← Book details Amani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 25

Sashe 24

Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji ya nisa yana fadi cikin ran sa,
na yi kuskure mai yawa a rayuwa ta.

Allah ka bani ikon gyarawa kafin ka dauki rai na.

Allah ya sa Mukhtar ya rike min Amani da dukkan nakasun ta, ba tare da ya goranta mata tarbiyya, ilmin addini da goyon gatan da na yi mata ba.

Yau ga shi ga dukkan alamu Amani na so na kasa lankwasa ta.

Wa ya janyo komai?

Alhaji ya kara kudirewa a ran sa sai dai Amani ta mutu, amma sai ya cika kudirin sa, in yaso ya wanke gawar ta ya fara kaiwa gidan Mukhtar kafin ya danganata da kushewar ta, amma ba ta da miji insha Allahu sai Mukhtar din sa.

Idan ta bijire masa wannan karon zai ba ta mamaki. (Alhaji ya manta icce tun yana danye ake tankwara shi).

Daidai lokacin da Mukhtar ya karya kan motar suka hau burjin da zai shigar da su garin Faskari, Alhaji na ta kallon garin iyayen sa da kakannin sa with nostalgia, yana kokarin tuna ko yaushe ne last shigowar sa Faskari?

In zai iya tunawa daidai tun lokacin da yake nema kujerar sanatan Katsina ta Tsakiya yana neman kuri
ar karamar hukumar tasa.

Da ya zo ya dan yarfa musu.

Ya tuna lokaci na karshe da Yaya Idrisu ya kira shi a waya yana gaya masa Kamilu dan sa ya kammala karatu an turo shi hidimar kasa cikin jihar Katsina ko zai ba shi muhalli ya zauna a gidan sa yayi hidimar kasan?

Yadda ya balbale shi da fada kamar kanin sa yana fadin ba ya son a zo a cika masa gida shi bai iya jaye-jayen
yan dangi ba.

Ya tuna cewa uwar Kamilun ita ta shayar masa da Amani, ba don ita ba da bata rayu ba, ko sai da madarar gwangwani.

Yau ga shi ya dawo Faskari babu kafafu sai dai a tura shi a keken guragu, rabin jiki ba ya aiki, kuma kai tsaye gidan Yayan nasa ya dosa, wato gidan su na gado, wannan abun kunya da kayan nadama har ina?

Ita dai Amani da ke gefen sa tana danne-danne a waya, sai gani ta yi Daddyn ta yana hawaye, ya kuma bar su suna ta zuba akan kundukukin sa ba ya ko sharewa wasu na korar wasu.

Idan ya kara tuna cewa uwar Kamilu ita ta shayar masa da Amani, amma shi ya kasa daukar ko Kamilun ne ya yi
yan watanni tare da shi na hidimar kasa duk irin arzikin da Allah ya yi masa da girman gidajen sa a Katsina.

Ya
ilahi!

Da wace fuska zai doshe su yanzu?

Da wane azancin harshe zai nemi gafarar su?

Ba tare da sun yi tunanin sai da lafiya ta kare masa ba ne ya neme su?

Don in bai manta ba daga waccan wayar da suka yi da Baba Idrisu har gobe Baba Idrisu bai kara neman sa ba, ya rike talaucin sa da mutuncin sa, ya rike
yan sa a kauye ko birnin Katsina ya haramta musu shigowa don ma kada su nemi kanin uban nan nasu da bai san muhimmancin zumunci da girman zumuncin Allah ba.

Alhaji shi ke nuna wa Mukhtar hanya har kofar gidan iyayen sa, soron gidan duk ya zube, kana iya hango tsakar gidan da duk abin da ke ciki duk da an kare da zangarniyar dabino da azara.

A nan ya umarci Mukhy ya yi fakin motar, daga can hanyar masallaci Alhaji ya hango Yayan sa Malam Idrisu na tahowa, Mukhtar ya fito ya bude but ya fiddo kujerar Alhaji ya warware ta ya dauko Alhajin daga mota ya sanya shi cikin kujerar.

Amani ta fito tana ta cin magani da yatsine-yatsine, har da zumbure-zumburen baki, ita ta tura Alhajin zuwa kofar gidan su, yayin da Mukhtar ya tsaya kici-kicin fiddo kayan su.

Daga nesa Malam Idrisu ya hango su babu bata lokaci kuma ya gane Amani tare da wani farin balaraben mutum da bai sani ba.

Amma dattijon da ke cikin kujerar wheelchair ko kusa bai kawo cewa kaninsa Usman ba ne.

Amani ta jira rike da hannun kujerar har ya iso, sai a lokacin ya gane dan uwansa.

Innalillahi wa
inna ilaihi raji
.

In ji Malam Idi, yana fadin,
Me ya same shi?

Me ya faru da shi haka?

Zuciyar
yan uwantaka!

Tuni ya karbe shi daga hannun Amani, da kan sa ya tura shi zuwa cikin gida.

Kai Isya je ka kasuwa ka kira Kamilu ya zo ya bude wa baki dakin sa su aje kayan su
Yaron da aka kira Isya ya zura da gudu yana waiwayen Mukhtar don ya dauka bature ne ko wani balarabe, fatar sa ta wanku da boko, ya karya hula damanga a saman kansa wadda ta dace da launin shaddah getzner lemon green da ke jikinsa, kai ba za ka ce haihuwar Africa ba ne shi ya fi kalar larabawa.

Uwa, ku ne tafe?

Sunan da yake kiran Amani, kasancewar sunan mahaifiyarsu ta ci, wato Inna Amina mai rasuwa.

Amani ta zumburo baki, kafin ma ta furta wa Yayan uban nata gaisuwa ta al
ada sai da ta saki korafi irin na rashin kunyar da ta saba yi wa Alhaji.

Za ka fara ko, daga zuwa na?

Kira na da UWA?

Shi ya ce min wani TAFISU kai ka ce min wani UWA, bayan ga suna na mai dadi na yanka
Dariya Malam Idrisu ya yi don shi a duniya yana son Amani, duk da halin ta kuwa, ya sa matar sa uwargida Talatu ta yi musu shimfidar tabarma karkashin katuwar dalbejiya da ke tsakar gidan.

Mukhtar ya gaishe shi cike da girmamawa, ya gaida Baba Talatu, Baba Idi na son tambayar Amani inda suka samo kyakkyawan mutum haka, shi kuma ba balarabe ba, don ga hausa ras a bakin shi, amma ya fi damuwa ya ji yadda aka yi dan uwan sa ya koma rayuwa a wheelchair.

Faduwa ya yi a bandaki, ka san yana da hawan jini, shine ya samu stroke.

An fidda shi asibiti har kaar Faransa Allah bai sa ya mike ba.

Amma yanzu a hakan da sauki sosai, tunda yanzu yana magana ras, yana kuma iya motsa duka hannayen sa
Baba Idrisu da Baba Talatu suna ta sallallami da jajantawa, tuni suka manta da halin Alhaji.

Baba Idi ya ce
sai a koma na Hausa, ya san inda ake maganin irin wannan lalurar ta hanyar gargajiya a garin Kaita
Wannan lalurar da suka samu Alhaji a ciki sai ta maida komai ba komai ba na laifukan Alhaji a gun su, don dan uwan ya damu sosai, tunda shi da ma ba wai yana kwadayin abun hannun shi ba ne, a
ah zumunci na Allah yake yi da shi, kuma kulawar sa garesu kadai yake bukata.

Kafin dan lokaci Kamilu da yayyen sa biyu Jibril da Usama sun iso gidan, Jibril da matar sa da
yan sa hudu haka shi ma Usman da
ya biyu.

Suna ta lale-marhabin da Baffan nasu, tare da jajanta lalurar da ta same shi.

Alhaji sai ya fashe musu da kuka yana neman gafarar Baba Idrisu, yana kuma tambayar Sahura.

Talatu ta ce,
Gobe insha Allahu za ta aika mata ta zo daga Funtua
Nan aka shiga mayar da zance tsakanin Alhaji da Yayan sa Malam Idrisu, ko ya rike dan uwan nasa a baya, ganin halin da yake ciki da nadamar da ya zo da ita duk sai ya ji rikon na narkewa a ran sa.

Duk da haka ya fito fili ya gaya wa dan uwan sa yadda yayi wasarere da zumunci bai kyauta ba, ba ya neman kobon sa amma dole ya kyautata zumuncin Allah muddin yana son gamawa da duniya lafiya.

Alhaji har su Kamilu sai da ya bi daya bayan daya ya nemi gafarar su, ya tambayi kowannen su abinda yake ciki, suka gaya masa, cewa wasu cikin su kasuwa suke zuwa wasu gona wasu sun yi karatun NCE wasu har degree, sai Alhaji ce wadanda suka yi karatu a cikin su zai tafi da su a duba ayyukan da suka dace da su a kamfanin Amani, wadanda ba su yi karatun ba ma duk ba zai rasa irin aikin da ya dace da su ba.

Baba Idrisu ya ce,
Ai kam ba ka kwashewa duka ka barmu mu kadai, sai kananan yara.

Ka dai dauki masu takardun bokon ka bar min sauran su ci gaba da kasuwa da gona
Alhaji ya ce,
Mukhy, sai a binciki irin sana
ar da suke yi din a nan a bunkasa ta, a ba su training a kai, sannan a ba su jari mai tsoka
Consider it done Alhaji
Abu dai ya yi dadi tsakanin Alhaji da dan uwan sa da
yan dan uwan sa.

Sai washegari Sahura ta iso don amsa kiran da Baba Idi yayi mata tun jiya, Alhaji sai ya ga duk ta tsofe ta mokade saboda wahala, don mijinta ya rasu ya bar ta da
ya takwas.

An yi sulhu cikin tausayin juna sun yafe wa dan uwan su, suka ce ba su taba kullatar shi ba ko don Amani da bata yada su ba ita, kullum addu
a suke masa koda kuwa sunan sa kadai suka ji an fada a kafafen yada labarai.

Baba Idi ya ce,
Ah toh ni ai ban damu ba, na sani ko ba-dade ko ba-jima za ka neme mu, tunda ba ka da wadanda suka fi mu
Kusan kwanan zaune suka yi ranar da Sahura ta zo ana ta maida zance da labarin juna.

Alhaji ya ce, tunda Sahura ba ta da karamin yaro duk ta aurar da su, na karshen ma yana makarantar Alkalam a Katsina, to zai tafi da ita gidan sa ta zauna tare da Amani kafin wucewar ta gidan mijinta.

Sahura, Baba Talatu da Baba Idi har suna hada baki wajen tambayar Alhaji cikin mamaki,
Uwa ta samu miji ne?

Don su kam basu ga mijin da zai iya daukar Amani ba.

Alhaji ya gyara zama da filon da aka sa masa a bayan sa, ya soma warware musu tun ranar farko na haduwar sa da Mukhtar a kasar Faransa, da irin gudunmawar da ya bayar ga habakar dukiyar sa, amanar sa, halayensa, rikon addinin sa da irin gudun duniyar sa.
Chapter 24 · 0% Book details