su a jikin gidajen ba.

Hakan ya sa dole ya bude mata hannun jari a kasar Mexico.

Mukhtar ya kan yi mamaki a cikin ran sa, mugun mamaki don bai san ana haka ba, wai uba ne ke kaunar dan da ya haifa har haka!

Wasu lokutan abun ya bashi sha'awa ko ya burge shi, don bai taso ya ga ana yin hakan a gidan su ba.

Bai san dadin kaunar Iyaye ba.

A nasu gidan ba'a san komai ba sai uwar riko sai 'yan ubanci, kishi tsakanin iyayen su mata, burin gado da horo mai tsanani da sunan tarbiyya, wannan itace rayuwar da ya taso ya budi ido ya ga ana yi a gidan su, wadda karfi da yaji ta koya masa zama independent.

Shi ko alfarmar gaisawa da nasa mahaifin ba ya samu a sanda yake tare da shi, yana raye ba wai ya mutu ba kuma suna cikin gida daya.

Amma sai ya yi wata biyar suna gidan da shi bai saka shi a idanun sa ba.

Ko fuskar sa baya samun alfarmar gani.

Wannan dan tunanin da ya mika a zaune, yasa kyakkyawar fuskar sa yin jajir, ta rikide zuwa yanayin ta na tun fil azal da aka san shi da shi wato yanayin sa na rashin walwala da kwantaccen bacin rai, irin bacin ran nan mai kwanciya a kasan idanun mutum, ya sauya ainahin kalar su zuwa brown, ya nuna zahirin rudanin da ke cikin zuciyar dan Adam.

Wanda a duk lokacin da ya tuna mahaifin sa ko ahalin sa hakan ce ke faruwa da shi, ya ji yana son kara nesanta kan sa da Diffa many more miles away!

If possible, har fiye da nisan da yayi da gida a yanzu, don Najeriya ba nisa da Nijar, zai fi son ya tafi can karshen duniya wato kasar China birnin Hong-Kong ya yi rayuwar sa a can.

Matsalar guda daya ce yana jin dadin zama da Alhaji Usman don soyayyar Uba yake nuna masa irin wadda bai san da ita ba, bai san irin ta na existing ba.

Shi kan sa yana mamakin soyayyar Alhajin gare shi a matsayin sa na bare a gare shi.

Ba don haka ba da ya kara lulukawa cikin duniya ya kafa rayuwar sa a can.

Dagowar nan da zai yi da zummar fita daga motar don zaman ya fara gundurar sa ya hangota tana takowa cikin rangajin ta na halitta, tamkar reshen bishiyar da iska ke kadawa ko kuwa Dawisun da ya baza adon halitttar sa yake tafiyar takama a doron kasa, sai kayi tsammanin beauty contest zata tafi.

Ta yi kyau ba dan kadan ba cikin wani material lace kalar ja da ratsin baki, an yi mata dinkin riga da siket wanda aka tsaga kafar sa ta baya, babu mayafin arziki a jikin ta baya ga wani rakani gantalin cantitly sai daurin kai da ta kalmasa gwanin sha
awa da dankwalin kayan kai bazaka ce ta hada jinsi da hausawa ba.

In da abinda yafi bakanta masa rai a dabi
un ta bai wuce rashin daukar mayafi da lullubi da muhimmanci ba, bai taba ganin ta da lullubi a kan ta ba balle a kai ga zacen hijabi ba.

Amma shi waye da ya isa ya yi mata magana a kai?

Zai iya yi wa Baban ta ya yi mata, amma ya lura Baban ma bashi da katabus a kan ta, tamkar itace uban shine
yar, babban abinda yasa ya tsani Amani kenan.

Duk halayen ta na sangarta, rashin ilmin zamantakewa da rashin sanin addini basa gaban sa, don ya san masu iya gyaruwa ne in ta samu uwa ko abokin rayuwa nagari, ba irin Hajiya Rabi ba uwar gantali uwar bisa titi wadda mijin ma baya gabanta irin kasuwancin ta da yadda zatayi ya bata kudi kullum, amma rashin girmama mahaifin nan nata da bata yi ko ta wajen magana yasa ya sallama mata, yana roka mata shiriya a kasan ran sa, don ya lura girman hannun namiji ce.

Irin su Amani suna abu bisa kuskure ne ba tare da sun san cewa kuskure bane, saboda tun farko basu tashi ana kwabar su ko ana nuna musu girmama na gaba ba, a
ah, an raine su ne a bisa tafarkin duk abinda suke so dole su samu karkashin soyayyar iyaye masu duniya a tafin hannun su, irin mai samar da komai na bukatar rayuwa ga yaro ba tare da ya yi gumi ko ya fidda hawaye ba.

A haka ta iso motar ta tadda shi, ta tsaya tana jiran ya bude ya fito ya bude mata yadda direbobin ta ke yi cikin rawar jiki, don da kunnen sa ai yaji Daddy ya ce daga yau shi zai dinga tuka ta which means yana matsayin sabon direban ta kenan.

Amma Mukhtar sunkuyar da kan sa yayi, kamar bai san da tsayuwar ta a wurin ba ya dukufa danne- danne cikin tsaleliyar wayar hannun sa amma fa shi kan sa bai san me yake dannawa ba, saboda kwarjinin Amani mai bi har cikin bargon sa.

Hey!

Baka ganin mutane sun iso ne?

Ko makaho ne kai?

Mukhtar ya dago cikin slow motion ya zuba mata fusatattun idanun sa masu kama da an diga zaiba a cikin su.

Nan da nan Amani ta daburce, bata san sanda ta bude kofar motar ta shige ba.

Ta kuma rufe kofar motar da karfi.

Ko gama rufe kofar motar bata yi ba ya ja motar, saura kadan ta rufe da kafafun ta.

Wata irin shakkar Mukhtar ta soma shigar Amani, domin bazata iya fassara al
amuran data hango fal cikin idanun sa ba. idanun cike suke fal da abubuwan da shi kadai ya san su, ga tarin damuwa da fushi da rashin walwala, sannan tuki yake amma ko kallo bata ishe shi ba.

A rayuwa bata taba haduwa da namijin da bai yi mata kallon kwal uwar daka ba koko kallon kin yiwa sauran mata zarrah idan ta yi kwalliya sai shi wannan ba
abzinen.

Koda take ce ma Daddy bata son sunan TA-FISU tana fada ne kawai, amma fa tana son sunan, domin yana kara mata alfahari da kyawun surar ta mai ruda
ya maza, wani lokacin har mata
yan uwan ta (will not keep wishing they were like her).

Yau ga ta ga namijin da bai yi mata kallo na biyu a duniya ba, ta saci kallon kan ta kadan, to kyawunta ne bai ishe shi daga ido ya kalla bane ko kuwa kwalliyar data cancada bata kai ta kawo bane?

Ko kuwa shi din ma YA FI SAURAN MAZA ne?

Kwafa tayi tace cikin
yar rawar murya
Malam ka rage gudu, ba
a gudu da ni a mota, I think Daddy ya gaya maka, drive with care
.

Yayi fumfurus kaman bai ji ta ba, maimakon hakan sai ma karawa motar sa wuta da yayi yana fadi cikin ran sa
ai ni ba Daddyn naki bane, Mukhtar nake
Amani tayi kyacci, kamar ta ji me yake fadi a ran sa.
Chapter 8 · 0% Book details