Sashe 19
Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali yace
Alhaji labarin ka akwai darussa mai yawa a ciki Alhaji, sannan akwai tarin kurakurai a cikin sa.
Na farko Alhaji, ban yarda da abin da ka yarda da shi bana cewa Mama Jal
an na kin ka ne saboda baka da kyawun suffa wannan ba haka bane Alhaji.
Hanyar da kabi wajen auren ta bata dace ba, kamar ka sayo akuya a kasuwa ka kawo kasar ka ka ajiye ne, duk da mahaifin ta shi ya aura maka ita, akwai bukatar ka nemi soyayyar ta da fahimtar juna tsakanin ku, kafin akai ga maganar aure ba duka mata ake saye ba.
Amma irin wannan auren dama baya wata kima tunda da bakin ka kace min akwai wanda take so da suka dade tare, har suka yi alkawarin aure.
Don haka ka cire maganar wai don munin kane bata son ka, kuma Alhaji da bakin ka kace kana yi mata kankamo, mata da yawa musamman na kasashen Africa suna aure ne a inda zasu samu wadata da kwanciyar hankali fiye da na kasar su ta asali.
Mu koma maganar dangin ka na Faskari, zan iya cewa kayi wa Yaya Idrisu da Sahura butulci da rashin daukar zumunci da daraja.
Dukiyar ka ta rude ka ka wulakanta zumunci domin sun cancanci ace a irin wadatar da Allah yayi maka kamata yayi ace ka rungume su ka zama kaine komai nasu tunda kace basu da karfi.
Muhimmin abin da zaka yi a yanzu Alhaji shine gyara tsakanin ka da
yan uwan ka, neman yafiyar su, da janyo su a jiki, ka saka su a cikin ni
imar da Allah yayi maka
Alhaji yana girgiza kai yace
haka ne, haka ne Mukhtar, In sha Allah zan gyara, gobe-goben nan ka shirya mana tafiya Faskari don Allah ni da kai da Amani da yardar Allah zan gyara komai
Mukhtar yace naji dadin jin hakan Alhaji, saura iyayen Mama Jal
an da ita kanta ya kamata ka neme su ka sada su da Amani.
Mahaifiyar ta na da hakki a kan ta fiye da wanda kake da shi.
In ta mutu baka sada su ba sai Allah ya tambaye ka Alhaji, Amani (is desperate) ga son ganin mahaifiyar ta, har taso ta bi ta wata hanyar da baka sani ba don ta kai kan ta ga mahaifiyar ta ba don na hana ta ba, duk da togaciyar da kayi mata akan zuwa gare ta
Kafin Alhaji yace komai suka hango Amani na tahowa inda suke da hanzari da sassarfa, suka yi shiru suka maida hankalin su gare ta.
Tana isowa ta nufi Alhaji ta zauna kasan kafafun sa ta saka kuka.
Alhaji yace
ni fa dadi na dake shagwaba da sakarci maras dalili, yaya zaki zo muna magana ki saka mu gaba kina kuka?
Mutuwa aka yi ko dukan ki aka yi?
Amani ta dago jikakkun idanun ta ta dubi Baban ta cikin ido ta ce
Daddy sona ke ka saki Haj.
Rabi, kuma kada ka kara auren kowa, ba zasu taba son ka saboda Allah ba, dukiyar ka kawai suke so Daddy.
Muddin kuma suka fahimci ba zasu samu ba na rantse zasu iya halaka ka ko ni su sabauta ni.
Daddy don Allah ka sake ta, ni zan kula da kai, na fasa zuwa karatun, zan kare rayuwa ta gaba daya cikin kulawa da hidimar ka da lafiyar ka, in dai ka yarda zaka rabu da Haj.
Rabi kuma zaka fasa aura min Alhaji Sadi
Alhaji yace cool down Amani, duk me ya kawo wannan?
Maganar auren ki da Alh.
Sadi tana hannun ki yanzu, na bashi dama ne ya nemi soyayyah daga gare ki, wallahi in baki so duk amincin dake tsakanina da shi bazan miki dole ba.
Haj.
Rabi kuwa ai zaman ki take yi, ke kika hana ta tafiya tuntuni.
Ni da ke cikin rayuwa a wheelchair yanzu, rayuwa ta bata mata bace yanzu.
Ko dama saboda siyasa nake aure-auran nan amma tun daga kan Jal
an na gama auren biyan bukatar rai da kauna.
Share hawayen ki kin ji Amani?
Gobe in sha Allahu zamu tafi Faskari da wuri zan maida ke cikin
yan uwan ki na jini.
Amma Amani ta yaya zaki iya kula dani alhalin kina mace?
Da zaki yi min alfarma irin wadda baki taba yi min ba ki amince ki auri da na Mukhtar, ya zauna tare da mu, ku cigaba da kulawa da ni tare har Allah ya bani lafiya.
Na hanga na duba duk duniya ban ga wanda zan iya baiwa auren ki ba sai MUKHTAR Amani, da shi kadai na amince in yi surukunta, kuma da shi nake son jini na ya gauraya, koda kuwa ace daga sama ya fado, wato ba
yan Adam ne suka haife shi ba
Amani da Mukhtar a lokaci guda suka daga kai suna kallon-kallo, kallon son fahimtar ko me Alhaji ke nufi?
Sun shiga rudani mai yawa dukkan su, amma Amani ta fi Mukhtar gigicewa.
Mikewa tsaye ta yi zumbur tana kallon Alhaji a tsorace, kafin ta soma ja da baya, da kyar ta iya cewa,
Daddy ai gara min Alhaji Sadin, da dai wannan mara mutuncin mara tausayin kuma mara jin kan mace.
Gara min Alhaji Sadi bakikkirin mummuna da wannan mai kyan dan macijin.
Gara min Alhaji Sadi tunda ba a karkashin uba na yake cin abinci ba, kuma yake min keta da Gadara ba.
Na rantse da Allah gara in auri Alhaji Sadi sau dubu da wannan sumumu-kasau din wanda bai san darajata a wurinka ba, saboda takamar yana da fada a wurin ka
Tana gama fadin haka ta juya ta bar wurin da gudu-gudu, sauri-sauri babu inda ba ya kyarma a jikinta saboda dimauta.
Mukhtar kuwa komawa ya yi tamkar mutum-mutumi a wurin, ko kwakkwaran motsi bai iya ya yi ba.
Haka ya kasa dago kansa da ya sunkuyar saboda kunya.
Ga mamakin sa sai ya samu kansa da jin kunyar Alhaji mai tsanani.
A can wani sako na zuciyar sa kuma ya samu kan sa da jin dadin wannan tayi da yayi masa.
Shi ma ya san ba ya kyautatawa Amani yadda duk ma
aikatan Alhaji ke mata, haka ba ya bata respect din da ma
aikata suke bata, kullum jin kan sa yake sama da ita, ba ya yarda da subordination, shi mutum ne da ba ya yarda da raini ko kaskanci, wannan kuma a cikin jinin sa ne na iyaye da kakanni.
Maganar aure da Alhaji ya yi yanzun kuwa tsakanin sa da Amani sai ta kashe duk wani kuzarin sa, ta jefa shi a wani yanayi da bai taba shiga ba na zurfin tunani da mutuwar jiki.
Maganganun Amani wadanda suka zamo raddi ga mahaifin ta, kuma zagi a gare shi ko kadan ba su dame shi ba.
Fassarar da ta dade tana yi masa a zuciyar ta ne yau Allah ya matsi bakin ta ta fada a gaban sa.
Da kyar ya iya mikewa tsaye lokacin da Alhaji ya ce ya tura shi a kujerar sa ya maida shi falo ya huta.
Har suka yi sallama da Alhaji, bayan ya bashi magungunan sa na yau ya sha, Mukhtar sanyin jikin sa da bugun zuciyar sa basu koma daidai ba.
Da kyar ya iya takawa zuwa gidan sa wanda bai da nisa da gidan Alhaji.
Ko motar sa a gidan ya bar ta don ya san ba zai iya tuki ba.
**** **** ****
MUKHTAR
Mukhtar ya yi kwance a tsakiyar lallausar gadon sa yana sake tariyo maganganun ubangidan sa Alhaji Usman Faskari, kauna ce zallah ya nuna masa wadda babu algus, kuma wani bare bai taba yi masa irin ta ba, kuma bai taba samun kwatankwacin ta ko daga iyayen sa da suka haife shi ba.
Ya soma laluba lungu da sako na zuciyar sa don son gano
stand
din da ya ajiye Amani, a zahirin gaskiya wannan yarinyar ba tun yau ta ke fizgar zuciyar sa ba, ta dade tana saka shi a faduwar gaban da bai san dalilin sa ba, sai ya bar wa ran sa a cewa kyawun halittar ta da kwarjinin ta ne yake razana shi, yake sanya shi faduwar gaban, kamar yadda duk wani lafiyayen namiji bazai iya kauda kai a kan ta ba ba tare da ya ji zuciyar sa ta motsa ba.
Ya sha zama a cikin dare yana tuno wasu abubuwa da suka shafe ta a duk lokacin da wata alaka ta hada su suka fita a mota tare ya kai ta wani wuri, bisa umarnin Alhaji.
A irin wadannan lokutan kwana yake da tunanin ta a ran sa.
Fitsarar ta, rashin kunyar ta, hararar ta da tijarar ta duk basu bace masa.
Ba don murmushi yayi kaura daga rayuwar sa ba da yace wadannan halaye nata duk da baya son su, to fa hakika suna saka shi murmushi a yawancin lokuta.
Amani Faskari, tana da babban al
amari a tare da shi wanda ya dade da kasa ganewa.
A yau da Alhaji da kan sa ya yi masa tayin auren ta ya shiga rudu, ya shiga dimuwa da tunani mai yawa, wanda hakan ya saka shi tono duk wasu tsofaffin feelings din da ya san yana ji a kan Amani; and he realized for himself cewa ya dade yana son Amani, in dai pleasant feelings din da yake ji a can kasan ran sa a kan ta shine SO, to ya
dade yana ninkaya a cikin sa ba tare da ya ankara ba, har sai yau da tayin Alhaji da kan sa ya ankarar da shi, amma kuma halayen ta sun sa ba ta burge shi, kuma ba ya son ko daya cikin dabi
un ta.
Ya na son ta a kasan ransa a can wani lungu da bai taba dauka da muhimmanci ba.
In ba haka ba me ya sa ko kadan ba ya son zancen auren ta da Alhaji Sadi?
Me yasa ranar da Alhaji ya gaya masa ya bada auren ta ga Alhaji Sadi ya kasa barci a tsayin daren bakidayan sa?
Me ya sa yake kishin ganin ta babu lullubi (mayafi?) ta fito waje ma'aikata maza na kallon ta, don duk lokacin da ya gan ta babu lullubi a gaban maza sai ya ji zuciyar sa kamar ta tarwatse.