Sashe 17
Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kana iya magana dai ko?
Alhaji ya ji ciwon wadannan maganganu na Alhaji Sadi, amma ko a fuskar sa bai nuna ba, sai yayi murmushi yace
ai ba sai ka gaya min na zama mara amfani ba yanzu, nima na sani, na kuma yarda duniya da dan Adam duka ba a bakin komai suke ba, yau ne kake mutum gobe zaka iya zama rabi gawa ko duka gawa, na yi kurakurai masu yawa a rayuwa ta dana ke neman yafiyar ubangiji a yanzu ba takara ce a gaba na ba, tuni na dade da janyewa.
Yanzu zan maida hankali na ne akan ibadah da neman guzurin lahira da nemawa diya ta kyakkyawan Future
Da kyau
.
In ji Sadi Talle, wannan tunani ne kayi mai kyau, amma ina fatan ba zai shafi yarjejeniyar mu ba.
Ka fadi duk abinda kake so daga gare ni in yi maka, koda tsayar da wannan balaraben yaron naka ne na ga alamun sa jajirtacce ne kuma namijin duniya ne ko daga takun sa, yana da leadership appearance, amma bayan ka bani auren Amani, yau da shiri na na zo don muyi ganawa ta musamman da ita
Alhaji yayi murmushi ya ce
yadda na fasa takara haka na fasa aurar da
ya ta, zan bata
yancin ta ne na tafiya karatu ta kuma kawo duk wanda take so da kanta na aura mata, ko da kuwa kai din ne, don haka a adalci irin nawa, na baka damar ganawa da Amani yau, ka ji ra
a yin ta a kan ka, ka nemi soyayyar ta, in ta amince zan fi kowa farin ciki tunda ba yau muke tare ba na san baka da matsalar da za
a hana ka aure.
Idan kuma Amani ta ce bata yarda ba sai kayi hakuri ka nemi wata.
Ina Mukhtar ina tsayawa takarar gwamnan Katsina shi da ba ma dan kasar Najeriya ba?
Ba
abzine ne fa!
Alhaji Sadi sai ya rasa abin cewa, amma tabbas ya ji dadi da Alhaji ya bashi damar ganin Amani.
Ya dauki wayar sa ya kira Amani, da kyar ta daga cikin magagin barci, ta fara korafi
Daddy ka san gajiyar da ke jiki na kuwa ka tashe ni da safen nan?
yi hakuri Tafisu, sauko yanzun nan amma kisa mayafi don na san ki da shirme
.
Kafin ta ce komai ya kashe wayar sa ya barta da mamakin ko lafiya yake fadin tasa mayafi?
Saboda ya ji Mukhtar din sa na korafi shine shima yau ya koya, wato duk inda takurawa take sai Mukhy ya nemo mata ta hanyar juya kan baban ta da irin ra
ayoyin sa na akida.
Tana mitar tana komai ta saka Abaya da mayafin ta da silifas din bakin gado, tana saukowa suka hada steps da Haj Rabi saura kadan Hajiyar ta bangaje ta, Amani ta kauce.
Haj.
Rabi ta ce
ji mana?
Amani ta dan dakata da sauka daga steps din ba tare da ta juyo ba.
Haj.
Rabi ta tako ta iso bayan ta ta soma magana cikin zafin murya.
Jiya na nemi saki a gun Baban ki don na fi karfin yi wa mai shanyayyen jiki takaba ko jinya, ni ba gado ba ba komai ba, ya ce magana tana hannun ki, ke kika hana shi sallama ta da tuni ya sallame ni.
To don uwar ki ke kike aure na da zaki hana a sake ni?
Da sauri Amani ta girgiza kai don bata taba jin wanda ya zagi uwar da ko gani bata taba yi ba sai yau, wadda duk da bata san ta ba, zuciyar ta cike take da kaunarta.
Haj.
Rabi ta cigaba da cewa.
idan kin haifu cikin Usman da Jal
an yau ki sa ya rubuta min shika uku, idan kuwa kin ki, in kun ki ji ba kwa ki gani ba.
Don wallahi sai na saka masa filo a hanci na karasa shi, ko in saka masa shinkafar bera a abinci ya ci ya karasa, kuma dole a bani tumunin takaba
.
Amani bata iya ta karasa jin maganganun Hajiya Rabi masu neman fasa mata kwanya ba, ta wuce falon Alhaji da sauri.
Ta fado dakin cikin gigita tamkar an jefo ta.
Zata yi magana ta ga Alhaji Sadi a zaune, ai kuwa fushin ta ya kara ninkuwa, ta juya za ta koma.
Alhaji ya ce
Tafisu bakon ka Annabin ka
Ba don jikin ta yayi sanyi ba ta dawo ta zauna, sai don bata son kunyata Baban ta a idon Sadi Talle.
Ta daga ido tace
me kake so a wajena Malam?
Alhaji ya soma gurgura kujerar sa mai tayoyi ya koma cikin dakin barcin sa ya bar su a falon.
Babu kunya babu tsoron Allah fuskar sa kamar gonar auduga ya ce
me kuwa na ke so ban da soyayyar ki Amani?
Wadda nake fatan ta kai mu ga aure nan ba da jimawa ba?
Amani ta yi kuta, ta ce
ina maka kallon Babana ba don haka ba da na ce an yi furfurar banza, ka so hada ni rigima da Babana Allah ya fi ka, yana zaman zaman sa ka sa shi a damuwar data kai shi ga faduwa, wani ya baka aure na ka bashi takara shin Katsinar taka ce?
Halan bai gaya maka cewa ta lafiyar sa yake ba yanzu ba ta sayar da
yar sa ba?
Aikin banza aikin wofi to bana son naka, ko a kafa aka daura min kai zan kunce in zura da gudu
Alhaji Sadi ya ce
ke mara kunya!
Ya ishe ki haka, kada kimin gorin halitta don duk muni na ban kai na uban ki ba. gara ni ina iya auren shi kuwa me yake kullawa matar sa sai dai ta je waje.
Don haka kada ki sake ki zage ni yanzu in tattaka ki a wurin nan
Sai gani suka yi an daga labulen dakin an shigo da sallama.
Mukhtar ya bayyana a falon cikin bakaken shirt da wando na
NEIMAN MARCUS
, sumar nan nannadaddiya ta sha gyara da Argan Oil tayi lub a kan sa har ta sauka kadan a kan wuyan sa.
Amani na ganin shigowar sa, bata san me yasa ba, sai taji duk wani rauni na duniya ya rufto mata, ga bakin cikin aj Haj.
Rabi da tsoron kalaman ta, ga na wannan mutumin, ji tayi tamkar wani savior ya zo gabanta don ya kawo mata dauki, kawai sai ta mike ta nufi Mukhtar da azama ta rungume shi ta fashe da kuka mai karfi.
Mukhtar ya kusa suma a tsayen da yake, sai kawai ya tsaya kamar an kafe shi a bakin kofar ya rike Amani dake kara neman mafaka a kirjin sa, yana kokarin zamewa tana kara rike shi, sai ya ga abin kamar a cikin mafarki amma duk da haka ya iya saita kan sa.
Tsawa ya daka mata ya ce
sakar ni nace, bana son sakarci
Cikin jin kunya ta cika shi tana kuka tana nuna Alhaji Talle.
Ka roki Alhaji ya yi min iyaka da su, shi da Haj.
Rabi, ka roki Alhaji kada ya kara bawa mutumin nan damar gani na, tunda ya zage shi ya ci mutuncin sa
.
Alhaji Sadi ya yi tsaki ya tashi ya fice daga gidan.
A ran sa yana cewa ba don albarkar abota ba sai yayi wa yarinyar nan asiri ta rasa mijin aure.
Mukhtar ya zuba hannayen sa duka biyun a Aljihu, ya zuba ma Amani ido tana ta kuka, ta cigaba da cewa
ka fada ma Alhaji na bashi wuka da nama ya aura min duk wanda ya ga dama amma ban da wannan mutumin kuma na yi masa lamuni ya saki Haj.
Rabi.
Ka rokar min shi ya gaya min inda uwata take, na yi alkawarin maido masa ita gidannan ko tana so ko bata so.
Amma ban yarda ya kara auren kowa ba in dai don siyasa ne ya hakura tunda bashi da lafiya
Tausayin ta ya tsirgawa Mukhtar har cikin ran sa, amma Mukhy da taurin rai irin nasa juyawa ya yi zai bar dakin ba tare da ya ce mata komai ba.
Amani ta tsanan ta kukan ta tana cewa
ka taimake ni!
Mukhtar saida ya dafa kofar ficewa ya juyo ya dube ta, da idanun sa da suka kada suka yi jazir, ba abinda yake gani sai Amani zaune da Alhaji Sadi suna zance, in the first instance ta san bata son shi me ye na saukowa kasa har ta kebe da shi?
Sai don ya zage ta zata zo masa da wasu zantuka da basu shafe shi ba?
A fusace ya ce
me yasa sai ni?
Me yasa sai ni zaki aika na gaya wa Alhaji sakon ki?
Baki da baki?
Baki fi ni kusa da shi ba?
Ko ko ni dan aiken ki ne?
Mtsw!
Yasa kai ya fice daga falon, zuciyar sa da gangar jikin sa da Amani ta makalkale suna vibrating.
Kai tsaye mota ya dauka ya bar gidan zuwa nasa gidan da Alhaji ya bashi wanda babu nisa zuwa na Alhajin.
Mukhtar yayi rigingine bisa makeken gadon dakin barcin sa ya na tuhumar kan sa akan me ke faruwa da shi haka?
Me ke addabar zuciyar sa?
Me ke saka zuciyar shi cikin jin zafin Amani, don kawai ya gan ta kebe da Alhaji Sadi?
Shin abinda yayi mata anya ya kyauta tunda yau ta zubar da makaman yakin ta ta nuna masa da gaske taimakon sa take bukata???
Why is he so harsh on her???
Duka baya da amsar ko daya, don haka ya ci gaba da tuhumar kan sa yana nemo hujjar kare kan sa daga tuhumar da ya samu zuciyar sa na yi wa kana sa da kan sa a kan Amani.
**** ***** **** ****
Amani da zazzabi mai zafi ta kwana, don bata iya ganin Daddyn ta ba sai a washegari.
Shi da Mukhtar suna balcony Mukhtar na bisa fararen kujerun roba da aka zuba a wurin suna Magana, Alhaji na zaune cikin Wheelchair din sa.
Da alama sensitive magana suke yi domin Alhaji har share hawaye yake yi da hannun sa mai lafiya.
Abubuwan da yake gaya wa Mukhtar yau ko Amani bai taba gaya wa ba.