Sashe 9
Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tsafta a gidan ba kamar yadda take hasashe ba. Nenne kuma ta fahimci cewa Siddiqah a ‘yar kankanuwar rayuwarta mara exposure wadda iyakacinta kauyen Billiri da zagayen Kumo da Gombe, bata taba jin wani abu positive (mai kyau) akan Yarbawa ba, ko me take ji akan su is ridiculous (na habaici da ba’a) ne tun tana yarinya, shiyasa ta girma tana ma bayeraben mutum wani kallo na dabam da bahaushe ko bafillace. Aisha-Siddiqah bata san cewa su din, kabilar yarbawa wata babbar kabilar Najeriya bace mai martaba da daraja da kima da rikon addini (ga musulman cikinsu) kamar koma fiyeda kabilun hausa-fulani, sai da ta fara zama da ahalin Nenne Sappa ne ta soma gane hakan, ta fahimci ashe bayarabun ma suna suka tara. Dabi’un Nenne da ‘ya’yanta (Fatima da Firdausi) dana sauran jama’ar gidan, har ma da hadiman gidan su (Chief Cook Femi) da masu share-share da goge-goge kai har da masu kula da shukoki wadanda duk sun kasance kabilar Yarbawa ne, wasu ‘yan Lagos dinne wasu daga Ilorin aaka debo su, bakidaya suka taru suna narkar da wannan negative perception din na Aisha-Siddiqah wanda ta girma dashi a ranta akan kabilar Yoruba. Domin zuwa yanzu data saki ranta kadan a cikinsu, sai ta soma ganin abubuwa sabani ga tunaninta. Ta ga cewa Princess Firdausi da Princes Fatima ‘yan gayun ‘yammata ne na karshe masu ajin daya take nata, a bana suka kammala karatun jami’a, a irin tsarin kwalliyarsu ma kadai da tsaftarsu wadda ta take tata, Siddiqah ta gane ashe Bayeraben ma suna ya tara. Bayan an sallamosu sun dawo gida saboda ganin yadda yunwa ta kusan lahantata dole ta yarda take cin abinci, shima Nenne ta bata damar ta dinga fadin abinda take son ci, har tace ita da kanta zata dinga shiga kitchen ta girka mata, ba masu aikinta zata sa ba. Sanda Nenne ta fadi haka sai da Siddiqah taji kunya sosai, tayi duba ga girman shekarun Nenne da matsayinta da mukaminta a cikin gidanta, hadimai sai sun fadi kasa sunyi gaisuwa in zasu fadiwa Nenne sako. Dade da kansa yana girmama Nenne. Amma tace zata shiga kitchen saboda ita, alhalin mijinta kadai take yiwa girki da kanta, ta rasa wace irin kauna wannan baiwar Allah ke yi mata. A rashin saninta damshin son danta Prince ne ya nasheta. Siddiqah don kunya da nadamar abinda take yi sai ta sunkuyar da kai tace “Nenne ki bar ni in dinga yi da kaina, ko a gida nina ke yiwa Ummata girki”. “Lallai zaku shiryawa keda tawa Nanin (Nani Oummana) tana son mace mai yin girkin gidanta da kanta”. Ta shiga bata labarin Nani Oummana dake Gombe. Da yawan shekarunta amma bata fasa shiga kitchen ta yiwa iyalita girki ba musamman idan Prince Kehinde ya je wurinta. To kuwa har ya tafi Oummana da kanta take bashi abinci mai kyau na alfarma. Siddiqah tace “sunan mutum ne KEHINDE?” murmushi Nenne tayitana duban kyakkyawar fuskar Siddiqah with affection na Kehinde din akan fuskarta. Tace “shine Hammansu Firdausi. Amma shekaru masu yawa ya basu. Kehinde ba sunan yanka bane sunansu ne na yaren Yoruba me nufin Hassan da Hussaini ko Hassana da Hussaini. Sunansa na yanka Prince Abdulrasheed”. Da murmushi Siddiqah tace “Nenne shima ‘yan biyu ne kenan?” Nenne ta gyada mata kai “yes-yes. Shi da ‘yar uwarsa Taiwo”. Sai Siddiqah ta hau dariya tana cewa “Nenne uwar biyu sau biyu”. Suka fara hira tiryan-tiryan gwanin ban sha’awa. Ita kanta Siddiqah daga ranar ne ta fara sakewa da Nenne ta kuma fara jinta a ranta a kamar Ummanta. Nenne ta baiwa Femi Agbode Chief cook tagidan umarnin ta bar Siddiqah ta dinga girki da kanta, ta kuma dinga taimaka mata da duk abinda take bukata. Siddiqah aka shiga kitchen din Nenne aka sanya apron kamar gaske tafi awanni biyu tana aiki kuma ta sallami Femi. Kai saika rantse wani special abu take dafawa yadda ta tara hankalinta da nutsuwarta akan girkin. Can a jima sai ga kamshin suyar manja ya karade madafin Nenne. Daidai lokacin Nenne ta taso daga barcin rana tana mai jin yunwa sosai, ta zauna a karamin falonta kafarta daya kan daya ta kwalawa Femi kira. “Femi me kuke dashi mai sauki zan iya ci?” Femi ta amsa da yarbanci cikin damuwa cewa bata dora komi ba, bakuwar nan Aisha tana kitchen tun dazu ta hanata nata aikin komai, tace sai ta gama nata “Hausa food”. Dariya Nenne tayi tace “shine nake ta jiyo kaurin manja kuma maimakon kamshin girki? Siddiqah manya rigimammiya’yar Ummanta”. Ta dau waya ta kira Haj. Zainab suna gaisawa tana bata labarin cigaban da aka samu yau na cewa Siddiqah ta saki ranta har ta shiga kitchen tana girki da kanta kuma tana shan magungunanta. Suna cikin hirar nan Umma na cewa “ai na gaya miki zata ware, don bata saba zuwa ko’ina ta kwana bane bayan makaranta. Tace kuma dai dama Petel uwar makon gida ce ina tausayin ta ranar auren ta. in aka koma hutu koyaushe da kuka take komawa makarantar sai daga baya ne take warewa ta shiga sabgoginta”. Sun jima suna hirar Petel din kafin suyi sallama. Femi na tsaye Nenne na ce da ita tayi hakuri da Siddiqah. Amma ta sani ba bakuwa bace daga yau ba kuma ta zo ne don ta tafi ba a’ah ta zo kenan, ki kirata daya daga cikin yaran gidannan ki girmama sha’aninta kamar Firdausi da Fatima”. Sai ga Siddiqah an fito daga kitchen, da katoton tray a hannunta ta isa ga tebirin cin abinci ta dora. Da murmushi tace “Nene barka da tashi barci” Nenne tace “ba jiya naji na gyara miki ba? Nenne ne ba Nene ba?” Siddiqah tayi murmushi ta ja kujerar dining daya ta zauna a rashin saninta kujerar Prince Abdulrasheed ce har sai da Nenne taji gabanta ya fadi. Siddiqah tace “afuwan Nene, ni nafi so ince Nene” sai Nenne tayi dariya tace “Petel din Nene me aka dafa mana haka ya sha manja da yaji?” Femi ta leka tana son gane ko menene wannan abun da Siddiqah ta dafo amma ta kasa gane ko meye. Tana dariya don a zatonta Nenne bazata iya ko tabawa ba balle ta kai ga ci, tace da Nenne cikin yamutsa fuska “you are having delicious meal Ma”. Nenne ta kai idonta ga farantin Siddiqah taga ta shaqoshi ne da “danmalele” wanda akasari abincin ‘yammatan hausawa ne da yaji manja da uban yaji (borkono) tace “shagali wan dinner, to bari in zauna mu kwashi wannan garar tare”. Siddiqah na dariya daga tsaye ta dauka Nenne wasa take yi, bazata iya cin Danmalele ba, sai ga Nenne ta saka cokali tana kai loma cikin sukuni, ta zauna a kusa da ita suna ci tare suna hirar duniya abinda ya baiwa Femi mamaki. Ire-iren hakan da Nenne ke yi mata kullum, na janta a jiki da nuna mata cewa itama uwarta ce kuma kawarta ce kamar Haj. Zainab ya koya ma Siddiqah sakin jiki da ita, ya taimaka wajen da cire mata kabilancin dake damunta, yasa damuwar data ke ji a baya akan zaman gidan da kewar su Ummanta yanzu ya ragu hamsin cikin dari. Nenne da Siddiqah sun zama kamar uwa da autarta, kai sai ka dauka Gambon su Fatima ce. Tunda Dade ya tafi Ilorin kullum suna tare itada Aisha. Musamman da ya kasance Firdausi da Fatima basu cika zaman falon gidansu ba, ita Fatima bama ta dawowa gidan da wuri yanzu sabida haushin Siddiqah. Don haka Nenne da Siddiqa kadai take harkarta cikin gidan. Princesses koyaushe zaka samesu a daki suna waya da mazan da aka yi musu baiko wadanda duk family friends suke da zuri’ar Akanni, kuma ’ya’yan manyan sarakuna ne a yammacin kasar Najeriya, mijin Fatima Abdussalam Kayode dan Ohinoyi of Ebiraland ne, mijin Princess Firdausi kuma Prince Adesina, Da yake ga Oba of Ibadan. Ranar yau Firdausi ta dawo kasuwa ta tadda Aisha da Nenne a dakin Nennen, Aishah na kitse kan Nenne suna hirar kawayenta na makaranta wato ‘yan gang dinta su Amintako, Firdausi ta sha mamaki sabida a sanin ta Nenne ta yarda Nenne da bata son kitso, kai bata yarda ma kowa ya taba mata kai ita da kanta take gyara gashin kanta ta kitse ko ta fake shi, amma tun da ta fahimci Siddiqah ta iya kalba mai kyau don taga tana yiwa kanta yau tace ta yi mata. Princess Firdausi tace cikin tsokanar Aisha “Nenne I am jealous, kin yi auta kin ture ni gefe, yau tun safe baki neme ni ba sai Siddiqah” Saddiqah ta sunkuyar da kai tana murmushin jin nauyi. Nenne tace ma Firdausi “ai tuni na yaye ki kam!”. Aunty Taiwo ma tayi korafin Nenne bata kiranta a waya a dan tsakanin nan ko lafiya? Don in ta kira itama ba koyaushe take samun ta ba. Hankalin Nenne yanzu yana kan koyawa Siddiqah girkin data san shi Prince Abdulrasheed yake son ci, kullum suna kitchen tare. Ga Toufeeq yana gari ba damar ta zo Lagos har sai ya koma UK. Fatima sarkin korafi ta shiga tunawa Taiwo “Aunty Murja kin manta da zancen da nayi maki kwanaki na wata yarinya da Nenne tazo da ita wai Siddiqah?” Nan ta shiga labartawa Aunty Taiwo cikakken bayani cewa wata ‘yar farar yarinya da Nenne ta dauko daga Gombe a wannan zuwan data yi gida, tana nan mai ruwan fulanin kauye da rashin koshin lafiya kamar ba nutrition a jikinta, sai iyayi da kidifiri”, ta kara da cewa “amma kuma yarinyar mai kyauce fa, ko ni da bata yimin ba saboda abinda na gaya miki naji tana fadiwa Nenne kwanaki akan yorubas, na sallama kyawunta, daga haduwa da Mamanta a Saudi ta shige sukuf jikin Nenne. Nenne yanzu bata da lokacin kowa a gidannan sai nata, tunda Dade yayi tafiya”. Aunty Taiwo bata yi mamaki ba don tasan halin uwarsu da son kyautatawa mutanen dake kasa da ita, wadanda wata alaqa mai kyau ko yaya ta hadasu, amma bata daukosu ta ajiye a gidanta, don haka Siddiqah ma bazasu barta tare da uwarsu ba in taimako take son yi mata tayi mata daga nesa, amma ba’a cikin gidansu a dakin Kiki ba, duk wani taimako da Hajiya Nenne Sappa zata yi maka tana yi ne daga inda kake zaune, to