Sashe 18
Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana gaya masa tarihin sa ne da kauyen da ya fito wato Faskari da yadda duniya da dukiya suka rude shi yayi abondoning dangin sa ko ziyara baya kai musu balle ya taimake su, bayan dukkan su talakawa ne na gamu kashe mu masu tsananin bukatar taimako.
Yace
Mukhtar ban san halin da suke ciki ba yanzu, bani da masaniyar suna raye ko sun mutu sun bar
yan su na garari cikin babu, ban tashi tuna cewa ban tafiyar da rayuwa ta dai dai ba sai yau dana nakasa, ina kuma son su yi min wani amfani wato daura wa Amani aure
Gaban Mukhtar ne ya yi bugawar dakikai masu yawa, kan sa ya wani irin sara.
Ya dauka Alhaji ya janye kudurin sa na aurar da Amani ga abokin sa?
Ya tuna rokon da ta rika yi masa jiya a kan ya taimake ta ya roki Alhaji ya fasa bata so, ko cikakken sauraro bai yi mata ba sabida a wajen sa Amani ba mai cikakken hankali bace.
Shi kan sa Alhaji, sai da yayi noticing canjawar da fuskar Mukhtar tayi.
Mukhtar bai ce komai ba a kan duka abubuwan da Alhaji ke fada masa, Alhaji ya cigaba da bashi labarin rayuwar sa inda ya ce.
***** ***** ****
ASALIN HON.
USMAN FASKARI
Na fito daga garin Faskari ta Jihar Katsina, mu uku ne a wajen mahaifin mu, mu biyu cikin mu guda ni da Malam Idrisu.
Dayar mace ce uwar ta daban wato kanwar mu Sahura.
Malam Idrisu yana da bataliyar Iyali domin kuwa matan sa uku kowacce tana da
ya maza da mata sun haura goma.
Sahura an yi mata aure a garin Funtua.
Ban san adadin yaran da ta haifa ba.
Asali na fito birni ne neman ilmin boko, sabanin yaya Idrisu da yafi maida hankali akan sana
ar mahaifin mu wato
Dukanci
A rayuwa ta ina da burin in tara kudi, in kuma auri kyawawan mata in cika gida dasu,duk da ana yawan cewa ni mummuna ne Idrisu ya fini kyau.
Nayi makarantar koyon kanikanci a garin mu Faskari, da mahaifin mu ya rasu sai nayi wa yaya na da kanwar mu Sahura sallama na ce na tafi karatu birni.
Mahaifiyar mu a lokacin bata tare da mahaifin mu tana aure ne a wani gari Kaita.
Duk dai a cikin Katsina ne.
A wannan lokacin samun gurbin karatu a jami
in Najeriya ba abu ne mai wahala ba, saboda gwamnati neman masu yin karatun take yi ruwa a jallo.
Na samu gurbi a Katsina state Polytechnic inda nayi
dina a fannin Engineering, daga nan na samu gurbi a Jami
ar Bayero ta Kano, naje nayi digiri na na farko akan Architectural Engineering.
Na dawo Katsina na fada harkar siyasa.
Na shga siyasa da kafar dama, amma hakan bai hana ni sha
awar kasuwacin kayan gine-gine ba wanda akan sa nayi karatu na.
Alhaji Sadi Talle aminina ne tun na kuruciya a lokacin shi yana kasuwanci da kasashen Africa.
Shi ya sakani cikin harkar fitar da Aluminium Ore da Iron Ore daga Sierra Leone zuwa kasar France.
Kasuwanci ne wanda yayi mana sanadin samun arziki mai yawa, wanda idan zamu dawo sai in saro kayan gine-gine daga can in taho dasu kasar Najeriya.
Cikin dan lokaci Allah ya saka min albarka a cikin nema na.
Na soma tunanin wasu hanyoyin kasuwancin daban-daban har na samu na kafa kanfani na na farko wato Faskari Investment, amma duk da haka ban bar siyasa ba.
Cikin irin tafiye-tafiyen da muke yi ni da Alhaji Sadi ne zuwa kasashen Africa muka shiga Freetown wato babban birnin Saliyo, wannan karon mun zo ne musamman neman matar da zamu aura, don mun jima muna sha
awar auren kyawawan matan da ke wannan kasa.
Abokin kasuwancin mu da muka dade tare shi ya gaya ma na hanyoyin da ake bi a nemi aure a wannan kasa, yace
yan attajiran kasar basa auruwa ga bako sai
yan talakawa, wadanda iyayen su ke cikin yanayi.
Shi ya hada mu da mahaifin Jal
an wanda manomi ne a garin, kuma talaka ne sosai, tun a hoto naga Jal
an kuma tayi min dari bisa dari, na cika mahaifin ta da dukiya mai yawa ba tare da yayi shawara da ita ba ya daura mana aure, ya kuma ce in dauke ta in tafi da ita.
Shi kuma Alhaji Sadi ya auri wata Jenaba wadda ita ta zame masa uwar
yan sa.
In takaice maka labari Mukhtar, ban sha ta dadi ba a hannun Jal
an, domin bata sona ko kankani, ni na san saboda muni na ne, don babu abin da ban mata a rayuwa ba ita da iyayen ta, amma a cikin shekaru biyu da nayi tare da ita sau daya na taba morar sadaki na.
A wancan lokacin ni kuma son da nake wa Jai
an mai yawa ne, don har gobe babu matar da zan so kamar ta, duk matan da na aura bayan ta don na rufa wa siyasa ta asiri ne, amma ba don so ba ko neman
Kullum gorin Jal
an gare ni shi ne ba zata taba so na ba, domin tana da wanda tayi wa alkawarin aure, na yaudari iyayen ta da abin duniya.
Da tura ta kai bango na daina sakar mata bakin aljihu na don na gaji da gorin da take yi min.
Rana daya Allah ya bani sa
a a kanta kuma ranar ne muka samu rabon Amani.
Koda cikin ya isa haihuwa ta tubure lallai in maida ta kasar su ta haihu a can, ni kuma da bazan iya barin ta ta koma kasarsu ba sai na dauko mata mahaifan ta suka zo nan Katsina muka basu muhalli a cikin gidan nan, nace su zauna da ita har sai ta haihu, domin kuwa Jal
an tana ta min rantsuwa da barazanar ba zata haihu da mammunan mutum kama na ba.
Ranar ne na fahimci Jal
an saboda muni na take kina, in banda haka dame na rage ta da iyayen ta?
Har Hajji na kai su duka, in banda haka kiyayyar ta tayi yawa a kaina sai na soma kankame aljihu na nima.
San da ta shiga watan haihuwa Jal
an ta ci shinkafar bera don ta kashe kanta.
Allah ya so mahaifiyar ta da suke tare ta fahimta da wuri, muka kaita asibiti hankali tashe, likitoci suka yi mata tiyatar gaggawa suka cire Amani, ita kuma suka bata duk wata kulawar da ta dace.
Tun da aka bani
ya ta a hannu na,
yar da aka ceto da kyar, naji na tsani Jal
an, yau kuma na tabbatar ba zata taba kauna ta ba.
Sai kawai na rubuta mata saki na baiwa iyayen ta.
Na kuma basu kudin da zai ishe su koma wa kasar su da kula da lafiyar ta.
Tun a aibiti da na rabu da su ban kara bi ta kansu ba har gobe.
Wanda sai yanzu nake tunanin ban kyauta ba, don ban ma tabbatar da cewa Jal
an ta rayu ba ko ta zarce, ban kuma san ya suka yi suka koma kasar su ba.
Na dauki
Amina
wadda na sakawa sunan mahaifiyar mu na tafi Faskari da ita, garin da rabon in shige shi har na manta sai a dalilin siyasa wato lokacin da nake neman kuri
ar kauyen namu, Yaya na Malam Idrisu yana can da iyalin sa, har lokacin kuma da na fara karfi banyi kyan kan taimaka masa ba ko
yan sa.
Amma da yake aka ce naka sai naka, yau da bukatar taimakon su ta kama ni haka na murje kunya na kai masa Amani nace ya baiwa daya daga cikin matan sa ta shayar min da ita.
Amma bawan Allahn nan bai dubi hali na ba ya karbi Amani ya baiwa amaryar sa Maryama, ta hada da Kamilu dan da take goyo ta shayar da su.
Maryama ba tayi shekaru biyu cikakku tana shayar da Amani ba ta rasu.
Sai Malam Idrisu ya dauke ta ya maida rikon ta hannun kanwar mu Sahura dake aure a garin Funtua.
Amma zuwa na Funtua na farko naga bazan iya barin Amani ta cigaba da rayuwa a wannan gidan ba saboda rashin tsafta da cikowa, gashi nifa bawai ina taimaka musu da komi bane kan rikon da suke yi mata amma nazo na raina kokarin Sahura.
Na karbo Amani tana da shekaru uku na dawo da ita Katsina hannun matar da na sake aura, na daukar mata mai raino.
Amma hankalin Hajara na kan
yar kankanuwar yarinyar nan da yadda zata cutar da ita, shi yasa da na gane na saketa babu bata lokaci.
Na sake aure, saina daina baiwa mata na hidimar Amani, na daukar mata mai raino daya kwakkwara mai suna Rakiya, na sata a makaranta mai tsada, na ke kuma kirata AMANI don boye sunan mahaifiya ta.
In takaice maka ko Mukhtar, kafin Amani tayi wadannan shekarun nata na yanzu aure na goma, babu wadda na cika shekaru biyu da ita, don sun kasa kaunatar min
yar nan, wadda soyayyar da nake yiwa mahaifiyar ta ce bakidaya ta koma kanta.
Suma masu rainon kullum cikin canza mata su nake, Rakiya kawai na bari mai dafa mata abinci har gobe, har Allah ya raya ta ta isa kula da kanta.
Ita ta roke ni in daina aure-aure in kuma daina korar masu aiki saboda ita, shi yasa muka dade da Haj.Rabi.
To ka ji Mukhy, wanan shine labari na da
ya ta Amani, a yau ina cikin damuwar irin dabi
un ta da irin tarbiyyar da nayi mata, amma yaya zanyi?
Ni da mahaifiyar ta Allah yayi ba masu rayuwa tare bane na tsayin lokaci, kuma ban kyauta ba da ban kara bibiyar rayuwar Jal
an ba, su kuwa dangi na na Faskari wallahi sai dai Amani tayi masu kyauta amma ba dai ni ba, bana kai ta wurin su, amma ita tana kai kanta lokaci-lokaci bama tare da na sani ba.
Ba yabon nawa ba, Amani ta fini kirki, ta fini son zumunci kai dai bar ta da sangartar ta wadda rashin tashi karkashin kulawar uwa ko wata shaqiqiya mace ta jiki yayi mata sanadin sa
Mukhtar ya jinjina kai ya shafe gumi daga goshin sa.