Sashe 14
Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuka ya ci karfin ta.
Haj Rabi tace "toh?
Ashe ke kika jawo masa?
To ta Allah ba taki ba ban shirya yin takaba yanzu ba, in bai tashi nan da sati daya ba wallahi sai dai ku sallame ni don ban shirya yin takaba yanzu ba".
Amani ta juyo ta dube ta da fusatattun idanu ta ce "in kika kara shiga sha'ani na sai na karawa wannan katon bakin naki tsini, ina ruwan ki da ni?
Ko ina shiga sabgar ki?
In ni na jawo masa Uban ki ko nawa?
Ko kin haifa masa ko gunduren kashi ne?
Ba tumunin takabar kike jira ba me kike so in ba shi ba?"
Haji.
Rabi ta kama baki, tace "ke mara kunya, wadda bata ganin mutuncin kowa, na fi karfin ki yimin diban albarka don uban ki nake aure, shashasha da bata san komai ba sai sangarta da rashin kunya".
Likita ya shigo dakin ya na cewa "haba!
Haba bayin Allah.
Yaya zaku tsaya kan mara lafiya kuna daga murya?
To daga yau mun yafe zuwan ku.
Mukhtar kawai muka yarda ya zo har sai ya dawo gida".
Amani da ta riga ta zo wuya, ga haushin Mukhtar ga na Haj Rabi ga kuma na wannan likitan yanzu.
Ta ce "idan uban ka ne shi sai ka hana ni zuwa in gani" likita ya juya ya fita kafin yarinyar ta soma kai duka, ya fara tunanin tanada aljanu amma na rashin kunya da rashin tarbiyya.
Ta yi tsaki tana fadin "Daddy zan sa a dauke ka daga rubabben asibitin su ka ji?
Jidda zan kai ka a duba ka sosai.
Get well soon my Daddy".
Ta sunkuya ta sumbaci goshin sa, ta gyara masa rufuwa da bargo duk Alhaji na barcin allurar barci bai san me suke yi ba.
Waje ta fito tana tunanin abun yi, tana neman mataimaki da zai taimaka mata wajen fidda Daddy saudiyyah.
Amma Mukhtar shine yafi dacewa da ya taimaka mata din gashi ta gama caccakar sa ta masa gorin Uba.
Da sanyin jiki ta hau neman sa a reception amma bata gan shi ba.
Bata san ma shi a lokacin yana can yana cuku_cukun samun visar tafiya da Alhaji kasar Faransa ba.
Ya gayawa Haj.
Rabi niyyar sa ita kuma tace bazata jinya ba, saidai Amani ta je.
Ko kwai bata ajiye masa ba bazata jinyar shanyewar jikin sa ba, alhalin ko tumunin takaba bai rubuta a bata ba komai na Amani ne. don haka ta karata da uban ta ita kadai.
Mamakinta ya kusa kashe Mukhtar a tsaye, to dama ya bata hakkinta ne a matsayin ta na matar Alhajin.
Amma Shima baya so ta bi shi don baya jin zata yiwa Alhaji kulawar data kamata, wannan aikin sai namiji kakkarfa.
Yana tsaye a gate din gidan suna magana da Malam Tajudden yana gaya masa maganar zai tafi Abuja da Alhaji don Nemo visar tafiya asibiti a Paris.
Amani ta shigo gidan tare da Malam Audi Mai baiwa shukoki ruwa wanda shi ya tuka su zuwa asibiti.
Tajudden ya juya ya dan kalle ta sai yace da Mukhtar din ka sanar da Amani?" Yace "kaima ka san wannan yarinyar bata cikin 'yan shirgi na saboda rashin kunyar ta.
Dazu har zagi na ta kusa yi fa Tajudden".
Malam Tajudden ya dafa kafadar sa cikin lallashi yace "ka yi hakuri ka manta, na sha gaya maka sai kayi hakuri da ita in dai kana son albarkar Alhaji.
Daure ka gaya mata saboda hakkinta ne ta sani, son samu ma ku tafi tare ta zama a kusa da mahaifin ta duk sanda ya bude idon sa ya ganta don itace sanyin idaniyar sa".
Malam Tajudden ya karasa inda Amani ke kokarin fitowa daga mota yace "ran ki ya dade Malam Mukhtar na son magana da ke, a kan lafiyar Alhaji ne" Amani ta dalla masa harara tace "shi kurma ne?
Ko Kai ne bakin sa?
Bana son kinibibi bace min da gani".
Mukhtar ya karaso wurin yana cewa "in kika sake alaqanta ni da rashin ji sai na buge bakin ki, wannan dattijon bai haife ki ba?" Ai kuwa Amani ta fusata fiye da farko tace "ka fita hanya ta don ni ba tsarar yin ka bace, mai kama da jan kosai kawai" ya kusa ya buge bakin nata ya tuna mace ce, ya kuma yarda Amani tayi fama da
juvinile deliquency
a shekarun kuruciyar ta, wadanda suka mika mata har zuwa yanzu da take shekaru ashirin.
Bata ganin kan kowa da gashi.
Har ta wuce shi ta tuno maganar asibitin Alhaji sai ta dawo tana sosa keya tace "for your information inaso zan kai Alhaji asibiti a Jiddah don ban yarda da kwarewar wannan asibitin da ka kai shi ba".
Mukhtar ya hadiye haushin ta yace "France zan kai shi" tace "a wane dalilin zaka kai shi inda ban sani ba?" "Saboda ni Dan sa ne idan baki sani ba, daga yau ki sa a ran ki ba ke kadai ya haifa ba uwar tutiya da uban da bata iya masa biyayya" "to ban yarda ba Jidda zamu je.
Akwai asibitin da suke duba shi a can, tun ina karama can yake zuwa".
Musu ya kaure tsakanin Muktar da Amani, a karshe ya ce "wait pls, wai in aka bar ki kika kai shi Jiddan zaki iya jinyar sa ne?
Alhaji fa yanzu komai sai an masa har wanka da tsarkin lalura, kina mace me zaki iya kulla masa?
Na fada miki ki sakar min komai kawai, don ba abinda zaki iya kullawa".
Idanun ta fal hawaye, don ta tsani a dinga nuna mata gazawa don tana mace.
Shima Alhaji haka yake mata, komai tace zata yi sai yace Mukhtar zai yi don ita mace ce, shi yasa take kishin sa da cewa he snatched away her father's love from her.
Mukhtar ya ga ta rasa ta cewa a wannan gabar, sai ya juya zai tafi ya bar ta a wurin.
Sai ji ya yi ta ce da siririyar muryar ta mara amo.
"To ka shirya tafiyar da ni, in ba haka ba hankali na ba zai kwanta ba in bana tare da shi, ban kuma san halin da yake ciki ba".
Mukhtar ya daga gira ya ce "alright.
Yanzu kika yi magana Ma'am".
At long last.
Mukhtar Diffa ya sake yin nasara a kanta.
***** ****** *****
Kasancewar Mukhtar, Alhaji da Amani duk suna da 'Schengen Visa' yasa basu sha wahalar gama shirin fita da Alhaji zuwa Birnin Paris ba.
Inda tun kafin su zo Mukhtar ya gama yi musu kowanne tanadi ta yanar gizo da asibitin H
pital Saint-Louis dake tsakiyar babban birnin kasar na Faransa wato Paris.
Ranar Lahadi suka daga zuwa Paris daga birnin tarayya tare da Alhaji wanda zuwa lokacin yana cikin hayyacin sa sai dai baya iya motsa kowacce gaba ta barin daman sa.
Tuni asibitin na H
pital Saint-Louis sun shirya musu dakin da Alhaji zai yi jinya.
Babban daki ne na alfarma ciki da falo a rukunin dakunan physiotherapy department.
Daga zuwan su kuwa bayan Mukhtar ya gama settling bill din asibitin, likitoci na musamman suka fara yi wa Alhajin dukkan kulawar data dace da masu irin lalurar sa.
Mukhtar da Amani dambe ne kawai basa yi kullum saboda sa
in sa, don a kan baiwa Alhaji madara ko tea ma kadai kullum sai sun yi fada.
Kowanne yace shi zai yi.
Mukhtar a hotel ya kama nasa dakin wanda ba shi da nisa da nan da asibitin.
Amma kullum tun safe har dare yana dakin majinyacin, shi yake yiwa Alhaji alwallah, wanka, tsarki da komai.
Tare da taimakon ma'aikatan jinya maza.
Rannan Amani har da kukan ta, tana fadin duk ya kwashe ladan ya bar ta.
Bayan ita ce da uban shi dan karo ne.
Mukhtar ba kasafai yake tanka mata ba amma a sanda ta fadi hakan sai da ya kusa yin murmushi, amma ya shanye abinsa, kada ma ta ga murmushin sa, a ran sa ya ce
na ji din.
Dan karo kore dan gida kenan!
Shi ya san da ace gorin Uba na tsiro, da yanzu babu masaka tsinke a jikin sa sabida gorin Amani na Alhaji ba Uban sa bane.
Wani zubin yafi gane yayi mata banza wanda hakan yafi kona mata rai, har gara ya amsa mata su yi wa juna wankin babban bargo yadda suka saba tun a gida ta fi ganewa da samun biyan bukata.
Duk fadan nan da suke yi kullum Alhaji na jin su, don wani lokacin har sai ya daga musu hannun sa mai lafiya alamar yana rokon su yi hakuri su bari.
A ran sa ya rasa dalilin wannan rashin jituwa, gashi yanzu duka burin sa ya ta
allaka a kan mayar da su abokan rayuwar juna wato su zama ma
aurata karkashin inuwar aure shine kadai burin sa na karshe a duniya.
Kuma abinda zai bashi kwanciyar hankali a yanzu, tunda ya yarda yanzu kam ya nakasa, ba ya jin kuma zai sake tashi a kan kafafun sa nan kusa yadda yake jin jikin nan nasa.
Sannan Alhaji babu baki.
A kwance yake kawai yana karbar treatment amma yana hankalce da duk wani takun sakar Mukhtar da Amani mai saka shi a damuwa, don shi ba haka yake son gani daga gare su ba, so yake ya ga Mukhtar na kula da Amani kamar yadda zai kula da kanwar sa ta jini.
Ita kuma ta dinga respecting din sa tamkar Yayan ta. hakan kawai yake so daga gare su.
Kullum Alhaji na hango kujerar gwamna daga nesa a idanun sa, sai ya ji wani bakin ciki ya rufe shi.
Tun farko me yasa ya jawowa kan sa maganar siyasar nan?
Bayan duk daukakar da ya dade yana samu a siyasa karkashin jam'iyyar
Action Congress?
Watakila da bai kawo zancen ba da duk bai fada a damuwar data yi masa wannan sanadin wahalar ba.
Ya dade da sanin conditions din sa na hawan jini da sugar Amma ya zo ya saka damuwar aurar da Amani a ran sa har ta kassara shi.
Alhaji Sadi din bai san suna yi ba, ko irin abinda zancen auren da yayi sanadi ya janyo masa yanzu.