← Book details Amani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 25

Sashe 15

Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bakin Alhaji ya karkace baya iya magana amma kwarai ya ke so ya gayawa Mukhy maganganu da yawa masu matukar muhimmanci ciki har da son ya kira masa Alhaji Sadi Talle a waya don ya warware yarjejeniyar su.

Ya hakura da kujerar gwamnan, yanzu ta lafiyar sa yake, zai baiwa Amani dama ta koma karatun da ta ke so a Jami
ar da ta ke mafarkin zuwa wato Queen Mary University of London har Allah ya bashi lafiya idan ciwon sa na tashi ne.

Idan kuma ba na tashi bane zai yi kokari ya cika umarnin da zuciyar sa ke bashi akan rayuwar Amani dungurungum, wadda yake ganin shine kadai mafita ga rayuwar ta da tasa!

Wadda ba zai taba bari ta rushe ta hanyar fadawa hannun mijin da ba zai rike masa ita da so da kauna da amana ba, da kuma kiyaye mata dukiyar da ya karar da shekarun rayuwar sa yana tara mata ta hanyoyi daban daban na yaki halak da yaki haram, duk don ta ji dadi kada ta sha wahalar duniya.

Wanda ta kowacce fuska ya san Alhaji Sadi Talle bai cikin wannan tsarin na rukunin mutanen da ya ke yi wa rayuwar Amani wannan tanadi.

To wa ya dace?

Zuciyar sa a take ta halarto masa da kyakkyawar amsa cewa ba wanda ya dace da zama mijin Amani wanda zai cika dukkan wadannan attributes din da yake so a tare da mijin Amani, ya zame mata garkuwa kuma mijin marainiya, ya tallafi dukiyar ta da gaskiya, ya kuma saita dabi
u da tarbiyyar ta da bai samu damar yi ba sabida tasirin son da yake mata kamar Mukhy din sa.

Wato yaron sa kuma mataimakin sa Mukhtar Diffa.
**** ****** ****
Kamar yadda yake ga cutar stroke saidai a ji sauki ba dai a warke sumul kalau gaba daya a lokaci guda ba, to hakan ce ta faru da Alhaji Usman Faskari da aka fi sani da Hon.

Faskari.

Yau satin su guda kenan a asibitin.

Ya ji sauki a cikin jikin sa don yana gane duk wanda ke kan sa ya kuma fara magana amma bata fita sosai, yana zama in an jinginar da shi a jikin filo, daga baya Mukhtar ya samu hanyar da zai dinga jin abinda ke ran Alhaji, wato ta hanyar rubutu da hannun sa mai lafiya don ba
a iya gane abinda yake fada.

Mukhy yayi sallama ya shigo dakin asibitin da Alhaji ke jinya hannayen sa rike da ledoji na sayayyar abinci da yayo musu, a kalla likita ya ce zasu yi wata guda anan kafin a basu sallama, Amani dake zaune dai- dai kan Alhaji ko ta amsa sallamar tasa.

Ta maida hankalin ta ga hirar da ya samu tana yi wa Alhaji cikin kunnen sa.

Wannan abu bai yi wa Alhaji dadi ba, yayi burun-burun din maganar sa duka basu gane me ya ce ba amma Amani ta gane fada yake mata kan kin amsa sallamar Mukhtar, tayi mirsisi kamar bata gane me Alhaji ke nufi ba, sai Mukhtar ya ajiye ledojin da ya shigo da su akan bed side, daya a gaban Amani, ya karasa gaban Alhaji ya kama hannun sa yana tambayar sa kome yake son cewa?

Alhaji yayi masa alama da ya bashi biro, Mukhtar ya dauko jotar da suke magana ya bashi tare da biro, Alhaji yayi rubutu ya mikawa Amani, da ta karanta zumburo baki tayi don Alhaji cewa ya yi bai ji dadi ba da bata amsa sallamar Mukhtar ba, amsa sallama ga musulmi wajibi ne.

Ta ce
to Daddy in dai amsa sallamar wannan mutumin ce zan shekara ban amsa ba, tunda shima ba ya amsa tawa
.

Mukhtar yayi dan murmushin da ya kara masa kyau, ya matsa gaban Alhaji yace
Alhaji ka ga kuma ni sayayya ma na yo mana har da ita, wai ni mai kanwa, amma ko nagode na tabbata ba zata ce ba
.

Amani tayi maza ta ce
Daddy ka fada masa kada ma ya kara sayo komai da ni, kada ya kara alaqanta ni da shi, bamu hada jini ba bamu hada komai ba, idan ina son abu na san inda zan je na sayo ba shi kadai ya san hanya a garin nan ba
Mukhtar ya ce a ran sa
kin yi da dan halak
.

Amma saboda ganin damuwar da ke kan fuskar Alhaji sai bai tanka mata ba, amma ya ji haushi sosai da wannan gorin nata na basu hada jini ba basu hada komai ba, dama kullum ta tashi rashin mutuncin ta ta kance masa dan karo, ai Alhaji ba uban sa bane.

Sayayyar kayan ciye-ciyen snacks din McDonalds da ya yo mata da ya lura su take son ci kullum, bata da cin abinci sai su, ya dauke ledar daga gaban ta ya kaiwa nurses din da ke kula da Alhaji, bayan duk kamshin pizza ya gama cika ta, ya tado tsohuwar yunwar cikin Amani.

Amma sabida ki-fadi irin nata tabe baki kawai tayi.

A ran ta kamar tayi kuka, a kufule ta ce
to da ka fita da abincin ni me zan ci?

Ya ce
ai na dauka kin san hanyar inda ake sayowa?

Alhaji kan sa sai da ya harare ta don yana jin duk yadda aka yi.

Mukhtar ya zauna yana cin shawarma yana korawa da sassanyan lemon tuffaha bai kara kula ta ba.

Yadda yake taunar sa gentle-gentle ma kadai abun sha
awa ne ba zaka gaji da tsayawa a gefen sa kana kallon kyakkyawan bakin Mukhtar ba.

Ta yi kwafa ta mike don ta dauro alwalar sallahr azahar, amma me?

Sai ta ga bakon watan ta ya zo, ga shi bata yo guzurin kunzugu daga gida ba.

Ta rasa yadda zata yi, ta kasa fitowa daga toilet din, don ta san bada jimawa ba zata soma staining jikin ta.

Gashi yanzu ta gama cewa kada ya kara sayo mata komai ta san hanya, kuma da kunya yanzu shi ba mijin ta ba ba komai ba ta aike shi sayen kunzugun mata.

Da taga cigaba da zaman a toilet zai sa har jinin ya soma naso, cikin shagwaba irin tata sai kawai ta fashe da kukan da ta san yana rikita Alhaji.

Daga Mukhtar har Alhaji ba wanda bai jiyo kukan nata ba, Alhaji har gaban sa sai da ya fadi don ya dauka wani mummunan abun itama ya faru da ita a toilet din, tunda shima tsautsayin da ya same shi a toilet ya same shi.

Inkiya da buruntun magana ya hau yi wa Mukhtar da hannun sa mai lafiya a kan don Allah ya duba masa ita ya ga ko menene, shi Mukhtar kunya ce ta kama shi, ta yaya zai bita toilet alhalin ba matar sa ba ce ba kuma kanwar sa ba?

Sai yanzu ya ga rashin dacewar tahowar su ba tare da sun lallaba Haj.

Rabi an taho har da ita ba, don sau da yawa in ya shigo dakin sai dai ya koma in ya ga Amani ta baza dogon sassalkan gashin kan ta tana tajewa babu mayafi a jikin ta, wannan gashi yana matukar kidima Mukhtar, ita kuma ta kasa sabawa da barin lullubi a jikin ta, kamar yadda take yi a gida a nan ma haka take rayuwar ta babu takura saidai shi ya takura ko ya rufawa kan sa asiri ya fice in ya kasa jure kallon ta, sabida dalilai na shari
ah, ita kuma idan ta zauna da lullubi duk sai ta ji ta takura don bata saba ba, shi da kansa ya gaji ya yi mata magana jiya da kakkausar murya a gaban Alhaji ya ce mata
ki dinga saka lullubi a kan ki idan ina nan.

Me yasa ke baki san duk wani ya kamata bane?

Me yasa Baki gudun fitsarin shaidanu a kan ki?

A lokacin zumbura masa baki kawai ta yi bata tanka masa ba.

Bata san cewa wannan zumbura bakin ba karamin kyau yake yi mata ba, ya kara fiddo zahirin kuruciyar ta a fili, ko ina ruwan Mukhtar da lullubin ta da zai nemi takura mata?

Lullubi zata wuni tana yi saboda shi ko me?

Shi waye dinta?

Me ye gamin ta da shi baya ga kasancewar sa ma
aikacin Baban ta wanda ya dace a ce respect yake bata?

Wannan mutum akwai wuce gona da iri in ji Amani.

Ko an gaya masa don shi ta zo jinyar?

Ko zaman sa ta ke yi a asibitin ba zaman jinyar mahaifin ta ba?

Abinda ta fada a ranta kenan ba tare da ta tsinka masa ba wai aka ce kulawa ma yabawa ce.

Mukhtar ya san yanzun ma in aka bibiya abinda take yiwa kukan nan bai kai ya kawo ba, sangartar ta ce kawai don bai ji alamar faduwa ko makamanciyar ta ba.

Alhajin ba lafiya ma ba zata bar shi ya huta da shagwabar ta ba.

Amma yadda ya ga Alhaji ya shiga damuwa sai tausayin sa ya kama shi, wannan
ya tasa ko fitinanniya, ya mike zuwa kofar toilet din ya na kwankwasawa ya ce
ke lafiya?

Ki fito menene?

Amani ta rasa abunda zata ce masa, dole ta share hawayen ta fito tana tafiya kamar a kan dan yatsan ta ko wadda kwai ya fashewa a ciki, Mukhtar ya hau kallon wannan tafiya kamar ta mai koyon tafiya ya rasa me take ciki haka?

Ita kuma bata ce masa komai ba don ta san da kunya kuma ta aike shi wannan hidimar, bayan gwaleshin data gama yi yanzunnan, sai ta dauki Jakarta ta fita da sauri don ta taimaki kanta.

Allah ya taimaketa a nan cikin asibitin ta samu akwai pharmacy, ta sayo pad ta dawo ta sake shigewa toilet wannan karon da gudu-gudu ta rufe, bata ko kula tambayar da yake yi mata ba daga inda yake tsaye harde da hannuwa a kirji.

Are you okay?

Tayi masa banza.

Ba karamin haushi ta bashi ba da share shin nan data yi, ya kudire a ran sa bazai kara shiga shirgin ta ba har su koma gida.
Chapter 15 · 0% Book details