← Book details Amani Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 25

Sashe 1

Amani Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
Normal
Heading 1
Heading 2
Heading 3
Heading 4
Heading 5
Heading 6
Heading 7
Default Paragraph Font
Table Normal
No List
Header Char
Header
Footer Char
Footer
No Spacing
Title Char
Title
Heading 1 Char
Heading 2 Char
Heading 3 Char
Heading 4 Char
Heading 5 Char
Heading 6 Char
Heading 7 Char
Hyperlink
List Paragraph
Footnote Text
Footnote Text Char
Comment Text
Comment Text Char
Body Text
Body Text Char
Body Text Indent
Body Text Indent Char
Subtitle
Subtitle Char
Body Text First Indent
Body Text First Indent Char
Body Text First Indent 2
Body Text First Indent 2 Char
Comment Subject
Comment Subject Char
Balloon Text
Balloon Text Char
AMANI
Littafin
SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)
[email protected]


AMANI
TARE DA NI, SUMAYYAH ABDULKADIR
SHIMFIDA
Safiyar yau wadda ta kasance Lahadi, an wayi gari da lullumin hadari mai hade da sassanyar iska mai dadi a gidan su Amani, wanda ke cikin rukunin gidajen GRA a birnin Katsinan Dikko.

Kasancewar lokacin ya kasance lokaci ne na tsakiyar damuna, kada ka so ka ga yadda shuke-shuken dake harabar gidan suka bude ganyayyakin su suka yi korra sharr, suna bada kamshin furanni da bishiyu kala-kala, musaman da bada jimawa ana iskar sai yayyafi ya soma sauka, don haka iska ce mai dadi kawai take kadawa a gidan mai sanyawa al
ummar gidan nishadi, ciki harda Amani dake can upstairs, ta bude tagogin dakin ta iskar na tadda har cikin toilet din da takw wanka.

Dai dai lokacin da aka tsuge da ruwan saman kamar da bakin kwarya.

Amani ta fito wanka, daure da towel a jikin ta, ta karasa ta rufe tagogin ta don dakin ya soma jikewa, ta zauna gaban mudubin kwalliyar ta dan kasar Mexico mahadin furnitures na gogaggen katakon kasar waje dake dakin kamar dakin matar aure.

Kamar yadda yake a al
adar ta kullum, daga fitowa wanka sai ta bata lokaci tana kwalliya a zaune a kan stool, kamar mai shirin tafiya
beauty contest
in ka ga yadda take bata lokaci wajen tsantsara kwalliya kullum.

To yau ma hakan ce ta kasance, Amani ta kwashe kusan mintuna talatin tana gyara fuskar ta da serene make-up, bakin nan ya dauki maikon wet lips na
Elizabeth Arden
sai sheki yake kamar ka sace bakinka gudu irin wanda ake kira
kissable lips
, ta shirya cikin wani dan shafal din
swiss lace
ruwan gwaiduwar kwai da feshin
golden
a jikin sa, duka wannan adon na karshen mako ne bana zuwa wani waje ba, koda-yake dama tun fil
azal ita ma
abociyar ado ce da son kyale-kyalen mata irin wanda ya wuce kima, musamman a renaku irin wadannan na karshen mako da take wuni a gida, don ita bata yawace-yawacen gidan kawaye ko bukukuwa don basu ishe ta kallo ba.

An yi mata wani kyakkyawan dinki na zamani na doguwar riga wadda ta kama ta daga sama ta bude daga kasa sosai kamar (A shape).

Kai da ganin dinkin nata kasan na
yan gata ne kuma ya ja kudi a jikin sa.

Amani tana sakkowa daga matattakalar bene inda dakin ta yake a cikin gidan su, wata irin tafiya take yi kamar hawainiya, kamar bata son taka kasa, kuma kamar tsinin takalmin ta bai dame ta ba.

Sakkowa take daga benen cikin takun ta na kasaita da rangaji irin na
yan matan da ke cikin lokacin su, suka kuma yi katarin samun rayuwa ta gata da wadata, dai-dai da yadda suke buri ko suke son samun ta a duniya.

Daga nesa sai tayi maka kama da matashiyar macen Dawisu saboda iya ado da iya baza tafiyar kasaita, koko zangarniyar dabinon da iskar hunturu ke kadawa sabida yadda ilahirin kyakkyawan jikin ta ke rangaji tana zuba kamshi.

Kai Amani karshe ce a
class
da
gayu
karshen duk inda zaka iya kwatanta ta.

A haka ta isa babban falon gidan su, inda ta tadda mahaifin ta yana aiki cikin wasu muhimman takardu da na
ura mai kwakwalwar bisa cinya (laptop) a gaban sa.

Tun kafin ta gama sakkowa daga benen hankalin mahaifin ta Hon.

Usman ya kai gare ta sabida karar takalmin ta mai tsinin dunduniya.

Ya daga ido ya dube ta, sai ya sunkuyar, yana cigaba da danna na
urar gaban sa cikin kwarewa, ita ta san baban ta Guru ne a computer da lissafi bay a taba yarda kwandalar sa ta bata cikin lissafin sa, in ma ka sace ta don kana ma
aikacin sa zai gane, kuma sai ka yi aman ta.

Cikin sigar kirari kamar ba mahaifin ta da ya haife ta ba, sai ka yi tsammanin wani sa
an ta ne koko abokin wasan ta, Alhaji shiga fadin
TA-FISU
YAR GIDAN BABAN TA!

Ya saki dariyar farin cikin ganin ta ba tare da ya dago ba, hankalin sa na bisa lissafin sa don kada ya bata kwandala, ya ce
Ta-fi-sun Daddy an fito?

In ji Alhajin cikin kulawa, sai yanzu da ya kammala kirgen sa kaf!

Sannan ya dago ya dube ta, ya kuma bata hankalin sa, bayan ya kashe na
urar gabadaya, cikin murmushin kauna da kulawa cikin
yan kananun firi-firin idanun sa masu kama dana
yan China.

TA-FISU-KIN FI SAURAN MATA!

Ya kara fadi cikin kambama
yar tasa, wadda a kullum ya dube ta surar mahaifiyar ta
ke masa gizo, har kullum yana godewa Allah da wannan kyakkyawar halitta da ya bashi a matsayin diyar sa, yana godewa Allah da ta debo komai na
bata ko dauko farcen sa ba, ji yake kamar ya lika ta a goshi don So da alfahari, banda Allah sarkin hikima da tsara halitta yadda yake so, wa zai iya hakan?

Mai sanya mummunan mutum bakikkirin kamar sa ya haifi irin wannan kyakkyawar halitta?

Ai sai Allah
Al Khaliqu
Sarkin kaga halitta a yadda ya ga dama, Ubangijin sammai da kassai.

Mai sanya mummuna ya haifi kyakkyawa.

Shi da kan sa Uban yau da ya dube ta sai da ya ce
tsarki ya tabbata ga sarki Allah!

Domin gani yayi gabadaya ta rikide masa ta koma mahaifiyar ta Jal
an, sau tari har gizo take masa da Uwar ta, shi yasa har kullum yake kara kaunar ta, duk soyayyar da yake wa uwar ta kan ta ya koma.

Har gobe bai auri macen da yake so yake darajjawa irin Jal
an ba.

A yau ganin ta yayi replica din Maman ta, wato kamar Jal
an ce gaban sa shekaru ashirin a baya.

Amma Amani har ta fi ta sheki da daukar ido, don nata kyan ya hadu da gyara da kyale-kyalen zamani mai tsada.

Alhaji Usman Faskari, baki ne wuluk, tittirna, gajere, kuma mai dagaggen hanci da kananun idanu mitsi-mitsi kamar na
yan birnin Sin.

Kai babu wata suffa a jikin Alhajin da za
a kira kyakkyawa, a cewar sa shi yasa Jal
an ta ki zama da shi duk arzikin sa.

Jal
an mai kama da matan Hurul-eeni don kyau.

Ta sha ce masa firgita ta yake cikin dare, ya daina shigo mata daki in dare ya yi, ya dinga bari sai gari ya waye.

Ta fannin halayyar Alhajin ma sai mu ce sai a hankali, domin dai a zahiri shi mutum ne mai mammako (marowaci) kuma mai son kan sa da
yar sa kadai.

Ya mallaki mahaukaciyar dukiya da shi kan sa bai san adadin ta ba, wadda ya mallaka ta hanyoyin duka yaki halaal, da ya ki haraam, tunda kuwa gogaggen dan siyasa ne na jiya ba na yau ba, wadanda suka dade suna ci da tada kai hadi da birgima cikin dukiyar al
umma da sunan siyasa da cigaban al
umma.

A halin yanzu yana rike da shugabancin jam
iyya mafi karfi, mafi shahara da farin jini a wurin al
ummar kasar Najeriya.

Wato jam
iyyar AC da aka fi sani da (Action Congress) ta kasa bakidaya.

Ya iso ga matsayin shugaban jam
iyya ne bayan ya rike manyan mukaman Siyasa da baza su lissafu ba, tun daga karamar hukumar sa ta Faskari, har zuwa matakin jiha, wato jihar sa ta Katsina, har zuwa halin da ake ciki yanzu da ake damawa dashi a Gwamnatin Tarayya.

Cikin manyan mukamai na karshe-karshe da Hon.

Usman Faskari ya rike har da Sanatan Katsina ta kudu sau biyu.

Idan ka cire harkar siyasa da yafi bada karfi da yin kaurin suna a kai, don da ita aka san shi, da ita yayi ficce, har ila yau, shi din kuma babban dan kasuwar ketare ne (International Business Man) wanda koda siyasa ko babu ya riga ya haye tudun mun tsira.

A can baya tun kafin ya haifi Amani har kasuwancin fidda
Iron ore
da
aluminium ore
yayi, wato exporting natural resources da ake hakowa a kasashen Afrika daban-daban irin Saliyo da Madagascar, yana da shahararrren kamfanin sa na kan sa a Katsina mai reshe a birnin tarayya, Abuja wato
FASKARI INVESTMENT
amma rayuwar sa tafi yawa a garin Katsina.

Daga baya bayan Amani ta tasa ya mayar wa da kamfanin suna
Amani Faskari Investment
, kamfani ne na komai da ruwan ka a harkar shigo da kayan ginin gidaje dana sakawa a gidaje, ba irin kayayyakin da basa shigowa da su da suka shafi wannan bangaren daga kasashen ketare musamman kasar Faransa da kasar Mexico inda ya zuba mafi rinjayen hannayen jarin sa, har ta kai ta kawo rabin rayuwar Usman Faskari ya zama na yawo tsakanin Najeriya da Faransa da Mexico, komai na kamfanin sa kowa ya san daga kasashen nan France ko Mexico yake kawo su, wato daga makerar su sai kamfanin sa kadai, shi yasa ba
a fiya samun irin kayan sa a Najeriya sosai ba, abin nufi, kayan ginin kamfanin
AMANI FASKARI INVESTMENT LTD
sun fita daban.

Kama daga kofofi, tagogi, tiles, marbles, da duk abubuwan ceramic da ake amfani dasu wajen ginin gidaje.

Masu ginne-ginen estates da gidaje a Katsina da Abuja yawanci duk a kamfanin sa suke order.

A halin yanzu, Alhaji Usman Faskari, wanda al
umma ke kira Hon.
Chapter 1 · 0% Book details