← Book details Amani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 25

Sashe 11

Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dangi da kike gani suna da matukar muhimmanci a rayuwar mutum, musamman ke da kike mace, daya tal a wurin iyayen ki, babu dan uwa babu
yar uwa, it is your duty ki nemi dukkan su ki gyara gurbin rashin zumuncin dake tsakanin ku don hakika kina bukatar su, amma karkashin yardar mahaifin ki, don
t ever try to hide anything from him no matter how bitter, ba abunda lallashi da ban baki ga iyaye bazai sa su yi maka ba
Jikin Amani yayi sanyi kadan, don ta sani bata lallashin Baban ta sam kullum sai rigima da rikici in tana son ya yi mata abu dole ya yi, a kan zuwa gun maman ta ne kawai da korar Mukhy daga gareshi kawai ya taba turje mata, tace cikin murya mai ban tausayi,
ka ce zaka nemo min Mama na?

Mukhtar ya ji wani iri a jikin sa da yadda tayi maganar murya na shaking, ya bude mata kofar yace cikin basarwa
idan na lallashi Alhaji ya yarda ki je din, ni da kai na zan nemo ta, zan kuma kai ki duk inda take
Amani ta fita tana dan murmushi, a ran ta tana fadin
ashe dai yana da dan kirki ko yaya ne, ga taushin murya, ga jan class, fuskar ce dai bata taba canzawa daga yanayin ta na rashin annuri da bacin rai.

Tamkar wanda kullum ake yi wa mummunar bushara ko ake yankan naman jikin sa
Bai tsaya ta gama bacewa ba ya ja motar sa ya nufi airport don cika daya umarnin na Alhaji.

Wato dauko matar sa.

Ya dauko Hajiya Rabi suka kamo hanyar gida, a hanya tana ta mitar an bar ta a shanye a filin jirgi, ba
a zo daukar ta da wuri ba, mota ba tasa ba amma ya tafi yawon banza da ita yana kwambo a cikin gari gurin
yammata, idan yana ikon sa da jin kan sa ya dinga tsayawa iya kan Alhajin da ya kawo shi ya kuma daure masa gindi yana baza iko a gidan mutane, kada ya kuskura ya shiga gonar ta.

Ita warki ce daidai kugun kowa yanzun nan zata yi maganin mutum, ko Amani bata isa ta shanyata ba balle shi wani banza a banza.

Mukhtar ya sunkuyar da kai yana jin ciwo a cikin ran sa, yau wata wadda bata ko kai matsayin mai gugar takalmin sa ba ke zagin sa haka, wai kwambo!

Duk ba komi ya janyo masa ba sai zabar barin gida da independent life, an ce kuma a kowanne neman halal akwai challenges, ya cigaba da tuki bai ce mata komai ba.

Ba tun yau ba ba sa ga maciji da Hajiya Rabi, ta fannin ta ba don komai bane sai don son da ta lura Alhaji na masa.

Daga Amani sai shi a wadanda bata so ta bude ido ta gani a gidan nan, amma fa bata taba nuna hakan a gaban Alhaji ba.

Kullum nuna masa take tana kula da Amani irin kulawar da uwa take yi wa dan ta, tana kuma son wannan yaro nasa mai hankali da amana da kullum yake yabo a gaban kowa.

Shi kuwa Mukhtar ya san wacece Haj.

Rabi sanin da ko Alhaji bai yi mata ba, shiyasa kawai ya ji baya son matar, wato ya san tana dan taba yawon barbada a waje don ba sau daya ba ba sau biyu ba ya taba ganin ta a hotels daban daban tare da wani mutum.

Kuma har kofar gidan mutumin ya sha kawo ta.

Duk da ba zai ce ga hakikanin abinda suke yi tare ba jikin sa yana bashi tarayyar banza ce don Alhaji yana da ciwon suga mai hana lafiyar auratayya.

Yana ajiye ta ya juya ya koma Company, akwai muhimmin aikin da zai yi wa Alhaji amma tun shigar sa office din sa sai ya kasa zaune ya kasa tsaye.

Mukhtar Diffa, ya hau safah da marwah, hannanyen sa biyu zube cikin aljihun farar shaddar da ke jikin sa.

Ya rasa abinda ke tsaye a wuyan sa ya ki wucewa.

Ya rasa meye ya tsaya masa a rai.

Sai da yayi tsam da ran sa ya fafimci ba komai bane kukan Amani yake tunawa da shagwabar ta, da fyatar hanci cikin yanayin sakalcin ta.

Sai ya ji wasu sassa na jikin sa suna respoding.

Zuciyar sa na vibrating.

Ya tuna matsananciyar damuwar da ke kwance kan kyakkyawar fuskar ta a kan son ganin mahaifiyar ta, sai ta kwadaita masa son ganin tasa Ummamin shima, kwarai ya gane da gaske take son ganin Maman nata, wasu abubuwan data yi a yau sun tsaya masa a rai, sun kasa bacewa, musamman kukan shagwabar nan nata is arousing something in him komai dakewar sa don bai taba ganin wanda kuka ya yiwa kyau irin Amani ba.

Tsaki yayi cikin jin matsanancin mamakin kan sa, ya dauki kiran Alhaji da ya shigo masa a daidai lokacin.

Ya ce
Mukhy kana ina ne?

Ina office Alhaji
ya fada a kasalance.

Alhaji ya ce
to in ka kammala ka zo zamu yi wata muhimmiyar shawara.

Kai bari kawai in gaya maka.

Haka kawai ina zaune wani tunani ya zo min, ina son tsayawa takarar gwamnan jihar Katsina
Mukhtar ya yi azamar rufe baki sannan ya bude, yana mai jinjina hadamar duniya irin ta uban gidan sa, me Alhaji yake nema kuma a siyasa da rayuwar sa bakidaya?

A tunanin sa duk abinda dan adam ke nema a duniya Alhaji Usman ya gama samun sa, kamata yayi ya maida hankali ga kula da tarin dukiyar sa da neman lahira da aurar da wannan gansamemiyar sakaltacciyar diyar tasa, ba neman wani mukamin siyasa ba a yanzu, wand aba lallai yayi nasara ba, a fili ya ce
Alhaji bari in zo kawai, wannan ba maganar waya bace
Yana tafe a hanya yana tunanin ta hanyar da zai bi ya lallashi Alhaji kada ya tsaya takarar nan, ba don komai ba sai don ya san mawuyaci ne al
ummar Katsina su zabe shi yanzu, don duk wani mukami da ya rike a baya bisa magudi ake bashi ba don al
ummah na so ba, sai don kasancewar yana da iyaye a babbar jam
iyyah masu karfi a gindin murhun, jama
a basa son Alhaji Faskari ne saboda kankamon sa, da rashin jan talakawa a jiki sai ka ce ba dan siyasa ba.

Wasu
yan jaridar ma kan ce,
HON.

USMAN FASKARI; dan siyasar da ya rasa dukkan attributes da qualities na
yan siyasa amma yana da sa
a a siyasa
Mukhy na tunanin karshen ta ya salwantar da dukiyar kamfanin sa a banza, wajen kamfen, kuma ya zo bai ci ba.

Mukamin Sanata daban na gwamna daban.

Mukamin gwamnatin jiha tabbas sai da soyayyar talakawa.

A sanin sa ko Zakkah Alhaji baya iya badawa, har sai bayan zuwan sa gare shi, shi Mukhtar din, da ya tsaya tsayin daka da lallashi da nasiha a kan Alhajin, bisa dole ya sa shi ya dinga fidda zakka don tsaftace dukiyar sa.

Sau tari, Mukhy kamar shine Ogan Alhaji subordinate, da wuya ya fadi abu Alhaji ya tsallake, don yayi amanna ba zai cuce shi ba, in Mukhy yayi magana akan abu, Alhaji baya iya tsallakewa saboda son da yake masa da yardarm da ya yi masa.

Sanda ya iso gida Alhaji na tare da baki.

Ya yi sallama ya shiga falon, Alhaji ya bashi iznin zama, Mukhtar ya gaida hamshakin mutumin dake tare da Alhaji, cikin ladabi y ace da Alhajin yace
zan jira a karamin falo kafin ku gama Allhaji
no Mukhtar, zo zauna, gara a yi shawarar nan tare da kai, you are part of me, samu wuri ka zauna
Mukhtar ya zauna bisa kilishi can gefen kafar Alhaji.

Alhaji da bakon sa suna kan kujera, Alhaji yace
Mukhy, wannan da kake gani shine aminina Alhaji Sadisu Talle, shugaban sabuwar jam
iyyar data take tamu yanzu a farin jini wato PRC (Public Relation Congress) da ake wa lakabi da SAWUN GIWA
. (ya take na Rakumi).

Mun yi shawara da shi zan bar AC in koma PRC don AC bazasu yarda su bani takara ba.

Sun riga sun tsayar cewa wannan karon yaro matashi mai jini a jika zasu baiwa takara
Suna cikin wannan maganar kafin Mukhtar ya furta komai Amani ta sauko daga upstairs da zummar wucewa kitchen (madafi), yunwa take ji, ga mai aikin ta Rakiya ta je kasuwa, sai idanun Alhaji Sadi suka sauka akan kyakkyawa Amani.

Babu wanda ta gaisar a cikin su ta wuce zuwa kofar da zata kaita kicin, shi kan sa Alhajin yau sai da yaji kunyar wannan rashin tarbiyya ta Amani.

Sabida matsayin Alhaji Sadi a wurin sa a ce
yar sa ta wuce bata gaida shi ba, shi dama Mukhy baya layin ta.

Data damo abinda zata sha wato
quaker oat
da madarar ruwa ta peak tazo zata wuce ta koma sama batare da tace musu uffan ba.

Alhaji Usman ya yi jan wuya yace.

Shin Tafisu baki ga Alhaji Sadi Talle bane zaki wuce baki gaida shi ba?

Ta zumburi baki, kafin ta ce da Alhaji Sadi din
ina yini?

Ba tare da ta juyo ko ta durkusa ba, ko jira ya amsa bata yi ba tayi wucewar ta sama.

Alhaji Sadi ya shiga yage baki duk sai ya dabarbarce ya rasa nutsuwar sa, sai mutsu-mutsu da baki yake yi ya kuma rasa abin cewa tun saukowar Amani falon ta tafi da imanin sa, yana tambayar kan sa ina Alhaji Usman ya samo wannan kyakkyawar diya haka?

Babu kama ko ta farce shi da ita, ko adopting din ta yayi?

Ya rasa yadda zai yi ya tambaya sabida Mukhy da ke zaune ya tsare shi da fusatattun idanun sa don ya gane canzawar sa da rudewar sa tun saukowar Amani.

Shi Mukhtar takaici da haushin yadda dattijon ya kwalalo ido da baki yana bin Amani da wani mayataccen kallo har da hadiyar miyau yasa ya mike.

Alhaji yace
ya zaka tafi Mukhy bamu gama shawara ba?

Yace
Alhaji ban yi sallah ba ina zuwa
.

Nan kuwa ko zancen takarar Alhaji baya son ji, balle ya bar jam
iyyar sa ta amana wato AC da ya dade a cikin ta ana damawa da shi.
Chapter 11 · 0% Book details