← Book details Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 27

Sashe 19

Aisha Siddiqa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

THE PRINCE Bayan ya koma Qatar baifi da sati biyu ba aka turashi consultation na aiki a Abu-Dhabi Kamfaninsu ‘Qatar Refinery’ ne ya tura Engnr. Abdulrasheed consulting wani aiki na sati biyu a (Abu-Dhabee National Oil Company) don haka yau da safe ya kira Nenne a waya, don ya sanar da ita, yaso kwarai a satin da za’a shiga suzo masa hutu Qatar yadda ya riga ya tsara tunda farko, lokacin da Abdulrasheed ya kirata ko fitowa Nenne bata kai ga yi daga dakin barcinta ba don safiya ce sosai a wurinsu Dade kuma ya jima da fita jogging. Bayan sun gaisa yadda suka saba shi da mahaifiyarsa, kasancewar baya yiwa Nenne kowanne yare sai fulatanci, don yasan shi tafi so su dinga yi mata musamman in shi da ita ne, yarbanci wannan saisu Fatima, sam basu cika yin fulatanci ba sai harshensu na gado. Aunty Taiwo kuwa dama maganarta duka rabi turanci ne ita saboda mijinta Toufeeq da yaranta su Kiki shi suka fi yi a junansu. Yace da Nenne cikin fulatanci “Nenne inata dokin son ku zo wannan watan gabadayanku keda twins, har Hakeem, muyi hutun Easter dinnan tare duk da babu Kiki. Itama naso ince ta samemu anan don ta kusa Hutu. Amma tafiyar aiki ta sameni unexpextedly zuwa Abu-Dhabee sai suka rushe min plan, sai idan na dawo in sha Allah sai kuzo”. Nenne tace “to sarkin kanne Uban Hakeem da Kiki. Sune kawai ababen kulawarka iyali ko oho. ‘Allah hokku sa’a ko ayahi dabbutugo Albarka Annabijo" wato (Allah ya bada sa’ar abinda aka je nema albarkar Annabi), Ya kuma dafa muku”, sannan ta nisa tace. “Hammansu bazamu zo ba wannan Easter Holiday din, saidai kai kazo. Am not feeling fine da zan iya hawa jirgi nan kusa”. Amma Prince ya riga ya sakawa ransa nan kusa shikam nan kusa bai zuwa Lagos ko Ilorin, ba don komai ba sai don gujewa fushin Baffanninsa. Yayiwa Nenne alkawarin zai zo amma sai bayan wani lokaci. Yayi mamaki da bata yi masa korafin Baffanninsa sun bude mata wuta akan rashin zuwansa ba yadda ta saba. Sunyi waya da Aunty Murja ma duka a ranar, wadda ke can cikin bacin ran Nenne ta hanata sanar dashi maganar aurensa har yanzu, balle ta san yadda ya karbi al’amarin ta bangarensa. Da yake bakinta nata kaikayi saida tace masa “Kehinde!” Yace “Na’am” ta sake cewa “Prince! Sau nawa na kiraka?” Yana dariya yace “Taiwo! Kin kirani sau biyu, wani abu?”. “Ka daure kaje gida immediately daka gama aikin da zaka je dinnan”. Ya nemi karin bayani dalilin kalmar immediately din, don yaji seriousness sosai a kan muryarta, sai kawai ta kashe wayarta ba tare data bashi amsa ba. To haka su Fatima ma baki nata kaikayi, kamar sun ci bawon Doya, musamman Princess Fatima uwar tsegumin gidan bakidaya, komai a bakinta Taiwo ke ji. Har hotunan Siddiqah ta tura mata. Amma wane mutum a gidannan Nenne tayi umarni yayi fatali dashi? Ko tasa kara mutum ya tsallaka? Ko basa so zasu bi. Don kowa na gudun bacin ran Nenne Sappa. Da wuya tayi bacin rai a cikin iyalinta amma in tayi shi basa ji da dadi, don bata sauka ta sauki sai kowa yaji a jikinsa. Yau da ba don Nenne uwarsu bace kuma itace da kanta ta hada auren nan na Prince da Aisha, da Murjanatu tace an kwari Kehinde dinta, an zubar masa da class a inda bazai kwasu ba, da aka aura masa Aisha. Ta fadi hakan ne lokacin data ga hoton Aisha Siddiqa a wayarta. Ba wai Siddiqah din ba kyakkyawa bace, a'ah don kyau Masha Allah ko makiyinta ya san ta kere sa'o'inta a kyawun sura. Amma a ganin Aunty Murja kyawun ba shi Prince yake bukata a halin yanzu ba da shekarun girma suka riskeshi. A yadda Prince ya kwashe shekarun kuruciyarsa babu aure a ganin ta cikakkiyar mace kuma kilalliya wayayya preferably ‘yar kabilar Yoruba ce ta dace dashi in har ba Haseenah ba, mace 'yar shekaru akalla Talatin wadda zata kula da komai nasa, ta tarairayeshi ba hijabin kunya, sannan ta jiyar dashi dadin aure da ya jima bai sani ba, amma ba dai shi Prince a halin yanzu yayi zaman rainon ‘teen’ ba. A yadda Fatima ke fasalta mata abubuwan da Siddiqa keyi a gidansu na kauyanci da kuma hotonta data gani ba maraba da ‘yan tallan nono a kasuwar Gombe. Don haka zamu iya cewa, from Day 1, Aunty Taiwo bata yi na’am da dacewar Siddiqah da Prince ba a matsayinta na mafi kusanci dashi data fi kowa sanin likes and dislikes dinsa. Ko dalilinta ya isa dalili? Ko kuma na son zuciyarta ne bazan iya cewa ba. Dan adam din kenan, har kullum halinsa sai shi. Marar godiyar Allah marar tuna baya. In banda haka sai muce ko dai Aunty Murjanatu ta mance yawan shekarun dan uwanta Prince Abdulrasheed dinne? Da dadewarshi yana Polo babu aure, kuma har gobe bashi da niyyar yi? Maimakon Taiwo tace dan uwanta ya tsinci dami akala, na samun yarinya danya sharaf (in her teens) wadda bazai sha wahalar tankwarawa zuwa duk yadda yake so ba. A ganina, Aisha-Siddiqah ce za’a ce ta kwaru da auren Prince Kehinde, wanda a haife sai mu ce ya haifeta, ko mu ce ya kusa haifarta da yayi aure a farkon samartakarsa, amma ba Prince za’a ce an kwara ba a logical reasoning. Taiwo-Murjanatu, bata duba duk wannan ba, ji tayi kamar ta fashe don haushi da taji cewa matar da aka aurawa Prince ma wai ko sakandire bata gama ba, sannan ba ‘yar kowa bace a Gombe, kawai haduwar kan titi ne ita da Nenne. Sai taji fit! Matar Prince bata da muhallin kima a gunta. Wani abunda zai baka mamaki a lokacin ma sai Haseenah ta dawo ranta. Wadda a lokacin suna tare a gidanta ta kawo mata ziyara har Lancashire. Wannan ba shine zuwan Haseenah na farko gun Aunty Murja ba. Don haka a wurin Aunty Taiwo ma kamar danginsu na Ilorin, zamu iya cewa Siddiqah bata samu maraba ba, amma ba yadda zasu yi tunda zabin iyayensu ce. Taso kwarai ace da Prince bai auri Haseenah ba, to zama ya auri wadda zata iya kula dashi, wadda ta fi Haseenah komai na kyau, ilmi da wayewa, Uwa Uba babbar nasaba ta sarauta da da zasuyi tinkaho da ita a cikin dangi tunda akan nasaba ne Nenne taki Haseenah, kuma mace mai cikar halitta da Kehinde zai iya jerawa da ita a ko’ina, amma ba wadda ko a shekaru da matakin ilmi bata kai ya jera da ita ba. A cikin watanninta na uku tareda iyalin Abdulrasheed, sai ga Siddiqah ta fara cikowa, jikinta na faman murmurewa a hankali yana glowing, fatar jikinta tayi lukui-lukui, ta zama wata danya (fresh) wanke hanu ka taba sakamakon zaman waje daya, sanyin iya kwandishan da shan fruits (kayan marmari) da ake yi a gidan kala-kala ya fara huda fatar jikin Siddiqah, hatta farcenta na kafa da hannu wani irin jazur ya koma, kumatunta luwai-luwai sumul-sumul dasu fatar bakinta ta koma wani irin soft, pinkish da ita. Kugunta ya shiga wani irin budewa a hankali ta zama kamar kwalbar nan ta coca-cola daga kasa. Siddiqah zuwa yanzu ta zama kamar an barota daga cikin kwai don kyau da kyawun fasali, sulbin jikinta har daukar ido yake. Madallah da kulawar uwar miji irin Nenne Sappa, madallah da kyawun abincin yarbawa mai inganci da gina jiki (freshy Yoruba food), ga kamun gero da cukwi din Nenne, tabbas yana aiki ba kakkautawa a jikin Aisha-Siddiqah. **** **** **** CIKA ALKAWARI Yau dai Nenne ta cika alkawarin data daukarwa mahaifin Siddiqah, domin kuwa ta shigo dakinnta ta sameta ne tana gyaran kumba, sai ta mika mata littafai da uniform harda takalmi da jakar makaranta, ta gaya mata gobe in Allah ya kaimu zata fara zuwa makarantar da Kiki tayi. Har ila yau, ta sanar da Siddiqah cewa ta shirya an daukar mata malama da zata dinga yi mata lesson Asabar da Lahadi akan jarrabawar WAEC din dake gabanta. Hakan yasa Siddiqah ta kwana cikin zullumin wayewar garin, maimakon farin ciki, wanda shi ya kamata ace tayi, don samun damar karasa karatunta data yi cikin sauki kamar yadda Nenne ta dauki alkawari tuntuni ga iyayenta, ba kuma don komai ta shiga zullumin ba sai wani tunani daya tsirga mata babu gaira babu dalili. Wai gata dai yanzu ta tsinci kanta dumu-dumu a garin Yarbawa ta dalilin auren da bata shiryawa ba, duk wannan bai isa ba, yanzu gashi gobe zata fara cudanya da dalibai suma yarbawa, ta tabbata duka daliban makarantar Yarbawa ne tunda su suka fi yawa a garin Lagos, kuma cikinsu za’a kaita tsundum a barota suyi tayi mata yaren da bata son ji dinnan, in a gida ana ragewa sabida ita. Shin ko yaushe hakkin Bisola Akanbi zai barta ta huta? Ta tabbata shiyake ta bibiyarta har yau. Kabilanci yaki sakin ranta ta sarara, kullum tana tunanin ko ta koma Gombe. Gabadaya rayuwarta ta dawo cikin yarbawan data raina matukar rainawa, takewa shagube da mockery yadda ranta yake so, Allah kenan. Yau dai gata tsundum a cikinsu da sunan zama na dindindin har inda bata taba mafarkin shigowa koda ziyara ba (masarautar yarbawa). Babu ko shakka alhakin Bisola ne ya tsundumota cikin kabilar yarbawa, ya hanata samun rayuwar fulani yadda ta yi mafarkin samu, ta kuma yi burin samu tareda wanda takeso, saurayin bafillace dan uwanta, wanda ya san ciwonta da darajarta, suke harshe da yare guda (Ishaq Nafada). Sai Allah ya jefo ta duniyar yarbawa data ke yiwa wani kallo-kallo da shagube. Yanzu idan taje makarantar itama daliban suka yi mata irin abinda take yiwa Bisola fa a matsayinta na bahaushiya ita kadai? Duk sai taji zancen karasa makaranta ya fice mata aka, gara ta cigaba da zamanta a gidan tunda su suna raga mata, Fatima ce kadai bata raga mata in taga ba iyayensu a wuri ma da gayya ma take suburbuda yarbanci, da zata iya da tace da Nenne bata so kawai a kyaleta. Ta hakura da zana WAEC din don dam aba wani jami’a take son zuwa ba. Dan ilmin data samu na karatu da rubutun hausa ya isheta ya wadaceta Allah ya amfana. Don ko turanci ba
Chapter 19 · 0% Book details